
Post
Kida a ruwa Book 3 page 18
.....i took out the pictures inside and looked at them one by one. He had to reach the end before he looked up and looked at Dadan. "Surely the drivers who passed by with the goods are there. Because it's the cars, and then it's the desert. Who has this job?". "This is my question Imran." "And who is this? Nagansa with Buba driver?". Instead of answering straight away, Dada went to the private room. Imran must stand up and praise him. Here too they had to enter a password. As they entered, Imran pressed something on the door after it was closed, and the light was mixed. This room is really neat and must be called the secret room. Dada went to a big screen with pictures on it, and immediately took out a picture on the second row and handed it to Imran. Imran stared at me, then he looked at Dada. He showed him those pictures with his eyes. He didn't say a word and he went out again. Fortunately, I was in the car with Dagger's face opening first. Imran looked at the picture and looked at the one that Dada had given him and he just rolled his eyes in desperation. "What?! Criminal 0079?!. Do you really believe that Dabo's investigation has confirmed that they did not die in the plane cr
18
........Lokacin da Dada ke fitowa babu wanda bai bishi da kallo ba a falon. Dan shi bai kalli kowa ba a cikinsu ya fice. Dama sun zagaye Nimrah ne da tambayar miya faru da ita. Dan yanda ya fito ba'a nutsuwarta ba. Duk da tana ta yaƙin danne kanta kuwa. Sai kuma ga Dada ya fito shima ba'a yanda ya shiga ba. Ko kallonsu baiyi ba kuma ya fice. Ta tabbatar musu babu komai, badan sun yarda ba suka ƙyaleta saboda Mammah data girgiza musu kai alamar su barta. Sam Nimrah bata cikin nutsuwarta, burinta ta kira Dagger yanzun nan a waya. Sannan tayi magana da Malam Buba. Amma ta rasa ta yanda zata bar falon ma balle yin hakan....
>>>>>★<<<<<
Gudu sosai Dada ke zubawa a titi dan shi ke driving ɗin da kansa. Kusan lokaci guda suka isa da Imran. Kowa na kammala parking ko gaisawa basuyi ba suka nufi hanyar shiga ciki. Daddy Imran ya saka Password ɗin ƙofar, bayan ta gama turance-turancenta daya sakasu matsuwa ta buɗe. Ko zama basu gama yi ba Dada ya miƙama Imran envelope ɗin. Shima da sauri-sauri ya fiddo hotunan ciki yana kallo ɗaya bayan ɗaya. Sai da ya kai har ƙarshe kafin ya ɗago yana kallon Dadan. “Tabbas drivers ɗin da suka wuce da kayan can ne. Domin kuwa motocin ne, sannan jejin ne. Waye da wannan aikin?”. “Wannan shine tambayata Imran.” “Shi kuma wannan waye? Nagansa tare da Buba driver?”. Maimakon amsawa miƙewa kawai Dada yayi zuwa ɗakin sirri. Dole Imran ya miƙe yabi bayansa. Anan ma sai da suka saka Password. Suna shiga Imran ya danna wani abu a jikin ƙofar bayan ta rufe, a take haske ya gauraye ko ina. Lallai wannan ɗaki ya tsaru, dole kuma a kira shi da ɗakin sirri. Wani ƙaton bakin allo dake liƙe da hotuna Dada ya nufa, kai tsaye ya ciro wani hoto a layi na biyu ya miƙama Imran. Sosai Imran ya zubama hoton ido, sai kuma ya kalla Dada. Da ido yay masa nuni da waɗan can hotunan. Baiyi magana ba shima ya sake fiddosu. Cikin sa'a kuwa na cikin mota da fuskar Dagger ke buɗe ne farko. Imran ya kalla hoton ya kalla wanda Dada ya bashi sai kawai ya zaro idanun cikin razani. “What?! Criminal 0079?!. Kenan da gaske binciken Dabo ya tabbata fitar da su akai basu mutu a haɗarin jirgin ba. Ya ARRAHAMAN. Abin mamaki!. To amma miya haɗa shi da malam Buba kuma?”. “Shi ne ɗan leƙen asirinsa. Sannan Nimrah ta san su”. “Nimrah?! How?”. “Wannan shine tambayata nima? Yarinyar nan ta fara rikita min lissafina Imran. Dan Driver ɗin nan yana ɓoye ainahin fuskarsa ne, tun a ran farko dana fara ganinsa na fahimci hakan. Aikina ne kawai bai biyo takansa ba shiyyasa ban damu da shi ba. Amma ya zama dole yanzu nayi hakan”. Rasa ma abin cewa Imran yayi, dan shi zuciyarsa ma bugawa take da ƙarfi. Ta ina Nimrah zata san Dagger to?..... “Ina buƙatar su Faro yanzun nan. Dan daga nan zuwa 24h nake son information akan waɗan nan drivers ɗin”. Kai kawai Imran ya jinjina masa yana ciro wayarsa ya fita. Dan anan ɗakin kira baya shiga kai tsaye sai idan sune suka buƙaci hakan... Zama Dada yay yana furzar da huci. Nimrah ce kawai ke dawo masa a zuciya da yanayinta na daren jiya da na yanzu, dan ɗazun ya danne kansa ne kawai kada ya rikitata. Yana buƙatar shan coffee ko nutsuwarsa zata dai-daita. Dan haka ya miƙe zuwa inda coffee maker take...
+++++++++++++
“Kulu ina abincin su maigadi?”. Kallonta Kulu dake ɗauke da babbar kular abincin gidan zata kai dinning tayi. Sai kuma ta nuna kular abincin su maigadin da Hinde ke zubawa. “Gashi nan Hinde na zubawa.” “Okay bani nakai musu”. Ba Kulu kawai ba, hatta Hinde sai da ta juyo ta kalli Nimrah. Duk da sun san hakan ba wani abu bane sunyi mamaki. Nimrah da taga sun zuba mata ido ta ce, “Akwai matsala ne?”. Da sauri suka shiga girgiza kawuna. Kulu tai ƴar dariya da faɗin, “A'a kawai dai yau naga Ninah abin arzuƙa take ji a gidan namu”. Ƙaramar dariya Nimrah tayi tana nufar Hinde. Ta ce, “Kulu dama nasan kin saka min ido ai. Kawai so nake na ɗan miƙe ƙafafu, bana son fita hakan nan kuma Mammah tai magana”. Sun gamsu da bayanin nata, dan haka Hinde na kammala zuba abincin ta tura mata kular. “Bari to na ɗauka miki plates ɗin ko?”. “A'a barsu zan dawo na ɗauka”. Cewar Nimrah tana ɗaukar abincin ta fita. Da lafiya lafiya ne zatace ya mata nauyi. Duk da kular ba irin ƙatuwar nan bace ba kuwa. Addu'a take ALLAH yasa ta samu baba driver harta ƙaraso. Aiko ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ganinsa zaune shi kaɗai a kujera yana latsa waya. Daga can gefe maigadi na alwala. Sai Sanda na barci a barandar ɗakinsu ya juya baya. Kai tsaye wajen Malam Buba ta nufa. Duk da yanda take jin bugun zuciyarta na ƙaruwa, hakan ya zame mata jiki a duk lokacin data kusanceshi. Tunma yana damunta har ya daina. Ƙasa takai duƙe tana ajiye kular da gaishe shi. Idanunsa a kanta ya amsa, itama sai ta ɗan ɗago ta kalleshi. Cikin raɗa ta furta, “Baba mutumin kwanaki yazo nemana da bana nan ko?”. Sosai gaban Malam Buba ya faɗi, a ransa yace (A ina tasan hakan?) a zahiri kuwa sai ya fara inda-inda. “Baba ka faɗa min dan akwai matsala ne. Wani munafiki ya ɗauki hotonka kai da shi kuna a mota ya kawo ma Dada......” Kaɗan ya rage zuciyar Malam Buba ya fito ta baki. Ba arziƙi yaji fitsari na neman zubo masa. Ita kanta Nimrah taga firgitarsa a zahiri. Amma sai fahimtarta tasha banban da halin da yake ciki. Ta cigaba da faɗin, “Wlhy kuwa Baba nima hankalina ya tashi. Shiyyasa tun ɗazun nake son fitowa na amshi wayar Sanda na kira shi.” Ai malam Buba bai ma san ya furta, “I...ina da lambarshi U...u..w...a. amshi maza kirashi. Idan kuma ni na kira shi to”. “Baba ka tabbatar wadda zaka sameshi ce yanzu?”.. “In sha ALLAHU”. “To Baba dan ALLAH kayi da sauri kawai ka kirashi kai. Dan Dada ya fita da hotunan, kuma ban san mi zaiyi akai ba”. Kansa ya jinjina mata yana haɗiye yawun dake neman sarƙe masa numfashi. Ita kuma tabar wajen...
★Nimran na shigowa falon Abees daya fito a bedroom ɗin Mammah ya tareta da faɗin, “Aunty Mammah tace kizo”. Kanta ta jinjina masa, sai kuma ta ce, “Muje to”. “Aunty zanje wajen Mamy ne, ta aikoni na kawoma Mammah abu”. Anan ma kan nata kawai ta jinjina masa. Ya wuce ita kuma ta shige bedroom ɗin Mammah. Afeef dake zaune a falon yana binta da kallon harara ya taɓe baki. Sai kuma ya saki murmurshi a fili ya furta, “Shegiya ƴar iska. Na kusa maganin ki ai. Sai na tona muku asiri a gidan nan. Dama na faɗa miki, idan na tashi ramawa sai na miki mai zafin da har ki mutu bazaki manta da ni ba.” Daga haka ya miƙe ya haura staircase.
Nimrah kam ta samu Mammah na waya. Dan haka ta nema waje ta zauna tana jiranta. Sai da ta kammala sannan ta sake miƙewa ta koma kusa da Mammah ɗin. Mammah ta riƙota tana kwantar da kanta a kafaɗarta. Sai da ta shafa fuskarta cikin damuwa ta ce, “Autana duk kin rame min a ido. Inaga ɗurar abinci zan fara miki gaskiya”. Murmurshi Nimrah tayi, ta kama hannun Mammah ta sumbata. Cikin shagwaɓa ta ce, “Mammah idan kikai min ɗura zan zama ƙatuwa ALLAH. Ni kuma bama son ƙiba no da Buddy.” “Uhm-uhm yaran zamani sai a barku. Yanzu miye abin gudu a ƙiba kuma?”. “Mammah ALLAH ƙiba ciwo ce. Mutanenmu ne kawai ke ganin sai kayi ƙiba wai kake jin daɗin rayuwa. Amma ƙiba ai ba abin so bace.” Mammah tai dariya kawai da sake shafa kumatunta. Sai kuma cikin kulawa da iya sarrafa zuciyar yaro ta ce, “Tun juya nake son mu zauna ki bani labari, amma iyayenki sun zagayeki. Bani labarin miya faru da kika fita ranar?”. Daga Ruƙayya har Nimrah basu san ɓoyema Mammah damuwa ko magana ba. Ko Dagger yaci galaba a kan Nimrah ne saboda barazanar kashe Ruƙayya da yay mata. A yanzu ma akwai dalilan da bazata iya sanarma Mammah komai da komai ba. Amma akwai abinda bazata iya ɓoye mata ba. Sannan tana son sanin wanene akai mata aure da shi, idan taji a bakin Mammah kuma zatafi gane abinda ake nufi. Dan haka ta gyara zama ta fara bama Mammah labari tiryan-tiryan. Har batun fashewar bomb bata ɓoye komai ba. Tadai yanke labarin daga inda su Leo suka fiddata a gidan da aka fara kaita, duk abinda ya faru a gaba bata faɗa ba. Ta share hawayen da suka zubo mata, cikin rawar murya ta ce, “Mammah sunce an min aure, kuma assignment ne naje na bincika waye mijin da kaina.” Sosai ƙirjin Mammah ke duka, amma sai ta danne tana murmurshi da kamo Nimrah ta sake rungumewa a jikinta tana share mata hawaye. “To shine kuma abin kuka Autar Mammanta. Ai aure alkairi ne, sannan Rahama ne. Ɗan gata kuma akemawa da ƙarancin shekaru. Ke da Ruƙayya kuma ƴan gatan Mammah da iyayenku ne. Tabbas basuyi ƙarya ba ke matar aure ce. Kuma kina da shekara bakwai aka ɗaura......” “Mammah saboda mi?”. “Saboda ke ƴar gata ce Nimrah. Duk da dai akwai ainahin abinda ya faru a lokacin, amma bazan faɗa miki ba sai kin ƙara girma”. “Mammah waye mijin?”........✍️