Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 17

Post

Kida a ruwa Book 3 page 17

.....release her body. Alhamdulillah that is also effective. Especially when it comes to going to the hospital to see Lailah and her baby. Right when they were going out, she contacted Shariffa's department and found Nasir, he had a cold, she didn't want to go out with him, that's why she gave up and let him come back. Mammah's order to come and fix Dadan's room stopped standing, now there is nothing she wants to be close to like Dada's room, she understood that all the things she was looking for were in the room. She had to collect the trash and everything she needed and left. Bayi went in to fix it, then she got his underwear and put the sign to wash. She should be ashamed. She beat her head for about three minutes and decided to wash her hair and leave them where she saw them? There is a lot of shame in the washing, and if she even lets her mend the servants, he must know that if she skips the mends, she doesn't care. She could hardly control her heart and closed her eyes and poured it into the washing machine, mixed soapy water in it and turned it on. She started to fix the servants, and when she finished, she returned to the washing machine and one of them killed himself.....

Standalone post1,623 words

17

........Anan Gidan Mammah kam Nimrah ta tashi da ɗan dama-dama. Kasancewar ba makaranta suka koma ba suna gama aikin da duk suka san sunayi suka sake komawa barci. Sai wajen ƙarfe goma Mammah tasa Biebah tashinsu suyi kalaci. Dada baya gidan, dan daga sallar asuba bai dawo ba. A waya ma ya kira Mammah suka gaisa babu jimawa, ya sanar mata yaje wani waje ne amma zai dawo nan kusa. Duk wani motsin Nimrah Mammah na hankalce da shi, ta kuma fahimci a sanyaye take tun jiya. Sannan bata yawan magana. Ganin yanda take kafe mazan gidan da idanu ɗaya bayan ɗaya a kaikaice yasa Mammah fahimtar batun auren da mutanen suka sanar mata ke damunta. Sannan tana son fahimtar waye mijin. Mammah tai ɗan ajiyar zuciya tana ɗauke kanta. Sauran kuwa fahimtarsu daban data Mammah. Dan sunfi jingina batun kidnapping ɗin da akai mata ne da yanayin nata na shiru-shiru yau. Balle rashin lafiyar Imran ta basu tabbacin sai da akai gumurzu wajen samota, dan haka suka maida hankalinsu akan janta da labaran da zata saki jikinta. Alhamdullahi hakan kuma da suke yayi tasiri. Musamman da taji batun zuwa asibiti duba Lailah da babyn ta. Dama suna fitowa saida ta dangana da sashen Shariffa ta gano Nasir, yana mura ne ba'a son fitowa da shi shiyyasa ta haƙura ta barshi ta dawo. Umarnin da Mammah ta bata na zuwa ta gyara ɗakin Dadan ya sakata miƙewa, dan a yanzu babu abinda tafi son buƙatar kusanci da shi kamar ɗakin Dada, ta fahimci dukkan abubuwan da take nema suna a ɗakin. Sai da taje ta tattara kayan sharar da duk abinda take buƙata sannan ta tafi. Bayi ta fara shiga domin gyarawa, sai ta samu underwers ɗinsa ajiye alamar zai wanke. Kunya taji ta kamata. Ta duƙar da kai kusan na mintuna uku tana shawarar ta wanke kota barsu a inda ta gani? Wankewar dai akwai ɗunbin kunya a ciki gaskiya, sannan idan ta bari ma tayi gyaran bayin dole zai san ta gani, idan ta tsallake bayin bata gyara ba bata ƙyauta ba, tunda daga shi har Mammah data sakata babu abin rainawarta a ciki. Da ƙyar ta iya danne zuciyarta ta ɗibesu idanunta a rufe ta zuba cikin worshing machine, ta haɗa ruwan sabulu a ciki ta kunna. Gyaran bayin ta fara, sai da ta kammala tsaf ta dawo wajen worshing machine ɗin daya kashe kansa tun ɗazun ta fara cirosu. Nan ma idanu ta rufe sannan take matsesu ta sake canja ruwa. Sai da ta tabbatar sun mata yanda take so ta ɗauraye ta zuba a dryer ta busar. Sannan ta kwaso su ta fito. A kujera ta ajiye su ta fara gyaran ɗakin shima. Tayi har mopping ta saka turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Har zata tattare kayan sharar sai idanunta suka sauka akan underwers ɗin data wanke. Da kunya ta barsu a wajen yana shigowa ya gani, sai kawai taje ta kwashe ta nufi wadrobe da su dan gyara takai can ta ajiye salin alin. Sai da ta babbuɗe harta gano inda ake ajiyesu sannan tai ƙoƙarin ajiyesu gefe domin fara shiryasu a wajen. Babbar brown envelope dake wajen data ɗorasu ta faɗo, take hotuna dake ciki suka watse a ƙasa. Binsu tai da kallo, sai kuma ta kai duƙe da sauri ganin fuskar Dagger, ba fuskar tasa ce ta ɗauki hankalinta kawai ba ganin wanda suke tare, drivern su ne Malam Buba. Gabanta ya faɗi, tuna itace sanadin haɗa Dagger da malam Buba, ta kuma tabbatar ita Dagger ɗin yazo nema. Sauri-sauri ta kwashe hotunan duka tana kallo. Guda uku duk mutumin ne, ɗaya zai buɗe mota data kasance ta gidan ce ya waigo alamar tabbatar da babu mai kwallon sa, sai kuma dai-dai ya fito daga motar dai, wanda ya fara gani suna cikin motar ne ta gaba aka ɗauka kuma tabbas basu san anyi ba. Sauran hotunan bata gane komai ba, dan wasu mitanene daban. Bata da zaɓin daya wuce kwashe hotunan Malam Buba da mutum nan da ko sunansa bata sani ba. Dan inta bari Dada ya gani komai na shirinta zai rushe. Gaba ɗaya ta miƙe tana ware iya nasu, sai dai cikin rashin sa'a ta ɗaga rigar jikinta zata saka cikin skirt aka buɗe ƙofar a bazata. Ba ƙaramin daburcewa tayi ba, musamman ganin mai shigowar. Shima da bai san da ita a ciki ba sai yay ɗan tsaii yana kallonta, dan kai tsaye ya gane a firgice take. Waccan ranar da taga file ɗin nan ne yazo masa a rai. Ya sauke idanunsa ƙasa da take ƙoƙarin cusa abu a jiki. Farin abu ya gani, sai dai bai san minene ba, dan itama da sauri ta saki rigar ganin inda yake kallo. Nimrah da illahirin jikinta ke tsuma ta aro jarumtar dole ta yafama kanta tana haɗiye yawu masu ƙauri. Cikin gyara yanayin ta ƙwarai da gaske ta ce, “Dada sannu da zuwa. Ina kwana?”. Bata jira amsarsa ba ta juya tana fara ɗaukar underwers ɗin nan..... Dai-dai lokacin ya ƙaraso wajen, ya tsaya a bayanta gab har tanaji hucinsa. Idanu ta runtse tana karanto addu'ar duk da tazo mata a zuciya. Sai kawai ta fara cusa kayan inda ba'a nan ya dace ba. Hannunta ya riƙo, hakan ya sakata ƙara rumtse ido da cije lips da masifar ƙarfi, ta kuma runtse vest ɗinsa dake a hannunta daya riƙo da nashi. “Mi kike yi anan?”. Wani busashshen yawu ta haɗiye da ƙyar, har tana jin kamar yana yanka mata maƙoshi. Da ƙyar ta iya fisgo kalaman bashi amsa da. “Ina gyara kayan wanki n...ne”. Kayan hannunta ya kalla na sakanni, sai kuma ya ɗan ja baya daga jikinta. Har tana murnar ta tsira murnar ta koma ciki. Dan kuwa kafaɗunta ya dafa ya juyo da ita suna facing juna. Cikin golden voice ɗinsa dake fita da tsantsar gizago da zurfin iko ya ce, “Buɗe idanun ki”. Jitai idanun ma sun cika da hawaye kafin ta buɗe. Tadai yi jarumtar haɗiyesu tana sake kame kanta. Koda ta buɗe ta kasa kallonsa gaba ɗaya, sai dai shi tana jin kaifin nashi har a cikin magudanar jininta. Bata san mi yake kallo ba a jikinta, gashi yaƙi yay magana. Ta takura matuƙa saboda kwarjininsa da yanda ya cika mata waje. Jinta take kamar a gaɓar ramin gacci mai matuƙar zurfi, gabanta kuma zaki dake a yunwace ya zuba mata idanu... “Kayi haƙuri Dada”. Kalmomin uku suka suɓuto daga cikin bakinta batare data shirya ba. “Ba sai anyi laifi ake bada haƙuri ba?”. Idanunta da suka cika da ƙwalla ta ɗago ta kallesa. Zata maida ta risinar ya dakatar da ita cikin umarni. “Idan suka zubo sai kin kwashesu kin maida.” Mar-mar ta shiga yi da idanun tana maida hawayen kuwa. Dai-dai yana kai hannu ya ɗaga t-shirt ɗin jikinta baƙa. Dan skirt ne light brown da bai kai mata har ƙasa ba, sai da ya wuce gwiwa sosai, sai baƙar t-shirt ta mata da hoton katon teddy bear a gaban. Sosai kayan sun mata ɗas. Hannu takai da sauri zata hana shi. Ya wani ɗago birkitattun idanunsa da suka sake juyewa saboda halin da yake ciki ya watsa mata. Tare da faɗin, “Zan karya hannun nan”. Ai da sauri ta janye hannun nata, shi kuma ya ƙarasa ɗage rigar ya jawo hotunan data saƙe a cikin skirt. Maimakon sakin rigar sai ya tsaya yana kallon wani tawwadan ALLAH dake gefen cikin nata babba sosai. Itama jin shiru ta buɗe idanunta, motsin da tai ya saka shi farga shima, sai kawai ya sake rigar yana ƙara tsuke fuska. Hotunan ya fara kallo, guda uku ne, ya zubama fuskar Dagger ido sosai cike da nazari, dan akwai handkachiff a fuskar tashi, ita kanta tsantsar basirar da ALLAH ya bata ne yasa a gani ɗaya ta gane shi. Duk da dai a na cikin mota babu handkachiff ɗin, amma kuma bai fita ba kamar na wajen. Shima ana cikin motar kai tsaye ya gane shi, hakama Malam Buba. Ɗagowa yay yana kallon fuskarta. “A ina kika gani?”. Ai ko musu batai ba ta nuna masa envelope ɗin data danne da ƙafafu. Hannu kawai ya miƙa mata. Dole takai duƙe ta ɗakko ta miƙa masa. Ya kalla fuskarta sannan ya buɗe envelope ɗin ya ciro sauran hotunan. Mutane ne mabanbanta har guda shida, yanayin inda aka ɗauka hotunan yay mugun jan hankalinsa. Cikin envelope ɗin ya sake maida hannunsa, sai dai babu komai kuma... “Waya baki?”. “Dada wlhy anan na gani”. Tai maganar tana nuna inda ta ɗauka. Jimm yay na tunani. Tuna da kansa ya ajiyesu jiya ya sashi ɗan furzar da iska. Sai kuma cikin sauke murya ya furta, “Little Shadow kina da hannun ɓarna. Bincike ko?”. “ALLAH ba bincike nayi ba Dada. Kawai zan saka kayan nan ne na gani.....” “Shine kika buɗe tunda kin raina Dada”. Idanu ta waro sosai da jin furicinsa na ƙarshe tana girgiza kainta. “Wlhy Dada ban raina ka ba, na tuba bazan sake ba”. Yanda tai maganar hawaye na zubowa ga kunnuwa ta kama ya sashi tsayawa yana kallonta kawai. Dan sai kawai tai masa ƙyau a hakan, har wani babban al'amari na tsarga masa. Dole ya kauda idanun nasa da sauri yana haɗiye yawu. Sai kuma ya bar wajen da sassarfa yana faɗin, “ALLAH ya shirya min ke. Shige ki tafi”. Ai kafin ma ya rufe baki ta kusa ƙofa, shima sai kawai ya kai zaune yana sake kallon hotunan. A ƙasan zuciyarsa kuwa tunanin yake waye yayo masa wannan aiken?. Hannu yakai ya riƙe goshinsa, sai kuma ya miƙe tsaye ya fara kai-kawo. Dole yana buƙatar zuwa UNIT ZERO yanzu nan. Hotunan ya maida cikin envelope ɗin, a ya da ya shigo a haka ya sake fita..........✍️ [1/16, 3:03 PM] Zeenaran 😘: