
Post
Kida a ruwa Book 3 page 28
....but she knows what she will do now. She made a promise to herself that she will never let Nabeeha arrange with Haysam....... ÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷ When Mammah was in the living room, Nimrah went to the kitchen. No one spoke except Aunty Mimi standing behind her. She found her washing a pot, so she asked her a question. "What are you going to do to me?". Pushing her lips, she said, "Mommy Dada said I made coffee for him". (Come to the place) Saying Mimi in the heart. In fact, she smiled and approached where she was saying, "Okay, pour some water and do something else". They don't have any, Nimrah answered her. Before she finished where she was. With the help of Aunty Mimi, the coffee was cooked and the tea was cooked, each one was poured in the right place and she prepared it in a beautiful basket to be taken out of the house, including a little touch of baked snacks, Dada's son does not eat fried things or miye. Even yams or potatoes will be eaten unless they are baked. And he doesn't eat all the time, his food is a set of rules and regulations to build a strong and healthy body. The reason why Nimrah came out before Nabeeha even though her clothes were more than the sugar worker cho
28
........Sosai zuciyar Nabeeha ke tafasa da bayanin Amima. Sai dai batace komai ba har Amima ɗin ta kai ƙarshe. Sai kuma ta ɗora da faɗin, “Aunty wannan dama ce a gareki da zaki je ki tambayesa zuwa gidan Aunty Jiddah. Kinga sai mu tafi yanzu ko anjima ko? Dan gara muyi abinda ya dace da wuri. Na kira Aunty Ismat ma tace anjima kaɗan zata zo”. Ajiyar zuciya Nabeeha ta sauke tana shanye damuwarta ta ce, “Kuma fa haka ne Amima. Bari kiga na ɗan gyara fuskata to. Ita kuma ALLAH ya kawo ta”. “Aunty ai ba gyara fuska ma kawai ba, bari na saka Nana ta dafa shayi ki tafi masa da shi, irin kamar abinda kika kawo masa dama kenan. Ko lemo za'a haɗa da ruwa?”. “A'a a dafa shayin, dan nasan shi da son shayin zai fi son sa. Haysam baya shan kayan zaƙin nan kin manta”. “Af haka ne fa. Yauwa to shirya, bari naje itama na sakata dafa shayin, sai kin fito. Amma dan ALLAH kiyi ƙyau sosai”. Dariyar yaƙe tai mata. Itama ta fice tana murmushi. Rayhana dake ƙofar tsaye yabar wajen tana dariya. Dan harta gama kitsama kanta abinda zatayi yanzun nan. Ai tayi ma kanta alƙawarin bazata taɓa bari Nabeeha ta shirya da Haysam ba.......
÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷
Su Mammah na falo Nimrah ta wuce ta shiga kitchen. Babu wanda yay magana sai Aunty Mimi data miƙe tabi bayanta. Ta sameta tana wanke tukunya, dan haka ta jefa mata tambaya. “Ninah mi zakiyi?”. Cikin ɗan tura baki ta ce, “Momy Dada yace na dafa masa Coffee”. (Anzo wajen) Cewar Mimi a zuciya. A zahiri kam sai tai murmushi da matsowa inda take tana faɗin, “Okay zubo ruwan kizo kiga wani wani abu to”. Babu musu Nimrah ta amsa mata. Kafin ta ƙarasa inda take. Da taimakon Aunty Mimi aka dafa Coffee ɗin aka kuma dafa shayi mai shegen daɗi, kowanne aka zuba shi a inda ya dace sannan ta sakata ta shirya a kwando mai ƙyau kai kace wajen gidan za'a fita da shi, harda ɗan abin taɓawa na snacks da aka gasa, dan Dada baya cin soyayyen abu ko miye. Hatta doya ko dankali in har zai ci sai dai a gasa. Kuma ba koda yaushe ma yake cin ba, dan abincinsa nada tsari da ƙa'idar gina jikin ƙarfi da lafiya..
Abinda yasa Nimrah ta riga Nabeeha fitowa duk da kayanta sunfi yawa acan mai aiki sukari ta zabga a shayin. Nabeeha na ɗan ɗanawa dan taji ko yayi daɗi taji sukarin zau. Ai ko sai da Nana tasha mari a hannunta tana masifa. Dan Dada baya shan sugar kwata-kwata ma shi. Ko zuma sai lokaci-lokaci ba kullum bane. Ko maggi duk yawan abincinsa zakaga baya wuce ɗaya jal a ciki, balle su gishiri ƴan ƙarshen layi. Nana na kuka tana bata haƙuri da faɗin, “Aunty wlhy ban sani bane da bazan saka ba. Dan ALLAH kiyi haƙuri, kuma wlhy kaɗan ma na saka ban san yaya akai ya haura haka sama sosai ba”. Harara Nabeeha ta zabga mata da faɗin, “Dalla naji wanke tukunyar ki sake haɗa wani bana son surutun banza wawuya kawai baƙauya. Banda ƙauyanci uwarki tace kisa sugan baki tambaya ba”. Jiki na rawa Nana ta fara yin yanda tace, sai dai a zuciyarta duk zagin da Nabeeha tai mata sai da ta rama. Tama ƙara mata da wasu da sukafi nata. amma a zahiri tana mamakin yanda akai sugan yayi yawa ɗin dai. Dan tasan kaɗan ta zuba, kuma babu wanda ya shigo kitchen ɗin sai Rayhana. Hakan na nufin ita ta ƙara sugan kenan?. Bata da mai bata amsa, dan haka ta cigaba da aikin dan Nabeeha ta fice falo. Maimakon ita ta amsa ta dafa ɗin dan rashin dabara.. Duk da Rayhana taji haushin haƙarta bata cimma ruwa ba sai ta share, acewarta ai yanzu aka fara wasan...
Dada na zaune a rumfar yana aikinsa hankali kwance lokaci-lokaci ana kiran wayarsa ko shi ya kira ya hango Nimrah na nufo shi cikin tafiya salaf-salaf kamar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki. Su Ruƙayya sun bar compound ɗin tun ɗazun suka shige sashen su Lailah. Daga su maigadi a gate koma muce maigadi kawai, dan tunda Dada ya fito Sanda yay wuff ya shige ɗaki bai sake fitowa ba. Malam Buba kuma kwana biyu baya nan, yace musu tafiya ce ta kamashi matarsa babu lafiya, dan su ya sakama su isar da saƙon gasu Mammah a shekaran jiya da safe. Dan haka babu wanda ya sake bi ta kansa duk da Mammah ta ba maigadi kuɗi ya tura masa ya ƙara ya kula da matarsa. Nimrah na zaune akai hakan, sai ta dinga sauke ajiyar zuciya dan ta fahimci dai Baba Driver maybe ya gudu ne, har komai ya lafa sannan ya dawo. Shi kuma sai yanzu ma yake ji a bakin Mammah daya fito ɗin nan..... “Assalamu alaikum”. Sallamar Nimrah ta saka Dada ɗan ɗagowa tunaninsa na katsewa, kallo ɗaya ya mata ya maida kansa ga wayarsa, sai kuma ya kaita kunnensa yana faɗin, “Dabo kana jina?”. Bata san mi akace daga can ba, ya dai cigaba da faɗin, “Ku tabbatar dukansu sunzo hannunku da rai, koda ta kama zakuyi harbi kar ya wuce ƙafa, hannu ko cinya ba inda za'a mutu ba”. Yanda gaban Nimrah ya faɗi sai da ta ɗago ta kallesa. Suna haɗa ido tai saurin maida nata ta risinar. Shima daga haka ya ajiye wayar, sai kuma ya kalla basket ɗin data buɗe. Ganin kaya sosai daya wuce abinda ya buƙata ya furta, “Ni da nace Coffee, miye da miye haka duk kika haɗo?”. Yanayin da take ciki ta haɗiye, fuskarta da ɗan murmurshi ta masa bayani tana nuna masa komai. Sai ya murmusa da faɗin, “Okay to bani shayin, anjima nasha coffee ɗin”. Jitai ranta ya mata sanyi bai kusheta ba, dama abinda take ta tsoro kenan. Ga shi yama bar abinda yake so yace ta bashi wanda ta kawo batare da yasan da shi ba. Sai taji hakan girmamawa ce yayi a gareta. Dai-dai ta gama zuba shayin ta ɗago zata ajiye masa Nabeeha ta iso wajen. Sallamarta ta saka shi da Nimrah ɗin ɗagowa suna kallonta. Ƙaramar harara ta zuba ma Nimrah. Babu ragi itama Nimrah sai ta taɓe baki tana yamutsa fuska ta ɗauke kanta kamar taga wata bola. Nabeeha da abin ya mata zafi wai ƙaramar yarinya ƴar cikinta na mata wannan iskancin ta haɗiye yawun takaicin ta saboda tuna shawarar Amima. Kanta ta maida ga Dada tana sakin murmushin danne abinda ke taso mata kamar yanda Amima ta bata shawara. “D. Barka da yamma”. Ta faɗa a hankali. “Uhmmm”. Ya amsa mata a taƙaice. Duk da bataji daɗi ba sai ta danne, dan ta fahimci ita mai laifice a garesa, ta buɗe baki zata sake magana motar Imran ta shigo gidan. A kuma dai-dai lokacin Ammar da Adeel suma suke shigowa da ƙafa. Dan tun ɗazun Ammar na tare da su Adeel ɗin kasancewar yanzu sun gama janye ra'ayinsa har estate ɗin su yana shiga musamman weekend, sannan suna fita yawo jefi-jefi. Nan gidan ne dai Adeel bai taɓa zuwa ba sai yau Ammar ya matsa masa da ƙyar akan sai fa ya shigo ya gaida Mammah. Shine fa ya biyoshi suka shigo. Hango Dada kuma ya sashi jan hannun Adeel ɗin. “Ga Dada ma na gida. Muje ka gaida shi, shima Yaya Imran gashi yazo”. Haka kawai Adeel da yayma sashen Dada kallo guda yaji shakkar kamilallen mutumin da kwarjininsa ke cika ido tun daga nesa. Ya ɗan shafa gashin fuskarsa da faɗin, “Abiy ɗinku ne?”. “Eh matsayinsa kenan a garemu. Amma shine babban yayanmu gaba ɗaya. ALLAH yayima Abiy rasuwa tun ina watanni baifi huɗu ba”. Sosai Adeel ya zaro idanun. Sai kuma tausayin Ammar ya bayyana a fuskarsa sosai. Ammar yay murmurshi da faɗin, “Manta kawai. Muje kaji”. Addu'a Adeel yay ya neman gafara ga Abiy. Sannan yay ya ta'azziya ga Ammar. Ammar ya amsa masa da Amin yana godiya. Sannan suka nufi inda Dadan yake da matansa biyu da suka saka shi tsakkiya. Wanda Adeel baiga fuskokinsu ba kasancewar sun juyama ta inda suke baya ne. Isowarsu dai-dai da juyowar Nabeeha da Nimrah dake amsa sallamar Daddy Imran da shima ya iso wajen. Sai ko idon Nabeeha akan Adeel, da shima kamar ance ya kalletan nashi suka sauka a cikin natan. Wata irin girgizawa ƙirjinta yayi, zuciyarta ta buga tamkar zata tarwatse. Duhu ya mamaye ganinta, kunnenta yay irin dummmm ɗin nan kamar an daki ƙarfe a cikinsu. Ai bata ma san ta saki butar shayin hannunta ƙasa ba tsabar yanda illahirin hankalinta yay mugun nisa da gangar jikinta da numfashinta gaba ɗaya..........✍️