
Post
Kida a ruwa Book 3 page 21
....."But this man is a conspiracy". "Makiri or a barracks boy". "Who is plotting here, he did what was right. And I am right. This is the kind of president we want." "Hmmm, you're right, you loaded it." Many Facebook groups are also theirs, even if I don't want to see them.... "This is the end of politics for the elderly." "They brought the military into the government." "I think there's something down there." "At least there must be a talk of this man with his power. Look at all the two-faced hypocrites. Go to the X program and see how the country's leaders are talking about the sign of their chest with fire." "Since then, I was laughing as if she was going to kill me. Did you see the illegitimate person walking there as if he was going to let me go? But I saw that he got the right answer saying, "I am a white man. "Hahaaaaa, we are having fun". "The General is giving them fire." He's a bit of a scumbag, he's doing everything he can. And Zaki came into everyone's team and ate his father's ball. Children who don't know who ZAK-SHADOW is should get ready to know him now." "GOD help the General." "Finally there's a human with our developing back bones." "If this person does not fix
21
........Fitar sanarwar shugaban ƙasa baifi da minti goma ba ƙasar ta shiga hayaniya. Kamar wutar lantarki da aka saki a ruwan sama. Wayoyi suna ringing a tsakani musamman manya masu faɗa aji. Screenshots na yawo a tsakanin talakawa. Hashtags na tashi tare da hotunan mazaje biyu da mukaminsu yafi na kowa ɗaukar hankali. Ire-iren sakwanin dake yawo a media sune......
“Chief of Staff? Zak-Shadow???”.
“Wannan ba shine mutumin da aka cire a prison ba kwanakin baya, aka kuma tabbatar ya ajiye aikin soja ɗin ma saboda rashin isashen lafiya?”.
“Imran Abbas NSA? Soja ne fa, ba ɗan siyasa ba!”.
A Twitter (X) ire-iren saƙonnin manya sune,.....
“Janar Tafida ya raina jam’iyya.”
“Wannan naɗin barazana ne ga tsarin dimokuraɗiyya.”
“Ko ya manta da gwamnatin ba tashi bace shi da sojoji, shima alfarma akai masa ne?”.
“ALLAH ya ƙara, bamu an hana mu shi an bashi ba. Saboda ya fimu iya munafunci”.
“Kaɗan ma kenan daga aikin tsohon soja, wataran ma ƴan jam'iyyar duk sai ya koro su ya canja da sojoji”.
“Amma mutumin nan fa makiri ne”.
“Makiri ko ɗan bariki”.
“Miye abin makirci anan, abinda ya dace shi yayi. Kuma ni yamun dai-dai. Wannan shine irin shugaban da muke so dama”.
“Hummm ai dama kune kuka ɗora shi”.
A Facebook groups talawa suma na nasu koda ba za'aji ko a gansu ba....
“Wannan shi ne ƙarshen siyasar tsofaffi.”
“Sun kawo sojoji cikin gwamnati.”
“Ina ganin akwai wani abu a ƙasa.”
“Kaima kasan dole akwai magana mutumin nan da ƙarfinsa yazo. Ai kaga duk ya rikita munafukai masu fuska biyu. Jeka manhajar X kaga yanda manyan ƙasar ke ɓarin zance alamar ƙirjinsu naci da wuta”.
“Ai tun ɗazu ina can dariya kamar zata kashe ni. Wai kaga shegen can mai tafiya kamar zai saki kashi mi yace? Amma naga ya samu amsa dai-dai shi wajen Na bature kasan shi baya barin sai ta kwana gwamnan mu abin alfarinmu”.
“Hahaaaaa anayi muna jin daɗi”.
“Ai Janar yana basu wuta.”
Ai ɗan ƙunar ɓakin wake ne, kan mai uwa da wabi yake yi. Ga kuma ZAKI ya shigo tawagar kowa sai yaci ƙwal ubansa. Yara da basu san waye ZAK-SHADOW ba duk sai su shirya saninsa yanzu”.
“ALLAH ya taimaki Janar.”
“A ƙarshe an samu mutum mai ƙashin mu na baya masu tasowa.”
“Idan wannan mutumin bai gyara ƙasar nan ba, babu wanda zai iya.”
“Mudai nema ALLAH ya gyara ba mutum ba”.
“To ina ruwanka ɗan hau”.
“Ai gaskiya na faɗa. Ya kamata Ku dinga sanin mi kuke rubutawa a media”.
“Anƙi a kiyaye ɗin. Kai wlhy sai na saka a nemomin kai naci uwarka”.
“Wanda ya fasa”.
🤣Haka dai media ɗin ke a rikice taki ina. Talakawa sun kasu gida biyu. Masu kuɗi sun shiga shakku. Masu iko sun shiga firgici. Amma Jam’iyya ba hayaniya suke yi ba. Cikin shiru suke a zahiri, irin shiru na haɗa kai da neman juna a ɗakin meeting na gaggawa.....
Lallai Ƙura ta tashi a ƙasa gaba ɗaya fiye da yanda Janar yay tsammani. Dan wannan kujeru sun sake fito da ƙarfin alaƙar dake tsakaninsa da Imran da Zak-Shadow. Cikin abinda bai wuce minti talatin ba sanarwar tayi bala'in tafiya sama mai ban mamaki. Masu murna nayi, masu mamaki nayi a cikin talakawa. Ɓangaren jam'iyyun adawa sunyi caaa suma fiye da yanda kuka ga sakwanin wasu a sama... A zahirance ka-ce-na-ce ɗin jam'iyyun adawa normal ne, dan abu ne da kowa yasan yana faruwa a siyasar ƙasar kuma dole ne ma ayi. Babbar ƙurar data tashi a cikin gida ga ƴan jam'iyya itace ainahin rikita-rikita, dan cikin abinda bai wuce awa biyu ba suka haɗa meeting da tun kafin su zauna shugaban ƙasa ya samu labari. Dariya abin ya bashi, bai kuma ji abin ya damesa ba. Shi ya gama nashi, ya barsu da nasu a yanzu kam. Tsabar ma yanda yake jin ransa fes kashe duk wayoyinsa yay ya miƙe ƙafa tsakkiyar yaransa cike da nishaɗin da ya ba First Lady Hajiya Zainab Tafida mamaki. Ya haɗa tarzoma da yaƙin baki yazo yana nishaɗi, rikita-rikitar mijinta na ɗaga mata hankali. Fatan ta dai a gama mulkin nan lafiya..
^^^^^^^^^^^^^
“Sam bazai yiwu ba, domin mutumin nan yama maidamu ƴan iska a zahirance.” “Ai mun wuce ƴan iska a wajensa Honorable. Sai dai watsatstsu, wai taya zamu tura mota ta tashi sannan ta koma buɗemu da hayaƙin ta. Halan sojoji ne zasu koma mulkin ƙasar bamu sani ba”. “Ga zahiri ka gani kuwa Professor. Shugaban ƙasa tsohon soja, Chief of staff soja, National security advisor soja, to a ministoci ma da suka rage sai mu jira wasu sojojin zasu shigo.” Yanda suke ta surutai har wani baya tsayawa yaji na wani ya sake harzuƙa manyan jam'iyyar tasu. A fusace shugaban jam'iyya ya furta, “Wai cece kuce ɗin naku zamu ji ko abinda ya tara mu?!!”. Tsitt meeting room ɗin yayi a karo na farko, sai dai kowa fuska a kumbure. Ji suke kamar da suna da iko yanzun nan su zartar da takardar sauke shugaban ƙasa a kujerar nan tashi, sai dai shugaban jam'iyya ya bari kowa ya sarara sannan ya cigaba da magana. “Tabbas munyi kuskuren zaɓar mutumin nan sama da kowa. Sannan munyi kuskuren yarda da shi kai tsaye batare da mun zurfafa binciken gano ainahin abinda ke ransa ba. Kuskure na ƙarshe a jiya muka tafka shi, ya kamata kafin mu sallama masa musan wanene zai bama waɗan nan appointment ɗin ko kuwa Barrister?”. Yay maganar ƙarshe yana kallon wani kamilallen mutum dake gefensa. Tunda ake cecekun baiyi ko tari ba, bama shi kaɗai ba akwai waɗanda da yawa basu ce ba dan su basuga abin tada jijiyar wuya ba anan. Hakan ta faru ne kuma sakamakon su zukatansu a tsarkake suke akan siyasar dama can. Barrister yaja numfashi da sauke ajiyar zuciya sannan ya gyara zamansa da ƙyau. Idanunsa na bin kowa da kallo kafin ya furta, “Chairman ba lallai tunani na ya zama irin na kowa ba, amma a nawa ra'ayin ni banga abinda ba daidai ba anan. Na farko dai mune muka gindaya sharaɗin shugabanci 60-40. Duk da yaja kamar yanda aka saba yazo ya sakar mana. Ba kuma hakan na nufin bashi da ra'ayin kansa bane ba ko bashi da wasu buruka a cikin mulkinsa. Tunda har ya amshi namu buƙatun, ya kuma fara bada kujerun ga dukkan wanda muka zaɓa way note shima mu bashi tashi damar. Sannan mutanen nan biyu fa da ake magana a kansu mutanen kirki ne, mu cire batun ɓata su da akayi a baya, mu kalli gudunmawar da rawar da suka takama ƙasar musamman akan rikicin shekarun baya da yaso kassara mana ƙasar. Shin bayan wannan akan aikinsu akwai wani kuskuren da zai sa mu ƙyamace su ne?”. Shiru hall ɗin yayi kamar ruwa ya cinye su. Masu zuciyar gaskiya irin tasa nata jinjina kawunan gamsuwa. Ruɓaɓɓu masu manufa zukatansu na harzuƙa. Dan wasu a cikinsu sun so kujerar a bayan fage basu samu ba. Wasu kuma a bayyane, wasu ko yaran manyan shegun ne ƴan ƙunyar duhu. Wani matashin dattijo da bai wuce arba'in ba ya katse shirun da faɗin, “Tabbas gaskiya Barrister ya faɗa, sannan ya farkar damu abinda idanunmu ke neman rufewa a kai. Haysam Abdul-rasheed Shehu da Imran Abbas basu da wani mummunan record na rayuwa idan ka cire abinda ya faru shekaru takwas da suka gabata da har yanzu babu mai bugar ƙirji yace gaskiya ne. Sannan suba ƴan siyasa ba balle muce. Ina ga maimakon ɓatama kammu suna da biye jam'iyyun adawa kawai mu goyama Mr President baya akan abinda ya dace. Mu fuskanci waɗancan dake sukarmu a waje yafi rikita kammu a cikin gida har azo a samu rarrabuwar kawuna. Ya mana abinda muke so, shima yayi wanda yake so zance ya ƙare ai?”. A zahiri kowa ya amsa daga waɗan nan jawaban, sai dai a zukata wannan tamkar shine mabuɗin buɗe rarrabuwar kawunan ƴan jam'iyya. Dan meeting ɗin na watsewa wasu suka kafa nasu a bayan fage......
°°°°°°°°°°°°°° °°°°°°°°°°°°°°°°
Tunda ya shimfiɗe ta a gadon idanu kawai ya zuba mata tsawon lokaci. Kafin ya ɗan sauke numfashi da salon ɗan burzoshi ta hanci yana janye idanun nasa slowly. Ruwan dake a drawer ɗin gefen gadon ya ɗauka yasa kaɗan cikin tafin hannunsa sannan ya kai fuskarta ya shafa mata. Nannauyan numfashi ta kawo har jikinta na motsawa na yanayin farfaɗowa. Sai kuma ta koma laƙwas tana ƙara sauke ajiyar zuciya a jere. Fin sakan goma kafin ta shiga motsa idannunta da eyelashes ɗin ke a jiƙe. A kansa ta sauke su, yana zaune kusa da ita gab ya zuba mata nasa firgitattun idanun da a yanzu ta jisu da kaifi fiye da baya. So take ta risinar da nata kota maida ta rufe, amma hakan ya gareta. Sai ma wasu hawaye ne da gudu suka gangaro ta gefen idanun har suna shigewa a kunnenta. Dada da gaba ɗaya yanda take kallonsa da wani irin yanayi kamar na mai roƙon ka tausaya min ɗin nan sai ya ji tana kassara illahirin jarumtarsa da ƙarfin garkuwar jikinsa. Kalaman mahaifiyarta suka shiga dawo masa cikin zuciya da ƙwaƙwalwa tamkar a yanzu ne take jera masa su. Dole shine ya lumshe nasa idanun a yau, tare da motsawa a hankali ya kai hannunsa saman fuskarta ya fara share mata hawayen. Karo na farko ta maida fuskarta gefe alamar bata son share hawayen da yake matan. Dan haka shima ya tsaya kawai yana kallonta. Sai dai bai janye hannun nasa daga fuskarta ta ba. Kukan ta cigaba da yi, ta kuma ƙi juyowa ta sake kallonsa. Motsi lips ɗinsa sukayi kaɗan alamar murmurshi yake son yi, amma dai ya basar bai bari ya bayyana ba. Sai ma hannunta dake saman cikinta daya kamo da ɗayan hannunsa ya rumtse. A salon yanda yay ɗin ya tilasta Nimrah ɗan matse idanunta. Cikin suɓucewar harshe ta ce, “Dadaaaah!”. “Na'am MATAR Dadah!”. A bazata ya amsa kiran da waɗan nan kalmomin da suka sakata tashi zaune a zabure. Jikinta har rawa yake tsabar yanda ta tabbatar daga fa bakin nasa suke. Dan kuwa ya wani zuba mata idanu da kallon da zata rantse bata taɓa ganin yama wani ba a gidan balle ma ita ƴar ficikar nan. Rawa lips ɗinta suke alamar son sake yin magana, ga idanunsu cikin juna amma ta kasa iya furta komai..........✍️ [1/20, 3:46 PM] Zeenaran 😘: