
Post
Kida a ruwa Book 3 page 23
..... now that it is said that his wife is discovering something that Yaya Mu'azz also does not know. It's because of your marriage that she killed you..." "You're drunk! Say GOD?". "Wlhy I really am. Therefore, if you are going to put this nonsense aside, it is an area that we have been able to eat." "Uhmmm! Ruky, I understand you, but you don't know what this is like. And then you know that I don't want a rival from you. In our system of age marriage, there is no wife. Tuzuru is like that, you have forgotten the husband of the deceased". "This is our system. Now the Lord's plan is being discussed. Besides, you know that Dada will not let you go. My love, forget about any wish to eat the mother of sabada in this house. All the bad things that happened to our parents, we should avenge them. Then we snatched Dadan from her hand and she left the house even crawling, we had to cripple her legs since she was on her feet and cut you off. Besides, God forbid, Bestyna is lame now." Ruky ended the conversation teasingly pulling Nimrah's nose. She slapped her hand and laughed too. That will prove to you how pure their youth is. In a short time, Ruky changed Nimrah's mind about the violence
23
.........“Wace irin magana ce wannan Nimrah? Ni banga abin tada hankali anan ba. Wlhy kunyi matuƙar dacewa da Dada. Wannan ai abin farin ciki ne. Mi zaki yi da wasu su Yaya Mu'azz ana zaune ƙalau. Kefa kike cewa baƙya son auren yaro zaki raina shi, ALLAH kuma ya baki wanda ya dace shine kike faɗar haka? Haba Ninah ki buɗe idon ki ki kalla Dada. Cikakken mutum ainahin nutsatstse, handsome. Ga kwarjini, ga ibada, ga iya wanka ko su Yaya Bilal dake samari bazasu nuna masa iya saka kaya da gayu ba. Ga ilimin addini dana zamani. Idan yana magana ma kawai abin ka tsaya kana kallo ne, to wlhy kallo da idanu ma kawai na Dada na musamman ne. Ke banda ma rashin wayo ai wannan dama ce da zamu dama akan waccan shegiyar matar tasa. Dan wlhy jiya sanda kina ɗakin Dada ke da ita Yaya Mu'azz ya bani labari sosai a kanta da iskancinta. Ashe ta jima tana abubuwa a gidan nan Mammah na hana a ɗauki mataki kanta saboda Uncle Nasiru. Sannan ashe tabar gidan nan ne saboda yankan nan na cinyarki, to sai ma yanzu da akace matarsa ce ke na gano wani abu da shima Yaya Mu'azz bai sani ba. Saboda auren ku ta yanka ki ɗin kenan...” “Kam bu! Ki ce ALLAH?”. “Wlhy da gaske nake. Dan haka in ma zaki ajiye wannan shirmen ki ajiye, fili ne da muka samu aci uwar sabada.” “Uhmmm! Ruky na fahimceki, amma kema kin san abin nan da girma yake. Sannan kinfa san bana son kishiya daga ni har ke. A tsarin mu na auren masu shekaru babu mai mata. Tuzuru dai haka ko mijin matacciya kin manta ne”. “Ke dalla wannan ai tsarin mu ne. Yanzu kuma tsarin UBANGIJI ake magana. To banda ma abinki kin san dai Dada bazai sake ki ba. My love manta da wani burin mu aci uwar sabada a gidan nan. Duk abinda shegiyar can tama iyayenmu mu rama musu wlhy. Sannan mu ƙwace Dadan a hannunta sai ta bar gidan nan koda rarrafe, dan ƙafafun ma sai mun nakasa su tunda kema a ƙafa ta yanke ki. Banda ALLAH ya kiyaye da yanzu Bestyna gurguwa ce”. Ruky ta ƙare maganar da tsokana tana jan hancin Nimrah. Hannun ta buge mata tana dariya itama. Hakan zai tabbatar maka da zallar ƙuruciyarsu. Dan cikin ƙanƙanin lokaci har Ruky ta canja tunanin Nimrah akan tashin hankalin wannan aure. Kawai ma sun koma tsare-tsaren su akan yanda zasu gogema Nabeeha hadda ne.....
Kai ALLAH ya shirya waɗan nan yara, kwana biyu aljanu sun lafa ashe watan dawowarsu ya kama🥱🤣🏃🏼♀️.
••••••••••••••
Da mamaki Dada dake fitowa a bathroom yake kallon Imran dake zaune a ɗakin nasa. Gado ya kalla, dan ya tabbatar anan yabar Nimrah ai, sai kuma ya sake juyowa ya kalla Imran da shima ke kallonsa cike da alamar tambaya. “Wai lafiya?”. “Tana ina?”. “Wace?”. “Ƴarka mana”. “Ai ban sameta a ɗakin nan ba ni kam”. Ɗan jimmm Dada yay na mamaki, sai kuma ya nufi wadrobe ya kama buɗe-buɗe. Imran dake danne dariya ya ce, “Mi kake nema kuma?”. “Ita mana, nasan kaɗan daga aikinta yin hakan ai.” Yanzu kam dole Imran ya dara. “Na gode ALLAH daka fara fahimtar hakan. To kwantar da hankalinka ta fita, dan sai da naga saukarta ƙasa na hauro. Wai kasan mike faruwa ne?”. Ɓoyayyar ajiyar zuciya Dada ya sauke. Sai kuma ya girgizama Imran kai batare da yace komai ba. Waya Imran ya miƙa masa kawai shima. Kamar Dada zai yi magana sai kuma ya fasa, ya amsa kawai yana kallon screen ɗin. “What! Imran mike damun Janar ne?”. “Bala'i mana, da neman takife irin na tsohon soja. Ina ga so yake sai anyi bandar mu a titi hankalinsa zai kwanta. Ya mance siyasa ba gumurzun soja bane a jeji na ayi rai ko a mutu. Cikin awannin da basu gaza biyu ba ya hargitse ƙasar gaba ɗaya”. Karo na farko Dada daya rasa abin faɗa yay murmushin da har haƙoransa na bayyana. “Oh dariya ma abin ya baka?”. “To idan banyi dariya ba kuka kake so nayi Imran. A zahirance Janar ya fimu zama ɗan ta'addan ƙunar baƙin wake. Gaba ɗaya mantawa yake da suwaye mutanen nan a ƙasar nan”. “Wlhy yana sane Haysam. Kawai dai ɗan ƙunar baƙin waken ne kamar yanda ka faɗa.” “Ai ko dole yau mu samesa, dan bazamu iya haɗa wannan aikin dana bayan fage ba”. “Ina bayanka nima kam. Ya za'ayi da yaron nan daya ɗauka videon nan?”. Maimakon amsawa miƙewa Dada yay yana nufar gaban mirror. Hakan yasa Daddy Imran binsa da kallo. “Wannan su Ruƙayya ma ai sun ishe shi. Ka barsu da shi kawai. Uban dama akwai shirin da nake a kansa.” “Bincike kayi a kansa?”. “Dama zan barsa a jikin Mammah ne sakaka ban san waye shi ba a yanzu. Karka manta da abinda ya aikata a baya. Idan ita ta karɓesa mu sai mu karɓesa?”. “Ni a ganina karɓarsa ba wani abu bane. Koba komai ɗan uwanta ne. Tana cike da wannan ƙishin a cikin zuciyarta. Kasan shi ruwan kashe gobara kona gutter aka gani ɗiba ake a kashe”. “Ai ko zan shayar da wannan gobar mamaki, dan ni da fetur zan kashe ta ko gas..” “Hhhh ai kai baka tsoron a mutu ko ai rai. Shiyyasa kai da Janar ɗin ban san wa yafi nemo mana aradu da ka ba”. “A ya fini. Janar fa ainahin fitinannen mutum ne”. Sosai Imran ke dariya yanzun kam. Dada ma murmurshi yake yi. Sai da suka tsagaita Imran yace, “Uncle Jamilu fa ya iso. Uncle Nasiru ma yazo, ya kamata muje ƙasan. Amma yaya kuka ƙare da Daughter?”. Murmushi Dada yayi yana kaiwa zaune. Ya ce, “Hummm”. “Kai malam bani nasha miye wani Hummm.” Dada ya sake sakin murmurshi yana ɗan cizar lips ɗinsa kawai. “Yau kana sani surutu da yawa ALLAH. Bazaka gane bane, yarinyar nan darunta yafi na Janar ɗin ma ai. Wai kasan kuka ta dasa min ita bazata son kishiya”. Ba ƙarmin gwalalo idanu waje Daddy Imran yayi ba. Cikin matuƙar mamaki ya ce, “Nimrah ɗin?”.. “Wlhy karka ji wasa. Shiyyasa ma nai shigewata bayi na barta.” “Tofa babbar magana, kenan dai ta amshi auren?”. “Oho mata, dan tace wai ita dama Mu'azz ne dai ko miye na manta shirmen nata ma ni.” Daddy Imran yay dariya. “Uhmm ai aiki ya sameka. Dan ba'a fara komai ba ma. Ai tunda a haka abin ya tsaya Alhamdullah. Su dai mata duk ƙanƙantarsu sun san kishi...” “Humm ni kaina abin ya girmi kaina ai.” “Dolene ai. Kasan kuwa kana haurowa itama Nabeeha ta yanke jiki ta faɗi, sai lokacin ma duk muka farga da ita. Zakina inaga kayi haƙuri haka nan ka janye fushinka ka fuskanceta itama. Gara ku dai-daita kafin Nimrah ta tare.” “Amma wasa kake yi? Dan a cikin horon dana shirya mata bamma fara komai ba. Bani take ɗauka shashasha ba, saboda mamanta ta ɗaure mata ƙugu. Mu zuba nida ita...” “Ban hanaka horata ba, amma kayi mata kai da ita kawai. Bana son mutanen da basu san mita aikata ba a gefe ko suka manta su kalleka matsayin wanda ke watsar da uwargidansa saboda amarya”. “Matsalar su ce su masu wannan tunanin ɗin. Duk kuma namijin daka ganshi a wannan layin bai yarda da kansa bane ba. Ni ban taso gidanmu naga wani uwargida da amarya ba. Dan haka a gidana ma matana matana ne. Kowacce nada girma da darajar ta, ya rage naki ki riƙe na tayaki riƙewar. Ko ki zubar na tayaki takawa a ƙasa. Ƙyale ni na huta joooouh. Ka cikani da surutu barci ma ni nake ji?”. “Aiko bazakayi shi ba wlhy, tashi ma zakai mu sauka ƙasa.” Hararar da Dada yayi, Imran ya taɓe baki irin kai ka sani ɗin nan.....
===========
“Aunty kuka fa ba shi bane mafita. Tashi zaki ki ƙwaci ƴancinki a gidan nan. Sannan ki cirema zuciyarki tsoron Dada. Idan ba haka ba zai cigaba da takaki yanda ransa ke so.” “Hummm amma Amima ki cire son zuciya. Itama fa da laifinta. Ai ya cancanci yabo ma da salon hukuncin nashi. Idan wani ne ko ƙofar gate ɗin nan bazai bari ta sake takowa ba balle ƴan uwansa. Bai kamata kullum kuna ɗora masa laifi ba ita ku gagara gaya mata gaskiyar nata kuskuren”. Rayhana ta ƙarasa faɗa tana taɓe baki. “Wace irin magana ce wannan Rayhana?”. “Gaskiya mana. Koda yake ku mutanen duniya itace bakwa son ji”. “To ke ki fara gayawa kanki gaskiyar mana mtsoww”. “Iyeee lallai Amimah wai ni kike ma tsaki?”. “An miki ɗin. Kuma in baki da abin faɗa ga hanya nan ki kama gabanki”. Duka Rayhana ta kai mata. Tasa hannu ta tare tana faɗin, “Wlhy kika dakan sai na rama.” Ƙwafa kawai Rayhana tayi, fuuu ta fice a ɗakin tana jefama Nabeeha kallon banza. Itama Amimah rakata tai da harara. Kafin ta maida hankalinta kan Nabeeha dake kukanta har yanzu...
“Aunty kar shirmen Rayhana ya dame ki. Kamar yanda na faɗa miki yanzu lokacin yaƙin kwatar mijinki ne. Kuma in dai kina son cigaba da zama da shi dole kiyi hakan. Yanzu dai kinji da kunnenki, yarinyar nan bata san mijinta bane. Yanzu kuma ta sani, komai zaki iya gani a gareta. Zuwa yanzu dai kinga yanda take da rawar kai. Dan haka baki da wani isasshen lokaci ki nemi Aunty Jiddah na tabbatar zata ɗoraki akan duk shawarar data dace, in har kuma kikayi amfani da ita zaki ci riba”. Tashi zaune Nabeeha tai tana share hawayenta. Murya a dakushe tace, “Amima Jiddah zata iya min dariya idan naje mata da damuwata a yanzu. Tunda a baya tayi iya yinta amma naƙi saurarenta”..........✍️
Barkan mu da dawawa. Fatan kuna cikin ƙoshin lafiya.🙏 [1/21, 3:04 PM] Zeenaran 😘: