
Post
Kida a ruwa Book 3 page 25
..... and to assure them of the importance of friendship. He also praised Mammah's efforts and blessed her for the way she takes care of herself. But he looked at Dada and seeing how he was sitting like he was sleeping, he couldn't ask him anything. But he knows he can hear them all. However, his silence does not mean that there is nothing in his mind. He would not speak to him until they sat alone. So the matter stopped here. But Mammah insisted that the next morning Uncle Tasi'un would take the children home. Dan assured him the truth and she calmed down even if they would come back again. Tasi'u's mind was very excited, he kept begging her and giving her patience. In the same way Hanoon and Dayyan's mind was raised, and Hanoon's son now she doesn't want to live in this kind of house, since the matter of Nimrah was broken, Dada's wife feels her chest as if it will open a bit of violence. Even the cry that she has been crying for a long time is about Dada and not about their father. Likewise, one Dayan put his soul on Ruqayya. Today, after hearing about Nimrah's marriage and what happened, he made up his mind that he will start dating Ruqayya until marriage. Then this issue ruined
25
.........Ran Uncle Nasiru yayi matuƙar ɓaci da jin abinda Uncle Tasi'u ya aikata. Hakama su Ja'afar da akai komai basa nan. Dan yanda Ja'afar ke huci sai ka rantse duka zai kai masa. Sai da Ma'aruff ya riƙesa ma. Shi kansa Uncle Jamilu duk da rashin yawan maganarsa sai da ya tanka. Sannan yay ma Uncle Tasi'un da kunya ya kama dalla-dalla akan auren. Sai dai baya fito ya sanar masa komai daya faru bane. Uncle Nasiru ma faɗa sosai yayma Tasi'u irin wanda bai masa ko kwatankwacinsa ba a wancan karon. Sannan yaci uban Afeef dan saida yasha maruka biyu a wajensa. Hakan ya firgita Hanoon da Dayyan, suka kuma sake fahimtar Uncle Nasiru nada matsayi a wajen babbansu. Tunda ko tari bayyi ba sai ma haƙuri da yake ta bama Uncle Nasiru ɗin da Mammah. Duk bidirin da ake sai ka rantse Dada baya wajen. Amma yana zaune abinsa ƙafa ɗaya kan ɗaya ya jingina da kujerar ya lumshe idanunsa. Gefensa Imran sai Bilal. Bayan Tasi'u yasha faɗa a gaban ƴaƴansa harda su Gwaggo Khadijah Uncle Nasiru ya koma nasiha da tabbatar musu muhimmancin zumunci. Ya kuma yabama ƙoƙarin Mammah da saka mata albarka akan yanda take kauda kanta. Koda ya kalla Dada ganin yanda yake zaune ma kamar mai barci sai ya kasa cemasa komai. Amma yasan dai duk yana jinsu. Sai dai shirun sa ba yana nufin babu komai a ransa ba. Bazai masa magana ba sai sun zauna su kaɗai. Dan haka maganar ta tsaya iya nan. Sai dai Mammah ta kafe kan washe gari Uncle Tasi'un zai ɗauki yaran su wuce gida. Dan ta tabbatar masa gaskiya sai ta huce koda zasu sake dawowa. Hankalin Tasi'u ya tashi sosai, ya dinga roƙonta yana bada haƙuri. Haka ma hankalin Hanoon da Dayyan ya tashi, dan kuwa Hanoon a yanzu babu inda take son zama irin gidan nan, tunda aka fasa batun Nimrah matar Dada ce take jin ƙirjinta kamar zai buɗe dan tashin hankali. Ko kukan da take tun ɗazun akan Dada ne ba abinda akema uban su ba. Hakama Dayyan daya ƙwallafa ransa akan su Ruƙayya. A yau kuma jin Nimrah nada aure da kuma abinda ya faru sai ya tsarama kansa zai fara soyayya da Ruƙayya har akai ga aure. Sai kuma ga wannan batu ya ruguza musu dukkan shiri....
Hanoon na kuka ta rarrafa inda Mammah take. “Mammah dan ALLAH nidai zan zauna tare dake. Su Dayyan subi Dad ɗin, amma ni nafi jin daɗin zama anan. Kinga ni kaɗai ce mace a cikinsu, wlhy ina shiga kewar abokiyar hira, ga shi dangin Mom basa son muje inda suke ban san miyasa ba”. Duk da Mammah taji tausayin yarinyar sai ta gagara cewa komai. A mamakin kowa kuma a bazata suka ji furucin Dada daya saka kowa kallonsa. “Mammah ki barsu. Kar ki damu da makircin masu makirci, a ƙarshe kece da nasara. Dan kuwa sune ke ƙona kansu da kansu. Bibiyar wani da sharri ba shike nufin ka samu power ba, talala ce kake ma kanka, sannan alkairi kake kawoma wanda kake ganin bai kai ɗin ba. Wawancin wawaye kesa su kasa gane hakan. Idan kuma babu irinsu ai bama gane mun cigaba. Nasarace rayuwa da azzalumi. Kayita sama a gaban idonsa zuciyarsa na ƙara ƙonewa da zama a ƙunci da damuwar yaya zai yi da kai, shi baida tunanin yaya zai cigaba a tashi rayuwar. Kai kuma bama kasan da shi ba. A gama gwagwarmayar duniya aje lahira kaga mizaninka taf da ayyukan alkairi batare da kasan sanda ka tarasu ba. Ko kaga babu zunubanka ko ɗaya ka rasa yaya akayi. To ai ɗayan biyu ne. Kodai a ɗiba daga ladansu a ƙara maka, ko kuma a ɗiba daga zunubinka a ƙara musu idan basu da ayyukan ladar. Dan ni dai Haysam Abdul-rasheed da ƴan uwana, babu yafiya tsakaninmu da masheranta”. Yana kaiwa ƙarshen nan yabar falon gaba ɗaya. Falon yay tsitt, zuciyar Tasi'u nata faman kai kawo, harga ALLAH kalaman Haysam ɗin sun shigesa, bama akan su kawai ba, haƙƙokin ɗunbin al'umma dake kansa da matarsa da a yau tana cikin ƙasa.......
✨★✨★✨★✨★✨
A falo ana wannan cakwakiyar Biebah, Mu'azz, Nimrah na sashen su Lailah ne suna hirarsu. Hirar kuwa duk akan batun auren Nimrah da Dada ne. Abinda ya ke basu dariya yanda bakin Nimrah ya mutu rumus. Ko faɗan da Mu'azz ke takalar ta sai Ruky ke rama mata. Suko su Shariffa na dariya. Ana cikin hakan kira ya shigo wayar Biebah. Dan haka ta miƙe ta shige bedroom ɗin Lailah. Aiko Shariffa da Lailah suka fara tsokanarta suma. Dan soyayyar Faro da Biebah abin mamaki ce. Komai zakaga suna yinsa ne a ƙunshe. Ko su su Aunty Lailah ɗin sun jima kafin su san Yaya Haydar ke son Biebah. Hakama su Ja'afar. Balle su Nimrah da basu taɓa gane komai ba. Idan ma Faro zai zo hira wajenta mafi yawan lokaci Lahadi ne bayan Asr. Su kuma sun wuce islamiyya. Idan yay jinkirin tafiya suka dawo suka samesa a gidan sai ta nuna kamar yazo gaida Mammah ne. Sai da a dawowar nan ta Dada suka fahimta. (Haydar Galadima da ake kira da Faro dai kowa yasan amini ne a wajen Dada da Daddy Imran. Yanada mata har da yarinya ɗaya. Sai dai ALLAH yay ma matarsa rasuwa a wajen haihuwa a lokacin Dada na prison, shi kuma Daddy Imran ya fito babu jimawa. Ya jigatu da wannan jarabawa, dama yana tsaka da rashin aminai biyu kuma, duk da dai shi Imran ya fito lokacin. Daga baya dai ya haƙura ya barma ALLAH komai. Yanzu haka yarinyar na wajen mahaifiyar matar tasa. Shekaru uku kenan kuma da fara neman Biebah, duk da dai da farko ta nuna tsoron hakan saboda kasancewar sa abokin yayunta. Sai da Ammie ta saka baki da Imran cikin hikima sannan ta bada kai bori ya hau. Amma har yanzu ba gaba ɗaya ta iya sakin jikinta da shi ba dan tana masa kallon girmamawa kamar yanda take ma Imran da Dada)..
Anan sukaci abinci, sai wajen goma na dare suka miƙe dan komawa sashen Mammah saboda ganin su Uncle Ma'aruff sun shigo. Dama Nimrah kwance take shiru kamar mai barci, babu abinda ya tsaya mata a rai sai abinda Dada yay mata, kaɗan-kaɗan ta shafa lips tana jin abin kamar a mafarki ya faru, sai dai bata iya bama kowa labari ba, dan bazama ta iya hakan ba. Sai Baby Nasir dake saman cikinta shima yana barci. Ita kuma Babyn Lailah na bayan Aunty Shariffa ne ta goyata dan taji ɗumin baya ana kuma son cibiyarta ya ida faɗuwa da wuri. Kamar Nimrah bazata bada Naseer ba dai ta haƙura ta bada shin suka fito. Sun iske har su Mammah sun shige, sai su Hinde suma sun kammala duk abinda ya dace zasu shige ne. Mu'azz ya haura sama su kuma suka shige nasu ɗakunan....
💦💦💦💦💦💦💦
“Ke dai ƴar wahala ce. Wai bazaki daina ma mutane wannan kukan ba Hanoon. Dama mi zakiyi da shi. Mutum a murɗe. Ita wannan ɗin dake rawar kai ƙila rana ɗaya zai halakata har lahira. Banda ma rashin sanin hakkin ɗan Adam, taya za'a ɗauki wannan ƴar yarinyar da bata cika ko 18 ba a bama mutum irin wannan daya haifi wanda ya ma fita. 16 da wasu watanni fa naji ance. Koma 17 ɗin basu cika cif ba sai watan gobe. Ga uban ƙarfi. Ni wlhy ji nake kamar na kai su human right”. “Tunda baka da hankali ba. Wai Dayyan ina ruwanka. Kodai son yarinyar nan kake yi?”. “To Dad laifi ne idan naso ta. Ai ni ne ma dai-dai ita. Tana 17 ina 28 ya kaga haɗin?”. Sosai Uncle Tasi'u ya saki baki yana kallon sa. Shi bai san irin rainin da yaransa sukai masa ba. Har sha'awar yaga ƴaƴa na respecting ɗin iyaye yake. Jiba dai yau Adda A'isha da nata yaran, sun girma sun zama magidanta amma sai abinda tace sukeyi. Nashi ko gasu nan dai. Dayyan ɗin ne babba amma rashin hankali kamar kiwon tunkiyar wawa. Wani lokacin ma gwara Hanoon ɗin dake mace. Cikin sauke ajiyar zuciya ya ce, “Ya kamata ace kun canja ko yaya zuwa yanzu. Kodan zaman gidan nan da rayuwar da kuke gani masu gidan nayi. Yanzu kuna dai gani badan Haysam ɗin yasa baki ba wlhy sai kun bar gidan daga ni har ku. Kuma kunfi kowa sanin zamanku anan shine rufin asirinmu mu duka. Dan mutumin can ya tabbatar min idan ban biyashi kuɗaɗensa ba bazai bani gidan can ba. Kai a yanzu haka ya saka shi a kasuwa. Shiyyasa ma na biyema Afeef da tunanin ko videon zai taimake ni na samu wani abu wajen Adda na bashi. Ashe shi shashashan babu wani bincike yay abun. Na rasa ina zan saka kaina......” “Hummm Dad duk fa abin nan kai ka jawoshi. Itafa harkar nan yanzu ba wani tafiya take ba. Mutane sun riga sun gane. Na fara koyon yahoo ɗin nan kayi kutun-kutun ka hana. Yanzu ma badan ɗan live ɗin nan na TikTok da Hanoon keyi ba da kayan da zamu saka ma sai sun gagare mu. Ga karatun Afeef ya tsaya”. “To ya kuke so nayi Dayyan. Duk ba kune da uwarku kuka sakani a bala'in nan ba.....” “A'a Dad, mu ka daina saka mana uwa a maganarka. Ta mutu ka barta ta huta kaji da kanka. Kuma mu ɗin ba ƴaƴanka bane. Kasan bazaka iya ɗawainiyarmu ba miyasa ka haife mu?”. “Ni wlhy kuna damuna da surutu. Dad dan ALLAH ƙyalesu. Ni yanzu ka taimake ni kama Mammah maganar Haysam. ALLAH na yarda zanje a matarsa ta uku”. Gaba ɗayansu zubama Hanoon mai maganar ido sukayi, sai dai kowa ya gagara cewa komai. Tausayi take basu ko haushi ma su basu sani ba..........✍️
Hummm Uncle Tasi'u mi kake ɓoye wa ne? Da alama fa wuta ce ta kori ɓera daga rami ashe🥱. To muna biye maji ma gani matar ɗan hau ta zama malamar wa'azi🚶. [1/21, 3:59 PM] Zeenaran 😘: