Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 19

Post

Kida a ruwa Book 3 page 19

.....with tears in her eyes, she bravely said, "Mamma, you have had a hard time with Dada. But why didn't you stop him from serving in the army since he was first arrested?" Mammah's smiling face rubbed Nimrah's head. "Nimrah, everyone has their own destiny, and everyone has the kind of life that the LORD has planned for him. Your father loves military service, and I am satisfied with his courage for his weak brothers like us that he is trying to protect. Banning is not a problem, it is a prayer." "That's right, Mammah. I also felt today that I want to do military service." Now Mammah laughed and said, "Soldier, Auta?". "Yes Mammah, I want to be like Dada and Daddy". "Well, if they don't, let's pray that ALLAH chooses the best for us." "I swear to God, I will. But Mammah, where are the Bankaura villages where the massacres are taking place? I want to go to the town". Now you are quiet, Mammah is looking at her. She did not tell anything related to them and the matter of Muhammad, even what happened in Bankaura villages was the reason for closing Dada for 8 years. But she did not tell her anything about her, let alone that she is from this area. Nimrah interrupted her thoughts. Save

Standalone post1,610 words

19

........Sosai Mammah tai murmurshi mai yalwa da hango ƙuruciyar Nimrah a fili. Sai kuma ta shafa kanta. “Miyasa kike son ji tun yanzu? Kiyi haƙuri zaki sanshi. In sha ALLAHU kuma zakiyi farin ciki.” Kai Nimrah ta jinjina kawai tana sauke ajiyar zuciya. Sai dai taso tasan wanene mijin, amma bazata iya jayayya da Mammah ba. Zata cigaba da haƙuri, da juriya har lokacin da Mammah tace ɗin yayi. Mammah data fahimci halin da take ciki, sai ta ƙara gyara zama ta shiga lallashinta da nasiha mai tsada da daraja. Ta yanda a hankali komai ke shigar Nimrah tamkar ruwan allura a jijiyoyin jiki. Daga ƙarshe Mammah ta fara bata labarin tarihin rayuwarta. Ai gaba ɗaya sai Nimrah ta shagala, sai dai daga lokacin da tazo gaɓar rasuwar Baba Abdul-rasheed da ciwon Mama Yakura zuwa rasuwarta duk Nimrah ta rikice da kukan tashin hankali, ita kanta Mammah hawaye take, tama kasa ci-gaba. Sai da sukai kuka sosai sannan Mammah ta ƙarasa mata har ƙarshe lokacin da suka dawo garin nan da zama. Nimrah ta share hawaye, idanunta jajur ta furta, “Mammah kun sha wahala ke da Dada. Amma miyasa tun sanda aka rufeshi na farko baki hanashi aikin soja ba?”. Fuskar Mammah da murmushi ta shafa kan Nimrah. “Nimrah kowanne bawa da irin ƙaddararsa, kowa kuma da irin rayuwar da UBANGIJI ya tsara masa. Dadan ku na son aikin soja, kuma na gamsu da jajircewarsa akan ƴan uwansa marasa ƙarfi irinmu da yake ƙoƙarin bama kariya. Hanashi ba itace masalaha ba addu'a ce komai”. “Hakane Mammah. Nima yau naji ina son nayi aikin soja”. Yanzu kam sosai Mammah tai dariya da faɗin, “Soja fa Auta?”. “Eh Mammah, ina son na zama kamar Dada da Daddy”. “To bazance a'a ba, muyi addu'a ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi”. “In sha ALLAHU zanyi. Amma Mammah a ina shi ƙauyukan Bankaura ɗin da akaima kisan gilla ɗin suke? Ina son zuwa garin”. Yanzu kam shiru Mammah tai tana kallonta. Ta bata labarin komai daya shafi su da al'amarin Muhammad, har abinda ya faru a ƙyauyukan Bankaura daya zama sanadin rufe Dada na shekaru 8. Amma bata gaya mata komai daya shafeta ba balle tasan ita ƴar wannan yanki ce, tayi hakan ne kuma dan tafi son Muhammad ya sanar mata komai da kansa..... “Kinji Mammah”. Nimrah ta katse mata tunani. Ajiyar zuciya Mammah ta sauke. Cikin jinjina mata kai ta ce, “Saboda mi kike son zuwa?”. Nimrah tai murmushi tana haɗiye abinda ke ranta. Cikin nuna rashin damuwa ta ce, “Mammah haka nan kawai. Dan wani ma tunani nake yi...” “Na mi?”. “Zan fara rubutu a kansu. Mammah bayan aikin soja yanzu na ƙara jin ina son zama MARUBUCIYA”.......

×××××××××××

“Wlhy Daddy da gaske nake maka. Har video ma na musu jiya. Ai tun randa ya shiga ɗakinsu da daddare na fara saka musu ido. Sai naga ita ɗayar bata shiga ɗakinsa da daddare kamar yanda wannan shegiyar keyi. Aiko jiya dubunsu ta cika......” “Kaga katse kiran nan ka tura min video ɗin”. Babu musu Afeef ya katse kiran, yana wata ƴar dariyar ƙeta ya tura videon da jiya yay ma Dada da Nimrah batare da sun sani ba. Sai da ya kammala ya juyo yana kallon Hanoon datai tagumi... “Afeef wai baka jin tsoro, mutum nan daga ganinsa wlhy ba imani zai yi ba. Itafa shaidar zina ance sai ka gani da idonka...” “Ke ai dama wawuya ce, dan kina son shi shiyyasa ma kike kamar baki yarda da abinda na nuna miki ba. To kar ki yarda ɗin, ni ina ruwana da wani a addini sai an gani da ido. Sannan da kike wani magana baida imani ya kashe ni mana. Kuma ai itace taja masa, dama na rantse sai na mata abinda bazata taɓa mantawa dani ba.....” “To amma tunda itace ta maka laifin ka rama a kanta mana ba shi ba. Sannan kai ne wawa, kuma ina ji maka tsoron Daddy ya fitar da maganar nan ta dawo cikin gidan nan kaine zaka sha wahala”. Tana gama faɗa ta fice a ɗakin. Da kallo ya bita zuciyarsa na wani irin zafi. Sai kuma yay ƙwafa....

★A ɓangaren Uncle Tasi'u yana kallon video yana faman jinjina kai da sakin murmushi. Jinsa yake rai fess. Dan kuwa ya samu makamin da zai sami abinda yake so gun Adda A'isha. Duk da wani gefen zuciyarsa na gargaɗinsa akan halin Haysam. Amma wadda ke zugashi na dannewa. Fitowa yay daga cikin videon, kai tsaye ya sayi ticket ta online, dan dole ne ya je ƙasar haihuwarsa. Zuwa na bazata a yau ɗin nan. Daɗi sosai yaji na samu jirgi mai tashi nan da awanni goma. Dan haka babu ɓata lokaci ya hau shiri......

>>>>>>>%<<<<<<

Washe gari safiyar juma'a aka sallamo Lailah mai jego, duk da jiya su Nimrah tun yamma har dare suna asibitin tuni suka rikice da farin ciki. Dan sun tattare inasu-inasu sun koma sashen su Lailah gaba ɗaya. Tunda dai jarirai sun zama biyu sai aka raba rigima kowa ya ɗauki ɗaya. Sosai farin cikin kasancewa da babys ya kwashe rabin hankalinsu acan. Sai dai wani kaso na tunanin Nimrah nakan Dada ne. Dan tun fitar jiya da yayi bayan ya amshi hotuna a hannunta har yanzu bai dawo gidan ba. Ga Baba Driver ma tun jiyan bata sake ganinsa ba. Abin ya dameta ƙwarai da gaske, batare da ita kanta tasan dalilin yin hakan ba. Bayan sallar la'asar sai ga Mu'azz ya shigo, dawowarsa kenan daga makaranta. Bai ko shiga sashen Mammah ba yayo nan shima. Suna cikin caftarsu Aunty Shariffa na rabon faɗan akai baƙi ƴan barka. Dole suka fito dan basu waje kasancewar suna da yawa. Mu'azz ne ya takali Ruky sabuwar rigima, hakan yasa ta bishi da gudu. Nimrah uwar zuga ta bisu tana faɗin, “Yauwa Buddy na kada ki raga masa”. Tana maganar ne tana dariya har suka shigo falon. Da yake suna gabanta sun rigata. Ta shigo ta samesu tsaye cak, sai kuma muryar Mammah dake magana kamar cikin ɓacin rai ta daki kunnenta. Itama tsayawa tai dan in kaji Mammah na faɗa an kaita bango ne. “Nace Tasi'u mi kake nufi?!”. Furucin Mammah ya sake dukan kunnuwansu. Sai lokacin Nimrah ta fahimci ashe baƙo sukayi a gidan. Ba kuma kowa bane face Uncle ɗin nan da yazo kwanaki kuma Baban su Finga-fiyau kamar yanda Mammah ta sanar musu. Yana zaune a kujera gabansa da abinci da aka jera a Center table. Sai Mammah da itama ke zaunen tana facing ɗinsa. Da waya a hannunta fuskarta kuwa yanayi ne da zasu rantse basu taɓa gani ba... Gwaggo Khadijah da Gwaggo Alawiyya da suka fito suma saboda tsawar Mammah suka ƙarasa inda suke. Gwaggo Khadijah ta zaune tana riƙo hannun Mammah da faɗin, “Ayi haƙuri Maman Ma'aruff. Mike faruwa ne?”. Maimakon Mammah ta bata amsa sai Uncle Tasi'u ne ya amsa mata cikin ɓacin rai. “Yaya ki barta, na rasa miyasa Adda bata son gaskiya akan yaranta, dan fa kawai nace mata gyara kayanka, shine zai zama sauke mu raba......” “Karka kawo min zancen banza zancen wofi Tasi'u”. Mammah ta katse shi a tsawace fiye da tsawar ɗazun da sai da ta saka su Nimrah zabura. Cikin nuna shi da yatsa tare da wurga masa wayarsa dake hannunta ta cigaba da faɗin, “Mika sani akan yarana da har zaka yanke musu hukunci? Dama ka kawo min yaranka gidana dan su dinga saka maka ido akan al'amarin mu.....” Gwaggo Khadijah da hankalinta ya ƙara tashi ta riƙo Mammah. “A'isha dan ALLAH ya isa haka. Ya kuke abu kamar wasu ƙananun yara, wai mike faruwa ne? Ku fiddani a duhu....” Kuka sosai Mammah ta fashe da shi, ta nuna wayar Uncle Tasi'u dake yashe a ƙasa. “Yaya Khadijah na gaji da halin Tasi'u wlhy, ki faɗa masa in dai ba alkairi ya dawo dashi cikin rayuwata da zuri'ata ba dan ALLAH ya tattara yaransa su koma. Wai ki duba video cikin yaran nan wani ya ɗauka na Muhammad da Nimrah, shine yazo yana zancen banza akan hakan. Wai Muhammad na neman Nimrah...” babu wanda bai razana ba a falon, Mammah ta cigaba da faɗin, “To bari kaji kai da masu ɗaukar Videon ko zaku dawo cikin hankalinku. Nimrah MATAR Muhammad ce. An ɗaura musu AURE tun tana da shekara bakwai. Sai ka sake wani shirin”. Wani irin duka kan Nimrah yayi tamkar an saki irin tsawar nan mai girgiza gari a cikin tsakiyar ruwan da ke sauka da manya-manyan ƙanƙara. Kalaman Mammah suka wani irin sake maimaita kansu a cikin illahirin duk wata ƙofa dake amsa suna ƙofa a cikin jikinta. (Nimrah MATAR Muhammad ce. An ɗaura musu AURE tun tana da shekara bakwai). Ai sai kawai tayi luuuuu zata zube. Da wani irin ihu su Ruƙayya da sukai sumar tsaye dan suma kalmar ta dake su da girgiza su suka zabure kanta. Sai kuma suka tsaya cakk sakamakon ganin Dada da babu wanda zaice ga sanda ya shigo falon, da ga gefensa Daddy Imran ne. Nimrah da ta tafi zata zube ya tare da jikinsa. Yana tsaye ne ƙyam akan ƙafafunsa, hannunsa ɗaya tallefe da bayanta saboda tareta da yayi, ɗayan na cikin aljihu. Sai dai idanunsa da sukai masifar juyewa da wani irin hargitsatstsen yanayi tsaye suke ƙyam akan Uncle Tasi'u da shima ya juyo wajen kamar su Mammah saboda ihun Mu'azz da Ruƙayya... Tuni Hanoon da Afeef da Dayyan dake laɓe sun fito suma. Ganin Dada da basuyi zato ba tunda sun san tun jiya baya gidan tuni ya firgitasu. Dan Afeef ya jiƙe sharaf da zufa ga icayi na neman kufce mas a wando.........✍️

Afeef tsuntsun da yaja ruwa ba shi ruwa ke doka ba🤣. Ka ragema su Mammah aiki 🥱🚶👌.