Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 26

Post

Kida a ruwa Book 3 page 26

.....and Uncle Tasi'u is one of the recipients, then Dada and Imran, Ma'aruff, all four of them. Jaafar, Bilal, Ammar. We greeted each other respectfully, before Haydar's parents presented what they had brought. They asked to wait for a day. Dada said that if there is no problem, the marriage should be done now. There is no one who did not look at him in the hall, if you exclude Imran, Baffa, Uncle Nasiru and Uncle Jamilu who knew about the plan. Haydar's uncle, who was recovering, said, "We thank you for this generosity, Alhaji Haysam. God bless you and we accept it." Hearing this, the others also gave their support, it was the younger brother of his mother, his two brothers and the brother of his wife who died, and he was the younger brother of his father. At that moment, they deposited the dowry and married Haydar Galadima Faro and Habibah Nura in this hall with not less than fifteen people. The greetings were finished and we returned to the issue of Ruqayya and Ammar who were surprised. The son did not know about this plan until Ma'aruff and Ja'afar came to Dada as applicants for their younger brother's marriage to his daughter Ruqayya. Dada directly confronted them, they also

Standalone post1,615 words

26

..........Washe gari asabar. A gidan Mammah kowa ya tashi busy domin shirya tarbar baƙi. Dan yanda tsarin yake ƙarfe sha biyu zasu iso, anan zasuyi sallar azhar. Cikin amincin ALLAH kafin goma sun kammala komai. Babu abinda kake ji sai daddaɗan ƙamshin turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Ke tashi har compound. An gyara falon baƙi tsaff, duk abincin nan da aka haɗa an kaishi can an shirya. Babu wanda yaga Dada a gidan har sai da Daddy Imran ya iso. Lokacin da suke sakkowa daga sama Nimrah najin ƙarar takunsu ta gudu kitchen. Rabonta da Dada tun jiya a ɗakinsa. Wasan ɓuya take da shi. Yanda ta tashi da sauri ta nufi kitchen ɗin yasa Mammah da Gwaggo Khadijah ankara da ita. Sai dai babu wanda yace komai. Dada ma sarai ya ganta, dan sun riga sun kawo jiki sanda take saurin shigewa kitchen ɗin. Kauda kansa kawai yayi da maida hankalinsa ga Imran kamar bai ganta ɗin ba shima...

Alhamdullahi baƙi sun iso su biyar. Sai Baffa mahaifin Daddy Imran da Uncle Nasiru da Uncle Jamilu da Uncle Tasi'u daya maƙale ta ɓangaren masu karɓa kenan, sai su Dada da Imran, Ma'aruff su duka huɗun. Ja'afar, Bilal, Ammar. Anyi gaisuwa cikin mutunta juna, kafin iyayen Haydar su gabatar da abinda suka zo da shi. Sun nema a tsaida rana Dada yace in dai ba damuwa a ɗaura auren a yanzu kawai. Babu wanda bai kallesa ba a falon, idan ka cire Imran, Baffa, Uncle Nasiru da Uncle Jamilu da suka san da shirin. Kawun Haydar dake murmurshi ya ce, “Aiko mun gode da wannan karamci Alhaji Haysam. ALLAH ya bar zuminci mukam mun amince”. Jin haka suma sauran suka bada goyon baya, dama ƙanen mamansa ne sai yayunsa biyu da yayan waccan matar tasa data rasu, sai shi ƙanin mahaifinsa. A take suka ajiye sadaki aka ɗaura auren Haydar Galadima Faro da Habibah Nura a cikin falon nan da mutanen da basu gaza goma sha biyar ba. An kammala ana barka-barka aka koma kan batun Ruƙayya da Ammar da akama suprice, dan sam bai san da wannan shiri ba sai da Ma'aruff da Ja'afar suka matso gaban Dada matsayin masu nemawa ƙaninsu auren ƴarsa Ruƙayya. Kai tsaye Dada ya fuskance su, suma sun ajiye komai na aure dan ya tabbatar musu bazai raga musu ba dama su zo da shirinsu. Ya kuma yanka musu sadaki a wajen tare da faɗin, “Idan kun shirya ku kawo sadaki yanzu a ɗaura kuma, dan na shirya aurar da yarinyata. Amma biki sai sun kammala jarabawa ita da ƴar uwarta nan da wata ɗaya da kwanaki.” Rawa sosai jikin Ammar ya kama yi, sai da Bilal dake ƙunshe dariya ya riƙesa. Suko su Dada da basu san yana yi ba atake Ma'aruff yace sun shirya, idan babu damuwa a musu lamuni a ɗaura nan da awa guda zasu kawo sadaki cash. Amma sai Dada yace ga account number su saka. Shi bai bada ɗiyarsa sai yaji dumus. Ba ƙaramar dariya aka sanya a falon ba gaba ɗaya. Yayinda al'amarin ya sake rikita Uncle Tasi'u dan shikam ya gagara gane alaƙarsu da waɗan nan yara guda biyu. Ja'afar ya sanya kuɗin sadaki a account ɗin Dada. Daga haka aka ɗaura auren Abdul-rasheed Abdul-rasheed Shehu Kobi da amarya Ruƙayya Imran Abbas akan sadaki mai tsoka. Sosai Baffa da Daddy Imran suka ji hawaye ya cika musu ido. Haysam ya wuce ɗan uwa ko amini, shi gudan jini ne. Baffa najin tamkar shine ya haifi Imran da Haysam matsayin tagwaye. Kamar yanda su Bilal kejin Imran an haifeshi a gidansu ne tamkar Dada. Dan basa kallon wannan alaƙar matsayin abota a yanzu sai ta gudan jini. Abinda yaba kowa dariya yanda Ammar ya rarrafo ya rungume Dada yana hawaye. Aiko su Bilal suka fashe masa da dariyar da har su Mammah na joyowa daga falo. Hakan yasa suka fahimci lallai zaman na bada nishaɗi. Baffa ne ya katse yanayin nasu da faɗin, “Indai haka ne inaga maimakon wahalar da kai a gobe a sake wani zaman shima Bilal kawai ayita ta ƙare shi da Ma'u. Sai suci albarkacin juna. Ba ƙaramin daɗi Dada yaji da hakan ba, dan a ransa yaso kawo hakan ya ga dai kar suyi karan tsaye shiyyasa ya daure. Bilal aka mintsini Ammar irin yaro nima fa lokaci yayi ɗin nan. Aiko sai da Ammar yay dariya ga nashi hawayen yana karasa sharewa. Su su Ja'afar farin ciki fal ransu. Ƴan ƙannensu duk sun zama manya. A take yanzu kam Dada ya ajiye komai na ɓangaren Bilal shi kuma. Uncle Nasiru da Uncle Jamilu suka basu auren Asma'u, nan ma aka sake ɗaurawa a karo na uku. Hakan kuma yay dai-dai da kiran sallar Azhar dan haka suka miƙe idan sun dawo aci abincin da aka shirya kuma..

( Rige-Rigi yanzu dai auren falo ake yayi, na massalacin ma zakaga iya dangi ne🥱🚶. Amare ALLAH ya sanya albarka ya bada zaman lafiya. Su Ruky da Small Mom da Ma'u za'a shiga daga cikin🤭🔥💃).

Aurarraki kam sun ɗauru Alhamdullah, sai dai Dada yace su duka ba yanzu za su sani ba. Dan haka koda su Ma'aruff suka shigo an amshi kuɗi an kuma tsaida rana nan da wata ɗaya kawai aka sanar ma kowa. Sai dai Uncle Nasiru da Uncle Jamilu sun ja su Mammah gefe a ɓoye ita da Gwaggo Khadijah da Gwaggo Alawiyya sun sanar musu duk yanda akayi. ALLAH sarki Mammah harda hawayen farin ciki ta share. Jinta take sakayau kamar an sauke mata kaya. Alƙawarin UBANGIJI ya cika ta kammala aurar da ƴaƴan Abdul-rasheed ƴaƴan amana. Yau da Abdul-rasheed da Yakura na raye yaya zasu ji?. Kuka take sosai har sai da su Gwaggo Alawiyya suka koma lallashinta. Duk da suma sunyi irin tunaninta kuma sunyi hawayen tuna ɗan uwa mai zuminci da son kowa irin Yaya Abdul-rasheed. Basu kaɗai ba shi kansa yau Uncle Nasiru sai da yay hawaye. Rayuwarsa da ɗan uwansa, aboki, aminin arziƙi irin Abdul-rasheed da har yanzu bai maye madadinsa ba a wannan duniyar ta dinga dawo masa. Daren jiya sai da yay mafarki da shi sunata hira, ashe wannan alkairin ne na yau. Tuni su Ruky da Nimrah sun rikice da farin cikin zasu sha bikin Small Mom da Aunty Asmy. Harda zagaye Biebah su da Mu'azz suka fara raira waƙoƙi suna rawa abinsu. Daga ƙarshe ma suka kunna waƙar sani martaba ta MINE NE SO MINENE ƘAUNA a wayar Mu'azz suna mata. Dariya su Mammah suke musu, yayinda Ammar ya kafe Ruky da ido yana jin abin tamkar almara ko mafarki. Tsawon shekaru yake danne abun nan a ransa, badan komai ba sai dan yana burin har sai ta kai girma. Hatta Haneef shine ya samesa da uban gargaɗi akan Ruƙayya, har suka nema yin faɗa sai da Aunty Mimi ta shiga tsakani dan a gidanta akai abin. Ita a lokacin ne ma tasan Ammar ɗin na son Rukayya. Sai dai ya roƙeta tai shiru ba yanzu ba sai Ruky ta shiga University. Sai gashi yau cikin bazata su Dada sun masa abinda bai taɓa kawowa anan kusa ba. Caraf kuwa Ruky ta kama Ammar na kallonta, da yake babu man kai bata fahimci a yau salon kallon ya canja ba. Hasali ma zuwa tai gabansa ta zauna tana faɗin, “ALLAH sarki Uncle har ka bani tausayi. Ya naga kayi shiru? ko kana kishi ne Small Mom ta rigaka aure?. Karka damu zamu lallaɓa Dada ni da Ninah kaima a aura maka ko ƴar budur-bazar ce. ALLAH da gaske nake tausayi ka ya kamani. Yanzu fa duk iyayenmu na gidan nan sunyi aure sai kai kaɗai aka bari. Mammah ALLAH shima Uncle Ammar aure yake so a tausaya masa jibi idonsa ma kamar yayi kuka”. Tana maganar ne tana zabga tagumi da kallonsa irin da gaske ya bata tausayi ɗin. Bilal da su Ja'afar suka ƙunshe dariya. Sauran kuwa sun gaza hakan. Gaba ɗaya falon aka fashe da dariya. Ita ko ko'a jikinta. Sai ma ƴar uwar ɗayar ce ta matso suka saka shi gaba su duka. Ganin zasu addabesa ya ɗauki filo alamar zai dake su. Da gudu suka tashi suna dariya suma suka koma inda Biebah tasa hijjab ta ƙudundune kanta saboda waƙar da suke mata kawai sai taji kuka nazo mata. Haka kawai take jin kanta wani iri, harga ALLAH wata ɗayan nan da yayunta sukace an saka jitai ya mata kaɗan, dan ta zata kamar shekara za'a saka ma. Ba kuma taji kukan yazo mata ba sai yanzu da taga massage ɗin Yaya Haydar ya shigo wayarta. Dan wasu tsumammun kalamai ne masu zaƙi da saka zuciya nutsuwa tare da tabbatar mata ta kusa zama Halal ɗinsa ya turo mata. Sun sha bidirinsu har sai da Gwaggo Alawiyya ta korasu ɗaki suka bar Biebah da Uncle Bilal suka huta. Lokacin da baƙi suka wuce su Dada suka shigo basu samesu a falon ba ma......

==============

Bayan wucewar baƙi Dada da Daddy Imran sun kai Baffah gida ne. Daga can suka zauna hira da Hajjo. Basu baro gidan ba sai gab da magriba. Sai da sukai sallar magriba da isha'i suka nufi UNIT ZERO. Ba sufi awa ɗaya ba suka samu saƙon shugaban ƙasa da tun jiya suka tura masa na izinin ganinsa. Shine bai basu amsa ba sai yanzu. Suna ganin saƙon basu ɓata lokaci ba suka bar UNIT ZERO zuwa address ɗin daya tura musu, dan a ƙage suke dama da hakan. Tun a ƙofar ƙaramin gidan da sun jima da sanin nasa ne suka samu dogarinsa na jiransu. Bayan an buɗe musu gate suka shiga ciki. Dogarin shugaban ƙasa yazo ya isar da gaisuwa a garesu sannan yay musu iso ciki.........✍️

[1/21, 4:20 PM] Zeenaran 😘: