
Post
Kida a ruwa Book 3 page 14
.....he is cutting and they are asking what is going on. What Dadan said he informed them. Biebah caught Ruky in the kitchen with Mu'azz saying they were cooking Nimrah special. The answer is coming out. Dada's message told her, as she didn't know the cake that was being baked, she went to the top in her happiness. She entered the conversation and asked Mike what was wrong with her. Until one Dada was too busy looking at them to correct his voice. Ruqayya looked at him in shock, as if she was going to cry and said, "Is it Aunty Nabeeha who is there?". His eyes widened in surprise. In other words, she and her friend are in the same situation. Heard another bad thing. He had no choice but to shake Rukayyan's head before saying, "You should go to bed". Ruky should have said that, until they went out, he was following them with a look, in his mind he was praising this love for each other. After the love of blood, and the love of spouses, the most important and wonderful love for human beings is the friendship that has no blood relation in it. Indeed, all friends who share true love will enter paradise and be happy with each other. If pretense or greed comes in, they will end up insulti
14
........Anan falo Ammar na ajiye wayar su Aunty Ummi suka shiga masa alamar yaya dai. Dariya yayi, dama kuma ita suke yi tun fitowar Nabeeha da gudu tana kuka da basu san abinda ya korota ba. Tun wucewar Nimrah sama Mammah ta bar falon. Hakan yasa Gwaggo Khadijah da Gwaggo Alawiyya binta, dan sun san dai bai wuce lamarin Nabeeha ne ke damunta ba duk da tana ƙoƙarin ganin ta danne. Amma dai abinda Nabeehan tayi yau rashin kunyar tayi yawa ai. Wucewar iyayen nasu ciki daɗi yay ma su Ja'afar, dan a take suka shiga amaye abinda ke bakinsu game da Nabeehan suma, kowa cin alwashi yake akan koyama Nimrah abubuwan da zata ƙona Nabeeha da ruwan jikinta. Sai kuma gata ta sakko a kiɗime harma tana kuka. Tsabar wulaƙanci sai suka fashe da dariya a tare har wasu na tafawa. Aiko kamar sun izata, sai ta ƙara gudu tana danne bakinta saboda tahowar wani sabon kuka mai ƙarfi. Suna cikin dariyar ne kiran Dada ya shiga wayar Ammar. Da sauri ya ce, “Kuyi shiru Dada ne”. Tsitt sukayi ya gama amsa wayar, shine yana yankewa suke tambayar mike faruwa. Abinda Dadan ya faɗa ya sanar musu. Biebah ta ƙwalama Ruky dake kitchen tare da Mu'azz wai suna ma Nimrah special girki kira. Amsawa tai tana fitowa. Saƙon Dada ta gaya mata, da yake bata san wainar da ake toyawa ba ta nufi saman cikin farin cikinta.. Rikicewa Ruky tai da ganin Nimrah kamar tayi kuka. Ta shiga tattaɓata tana tambayar mike damunta. Har sai da Dada daya shagala a kallon su yay gyaran murya. Cikin shagwaɓa Ruƙayya ta kalleshi, kamar zatai kuka ta ce, “Dada Aunty Nabeeha ce ta dake ta?”. Idanu ya waro waje dan mamaki. Wato dai halin iri ɗaya ne ita da aminiyar tata. Ji wani sharri kuma. Bashi da zaɓin daya wuce girgizama Ruƙayyan kansa, kafin cikin umarni ya ce, “Kamata kuje ta kwanta”. Kamata Ruky tai, har suka fita yana binsu da kallo, a ransa kam yana jinjina wannan ƙaunar juna. Bayan soyayyar jini, da soyayyar ma'aurata soyayya mafi muhimmanci da ban mamaki ga ƴaƴan adamu itace ta abokantaka da babu alaƙar jini a ciki, lallai duk abokan da sukai tarayya akan soyayya ta gaskiya zasu shiga aljanna suna masu farin ciki da juna. Idan riya ko cin dunduniya ta shigo sai su ƙare da zage-zage da aibanta juna a ranar rarrabe ayyuka. (Ya Rabbi kasa mu rayu da masoya na gaskiya, mu kuma kasance a aljanna tare muna masu farin ciki da juna. Duk wanda zai zo garemu da fuska biyu, ya rabbi kasa shartinsa ya zamewa rayuwarsa bargo akan kansa can ya ƙarata shi kaɗai🙏). Cahh iyayen nasu suka yo musu da tambayoyi a falo. Sai da Nimrah ta sanar musu abu ne ya faɗo mata a ƙafa sai kuma ta ƙone sannan suka nutsu. Amma da kowa ya hau da tunanin Nabeeha ce. Har sun fara ɗaukar alwashi a zukata. Dariya ce ta nema suɓuce ma Mammah dake ƙoƙarin fitowa. Ta girgiza kai tana gimtsewa. A ranta kam ta fahimci dole tai wani abu kafin waɗan nan iyayen banzar su ɗora Nimrah kan wani layin daban, a haka ma yaya lafiyar kura tunda itama ba ƙyalen bace ƙyallece ita da aminiyar tata Ruƙayya da basa ɓoyema juna sirri....
^^^^^^^^^^^^^^ A ɓangaren Nabeeha kam yanda ta shigo sashen nata ya saka Amima da Rayhana dake cin abinci kallon juna. Sai kuma suka taɓe baki a tare. Amima ta ce, “Lafiya kuwa?”. “Ƙya tambayeni bayan muna tare”. Cewar Rayhana fuska a yamutse. Amimah ta ce “Hummm maybe korota sukai ko”. “Mtsowww matsalarta ce. Banda zubar da kai ka dawo miji baizo inda kake ba kai ka ɗauki ƙafa ka tafi nemansa. Itafa wannan da cikin aljihun baya aka haifeta muguwar kidahuma za'ayi. Bata gane komai sai son miji.” “Ikon ALLAH to miye dan taso mijinta Rayhana. Wani kike so taso to ne?”. Hararar Amima mai maganar Rayhana tayi, cike da takaici ta ce, “Kema fa wawuya ce wani lokacin. Inba hauka ba son miji ne kawai rayuwar aure?. Mijin ma irin Haysam daya san martabar kansa, wlhy sam bata dace da shi ba.” Galala Amima tai tana kallonta yanzu kam. Sai kuma tace, “Tofa wata sabuwa. Sai yanzu duk kika san wannan? Toke auren kikai da kika san mima mijin ke buƙata? Anya Rayhana babu wani abu a ranki?”. “Ubanki ne a raina. Shegiya munafuka”. Cike da son tura haushi Amima ta kwashe da dariya tana miƙewa da faɗin, “Oh to lallai abin ya girma. Ubana kam ai ubanki ne kema dole ya zauna miki a rai. Adai bi a hankali. Kar wajen tone-tone kaza ta tono wuƙar yankanta. Shi wannan NAMIJIN ZAKI ne ba Mazan club ba. Baya ɗaukar wargi balle shashanci. Itama data samu bata kasance ballagaza bane kuma tana cin darajar Abbanta. Amma kinga matsayarta, balle ke da aka saba leƙe-leƙ...” Jifan da Rayhana ta wurgo mata da saving spoon ya sata barin wajen da gudu tana dariyar iskanci data sake shaƙe wuyan Rayhana...
••••••••••••••••••••
9:pm na dare Dada daya fita a gidan shi da su Ma'aruff tun bayan sallar magriba suka dawo. Asibiti suka rakashi ya duba Lailah da Baby, daga can suka je duba Daddy Imran gida. Zuwa lokacin su Aunty Ummi duk sun wuce gida. Falon ma babu kowa alamar duk sun shige barci. Baiyi mamaki ba dan yasan masu ƙiriniyar gidan na fama da kansu. Mammah kuwa dama akwai barcin wuri. Su Bilal kuma office gobe. Har ya nufi upstairs sai kuma ya dawo da baya, ƙofar Mammah ya nufa, yay knocking a hankali. A mamakinsa sai yaji tana bada umarnin shigowa. Koda ya shigo a zaune ya sameta bakin gado tana duba wani littafin addu'oi. Ta ɗago tana kallonsa da amsa sallamarsa. Dai-dai yana kaiwa zaune take faɗin, “Ai har na fara tunanin kiran wayarka. Dan zaman jiranka nake daman”. Ƙaramin murmushi yay da faɗin, “To Mammah lafiya dai ko?”. “Lafiya lau. Yaya jikin Imran ɗin?”. “Alhamdullah ai ba a jigace yake ba. Kawai dai harda razani”. “Alhamdullah ALLAH ya kiyaye gaba. In sha ALLAHU zan je na duba shi gobe nima.” “ALLAH ya kaimu”. “Amin ya rabbi. Shaiɗancin mutanen nan ya fara bani tsoro Muhammad. Tunda har tunaninsu ya fara basu yin amfani da makusantanka domin samun biyan buƙatarsu. Abin akwai haɗari sosai a ciki, idan na farko an tsallake rijiya da baya nan gaba kuma fa?”. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, dan shi da farko ma yayi tunanin maganar Nabeeha zatai masa. “Kar ki damu Mammah in sha ALLAHU hakan bazai sake faruwa ba. Wannan ma da suka aikata zasu biya bashinsa harda riba da hannayensu. Akwai shirin da nake yi musamman akan su ƙananun nan. A cigaba da mana addu'a dai. Dan in sha ALLAHU nasara ce ke tunkaro mu. Ko ba komai abinda sukayi yanzu ɗin ya ƙara buɗe min tunani na akan sanin su waye su.” “Addu'a har mu koma ga UBANGIJI bazamu daina yi muku ita ba, ALLAH ya cigaba da baku kariya. Ya ɗora nasararku akan maƙiyanku. Suma ALLAH ya shirye su su gane gaskiya kafin lokaci ya ƙure musu idan masu shiryuwa ne.” “Hummm Mammah kenan, to Amin. Amma waɗan nan mutanen basa buƙatar shiriya.” “A'a ba'a yankema UBANGIJI hukunci akan ikonsa ai.” “Haka ne kam, ALLAH yasa mu dace. Ranar asabar iyayen Haydar zasu zo a tsaida magana. Kuma ina son ne kawai a saka rana batare da wani jeka ka dawo ba. Lahadi mu kuma sai muyi batun Bilal da Asma'u. Sai dai shima Ammar kawai zan haɗa da shi”. Murmushin Mammah ya faɗaɗa sosai. Ta ce, “Alhamdullahi ALLAH yasa ayi damu. Ya kuma sanya albarka a ciki. Amma Auta yana da budurwa kuwa?”. Yanzu kam sai da Dada ya ɗan murmusa. Kai tsaye ya ce, “Zan bashi Ruƙayyana in sha ALLAHU”. Wani irin farin ciki ne ya daki zuciyar Mammah. Har bama tasan ta zabura ta kamo hannun Dada ba. Ta ce, “Muhammad da gaske? Aiko idan kayi haka ka gama min komai. Wannan tunanin ya daɗe a raina. Tsoron halin ɗan yau yasa na shanye abina. Ya rabbi yanda ka bani wannan farin ciki a wannan dare kaima ALLAH ya faranta maka har ƙarshen numfashinka”. “Amin Mammah, tare dake da zuri'armu”. Sosai take farin ciki, dan har sai da tai sujidar shukur. Bayan ta ɗago ne take masa maganar shima lokaci yayi da Nimrah zata san wanene shi a gareta. Dan ɗazun Imran ya kirata sun tattauna sosai. Shiru Dada yay baice komai ba, itama bata damu da shirun nasa ba ta cigaba da faɗin, “Tunda har sun gaya mata yin shirun mu zai sakata a wasi-wasi. Amma idan mun sanar da ita zata kasance a nutsuwa koda zata shiga ruɗani. Nimrah yarinya ce mai wayo, suna da iliminsu da fahimtar abubuwa gwargwadon iko, idan bamuyi saurin yin hakan ba a yanzu suke tasowa samari na kawo musu caffa, idan sun tsallake tarkon wani bazasu tsallake na wani ba dan zuciya ba'ai mata shamaki ƙo ƙa'idar wanda zata iya so. Makarantar ma idan zata zama damuwa kawai su zana ssce wannan shekarar, maybe idan suka ga kansu a jami'a a samu sauƙin wannan ƙiriniyar tasu”............✍️
Hhuummmm! [1/15, 4:39 PM] Zeenaran 😘: