Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 13

Post

Kida a ruwa Book 3 page 13

.....before that, she was about to sit in front of the table, she opened the bowl of food and looked at him, even though he was on the phone with Imran, she heard him mention his name without stopping to say, "Dada, will it be poured for me?". While she was talking in a whisper and pointing at him with her hand, she was staring at him with her big eyes and he was looking at her with his own eyes. She had to look at her again and said, "Dadaaaah". Then he woke up with what he had and pulled back, pointing at her with his hand. She bowed her head and started to pour, but she distracted herself by looking at Nabeeha who was still standing where they confirmed that she choked on what he had given her. In her heart, Nimrah said (I haven't done anything, aunty, husbands) and actually, when she finished pouring the food, she just put the lid of the bowl with the salad on the edge of the table. Even though she tried to put her hand in, it was hard to touch. Zabura was shocked and her hand fell on the professor's collar. Aiko broke the volume of data and put Dada on the phone and turned her head... Itako was already standing up with one leg clasped in her hand and jumping with the other, th

Standalone post1,533 words

13

.........Dada shi kansa jiyay wata kunya mai tsananin ta rufeshi. Haba shi girma abin a riƙe ne ai. Baiyi ma Nabeeha magana ba amma ya zame jikinsa daga nata, yana nufar kan center table ya ajiye tray ɗin abincin. Yazo ya sake raɓasu ya wuce gaban mirror, wayarsa ya ɗauka ya sake gittasu dai again ya koma kan sofa ya zauna. Nimrah dake ƙoƙarin controling ɗin kanta ta kalli ƙafafun Nabeeha dake tsaye itama kamar an dasata, da alama abinda yay ɗin ya ɓata mata rai ne ko wani abu oho mata. Kawai sai taji murmushi na neman kufce mata sakamakon abinda zuciyarta ta ayyana mata akan matar. Amma sai ta danne shi ya tsaya cikin ƙirjinta. Dada dake ƙoƙarin kai waya kunnensa ya ɗago ya kallesu, shi sai ma suka nema sakashi yin dariya. Ya dai gimtse baiyi ba, dan saima ƙara ɗaure fuska da yay cikin bada umarni ya furta, “Kiddo zoki bani abinci”. Duk da wani haushinsa da take ji saboda rungumar da Nabeeha tai masa sai ta jinjina kai tana nufarsa, dan kurama ai tasan gidan mai babbar sanda. A kusa da shi gab takai duƙe gaban table ɗin, ta bubbuɗe kwanikan abincin sannan ta kalleshi, duk da waya yake da Imran dan taji ya ambaci sunansa bata fasa faɗin, “Dada mi za'a zuba?”. Yanda tai maganar cikin raɗa da masa nuni da hannu tana wara masa idanunta manya ya sashi ɗan zuba mata nasa idanun. Sai da ta sake waro natan sosai ta ce, “Dadaaaah”. Sannan ya farga da abinda yake ya janye yana nuna mata da hannu. Ta jinjina kai ta fara zubawa, sai dai ta raba hankalinta a kallon Nabeeha da har yanzu ke tsaye inda suka barta tabbacin ta shaƙa da abinda yay mata. A cikin zuciya Nimrah tace (Tun banyi komai ba aunty masu miji) a zahiri kuwa sai da ta kammala zuba abincin tsaff kawai ta saka murfin kwanon tangaran ɗin da aka zuba salad ciki baki-bakin table ɗin da gangan ta kaɓoshi ya wantsalo ƙasa sai kuwa akan ƙafarta. Duk da dai tayi dabarar saka hannu sai da ya taɓa bisa tsautsayi. Zabura tayi cikin gigita sai kuma hannunta ya tsumbula cikin kular farfesu. Aiko ta fasa ƙarar data saka Dada sakin waya ya juyo kanta... Itako tuni ta miƙe a zabure ƙafar damƙe a hannunta ɗaya tana tsalle da ɗaya, hannun daya shiga miya kuma tana yarfa shi har tana neman faɗawa kan abincin nasa. Ba arziƙi ya tarota gaba ɗaya sai kawai ta faɗa saman cinyarsa. Anan kam harga ALLAH bata san kansa take ba, dan da gaske zafin ya ratsata har cikin kai, gashi bibbiyu hannu da ƙafa, dama ga Nimrah da shegen ragwantaka. Rasa ina Dada zai kama mata yayi, dan ita kanta Nabeeha sai da ta zaburo, sai kuma taja ta tsaya tuna wacece da kuma yanda ya riƙota jikinsa. Tai bala'in waro idanunta waje ganin ya kama hannun Nimrah kawai ya saka yatsun data saka a farfesu cikin bakinsa. Ɗayan hannun kuma ya riƙo ƙafar tata. Itama kanta uwar haɗa wajen tsittt tayi a karo na farko, dan abune da yazo mata a matuƙar bazata, bazatar ma mai gigitar da zuciya. Dan yanzu kam ta fahimci an sauka daga layin abinda tai niyyar aikatawa an tafi wani layin sabo data gagara bama suna ko kalma. Dada da shima sai yanzu ya fahimci halin da suke ciki sai ya runtse idanu, kafin ya buɗesu a hankali kan fuskar Nimrah data zuba masa nata idanun cikin yanayin ruɗani. Sai kawai suka sarƙe cikin juna, kamar kuma waɗan da aka hana motsi kowanne ya kasa janyewa suka shagaltu. Shagala a kallon juna irin yanda basu taɓa yi ba cikin idanu dai kamar haka.....

=============

“Baƙo kuma?”. Hajiya Hasiba ta faɗa da mamaki tana kallon maigadi. Kansa ya jinjina mata. “Eh Hajiya. Kuma kamar ma baɗan ƙas.....” Ya kasa ƙarasawa sakamakon shigowar Adeel falon. Miƙewa Hajiya Hasiba tayi, dan ita kaɗaice a gidan su Amima na gidan Nabeeha. Cikin in-ina maigadi ya ce, “Ya....ya..yauwa Hajiya ai gama shi nan ya shig.....” Hannu ta ɗaga masa. Sai kuma tai masa nunin ya fita. Babu musu ya nufi hanyar ƙofa yana waigen Adeel. A ransa faɗi yake (Yau gani ga Balarabe ikon ALLAH) sai da ya kusa cin tuntuɓe ya dawo hayyacinsa...

Adeel dake kallon Hajiya Hasiba fuska a ɗaure hannayensa duk a cikin aljihun wandonsa ya kai zaune cikin kujera cike da isa da gadara. Sai wani bin falon yake da kallo a yatsine. Duk da kuwa ba laifi falon ya haɗu, kuma a gyare yake tsaff ga ƙamshin air freshener na tashi. Sake maida idanun nashi yay a kanta. Da sauri ta fara gaishe shi murya na rawa. Maimakon amsa mata sai yaja siririn tsaki. Cike da wulaƙanci ya furta, “K! Nine zakima ƙaryar kinyi tafiya?”. “Wlhy ba ƙarya nake maka ba. A cikin satin nan na dawo. Kuma na nemeka amma ban samu ba. Ban san ka dawo ƙasar nan ba shiyyasa nake neman layin Abu-dabi.” “Mtsoww!” ya sake jan tsaki. Sai kuma ya sake watsa mata kallon banza. “Nayi alƙawari dake kin saɓa. Kince mijinta na prison na bincika ance ya fita. Baki zo kin min bayani ba saboda kina ɗaukata wawa....” “Wlhy ba haka bane Sir! Idan baka manta ba nata ƙoƙarin mu haɗu kafin kayi tafiyar farko. Amma hakan bai samu ba. Lokacin daka dawo nan ma naso hakan amma baka ɗaga kirana ba, sai daga baya nake jin ka wuce a wajen First Lady”. “Wannan kuma damuwarki ce. Na baki kwana bakwai ku koma Dubai da ita. Idan ba haka ba zan yi abinda naga dama. Sannan duk abinda na baki komin ƙankantarsa ne babu sai kin cika. One week”. Daga haka ya miƙe abinsa ya nufi ƙofar fita. Cikin rawar jiki Hajiya Hasiba ta yunƙuro zatai masa magana. Hannu ya ɗaga mata tare da watsa mata kallon daya sakata dakatawa da sauri. Sai da ya fice ta bugo musu ƙofar ta zabura gefe.....

(Idan kwaɗayi.....🥱🏃🏼‍♀️)

>>>>>>%<<<<<<

A ɓangaren Daddy Imran da ƙarar Nimrah ta tayarma hankali tun yana kiran hello! Hello! Har ya haƙura ya yanke kiran. Vibration ɗin kiran daya sake yi da yanda Nabeeha da ke jin kanta na juyawa kamar zata sume a wajen ta nufo inda suke a matuƙar fusace jikinta har yana rawa ya dawo da Dada da Nimrah hayyacinsu. Hannu Nabeeha ta kawo a zafafe zata cakumi Nimrah. Amma sai aka riƙe hannun nata caraf a bazata. Ido cikin ido suka kalla juna ita da Dada. Da wani kalar kallon dake tabbatar da gargaɗinsa da barazanar da bata taɓa gani ba ya furta, “Kada ki taɓa koda mafarkin tsallaka wannan layin a karo na biyu. Dan tabbas bazaki ajiye ƙafarki kan ƙasa tana tare da gangar jikinki ba. Ni mai RIKICI ne akan wannan ANANAR. Ba lallai na iya kauda idanun TAƁATA ba koda akan kaina ne.” Sosai zuciyar Nabeeha ke bugawa da sauri-sauri a cikin ƙarjinta. Lips ɗinta na rawa ta buɗe zatai magana..... “Shiiii!!!” ya faɗa cikin ƙatseta yanama bakinsa alamar zipping da nuna mata hanyar ƙofar fita. Nabeeha dai tasan halin kayanta, ta kuma san mi zai iya. Ta kuma san fassarar gargaɗinsa da umarni musamman idan har ya buɗe baki yay magana akan abinda ke ransa. Ita ko tsuntsuwar tasa bama ta fahimci inda kalaman nasa suka dosa ba. Hasalima ba maida murtani ga Nabeeha datai niyya bane a wannan gaɓar damuwarta, kasancewarta akan cinyarsa ne tashin hankalin ta. Gashi ya riƙeta ta yanda ta gagara koda motsi. Sai da Nabeeha ta buga ƙofar da ƙarfi Nimrah ta zabura, tsalle ɗaya tai ta wantsalo ƙasan lallausan carpet ɗin wajen jikinta na tsuma, ga zuciyarta na wani kalar bugawa diff-diff-difff. Dada ma idanu ya runtse da ƙarfi, sai wani motsa yatsunsa yake kamar mai kiɗa akan hannun kujerar. Sai da ya tabbatar ya samu nutsuwar da yake buƙata sannan ya buɗe idanun tare da yin gyaran murya yana sake tsuke fuska tamau. Cikin dakewa a ainahin Dadan sa ya furta, “Naga hannun”. Nimrah dake jin kamar tayita kwarara ihu saboda kunya, har idanunta sunyi jawur ta ɗan kallesa. Sosai taji shakkarsa da kwarjinin sa na sake mamayeta. Dan duk da ba dariya yake mata ko surutu ba ƴar sakewar da yake da ita na sakata jin sauƙi. Amma yanda yay ɗin yanzu ita tasan wargi ma waje yaka samu. Sai da ya ƙarema yatsun kallo, ya kamo ƙafarta itama ya duba, duka farcinan sunyi ja daga na ƙafar harna hannun. Baiyi magana ba ya miƙe zuwa fright ɗin ɗakin, ice ya ciro babba ya dawo inda take ya zauna. Ita dai binsa take da kallon mamaki, handkachiff ɗinsa dake ajiye a saman kujerar ya ɗauka ya saka ƙanƙarar a ciki. Kai tsaye ya kamo hannun nata ya ɗora a wajen data ƙone ɗin duk da baiyi alamar tashi ba. Tako sauke ajiyar zuciya da har sai da ya lumshe idanu ya buɗe. Sai da ya saka mata kusan na minti uku sannan ya miƙa mata alamar ta cigaba da sakawa. Shi kuma ya ɗauki wayarsa. Bata san waya kira ba, kawai jitai cikin umarni ya furta, “Turo min Ruƙayya”. Daga haka ya yanke kiran.........✍️

Hajja Ninah Ai wanda bai ji bari ba yaji hoi🥱🏃🏼‍♀️.