
Post
Kida a ruwa Book 3 page 24
..... the leader of the country is always better than anyone else. If you follow them, you will eat the kingdom without you." "Thank you Amimah, the younger one, with the behavior of adults. Let me call Jiddah and ask her to come. Or let's go." "Let's go Aunty. My son, I don't think since they moved to their new house, you have never come. But you should start telling Dada if he agrees. If he doesn't agree, we will find another way". She nodded her head in satisfaction and went to the servants to wash her face... Rayhana was listening to them and biting her lips. Fuuu knocked on the door and declared her bad intentions in her heart about Nabeeha. Her son did not run away, there was no retreat. Aunty Jiddah also saw that before they went, she would go...... Everyone loves it more than anyone else. When we are looking for bad things, we need to pray for them. What if this little thing starts to become ugly for you?) ✨★✨★✨★✨ Son, I understand that you want to get stuck with this noise, let's go out of the room without a plan, son, I forgot". Murm.....
24
..........“Wlhy Aunty nasan Aunty Jiddah bazatai miki dariya ba. Sai dai ma taji daɗin kin fahimci abinda take son ki fahimta. Su Momy dai basu zauna damu ba balle gidajen nasu auren har da zasu fahimtar damu abinda zai fishshe mu. Damuwarsu kawai tara dukiya. Waɗan nan ƙawayen naki kuwa wlhy ba ƙaunarki suke ba. Hasalima wasu kamar suna hassada dake. Ki duba fa randa aka dawo dake yanda suketa ƙananun maganar wai ƴan uwan Dada sunyi kuɗi ba shi ba. Tunda ko gida yana prison suka gyara. Kuma in gaskiya za'a bi su gidan nan suna banbance dukiyarsu akan ta wane-da-wane ce? Komai nasu a haɗe yake, duk wata dai kowa za'a saka masa abinda ya sawwaƙa a account ɗinsa hidimar yau da kullum. Ko su Ammar dake ɗaukar albashi bana jin suna cinye kuɗin su kaɗai. To barshi ma gaskiya suka faɗa, yanzu ba gashi yau shugaban ƙasa ya bama Dadan appointment ba mai girman gaske. Chief Of Staff wasa ne. Duk fa wanda zaiga shugaban ƙasa a fadarsa sai yabi ta office ɗin Dada. Sannan shike da damar ganin shugaban ƙasa a koda yaushe fiye da kowa babu shamaki. Idan kika biye musu zako aci daular nan babu ke.” “Na gode Amimah ƙarama da halin manya. Bari na kira Jiddah nace tazo. Ko kuma mu muje”. “Muje ɗin dai Aunty. Dan bana jin tunda suka koma sabon gidansu kin taɓa ma zuwa. Amma dai ki fara gayama Dada idan ya yarda. Idan bai yarda ba sai mu nemo wata hanyar”. Cikin gamsuwa ta jinjina mata kai tana miƙewa domin zuwa bayi wanke fuskarta...
Rayhana dake laɓe tana saurarensu tai ƙwafa da cije lips. Fuuu tabar jikin ƙofar yana ayyana mugayen ƙudirinta a zuciya game da Nabeeha. Dan ita fa ba gudu babu ja da baya. Aunty Jiddah ma kafin suje ita zata je......
(Wato a wannan rayuwar babu abun mamaki irin halayyar al'ummar wannan ƙarnin, dole ne ma muyita ganin masifu. Kowa dai yafi son ace shine sama da kowa. Wlhy mu dinga bincikar kammu da zukatanmu, da munga abu mara ƙyau na neman mana tasiri mu dage da addu'a sai ALLAH ya wanke mana zukatanmu. Wani abin fa da kaɗan ɗin nan yake farawa sai kaga ya zame maka ƙawa har baka ganin munin abinda kake yin🥲).
✨★✨★✨★✨★✨
“Kulu kefa nake jira. Dan na fahimci kina son laƙewa da wannan hayaniyar data sakamu fitowa a ɗaki babu shiri dan na manta”. Murmushi Kulu tayi da dafa kafaɗar Hinde. “Hinde ki kwantar da hankalinki, ai ni na faɗa miki zan sanar miki ko. Yanzu kinga koba komai gidan da baƙi. Mammah bazata so mu kammala abinci a late ba.” “Hummm”. Kawai Hinde ta faɗa tana cigaba da aikinta. Itama sai Kulu tai dariya kawai ta cigaba da nata aikin. A ranta tana ayyana (Hinde kenan, lokaci da zai yi kisan wacece ni, kada ki damu)..
★_______________★
Mu'azz ne ya katse hirar Ruƙayya da Nimrah. Dan knocking ɗin da yay musu ya saka su yin shiru. A zatonsu Small Mom ce, dan basa son asan shirinsu balle ma Mammah ta hana su. Ganin Mu'azz daya ɗan turo ƙofar ya leƙo kansa ne suka sauke ajiyar zuciya. Doka ne baya shigo musu ɗaki sam sai da ƙwaƙwƙwaran dalili, shima ba shi kaɗai ba. Sai in da Mammah ko Small Mom haka. “Dalla kuna nan ina can ina neman ku, ku fito akwai meeting”. In dai Yaya Mu'azz yace akwai meeting ai wata tsiyar za'a ƙulla. Dan haka duk suka miƙe kowa na neman dan ƙwali. Suna fitowa suka sameshi a ƙofa yana jiransu. Hannunsa ɗauke da plate dake rufe. Ruky takai hannu zata taɓa ya doketa. “Kai Yaya Mu'azz dan ALLAH miye a ciki?”. “Koma miye ai zaki gani. Dalla kumuje abin taɓawa ne na samo mana, dan meeting ɗin yafi daɗi. Ku muje side ɗin su Uncle”. Tunda shugaban ƴan haɗa gwarama yayi kira ai dole mamu subi. Haka suka wuce su Mammah a falo kamar wani abin arziƙin zasuje ƙullowa. Babu wanda ya kulasu, dan iya manyan ne kawai ke magana. Dada da Daddy Imran ma basu kai ga sakkowa ba.
Can inda kujeru suke ƙasan bishiyar dake tsakiyar compound ɗin nasu Yaya Ma'aruff suka nufa. Bayan sun zauna Mu'azz ya gama waige-waigen tabbatar da babu kowa a kusa da su, har maigadi na can jikin gate yana gyangyaɗi, sai ya gyara zama. “Kun san wai minene?”. “A'a sai ka faɗa.” Cewar Nimrah. Mu'azz ya cigaba da faɗin. “Akan yaron nan ne Afeef. Bai kamata mu barshi ba. Dole yaji a jikinsa abinda yayi”. Nimrah ta kalli Ruky tai dariya. Kafin ta ce, “Haba Yaya Mu'azz dama kana tunanin zan barshi ne. Ashe ma shegiya aka haifeni ba uba. Yanzu ba dan akwai aure tsakani na da Dada ba shike nan sai ya min sharri ace mu ƴan iska ne”. A yanda tai maganar zaka tabbatar da zallar ƙuruciya a ciki. Dan shi kansa Mu'azz ɗin kasancewar ya girmesu sai da yay dariya da faɗin, “Eh lallai Ninah, abin ko kunya ma?”. “Yo kunyar mi zata ji, Yaya Mu'azz, kamar ma kana mana baƙin ciki banji ka tayamu murna ba”. Cewar Ruƙayya tana tsare shi da idanu. Yay dariya yana girgiza kai. “Nama fiki farin ciki ai. Kawai yanda abun yazo ne dai. Kinga bama gidan akayi labari Small Mom ta bamu. Amma idan banyi murnar auren Ninah da Dada ba nawa zan yi. Kema ALLAH ya kaimu naki”. “Sai da kai Yaya Mu'azz ɗin mu”. Suka faɗa a tare suna tafawa. “Kai jama'a wlhy yaran nan kun lalace. Yanzu dai muje batun Afeef, miza'ai masa. Dan ina son aci ubansa ta yanda zai san mu gidanmu akwai girmama na gaba.” Ruky ta ce, “Tabbas zancenka dutsi. Amma fa naji kamar Mammah tace ya kwashe su subar gidan”. “Uncle Jamilu ya hana ai. Na kuma tabbatar idan yama Dada magana zai bari shima.” Nimrah ta ce, “Kai Alhmdllh ai mu haka muke so. Amma ina ga yanzu a barsa ya ɗan more weekend ɗin nan a gama suna sai a bajeta. Koya?”. Duk sun gamsu da zancen Nimrah dan haka sukace Yayi. Daga haka suka miƙe zuwa sashen Aunty Shariffa.....
§§§§§§§§§§§§§§
“Ni wlhy gaba ɗaya ka rikitani Oga. Dan ALLAH ka daina kai-kawon nan kazo mu nema mafita. Kazo ka ajiye mu a tsakiyar jeji ga dare na neman yi”. “Mole! Na rantse da ALLAH idan ka dameni zan alburushe kanka da bindigar nan. Kai wai kaine ƙarshen jakanta a ƙauyenku halan?. Dalla malam ka barni naji da damuwata”. Idanu Mole ya zuba masa. Har ya saka hannu a aljihu da nufin shi bari ya alburushe nasa kan kafin shi yayi hakan zuciyarsa ta gargaɗesa. (Karka aikata dan yana da amfani a rayuwarka. Karka damu akwai lokacin da zakai hakan. Bari ka gama sanin sirrinsa kaf musamman na dukiyarsa. Kaga idan ka kashe sa a wannan gaɓar riba biyu gareka. Maye gurbin kujerarsa, da mallake dukiyarsa). Kansa ya jinjina tamkar mai amsa zuciyarsa. Daga haka ya koma jikin motar Dagger ya jingina shiru kawai yana kallon sa. Sun kwashe fin awa biyar a wajen, dan sai da duhun dare yayi sosai sannan Dagger ya nufi motar ya shiga. Da sauri shima Mole ya buɗe ya shiga gefen sa. Dagger ya kallesa a karo na farko. Cikin sassauta murya ya furta, “Lokaci yayi da zaka sanarma Nimrah kai ne mahaifinta. Kuma nan da wata biyu nake son ka ɗaura mana aure”. “Ta yaya Oga? Kuma saboda mi?”. “Saboda tabbas su Oga sunci amanarmu. Na gama karaɗe tunani na kaf na fahimci sune suka saka wasu sukai kidnapping Nimrah ranar. Dan a ranar da aka saketa an shigo da kayan aiki. Abin tambaya anan miyyasa suka saka wasu sukai musu aikin bamu ba? An fara munafuntata ne ta hanyar saka wasu aiki ko yaya?.” “Eh tabbas Oga kuma fa biri yayi kama da mutum. Kenan bayan mu akwai masu yi musu aiki a gidan. Kan uban can kai, wannan ai cin amana ce?”. “Aiko idan sukace zasuyi wasa da wuta zata ƙona su. Dan ni Dagger ba sha-sha-sha bane da zasuci moriyar ganga su yada kwaurenta. Komawarka gidan a yanzu akwai haɗari, dan haka zamu bi ta bayan fage tunda har yanzu bata gano mu su waye ba ka canja kamanni ka bayyana mata kai ne mahaifinta. Ni kuma ka barni da sauran aikin musamman akan su Oga. Zan gano mana koma mi suke shiryawa.” “Babu damuwa, sai dai gaskiya sai mun zauna mun tsara yanda zata kasance. Kasan Zak-Shadow ɗin nan shege ne wlhy. Kuskure ɗaya sai mu afka”. “Babu damuwa mu ƙarasa dai”. Ya faɗa yana tada motar suka ɗauki hanya. Ba ko ina bane kuma sai cikin jejin da suka sake danna kai dan Dagger nada haɗaɗɗen gida a wajen da komai na more rayuwa akwai a ciki. Ga mata ya zuba masu masa hidima sannan karuwansa. Banda wanda ake satowa a kawo masa yara ƙanana yana musu fyaɗe. Dan duk wadda ta shigo gidan ɗayan biyu ne. Kodai mutuwa ta fiddaki, ko ki zama baiwa mai hidima a garesa. Sai irin wanda suka zama yaransa da ake aika su yin ayyuka a cikin gari idan ta kama musamman akan manya. Mole dai duk abin duniya ya damesa, musamman akan batun aure da Dagger yayi tsakaninsa da Nimrah. Eh tabbas ya yarda zai bayyana ma Nimrah kansa. Amma badan tazo hannun Dagger ba, sai dan ya nisantata da ƙasar nan gaba ɗaya. Daga yau kuma zai fara neman wanda zai taimaka masa samun muhalli a ƙasashen maƙwaftan nan nasu. Tunda a yanzu dai haka akwai kuɗaɗe masu nauyi a tare da shi da shi kansa bai san adadinsu ba. Ya kuma tabbatar zasu riƙe rayuwar Nimrah nan da shekara fin goma ma, duk da yana da babban burin da target da yafi haka, babu tantama kuma sai ya cika, dukiyar Dagger sai ta zama mallakinsa shi da Nimransa. Hakama oganninsu lokacin da zai cigaba da tatsar kuɗi a jikinsu yayi, tunda har suka fara juyama Dagger baya hakan na nufin suma sun gaji Da shi..........✍️
Hummmmmmm🥱
[1/21, 3:36 PM] Zeenaran 😘: