
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 9
.....you put down her little horse". The girl's body began to dance, she started swearing that Ruky had harmed her. Her mother also started to feel bad that her daughter will not be harmed. But the principal should let the police take Nimrah away or she will sue the whole school. Ammar said in frustration, "Hajjaju, you are like a stranger, is there anyone here who is afraid to go to the police station? These children have told what happened until they had a fight with your daughter, instead of worrying about what she is doing, you are trying to make people laugh. Well, we can't believe it, it will spoil our children's education, besides the carelessness, children are looking at nothing and empty on the phone, the parents don't know, and who comes to school with a phone? These children don't even have a phone and they never worry even when they reach the age of one, it's better if they are left with it. It's not like that, in such a situation, these things are moving in their hearts, so we can't accept it, our children are disciplined, and they won't be wasted here, and.....
..........“Sir kawai fa dan na taka ita Ruƙayya ɗin ne ban kula ba, kafin na bata haƙuri sai ta hankaɗe ni ta ƙwace wayata ta jefar a ƙasa ta fashe, ni kuma na zuba mata ruwa a jiki ƴan class suka yi dariya. Itafa Nimrah ɗin ma bata ajin ta fita, kawai tana shigowa ba tambayar ba'asi ta hau dukana itama Ruƙayyan na tayata, ni kuma naji wahala na cijesu kawai suka gwara kaina da bango wai aljanunsu ya tashi...” “Da dai kin fito kin faɗi gaskiya yarinya da yafi miki”. Cewar Ruƙayya tana hararta. Uwarta zatai magana principal yay saurin tarar numfashinta. Idanunsa akan su Ruƙayyan ya ce, “Ke haka akai?”. “Sir ta ɓoye asalin zancen”. “To miya faru?”. “Yarinyar nan ƴar iska ce Sir, a bayan desk ɗinmu suke ita da ƴar iskar ƙawarta, kullum sai suna damunmu da kallon Film ɗin iskanci a waya, mun musu magana akan idan suna kallon rashin tarbiyyarsu a waya suna saka Bluetooth amma sun ƙi dainawa. Kawai yau suna kunnawa na juya na ƙwace wayar na fasa banza, shine tazo zata min hauka ni da Ninah muka sauke mata nata ƙaramin hau ɗin”. Rawa jikin yarinyar ya fara, ta fara rantsuwa ita sharri su Ruky sukai mata. Uwarta ma bala'i ta fara wai za'a ma ƴarta sharri bazata yarda ba. Kodai principal ya bari ƴan sanda su tafi dasu Nimrah ɗin ko kuwa tai ƙarar makarantar gaba ɗaya. Cikin takaici Ammar ya ce, “Hajjaju ya kike Abu kamar baƙya ganewa ne, shin anan akwai wai mai tsoron zuwa police station ɗin ne anan akace miki. Yaran nan sun faɗi abinda ya faru har sukai rikici da ƴarki, maimakon ma ki damu da abinda take aikatawa kina neman juye wa mutane shirme. To muma bazamu yarda ba, dan bazata ɓata mana tarbiyyar yara ba, banda ma rashin kula har yara na kallon banza da wofi a waya iyaye basu sani ba, kuma miye na zuwa da waya makaranta? Gasu nan ko waya basu da ita yaran nan kuma basu taɓa damuwa ba duk da sun kai ƴammatan daya dace ace an barsu da ita, idan anyi maganar ku daina bama yara waya ko ku dinga kula dasu idan kun basu musamman masu tashen sabuwar balaga irin su kuga kamar an raina ƙoƙarinku ne. Ba haka bane, a irin wannan gaɓar waɗan nan abubuwa suke kwaɗaituwa a zukatansu, dan haka muma bazamu yarda ba, yaranmu masu tarbiyya ne, bakuma za'a ɓata mana su anan ba, kuma yanda sukai mata sun min dai-dai....” Hayaniya sosai ta kaure a office ɗin tsakanin Hajiya da Ammar, sai da ƙyar aka fitar da Ammar itama Hajiyar principal yace taje zasuyi bincike akai. Dan haka an bama yaran suspension na sati ɗaya su duka ukun har sai an tabbatar da gaskiyar mai laifi. Suko ƴan sandan data kira suka sallamesu. Suma ƴan sandan sanin makarantar ta jiga-jigai ce basu ja da nisa ba suka wuce. Yaya Ma'aruff dake hararar su Nimrah ya ce, “Sai ku wuce muje masu kunnen ƙashi. Hankalinku ya kwanta ai ko. Banda ma fitina ku kuma haifeta da zaku hukuntata? Ba kusan hanyar kai report bane, jibeku da kawuna kamar kullun magani”. Babu wanda a cikinsu bai cika baki da iska ba. A haka suka fito suka shiga mota shima Yaya Ammar na zuba musu tashi hararar.....
★ Koda suka iso gida ko kallon inda suke su Yaya Ma'aruff basuyi ba suka shige ciki abinsu. Kallon juna Nimrah da Ruƙayya sukayi, cikin marairaicewa Ruky ta ce, “Wlhy yau akwai matsala Trouble Queen....” “Babba ma kuwa”. Aka faɗa daga bayansu, a tare duk suka juya, Mu'azz ne daya zama matashin saurayi ɗan shekara goma sha takwas, dan kuwa ya kammala Secondary ɗinsa ma yana shirin shiga jami'a. Yanzu kam Nimrah ce tace, “Ya Mu'azz kaji tsoron ALLAH”. “Oh, to da tsoron ku nake ji. Ba kunce ku baƙwa jin magana ba. To Daddy ma na nan zuwa dan Uncle J ya kirashi shima”. Wani mugun ƙwalalo idanu waje sukayi a tare, shi ko ya kwashe da dariya yana barin wajen. Da sauri sukabi bayansa, amma yaƙi tsayawa har suka shigo falon. Cak kuwa suka tsaya, ganin kowa yana nan har su Aunty Lailah. Yaya Ja'afar ne ya fara zuba musu harara da faɗin, “Sannunku ƴan wrestling ko ƴan boxing ma zance ban sani ba nikam”.
*_💦KIƊA A RUWA...!!💦_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_GENERAL FICTION_*
_Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._