Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 16

Post

Kida a ruwa Book 3 page 16

.....stop sharing your worries with your sister, your friend? After I came back, I didn't see you doing that. Did you start hiding things from her?". She shook her head quickly. "I want to talk to you." "I'm not hiding anything from her. It's just today I felt like I wanted to go back to the kitchen and cry." "Or die the death you want." She was silent and had nothing to say. It was as if he entered and read what was in her mind. He also understood that and continued to say, "Come here, since you don't love Rukayya, she is worried about you too. Make friends with me too. Since I've already met you, why don't we discuss the problem together? That won't make Ruqayya happy, let alone her mind will rise as she doesn't want". "Ai Mammah said there is no good friendship between a man and a woman". But it's me, Mammah won't stop. Don't you think she is also talking to me? But since my friend and I are strangers, he is here. I will ask Ruqayya to make a deal, and don't think we are separate and get angry. I'll do whatever I can to steal your beauty." Baki pushed forward, puffing up her cheeks. She said, "I agree." Laughter caught him, he was just a little embarrassed. Then he handed her ov

Standalone post1,495 words

..........“Yaushe kika zama sha-sha-sha ne da komai kuka-kuka?”. Yanda yay maganar can ƙasan maƙoshi, da sigar lallashi yana ɗan matsa hannunta dake cikin nashi har yanzu ya sata ɗan jin sassauci. Cikin muryarta dake a ɗashe ta ce, “Dada ina son na Mutu ne?”. Idanu ya zuba mata sosai, sai kuma ya ɗan motsa lips kaɗan ya ce, “Mutuwa? To idan kika mutu wazai haifa ƴaƴan soja Kiddo?”. Da sauri ta ɗago tana kallonsa, duk da bawani ta gane zancen nasa ina ya dosa bane ba. Kai ya ɗan jinjina mata alamar tabbatarwa. Ita kuma sai kawai ta tura baki tana janye idanunta daga cikin nashi. Mitsitsin murmurshin da bai shirya bane ya kufce masa. Sai dai bai bari ta gani ba ya gimtse abinsa. Gyaran murya ya ɗanyi, hakan ya sata sake ɗagowa, sai dai bata yarda sun haɗa idanu ba. Cikin son kamata a wuya ya canja salon sigar tambayar tasa. Dan ya fahimci ɗaya daga halayenta shine kafiya, dagiya akan abu. Idan ba ita taso ba akwai taurin kai. Sannan ya fahimci depression ne ke neman kamata. “Miyasa kika daina raba damuwarki da ƴar uwarki, aminiyarki? Bayan kuma sanda na dawo ba haka naga kuna yi ba. Kin fara ɓoye mata abubuwa ne?”. Kanta ta girgiza masa da sauri. “Magana nake so da baki”. “Bana ɓoye mata komai. Kawai dai yau ne naji ina son na dawo kitchen ɗin nayi kukan”. “Ko kuma kiyi mutuwar da kike so ba”. Shiru tai dan bata da abin faɗa. Kamar ma ya shiga ya karanta abinda ke zuciyarta ne. Shima fahimtar hakan ya sashi cigaba da faɗin, “Shike nan tunda baƙya son Ruƙayya tasan damuwarki itama ta damu. Ni kiyi abota da ni mana. Kinga tunda na riga na ganoki sai mu dinga tattauna matsalar a tare ko? Hakan bazai sa Ruƙayya taji ba balle hankalinta ya tashi kamar yanda baƙya so”. “Ai Mammah tace babu ƙyau abota tsakanin namiji da mace”. (Wata sabuwa) Ya faɗa a zuciya. A zahiri kam sai ya ce, “Haka ne gaskiya Mammah ta faɗa. To amma ai ni ne, Mammah bazata hana ba. Bakiga itama da ni take shawara ba. Amma tunda baƙya sona da abokin ai shike nan. Zan nema Ruƙayya mu ƙulla, kar kuma kiga mun ware ki kiji haushi. Dan zanyi duk yanda zan yi na ƙwace miki ƙawa”. Baki ta tura gaba tana kumbura kumatu. Ta ce, “Na yarda to”. Dariya ta kama shi, ya dai gimtse da ƙyar. Sai kuma ya miƙa mata ƙaramin yatsarsa alamar su ƙulla to. Yatsar ta kalla tsawon sakanni, kafin ta ɗago nata hannun slowly ta miƙa masa itama nata ƙaramin yatsan ya sarƙe waje guda. “Shi ke nan daga yau mu abokai ne ba?”. Kanta ta jinjina masa. Shima ya jinjina nasa yana faɗin, “Good. Ƙara zuba min shayin, sai kizo ki bani labarin miya saka ki kuka yau?”. Shayin ta sake zuba masa kamar yanda ya buƙata. Sai dai bata dawo saman gadon ba tai zamanta a ƙasa. Shima baiyi magana ba ya ɗauki laptop ɗinsa ya cigaba da aikinsa. Hammar data saki a karo na uku ya sashi kallonta. Sai da ya sha shayi daya kai baki ya ajiye kofin sannan yay magana. “Kinga barci yazo ma. Tashi na rakaki ki kwanta da safe ƙya bani labarin, maybe ma lokacin kin huce sosai daga fushin ko?”. Kanta ta jinjina masa nan ma, harta yunƙura zata tashi ya dakatar da ita. Cikin tsaurin murya ya furta, “Daga yau karna sake ganinki kina kuka a ko inama ba kitchen ba da daddare. Idan mutum yana cikin damuwa ba kuka bane mafita ko hana kai barci ko son a mutu ne hanyar yayewar damuwa ba. Alkur'ani ake ɗauka a karanta. Ko ai alwala ay salla a nema ɗaukin UBANGIJI. Dan shi mai Rahama ne da jin ƙai ga bayinsa masu dogaro da shi. Ko aita ma ANNABI salati ko istigifari”. Kanta ta jinjina. Tana mai cuɗa yatsunta waje guda ta ce, “In sha ALLAHU bazan sake ba Dada. Zan dinga yin kuma yanda kace”. “Good Negar. Idan kikai hakan zanyi alfahari da ke. ALLAH yay miki albarka”. “Amin”. Ta faɗa a hankali tana satar kallonsa. Ganin ita yake kallo shima sai tai saurin janye wa. Guntun murmushi yayi yana sakkowa a gadon. Dan haka tabar wajen da sauri tana ɗaukar tray ɗin kayan shayinsa. “Bar wannan”. Ya faɗa yana wuceta. Maidawa tai ta ajiye tabi bayansa. A haka suka fito a ɗakin tana biye da shi har suka sauka ƙasa. A bakin ƙofarsu yaja ya tsaya, sum-sum kanta a ƙasa ta ce, “Dada sai da safe nagode”. “Uhmmm”. Ya faɗa a maƙoshi kawai yana binta da kallo harta shige. Ta turo ƙofar zata rufe suka haɗa ido. Da sauri ta ƙarasa rufewa tana jingina a jiki tare da runtse idanun tana sauke numfashi. Sai kuma ta zabura tana leƙensa ta jikin Door peephole na ƙofar. Yana tsaye har lokacin shima ya zubama ƙofar idanu da wani kalar kallo data kasa bama suna. Kusan mintuna biyu kafin taga ya furzar da iska yana barin wajen. Itama iskar ta furzar tana sauke ajiyar zuciya. Kafin ta bar wajen zuwa gaban gadon Ruky ta gyara ma bargo daya zazzame a jikinta. Sannan ta nufi bayi yin alwalar barci......

Jin hawowar Dada staircase ɗin ya saka Afeef komawa da sauri cikin ɗakinsu yana danne baki da hannu. Kafin ya tsaida video ɗin da yake recording a wayarsa. Daga waje shima Dada tsai yay yana kallon ƙofar, sai kuma ya wuce abinsa ɗaki batare daya ce komai ba.

Hummm Afeef video kuma🤔?

_________________

Yau da wuri ya shigo gidan. Dan gaba ɗaya baida nutsuwa. Ganin har dare yayi hakan na nufin kwanaki biyu suka rage masa da wannan daren game da umarnin ƴan jam'iyya. Zuwa yanzu ya yanke ma kansa hukuncin da zai fishshe shi ya kuma taimaki ƴan ƙasa da wani abun koda ba komai da komai ba. Dan itace kawai mafitar data rage masa. Yayi alƙawari ma UBANGIJI da talakawan ƙasa da sukai faɗi tashi akan zaɓensa da tunanin ya cancanta wajen kamanta musu abinda ya dace matsayin shugaba. Idan kuma har ya miƙa wuya ga wancan layin ya tabbatar waccan burin nasa da alƙawarin zai tashi a banza ne. Dan shi bai ci ba, ƴan ƙasar basu ci ba, tabbas wasu zasu ci da saka hannunsa. Kuma dole ya amsa tambayoyi akan hakan ranar sakamakon rarrabe ayyukan bayi. ALLAH ne mai kare bawa akan komai. Amma yana buƙatar wani jajirtaccen mutum kusa da shi da zai dinga rarrabe masa gaskiya da saɓaninta tako wace fuskar data dace. Babu kuma wanda zai iya yin hakan sai mutum ɗaya tak. Mutum ɗayan da ya yarda da shi ɗari bisa ɗari a wannan duniyar. Sai dai fidda sunansa akan muƙamin da yake kallo wani sabon kalubale ne da dole sai ya jure, dan hatta ga shi mai sunan zai iya fuskantar tirjiya kodan sanin da yay masa akan ƙyamatar al'amarin mulki da siyasar ƙasar a bayyane. Dan hakama ya yanke bazai sanar ma kowa ba sai bayan ya ƙaddamar ya kuma zartar. Da wannan tunanin ya saki murmurshi, tare da ɗaukar wayarsa yay kiran ogansa na siyasa. Bayan sunyi gaisuwa cikin mutunta juna kamar yanda suka saba. Kai tsaye ya furta, “Sir na amince da buƙatun jam'iyya, sai dai da sharaɗi guda ɗaya tak nima daga gare ni”. Murmushi Oga yayi daga can, duk da yasan dama dole ne Janar ya amince ko yaƙi ko yaso. Kamar yanda ya saba cikin kwantar da kai ya ce, “Ina jinka General, kuma ni mai baka goyon bayane akan duk buƙatunka. Musamman a wannan gaɓar da ka faranta min ka saki wannan jayayyar da zata kawo ma kowa masalaha da kwanciyar hankali musamman ni da kuka saka a ysakkiya.” Murmushin takaici shima Janar yayi, kafin ya gyara zama da faɗin, “Ta ɓangarena Chef of staff zai fito”. Ɗifff numfashin Oga ya ɗauke kamar an daki kansa da guduma. Fin mintuna biyu kafin ya ja iska mai nauyi ya fesar. Bisa ga abinda zuciyarsa ta ayyana masa kawai ya ce, “Shike nan yanda kake so haka za'ayi, zan zauna da su, kuma nasan zasu amsa. Sai dai kayi ƙoƙari kaima ka cika musu alƙawarin su duka”. “Oga! Ni indai akai min hakan na amince da komai game da muƙaman da wanda ma suke buƙatar a baiwa. Daga yau kuma yanzu nan ma chapter closed kawai”. “Shike nan ka saurare ni, zuwa safiya in sha ALLAHU zaka ji dukkan bayani”. “ALLAH ya kaimu Oga na gode sosai a gaida iyali, mu kwana lafiya”. “Zasu ji. Amin”. Kai Janar ya jinjina kamar yana a gabansa shima yay murmushi yana ajiye wayar. Jinsa yake sakayau kamar an sauke masa kaya bisa kai. Sai ma ya miƙe ya shiga bayi dan watsa ruwa a jikinsa. Amma murmushi ya kasa barin fuskarsa saboda hango ƙurar da zai tayar a wannan satin cikin ƙasar dan tako wane fanni bai hango sauƙin al'amarin ba, dole ai kare jini biri jini tsakanin maƙiyan ɓoye dana zahiri.........✍️