
Post
Kida a ruwa Book 3 page 27
..... the offices are too big. They will keep looking at us like..." Wanting to interrupt him, the General smiled a little, a smile like the one who already knew it would be. "Because of the sugar like that, that's why I did it, Imran". Dada didn't say anything, he was just listening to them, but he kept his eyes on the General directly, without contempt, without a challenge. The second time Imran said again, "Sir, this physical title can distract us. We have work behind the scenes." The general bowed his head as he adjusted his seat after putting down his cup of tea. He said in a low voice, but with a heavy heart. "Imran, even if some offices are added after this, I know you can do it. Therefore, nothing will change from your physical efforts, and holding this office will cover our work behind the scenes, all of their minds will return here to throw two birds with one stone. So nothing will change in my opinion. If there is anyone who can change it is him... now they will be looking at your hands, not your heart." Imran blinked for a moment. He understood. Dada also understood. So, for the first time, he said, "But if your soul is long, the party will make noise". The general laug
27
.........Janar Yusuf Shu’aibu Tafida yana tsaye kusa da window ɗin falon duk yana kallonsu har suka shigo. Bai juyo ya kallesu ba har suka zauna. Shayi mai daɗin gaske da aka tanada dogarinsa ya zuba yakai gaban su, sannan ya ajiye na Janar a gefen kujerar da yasan yana zaune kafin shigowarsu. Sai a lokacin Janar ya baro jikin window ɗin shima, idanunsa a kansu yakai zaune a kujerar da yake tun farko dake facing ɗin su. Yanda yake ta gyara fuska zaka san dariya yake gimtsewa. “Da alama taron dangi aka zo yimin dai yau ɗin nan?”. Ya faɗa yana sake kafe su da ido. Karo na farko sukai murmushi da fara gaisheshi. Ya amsa da kulawa yana cigaba da faɗin, “Ina fatan tattauna yanda za'a tafiyar da Offices ya kawo ku, ba tambaya ba?.” Kallonsa duk sukayi, ganin tun a farko ya musu takunkumi akan abinda suka zo da shi. Imran ya kalli Dada na ɗan sakanni, sai kuma ya sake maida kallonsa ga Janar. Ganin yanda har yanzu shima yake kallonsu yasa ya janye, cikin nutsuwa ya furta, “Sir… waɗan nan offices ɗin fa sunyi girma da yawa. Za’a dinga kallon mu kamar......” Cikin son katse shi Janar ya yi murmushi kaɗan, murmushi irin na wanda ya riga ya san hakan zata kasance. “Saboda suga kamar haka ɗin, shi yasa na yi hakan ai Imran”. Dada bai ce komai ba yana sauraren su dai, sai dai ya zuba idanunsa akan Janar kai tsaye, ba raini, ba ƙalubale. A karo na biyu Imran ya sake faɗin, “Sir, muƙamin nan na zahiri zai iya ɗauke hankalinmu. Kasan muna da aikin bayan fage fa”. Janar ya jinjina kansa yana gyara zamansa bayan ya ajiye kofin shayinsa. Murya a ƙasa, amma da nauyi a cikinta ya ce. “Imran ko bayan wannan aka ƙara wasu offices ɗin nasan zaku iya. Dan haka babu abinda zai canja daga ƙwazonku na zahiri, sannan riƙe wannan offices ɗin da shine zai rufe wancan aikin namu na bayan fage hankalinsu duk ya dawo nan mu jefa tsuntsu biyu da dutsi ɗaya. Dan haka babu abinda zai canja nake gani. Idan ma akwai wanda zai iya canjawar shi ne… yanzu su zasu dinga kallon hannunku, ba zuciyarku ba.” Imran ya lumshe ido na ɗan lokaci. Ya gane. Dada shima ya gane. Dan haka a karo na farko ya furta, “Amma ranka ya daɗe kasan Jam’iyya zata yi hayaniya”. Janar yay ƙaramar dariya. “A tun a jiya take a motse, sai dai ko zata harmutse babu canji. Dama nayi ne saboda munafukai zasu motsa. Ƙungiyar duhu zata ɗauka dama ce a hannunta. Mu kuma sai muyi amfani da hakan mu damesu tamkar ana dama fura a ƙwarya”. Janar ya ɗan dakata yana sauke numfashi, sai kuma ya cigaba da faɗin, “Na bar musu hakan. Ku kuma ku biyun… ku zama abin da ba su zata ba.” Shiru ya sake biyo bayan a maganar tasa. Sai kuma ya sake cigaba da faɗin, “Ba umarni ba ne kawai nake bayarwa a gareku ba a wannan daren, alkawari ne na ɗora akan ku biyu matsayin inuwa ɗaya, ba duhu ɗaya ba”. Kawuna suka shiga jinjina masa cike da nuna gamsuwa. Janar ya ɗauki kofin shayinsa dake a kan teburi. “Litinin zaku shiga office dan bamu da lokacin ɓatawa. Amma daga wannan daren… aiki ya fara.” Yanzun ma kawuna suka jinjina masa irin na sojojin da suka san sun shiga yaƙin da ba a rubuta sunansa ba. Daga haka shiru ya biyo baya, Janar na murmushi da shan shayinsa, a ransa yana raya (ba sabon COS kawai aka haifa ba, ba kuma sabon NSA kaɗai ba. Ku makamin ƙare dangi ne waɗan nan sojojin guda biyu. Ina sha ALLAHU sai The two Shadow sun zama makamin tarwatsa munafukai a ƙasar nan....)
××××××××××××××
Washe gari lahadi da yamma su Nimrah na compound suna ƴar ɓurun-ɓurun kasancewar aminansu biyu suma a gidan suka yini yau. Bintu da Feedo. Su Mammah na daga falo suna tasu hirar. Mazan gidan kam zamu iya cewa babu kowa sai Dada. Shima yana ɗakinsa salla kawai ke sakko da shi, dan yau yace yana son ya huta a gida sosai. Su Ruƙayya sun shagala da wasan su sosai cikin matuƙar nishaɗi. Dan sunata guje-guje ne an ɗaure ma Feedo idanu tana faman bulayin neman samun wani ta taɓa amma ta kasa. Sai ma wannan ya taɓata ta nan ya gudu, wannan yaja mata riga. Wannan ya mintsineta suke. Ita ko ta kasa samun sa'ar kama kowa. Zuwa can tsautsayi ya kawo Nimrah ta ja mata riga, mai makon ta gudu sai ta kai hannu zata sake mintsininta. Aiko caraf Feedo ta cafketa. Miko zasuyi idan ba dariya ba. Nimrah na tuttura baki aka ɗaura mata, duk suka gudu domin ɓuya, lokaci-lokaci suna mata irin na Feedo amma ta gagara kama kowa. Sai faman lalube-lalube take kamar sabuwar makauniya. Duk wannan abu da suke yi Rayhana da Amima na barandar sashensu zaune. Sai dai sai faman taɓe baki suke suna zaginsu batare da sanin takamaimai laifin da sukai musu ba. Ga shi kuma babu damar zuwa su taresu faɗa dan sun san yaran tsagerancinsu yafi nasu, tas zasu goge musu hadda sai dai ƴar bayan fage ɗin wai faɗan mai tsoro. Ba Ruƙayya da Nimrah kawai ba, hatta Feedo ɗin da Bintu babu kanwar lasa a ciki. A wannan lokacin Dada ke fitowa a sashen Mammah, sanye yake cikin simple kaya duk baƙaƙe daga wandon har rigar. Sai slippers ɗin ƙafarsa daya kasance ash. Hannunsa ɗaya da files guda biyu da laptop, sai ɗayan riƙe da wayarsa daya manna a kunne alamar magana yake da wani. Tun fitowarsa yaga su Nimrah, amma sai ya basar ya cigaba da tafiyarsa, dan yana son zuwa rumfar bunun dake a compound ɗin can gefe ya sha iska tare da jiran Imran da ya kira shi a waya yanzun akan wani batu mai muhimmanci. Yazo gab da su Nimrah da sam basu san da fitowarsa ba. Ruƙayya ta mintsini Nimrah ta gudu, dan haka take laluben inda zata cafkota tana tafiya. A karo na farko Dada ya kalleta a kaikaice, ya kalla mota da take nufa, kuma ta saitin mirror ɗin gaban motar daya tabbatar idan ta ƙarasa mirror ɗin zata buga da cikinta. Dai-dai Nimrah takai jikin motar, ƙiris ta buga cikinta da mirror ɗin Dada ya shiga tsakkiya, cikin rashin sani ita kuma jin hucin mutum kawai ta tafi gaba ɗaya da nufin riƙe ko wanene sai gaba ɗaya ta faɗa jikinsa. Yanda kanta ya bugi ƙirjinsa da yanda ta faɗo masan yasa bayansa ɗan buguwa da mirror ɗin da ya bata kariya a kansa. Sosai yaji zafi, dan har sai da ya runtse idanunsa tare da yamutsa fuskarsa. Ita kuma a dai-dai lokacin ƙamshin turarensa ya gama gauraye hancinta zuwa brain. Da sauri ta kai hannu ta janye abinda aka ɗaure mata ido da shi. Aiko idanunta caraf a cikin nasa dake kallonta. Da gudun tsiya tai maza ta rufe nata idanun ƙirjinta na bugawa. Rabonta da shi tun ranar juma'a a ɗakinsa. Dan wasan ɓuya take da shi yau kuma ga shi an haɗu a bazata. Jikinta dake tsuma tai ƙoƙarin janyewa, sai dai bisa tsautsayi ta tuzguɗe ƴar ƙafar dole ta sake dawowa jikinsan dai tare da rirriƙesa. Shima kuma da yaji tana neman zubar da su babu arziƙi yasa hannunsa dake riƙe da waya ya tallafo ƙugunta da ƙyau yana manneta da jikin nasa sosai idanunsa akan fuskarta..
Wata ashariya Rayhana ta buga daga inda suke suna kallon komai. Hakama Amima cike da kishin ƴar uwarta ta tayata. Yayida su Feedo suka waro ido waje dan sun san yau Nimrah za taci ƙaniyarta maybe ma harda su. Ruƙayya kuwa idanu ta rufe tana dariya cike da farin ciki. A cikin ranta har da faɗin (Awwwwhh shoshalewa Dada da My Trouble Queen) sai kuma ta ɗan sake leƙo idanunta ta tsakkiyar yatsunta. A dai-dai lokacin Nimrah ke kiciniyar janye jikinta. shi kuma Dada yaƙi sakinta sai ma kallon nata dai da yake yi ƙasa-ƙasa. “Kiddo marayan ALLAH kike son zubarwa a ƙasa?”. Furucin ya suɓuto a bakinsa batare daya shirya ba. Shigarsa kunnen Nimrah kuma ya sata dakatawa daga mutsu-mutsun nata ta kallesa. Lips ɗinta ke motsi alamar son yin magana amma ta kasa. Gashi ya sarƙe idanunsu waje guda ya hanata janye nata da har sun fara tara ruwan hawayen jin matuƙar kunya daya sashi ganin sun ƙara ƙyau. Nasa ya lumshe a hankali tare da sake buɗe su a kan natan dai. Sai kawai Nimrah ta samu kanta da tura masa baki. Bugun da yaji zuciyarsa tayi ya saka shi kauda kansa gefe yana sakinta. Sai kuma ya yinƙura zai bar wajen da faɗin, “Jeki kawo min coffee”. Daga haka yay wucewarsa ya barta da bugun zuciya da tsumar jiki. Dan gaba ɗaya jin kanta take kamar a dokar jeji babu gida gaba babu baya ga ƙaton zaki tsaye a gabanta yana kallonta da lasar baki. Sai da Ruky tazo ta taɓata ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, suna haɗa idanu Ruky ta ɗaga mata gira da kashe mata ido ɗaya tana murmurshi. Harararta Nimrah tayi, Ruky ta ƙyalƙyale da dariya tana kai bakinta saitin kunnenta ta furta, “Madam bar wani borin kunya kin gama more min jikin Babana. Inyeee My Trouble Queen a jikin Dada shoshalewa”. Sai kuma ta fara rairai mata waƙa tana rawa da zagayata.
“Sunanki ne a zuciyata”.
“Ni naki ne Sahibata”.
“Aurenki ne manufata”.
“Hakkin ki ne na baki gata”.
“Wataran watara na, za'a kai ki gidana, matsayin matata. Kece madarata”.
“Wataran watara na, za'a kai ki gidana, matsayin matata. Kece madarata”.
“Na matsu, na matsu, na matsu naga wanan rana!!”.
“Na matsu, na matsu, na matsuuuuu. Nace! na matsu. Na matsu, Na matsu naga wannan rana. Na matsu- na matsuu na matsuuuu.....”
Dukan da Nimrah takai mata ya sata barin wajen da gudu tana dariya. Sukam su Feedo dake isowa yanzu cikin damuwa suke tambayarta Dada bai mata faɗa ba ko?. Kai ta girgiza musu, yayinda cikin shaƙiyanci Ruky tace, “Wane faɗa kuma ana harkar lada”. Sam basu mahimci abinda take nufi ba. Sai ma duka da Bintu takai mata. Nimrah kuma tabar wajen zuwa kawo coffee..........✍️ [1/22, 3:57 PM] Zeenaran 😘: