
Post
Kida a ruwa Book 3 page 22
.....!!!" he said putting one finger on his lips as a sign not to speak. As if the one who was thunderstruck couldn't speak, her son, Dadan's case seemed to start to disturb her thoughts. In a kind of slow motion, he brought his face close to hers until their breaths were mixed with each other's. She ran and closed her eyes, although she was not sure what to do. The sound of his breathing in her ear made her feel like she was going to die, especially one of them started talking with a voice that she never knew he had, because of the way the sound came out cold, soft, and his natural behavior of calmness and doing everything in a calm manner. "This DADAN can be a HUSBAND. So Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi is the real HUSBAND Kiddo, if you look at DADA as Dada it is your choice. But every YARD is sewn with the color of HIS THREAD, NAJA'ATU NIMRAHH MUHAMMAD BANKAURA!". Not only her body, even her blood had a kind of tingle that she could feel it going down in the corners of her brain. In a state of narrowing her eyes, she looked at Dada one. He pulled his face away from her ear and brought her back to her face as if their noses were going to connect with each other.. She pushed.....
. 22
........Bai hanata tashin da tai ɗin ba, sai dai a yanda ta tashin sai ya zama sun ƙara samun kusanci. Ƙafafunta ta matse tare da rungumesu da hannayenta. Sai zaman nata ya koma ta cure jikinta waje guda. Shi dai bai motsa ba, ya dai janye hannunsa dake riƙe da nata a lokacin da taje yunƙurin tashin. Cikin sake fashe masa da sabon kuka ta ce, “Dada kana nufin Mammah ba tsokanar Uncle take ba kawai? Kaifa Dadanmu ne, taya za'ace haka. Inama laifin ace Mu'azz aka aura min”. Har cikin rai kalmarta ta ƙarshe ta soke shi. Amma sai jarumtarsa ta danne hakan, ko'a zuciya bai raya komai ba. Ya dai zubama fuskarta da hawaye keta zarya idanunsa da suka sake kaɗewa, itama kallonsa take, so take ya amsa mata gaskiya ne Mammah tsokana take. Amma yaƙi furta komai, bashi da alamar zai ce wani abu. Ta ƙara langaɓe kanta lips ɗinta na rawa alamar son sake magana. Sai dai me, idanunsa da ke neman zubar da duk ƙwarin gwiwar ta ya wani kalar ja luuu kamar zai lumshe sai ya sake buɗesu a kanta. “Shiii!!!” ya faɗa yana ɗaura yatsarsa ɗaya akan lips ɗinsa alamar kar tai magana. Kamar kuwa wadda akaima tsawa ta kasa maganar, dan ita kam al'amarin Dadan kamar ya fara hargitsa mata tunani. Dan da wani irin slow motion ya matso da tasa fuskar gab da tata har numfashinsu na gwamuwa cikin na juna. Da gudu ta rufe idannunta, duk da bata da tabbacin abinda zaiyi. Jin hucin numfashinsa a cikin kunnenta ya sata jin kamar zata shiɗe, musamman daya fara magana a cikinsu da muryar da bata taɓa sanin yana da ita ba, saboda tsabar yanda sautin ya fita da sanyi, da taushi, da kuma ainahin ɗabi'arsa ta nutsuwa da yin komai cikin kamun kai da gadara-gadara. “Shi wannan DADAN zai iya zama MIJI. Dan haka Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi shi ne ainahin MIJI Kiddo, idan kin kalli DADA a matsayin Dada zaɓinki ne. Amma kowane YADI ana ɗinkashi da kalar ZARENSA ne NAJA'ATU NIMRAHH MUHAMMAD BANKAURA!”. Ba tsigar jikinta kawai ba, hatta jininta sai da yay wata irin yamutsawar da har tana jin gangarawarsa cikin lungu da saƙo na brain ɗinta. Cikin yanayin ƙiƙƙifta idanunta dake mar-mar take kallon Dada daya janye fuskarsa daga kunnenta ya maido ta gab da tata tamkar hancinsu zai haɗe kan na juna.. Baki ta turaasa tare da taɓeshi cikin tantsar shagwaɓa hawayen da ita kanta laimarsu kawai taji na gangarowa da gudu akan fuskarta. A zuciyarta faɗi take (Na shiga uku ta tabbata hakan ne kenan. Dada fa ake magana! Wannan zakin da ganinsa ma firgici ne, taya za'ace ni matarka ce. Kai wlhy bazan iya ba kafi ƙarfinta. Yo ko su Uncle Ma'aruff sunfi ƙarfina ai balle kai Dada, kankat ɗin fa ake magana, haba dai wannan zance nauyinsa yayi min yawa, ayyanashi a zuciya kawai firgitani yake. Badan kasancewarsa a gabana ba da tuni ta ƙwala riƙaƙƙen ihun da sai gidan nan ya girgiza....) Dada dake kallonta da karantar abinda take tattaunawa da zuciyarta akan fuskarta ya ɗan taɓe baki. Cikin sake kassarata ya furta, “Bazan hanaki kuka ba, kiyi har ki tabbatar da kin gamsu. Sai dai ki sani, abinda kika ji yana nan a yanda kika jishi, bazai taɓa canjawaba koda a labari ne, sai dai ma nace ki fara shiri Dan zaki shiga lavel 2 ajin sabuwar makarantar ki little Shadow.....” yana kai ƙarshen maganar da sai ka rantse ba daga bakinsa ta fito ba. Dan cike da basarwa da kame kai ya janye jikinsa gaba ɗaya daga nata ya miƙe abinsa yana ɓalle maɓallan rigar jikinsa. Tsabar wani ƙullutu da Nimrah keji a zuciyarta sai ta fashe da kuka tare da fara turza ƙafa da sautin ya sashi tsayawa cak. Sai dai bai juyo ba, bai kuma yi magana ba har sai da ta fashe da kuka da faɗin, “Ni wlhy bana SON...” Wani kalar bugawa zuciyarsa tayi tun kan ta ƙarasa, ya lumshe idanu yana matse yatsun hannunsa cikin juna. Sai dai dai-dai nan ta ƙarasa faɗin, “........KISHIYA ƴar daba”. Ai wani kalar kufcewa numfashin Dada da yay sama ya dawo cikin ƙirjinsa kamar mai farfaɗowa daga mutuwa saboda furicin farko da baiyi tunanin abinda zata faɗa ba kenan. Dariya ma ce taso kamashi yanzu, wato tabbas Imran yayi gaskiya, yanzu dai tana nufin matarsa Nabeeha ce ƴar daba? Sunan data kirata a shekarun baya, hakan na nufin bata manta ba, anya kuwa bai kamata ya fara tsoron al'amarin yarinyar nan ba?. Ƴar firit da ita har tasan wani kishiya, a lallai ya shiga ukun sa.....” “Ni dai Dada kayi maganaaaa!”. Ta ƙara faɗa cike da neman fitina tana ƙara ƙarfin tirje-tirjen ta. Wani kalar juyowa yay a bazatar da ita kanta ganinsa kawai tai a gabanta. Kafin kuma ta tantance a yanda yazo kawai taji ƙananun lips ɗinta cikin nashi. Kaɗan ya rage ta saki fitsari dan firgita. Ta waro idanunta da ƙwayar tai kamar zata faɗo ƙasa. Shima kallon nata yake, sai kuma ya kai hannu a hankali ya rufe idanun nata kawai ya cigaba da kissing ɗinta. Lallai wannan rana takai Nimrah ta kirata a mafi firgici da ruɗani. Abu ne da a duniya koda wasa babu wanda ya taɓa kwatanta mata shi sai Dada. Dada fa ba wani ba. Ya ilahi inama ta sake suma kawai ta huta...
(🤣Nima ji nake kamar na suman Nimrah. Shike nan Dada girma Yayi tangal-tangal. Ba kunya ya matse lips ɗin Kiddo a nashi🙈.)
Sai da Dada ya tabbatar ya huce takaicin lips ɗin nan dake damunsa da surutu da taɓara da rikici. Ya kuma lausasa jikin mamallakinsa sannan ya sake su, tare da janye tafin hannunsa daya rufe mata ido batare daya kalleta ba ya miƙe abinsa daga bakin gadon. Bai ko juya ya kalli sashen da take ba, dan da tasan fitinar tarnaƙin da take tayarwa da wannan lamarin nata da taja har ya kai ga abinda yake ta ƙoƙarin hana kansa da a bargo ta shige tun farko ta rufe kanta kawai zaifi sauƙi. Ƙofar Bathroom daya shiga ya maida ya rufe, tare da jingina a jikinta ya rufe idanunsa. Tabbas idan baiyi da gaske ba Yarinyar nan zata sakashi fara bin titi ne yana surutai....
<<••>><••••><<••>>
“Mammah! Gwaggo!! kuna ina? Shugaban ƙasa ya bama Dada da Yaya Imran appointment”. Muryar Bilal da yaje ɗaukar Uncle Jamilu airport ta karaɗe falon a dai-dai lokacin da hankalinsu ke komawa kan Nabeeha dake layi zata faɗi ALLAH ya taimaka Ruky ta tareta. Sai dai ta mata nauyi, an kuma rasa wanda zai yunƙuro ya taimaka mata su riƙeta. Dan kowa kallon abin yake kamar iskanci ne kawai, ganin haka sai kawai itama Rukyn ta saketa ƙasa timmm😂 tana yarfe hannaye. A dai-dai lokacin Amima da Rayhana ke shigowa sashen. Yayinda a tare Daddy Imran da Uncle Tasi'u suka furta, “Appointment?!”. “Wlhy kuwa, yanzun nan aka sanar. Yaya Imran NSA Dada COS”. “Bilal bamu a buɗe, miye NSA da COS?”. Cewar Gwaggo Khadijah tana yunƙurowa. Shi kam Daddy Imran kamar wanda yay sumar tsaye ma za'ace. Hakama Mammah abin ya daketa. Suko su Biebah tuni sun ɗauka wayoyi. Bilal ya bama Gwaggo Khadijah amsa da, “National Security Advisor shine NSA. Chief Of Staff kuma shine COS Gwaggo. Kujeru ne masu girman gaske da daraja a gwamnatance fa. Hummm wannan gwamnatin tamu ce”. “Tabbas tamu ce Bilalu”. Cewar Yaya Ja'afar dake shigowa shi da Ma'aruff. Kai da ka gansu kasan cikin matsanancin farin ciki suke. Sai ga Ammar shima tare da Uncle Nasiru. Ai tuni an manta da wani batun video an koma farin ciki kamar falon zai fashe. Dan tsabar shaƙiyanci rawa harda su Ma'aruff. Wannan hanayinayar tasu ta saka Nimrah dake sume a ɗakin Dada ƙarfin jan ƙafafunta ta fito kamar mai jin juwa. Yayinda zuciyar Uncle Tasi'u ke faman bugawa a cikin ƙirjinsa. Rayawa yake a ransa (Shike nan A'isha ta sake mun nisa). Oho shi kaɗai yasan yanayi, dan shi da ƴaƴansa ne kawai tsaye ƙiƙam suna kallon yanda falon ya harmutse. Dan suma su Lailah dake fama da jego musamman ita ga CS sai gasu kamar an jehosu dai-dai da sakkowar Nimrah daga upstairs. Tuni Ruky da ta fara ganin Nimrah taje ta tungumeta batare data lura da yanda take a hargitse ba. Dan murna biyu take yi, na samun appointment ɗin iyayensu da farin cikin Ninah ɗinta matar Dadansu. Nimrah ta tura baki da faɗin, “Wai miya faru Buddy?”. “Dada da Daddy aka bama appointment Trouble Queen ɗina. Wayyo ALLAH daɗi kasheni my Ninah matar Dadana.” Idanu sosai Nimrah ta waro tana danne bakin Ruky da hannu, a haka taja hannunta suka shige ɗakinsu. Tana maida ƙofar ta rufe Ruky ta buge mata hannu da faɗin, “Ke ana celebration zaki jawoni nan lafiya?”. Maimakon amsa sai kawai Nimrah ta rungumeta tana fashewa da kuka. “Ruky na shiga uku Dada fa? Wlhy ji nake kamar zan haukace dan tashin hankali. Ruky guduwa zanyi, bazan iya kallon Dada a matsayin miji ba yamin girma, shi uba ne Ruky, duk da abinda ke raina a game da shi shi da Daddy martabarsu bata da misali a zuciyata. Ko su Uncle Ja'afar sun min girma ai balle Dada. Inama laifin su Mu'azz..” Rawa jikin Ruky yake yi, ta kama Nimrah suka ƙarasa bakin gado. Zaunar da ita tai itama ta zauna. Sai ta sake rungumeta. Itama tata muryar na rawa ta ce,..........✍️
ALLAH dai yasa kar Ninah ta tonama Dada asiri a wajen Ruky munga idi, Dan ALLAH ku taro ta ba'a bama aminai wannan labarin🤣🥱🏃🏼♀️.
[1/20, 4:08 PM] Zeenaran 😘: