Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 15

Post

Kida a ruwa Book 3 page 15

...... He said goodbye to her and left, she was following him with a look.... But when he closed the door, he had to take out his phone and turn on the light so that the light in the hall was completely turned off. His pace was not more than five and he stopped before going up the staircase because he was crying. Even though he is in the heart, the ability to hear that God has given him to hear, and the night is quiet. Turn it on to set where it plays the sound. It must be in the kitchen, so he stared at the door with his eyes for a few seconds. Before he raised his feet, he went towards the place full of his heroic steps and physical health like the bards of men with long limbs. He covered the light of the phone with his hand, before he pushed the door of the kitchen.... He came in unexpectedly, with the light of the kitchen and his phone at the same time, he sang Nimrah a psalm. She was sitting on the floor in a small corner of the cabinet, and put her head between her legs. The kitchen light turned on, seeing who came in and stole it, her whole body was shaking. Dada kept his eyes on her and just looked at her from top to bottom. It's sleeping clothes, pants and a shirt that are

Standalone post1,581 words

15

.........Ya gamsu da shawarar Mammah kam. Dan haka yace, “Hakan yayi sosai. In sha ALLAHU zan duba naga yiwuwar komai Mammah.” “To ALLAH yay muku albarka. Ka sanar ma Jamilu ne?”. “Eh, in sha ALLAHU. Yace ma yana tafe ranar juma'a. Sai dai Uncle Naseer zuwa gobe in sha ALLAHU zanje shima muyi maganar. Sai waɗan nan yaran, su basa komai ne a gidansu suka zo nan suka tare?”. Ta san su Hanoon yake magana. Dan haka tai murmurshi. “To ban sani ba Muhammad. Amma dai nayi waya da Tasi'un ya tabbatar min sati mai zuwa shima zai dawo ƙasar. Amma ina son ka zauna dasu ko sau ɗaya ne ka tsawatar musu akan wasu ɗabi'u nasu marasa ƙyau kodan a taimaki rayuwarsu.” “Hummm Mammah, nifa akan abinda na isa kawai nake tsawa. Ki bar masa ƴaƴansa a yanda kika gansu yazo ya kwashe abinsa. Ai ya fiki sanin ba'a dai-dai suke ba. Amma ya zaɓi barinsu a haka. Yanzu dai kwanta ki huta. Nima zanje barci nake ji sosai.” Sarai ta fahimci dan ya kaucewa maganar ne kawai. Dan haka ta ɗan murmusa tana girgiza kanta. Har yay mata sallama ya fice tana binsa da kallo....

Koda ya maida ƙofar ya rufe dole ya ciro wayarsa ya kunna fitila dan an kashe hasken falon gaba ɗaya. Takunsa bai wuce biyar ba yaja ya tsaya gab da fara hawa staircase saboda kamar nishin kuka yake ji. Duk da anayi ne ciki-ciki ƙarfin ji da ALLAH ya bashi ya saka shi ji, ga kuma darene ko ina yay tsitt. Juyawa yay saitin inda yake jiyo sautin. Tabbas a kitchen ne, dan haka ya zubama ƙofar shiga idanunsa tsahon sakanni. Kafin ya ɗaga ƙafafunsa ya nufi wajen cike da takunsa na jarumta da lafiyar jiki irin ta baraden maza masu tsayin gaɓɓai. Hasken wayar ya ɗan rufe da hannu, kafin ya tura ƙofar kitchen ɗin.... Yanda ya shigo a bazata, tare da haska kitchen ɗin da fitilar wayarsa a lokaci ɗaya ya saka Nimrah zabura. Dan zaune take a ƙasa cikin ɗan lungun jikin cabinet, ta saka kanta a tsakiyar ƙafafunta. Fitilar kitchen ɗin ya kunna, ganin wanene ya shigo ya sata miƙewa tsaye gaba ɗaya jikinta na tsuma. Dada kam idanu ya zuba mata kawai yana kallonta daga sama har ƙasa. Kayan barci ne wando da riga masu taushi a jikinsa. Wandon har ƙasa, sai rigar mai gajeren hannu iya gwiwa. Kanta da hula, sannan ƙafarta da bedroom slippers masu taushi. Tunda tai masa kallo ɗaya ta duƙar da kai bata sake ɗagowa ba. Tana ta dai cuɗa hannun nata cikin juna yanda aka saba.... “Ki dafa lemon tea ki kawo min”. Ya faɗa kawai yana juyawa abinsa ya fita. Sharr hawaye suka sake zubo mata. Takai hannu ta share tana jan hanci. Batare da tace komai ba ta nufi inda tea pot ɗinsu suke ta ɗauka ɗaya ƙarama. Fanfo taje ta ɗauraye sannan ta saka ruwa dai-dai misali ta nufi gas. Ta ajiye tukunyar tana sake share hawayen da suka ƙi tsaya mata da shashshekar kuka. Abubuwane sun mata yawa a cikin ƙirji, musamman wanda ta gano a wajen mutanen can da wanda aka sanar mata game da zuri'arta da shi kansa Dadan da ƴan uwanta data gani jininta a karo na farko a rayuwarta, bayan labarin mahaifiyarta data rasu babu labarin wanda ta taɓa sani a danginta sai yanzu. Addu'ar da take ta ambato ce kawai ke saka mata nutsuwa da babu abinda zai hanata haukacewa a wannan gaɓar. Lemon tsamin data ɗauka babbar guda biyu ta wanke, tare da ganyen na'a-na'a da lemon grass ta koma wajen tukunyar ta zuba. Lemon tsamin kuma ta yanka ɗaya a ciki, ɗaya a cikin flaks data ɗakko shima....

Dada da yay ɗan jimm a bakin ƙofar kitchen ɗin yana kallo tamkar yana hangota jin ta fara kai-kawon aikin daya sakata, amma tana cigaba da shashshekar kuka sai ya furzar da iskar bakinsa kaɗan yana barin wajen. Sama ya haura abinsa. Sai dai bai wuce ɗaki ba sai da ya leƙa ɗakin su Mu'azz dana su Bilal ya tabbatar sun kwanta, sai Afeef ne ma ke latse-latsen waya, yana jin kuma za'a buɗe ƙofar ya kifeta shima yaja bargo yay likimo. Dan ya tabbatar Dada ɗin ne saboda duk dare haka yake musu.. Ɗakin sa ya wuce. Bayan ya zube wayoyinsa a saman mirror ya shiga kunce agogon hannunsa. Dai-dai nan Nimrah tai knocking. “Shigo”. Ya faɗa a taƙaice. Koda ta turo ƙofar ta shigo da sallama ƙasan maƙoshi saboda muryarta ta ma dishe, bai juyo ya kalleta ba amma ya amsa a lips. Hanyar bayi ya nufa yana rage botiran shirt ɗinsa da faɗin, “Ki jira ni anan” daga haka ya shige ya barta da bugun zuciya da kallon ƙofar bayin. Bata da zaɓin daya wuce bin umarninsa. Dan haka takai zaune a ƙasan carpet tana ɗan wasa da lallausan gashin jikinsa. Sai dai lokaci-lokaci tana share hawayen dake ciko mata idanu amma taƙi bari su zubo...

Ya ɗan jima kafin ya fito, sai dai kayan barci ne yanzu a jikinsa saɓanin kayan daya shiga da su. Tunda tai masa kallo ɗaya ta maida kanta ta duƙar. Shi kam baima kalla inda taken ba kai tsaye gaban mirror ya nufa yana ƙara tsane gashin fuskarsa da ƙaramin towel. Ya ɗan ja mintuna a wajen, dan sai da ya saka turare a jikinsa ya kammala uzirinsa kafin ya nufi gado abinsa. Ɗago kai Nimrah tai a karo na biyu tana kallonsa, a tunaninta koya manta da ita ne, ganin ya hau gadon sosai ya zauna, sai dai ya jingina bayansa da fuskarsa yaja bargo ya rufama ƙafafunsa zuwa ƙungunsa, ya kuma kashe hasken fitilar ɗakin gaba ɗaya sai lamp itama ta side ɗin da yake zaune kawai. “Bani”. Ya faɗa a taƙaice yana buɗe laptop daya ɗora saman cinyarsa bayan yasa ƙaramin filo. Shiru Nimrah bata motsa ba, dan batama fahimci da ita yake ba. Sai da ya ɗago ya kalla inda take, tare da faɗin, “Wai bada Nimrah nake ba”. Ƙirjinta taji ya buga, dan bayan a jeji data gudu sanda bomb zai tashi bata taɓa jin ya kira sunanta ba. Miƙewa tai gaba ɗaya ta ɗauki tray ɗin data saka ƙaramin flaks da tea cups guda biyu, sai tea spoons suma biyu da zuma cikin ɗan wani gora mai ƙyau alamar a haka aka sayeshi. A ƙasan carpet ɗin gaban gadon ta ajiye, daga tsugunne ta haɗa masa komai. Saman bed side drawer tai nufin ajiyewa sai ya miƙa mata hannu batare daya bar abinda yake a laptop ba. Hannun ta kalla, sannan ta ɗan kalla fuskarsa dake ciɗin-ciɗin kamar koyau she. Dole ta matsa sosai inda yake sannan ta miƙa masa. Maimakon amsa da ɗan plate ɗin da kofin ke a kai sai kawai ya kama hannun cup ɗin, ita kuma da ba haka tai zato ba sai taji kamar ya tafi zai ɓare ne, caraf ta kama hannunsa cikin nata hannun. Idanunsa dake kan screen ɗin yaɗan lumshe tare da buɗewa a lokaci guda kan hannayen nasu. Da sauri ta janye nata tsigar jikinta na tashi batare data san dalili ba. Shima sai bai ce komai ba, ya dai kalleta shaaa ya ɗauke idanunsa. Daga haka ya fara shan shayin yana aikinsa. Ganin lokaci na ƙara jaa yaƙi cewa kuma ta tafi cikin rawar murya ta ce, “Dada na tafi?”. Shiru bashi da niyyar amsata, bai kuma daina aikinsa ba balle shan shayinsa da yake matuƙar jin daɗinsa. Sai yaji tama fi Ammar iya dafawa. Dan kullum shi yake sakawa ya dafa masa. Ammar daya fahimta ma ko bai buƙata ba sai ya dafa ya kawo ya ajiye a ɗakin in ma baya gidan. Yau ma gaba ɗaya ya shafa'a ne saboda kasancewar su Aunty Mimi a gidan. “Tashi ki dawo sama”. Furucin yazo mata a bazata daga bakin wanda bazata iyama jayayya ba. Gadon ta kalla sannan ta kallesa, ganin har yanzu hankalinsa akan aikinsa yake sai taji kamar ta saki kukan da take ta faman dannewa. Bata da zaɓin daya wuce bin umarninsa, dan haka ta miƙe kanta a ƙasa ta ɗofanu acan ƙarshen ƙafafunsa dake cikin bargo. Sai da taja kusan mintina biyu kafin ya ɗago ya kalleta, kallo irin na tsaiii ɗin nan akan mutum dake sakashi yaji rikicewa, sai dai babu damar yin motsi balle yin magana dan anfi ƙarfinka. “Mike damun ki?”. Ya faɗa kai tsaye idanun nasa dai a kanta ƙyam. Jitai ta sake daburcewa, dan ta tabbatar dai amsar yake buƙata daga gareta kuma dole ta bashi. Cikin rawar lips da in-inar da yanzu tazo mata ta buɗe bakin zata fara magana... “Kar kimin ƙarya”. Ya katse hanzarinta cikin gizago. Sai kawai taji hawaye sun ciko mata idanu. Lips ɗinta sai rawa suke kuma. Idanunta ta ɗan ɗago kaɗan da nufin satar kallonsa sai taga nashi har yanzu ƙyam a kanta. Da gudu ta risinar da nata. Sai ga hawaye sharrr da take faman riƙewa sun ɓalle. Fuskarsa ya kauda gefe yana furzar da iska. Sai kuma ya janye laptop ɗin gefe, tare da ajiye kofin shayin da har ya shanye a bed side drawer ya miƙa mata hannu. “Zo nan”. Kamar dama abinda take jira kenan ta miƙe, gabansa tazo zata durƙusa daga ƙasa ya hana hakan ta hanyar riƙo hannun nata. A bakin gadon ya zaunar da ita tana facing ɗinsa, har jikinta na gogar nashi duk da shi a rufe yake da bargo. Dan haka ta ƙara duƙar da kai sosai..........✍️ [1/15, 5:05 PM] Zeenaran 😘: 16