
Post
Kida a ruwa Book 3 page 29
.....tse Dada did not see what was happening between Nabeeha and Adeel, but it is better than anyone to understand and analyze everything there. Dan Nabeeha was putting the bottle together, she lifted it up and stole Adeel's glance and stole Dadan's glance, a look that spread to her and she felt as if she was going to urinate there, and her body trembled. Daddy Imran sat down and Nimrah greeted him with a happy smile on her face. And Ammar pulled Adeel's hand and they also came into the booth saying, "Dada. How is Imran, my friend Adeel will greet you". Imran smiled and showed them the remaining two seats. Ammar sat next to Dada and Adeel next to Imran. Then it became Adeel facing Dada, Ammar facing Imran. Being only two cups, Nimrah poured tea for Daddy Imran as well. She looked at Ammar and said, "Uncle, what about now, you're going to eat?". Ammar scolded her by saying, "Ninah, I don't like the business of stinging. What is the matter?". Baki pushed and said, "Uncle, it was difficult to go to the kitchen and come back." Ammar laughed, she was going to talk again. When Dada was at the end of her beating and beating Ammar, one Adeel stood on his neck and said in a harsh voice, "Ki
29
.........Gaba ɗaya kallonsu ya dawo kan Nabeeha da jikinta ke tsuma. Ga butar shayi da shayi tarwatse a ƙasa. Ganin inda take kallo ya saka su sake maida kallonsu wajen. Sai dai banda Dada da tunda yay mata kallo ɗaya ya ɗauke idanunsa kamar bai san abinda ake ba. Cirko-cirko kowa ya sake yi ganin Adeel da Nabeeha ke kallo, yayinda shi kuma Adeel ke kallon Nimrah a yanzu. Wata banzar harara Nimrah ta zabga masa ganin ita yake kallo, ranta a ɓace ta kauda kai ta maida hankalinta ga Dada tana faɗin, “Dada a saka suga?”. Kai ya girgiza mata, sai kuma ya sake kallon Adeel da yake kallonta ta gefen ido. Ganin idanunsa akan Nimrah ne yanzu ya sake tsuke fuska. Cikin farga Ammar ya taɓa Adeel, ya ɗanyi firgigit alamar dawowa hayyaci yana sauke ajiyar zuciya. Imran dake nazartar kallon da Nabeeha kema Adeel shima yay gyaran murya. Kamar wadda ta dawo a suma taja numfashi ta fesar, sai kuma ta fara kame-kamen kaiwa duƙe tana tattara butar shayin data fashe hannunta na rawa. A zahiri zaka rantse Dada bai ga abinda ke faruwa tsakanin Nabeeha da Adeel ba, amma yafi kowa fahimta da nazartar komai a wajen. Dan Nabeeha na haɗa kwalaben waje guda tana ɗagowa ta saci kallon Adeel ta saci kallon Dadan, wani kallo da ya watsa mata sai da taji kamar zata saki fitsari a wajen, sai rawar jikinta ta nema ƙaruwa. Daddy Imran yakai zaune Nimrah na gaishe sa fuskarta da murmushin murnar ganinsa. Shi kuma Ammar ya jawo hannun Adeel suma suka shigo cikin rumfar sosai yana faɗin, “Dada. Yaya Imran ga abokina Adeel zai gaishe ku”. Murmushi Imran yayi yana nuna musu sauran kujerun biyu da suka rage. Ammar ya zauna a kusa data Dada, shi kuma Adeel kusa da Imran. Sai ya zama Adeel na facing Dada, Ammar na facing Imran. Kasancewar kofuna biyu ne kawai Nimrah ta zubama Daddy Imran shayi shima. Ta kalla Ammar cikin ƴar shagwaɓa ta ce, “Uncle kaima fa yanzu sai kace sai kunsha ko?”. Ammar ya ɗan harareta da faɗin, “Ninah bana son harkar rowa. Miye na kandagarkin to?”. Baki ta tura da faɗin, “To Uncle da wahala ne zuwa kitchen na dawo.” Ammar yay dariya, zata sake magana Dada da yakai ƙarshen ƙulewa da shagwaɓar da take ma Ammar ga Adeel daya tsaya masa a wuya cikin kaushin murya ya furta, “Kiddo bar wajen nan”. A yanda yay maganar bama ita kaɗai ba harta Ammar nutsuwa yayi. Imran yay guntun murmushi. Adeel kam jiyay zuciyarsa na girgiza. Dan har tsakiyar rai yaji fitar sautin golden voice ɗin Dada dake fita da ainahin gizagon mazan da basu san kalmar wasa ba. Ya haɗiye yawu da ƙyar yana kallon Nabeeha dake kallonsa cikin roƙo da magiya. Dan ita tashin hankalin da take ciki ma yafi na kowa. Dada daya ƙara ƙuluwa duk da ita Nimrah harta tafi ya watsama Nabeeha kallon gargaɗi itama. Ita kam ko kallo yay tana gane abinda yake nufi ba Nimrah da sai ya furta ba. Da sauri ta bar wajen jikinta na rawa zuciyarta na tsitstsinkewa. Tambayar kanta take, “Ya akai Adeel yasan gidan nan? A ina suka san juna da Ammar? Mi yazo yi gidan?”. Bata da mai bata wannan amsar, babban burinta kawai takai kanta sashensa ta kira Momy a waya......
>>>>>%<<<<<
A ɓangaren ƙungiyar duhu basu samu zama ba sai a yau a wannan yammaci na Lahadi. An samu tsaikon zaman ne sakamakon Oga Jush baya ƙasar da wasu jigajigan tafiyar. Sai a yau suka gama hallaruwa gaba ɗaya. Dan haka ko zaman hutawa basuyi ba akai zaman meeting na gaggawa. Kamar yanda suka saba. A meeting room ɗinsu suke mai zurfi da duhu duk da rana ce kuwa, amma fitila guda ɗaya ce ke haskawa an rufe windows an saki labule. Baka jin komai sai sautin bugawar zukatansu dake tabbatar da ɓacin ransu a bayyane. Wasun su sai zufa suke dan yau ko ac basu kunna ba tabbacin tashin hankalin da suke ciki. Oga Jush, da fuskarsa tafi ta kullum zama kalar firgici cikin umarni ya furta, “Ina buƙatar son jin sanarwar da kunnena”. Raven ya ɗauka wayarsa, kai tsaye ya shiga intanet ya samo videon dake ta yawo har zuwa yau tamkar wutar jeji saboda yanda bakunan ƴan siyasa yaƙi rufuwa daga cecekucen. “…Mr. Haysam Abdul-Rasheed Shehu Kobi is appointed as Chief of Staff to the President. & Mr. Imran Abbas is appointed as National Security Advisor…” Ɗakin yay shiru. Kowa yana jiran cewar Oga, amma yaƙi ya tanka sai da ya mula dan kansa sannan ya furta. “Ministoci nawa ne damu a ciki?”. Kai tsaye Mr Specter dake a tsorace tunda yasan shine ya kawo Janar ɗin ya furta, “Biyar a cikinsu duk namu ne. A wanda za'a sake badawa ma mune mafi rinjaye”. Batare da Oga Jush ya kallesa ba ya bashi amsa da, “Suma sauran duk su zama namu. A shirya vice president zai koma president nan da ƙarshen wannan shekarar”. Babu wanda bai girgiza ba, duk da su dukansu basu san kalmar tausayi ba. Amma furicin Oga na nufin ɗayan biyu ne. Kodai za'a kwantar da Janar yana raye komai sai an masa kamar na baya, ko za'a binne shi cikin ƙasa matsayin gawa. Sai dai babu damar yin koda musu. Amma a wannan gaɓar akwai masu alaƙa da Janar tun kafin wannan ƙungiya, akwai kuma irin su Garba da suka afka kansu ciki duk da suna gidan soja a zahiri. Cikin ɗacin murya Viper ya furta, “Su kuma waɗan ƘAYAR KIFIN fa? Ya haɗa su biyu fa a mafi girman muƙamai.” Cikin fushi Mr Scythe ya amshe zancen kafin Oga ya amsa ma Viper ɗin. “Viper wannan ba siyasa bane ai. Yaƙi ne tsakanin masarautu guda biyu. Dole kuma sarki ɗaya ne zai rayu. Kuma mune”. Black Spider ya ce, “Tabbas maganarka gaskiya ce Mr Scythe. Zak-Shadow bai fito fili ba sai da izini. Kuma idan ya fito… yana nufin an riga an shirya wani abu. Hakan na nufin a yanzu bama buƙatar hargowa ko fito-na-fito da shi. Yaƙin sunƙuru za'a fara. Ta hakane za'a banbance SARKIN da zai karɓi wannan KUKERAR IKON a tsakanin mu da shi”. Karo na farko Mr Specter ya furta, “Ai ni ban taɓa ji da ganin abinda ya girgizani ba irin wannan. A lokacin da naji ji na dinga yi kamar sunan aljanu aka ambata. NSA da COS… inuwa biyu a kusa da shugaban ƙasa. Ni Yusuf Tafida zai ma haka?”. Kafaɗarsa Iron Fang ya dafa, cike da son kwantar da hankali ya furta, “Karka wani damu kanka, ya kawo kansa ramin Damisa ne ai bai sani ba. Mu ma kuma a yanzu dole ne mu sake lura. Saboda idan mun kusanci Tafida, zasu ji. Idan mun matsi Zak-Shadow, zamu ji.” Ƙaramin tsaki Oga Jush yaja. Cike da takaici da zafin furuci ya furta, “Ku daina kallon mukami. Ku kalli abin da yake ɓoye a bayansa.” Ya ɗan tsaya yana jan numfashi, kafin ya cigaba da murya mai zafi, “Wannan naɗin ya tabbatar mana da abu guda… Tafida ya san muna nan.” A take meeting room ɗin ya sake zama tsitt. Wasu suka gyara zama. Raven yay ƙarfin halin faɗin, “Tabbas Oga maganarka nakan hanya, dan wannan abun da yayi tamkar yana son nuna shi KIDA A RUWA ne MAI SON TADA HANKALIN DODO. TO menene mataki na gaba?”. Kai tsaye Oga Jush ya amsa da, “Mu bar su su ji daɗin watan farko na sabon office. Litinin ɗin sabon wata… zamu fara gwada ƙarfin inuwa.” Jikake raf! Raf! Tafi ya karaɗe ɗakin. Wasu na murmusawa a duhu. Cike da shaƙiyanci Black Spider ya fusta, “The two shadows?”. Viper ya amsa masa da, “A’a… Yanzu sun zama targets.” A tare suka fashe da dariya irin ta mugunta da mugun ƙudiri......
<<••••••>><<••••••>>
Kai da kaga yanda Adeel ke mutsu-mutsu a wajen zaka san a takure yake. Ga Dada ya haɗe gabas da yamma ko gaisuwa a daƙile ya amsata. Daga nan ya cigaba da aikin gabansa kai kace yama manta da su a wajen. Sai Daddy Imran ne ke hira da Ammar. Tabbas a wannan gaɓar Adeel jinsa yake ba komai ba. Babu sarauta babu gadara babu fariyya irin ta jininsa. Yo ashe ma idan kaga shege na gwada shegantaka ga wani jinsin mutane irinsa sai a inda yake da ƙarfi da faɗa aji. Dan akwai a inda idan ya aikata ubansa zaici koda kuwa ace a zahiri ya mallaki duniya da dama data wanda yake ganin kaskantattu sai shine mafifici. A cikin mintuna ƙalilan ya fahimci dalilin da ya saka bazai taɓa iya burge mace irin Nabeeha dake fifita soyayya sama da kuɗi ba. Wanda keda wannan tsayayyen jarumin namijin a shi idan ka cire dukiya, kyan fuska da gidan mulki mike gareshi? Sufa irin waɗan nan mazan badan ƙyawu, dukiya ko wani matsayin duniya ake son su ba. UBANGIJI ya gama mallaka musu abinda ba waɗancan abubuwan ba, ko su maza irinsu da suka mallaka sai sun risina musu da jinjinar ban girma. Ya sallama baida abokin faɗa anan, amma zai wajiga rayuwar Nabeeha da Uwarta, dan dole ne suyi aman abinda suka ci nasa. Abu na gaba kwantar da kai, tabbas zai yi biyayya kuma anan ɗin dai domin samun ɗaya tilon sa Nimrah. Dan ya fahimci Nimrah ɗiyar mijin Nabeeha ce kenan. Maybe ma UBANGIJI ya jarabcesa da Nabeeha ɗin ne dan ya kawosa ga Nimrah, ba kuma zai yi sakaci da wannan damar ba. Ko zuri'arsa naso ko basa so, ko zasu sallamashi ma duniya sai ya mallaki Nimrah. Dan zai iya faɗa da kowa akanta, duk tsanani kuma bazai iya sallamawa ba koda a numfashinsa na ƙarshe ne. A yanzu haka yana shirin saye estate ɗin su Yohan ne gaba ɗaya, dan kasuwanci ma yake shirin kafawa a ƙasar saboda yanda yake jin daɗin zama cikinta, wasa ɗan gaske ya shirya yi akan Abu biyu. Nimrah da Hajiya Hasiba da ƴarta Nabeeha koda yaƙin zai ci ƙasar.........✍️
Hhhhhh anayi muna shan shayi, to Adeel bari muga ko wasan naka zai zama abin kallo a gare mu🤣. Ƙasar dai idan bata tashi dan kai ba, to zata tashi da kai a ciki kuwa🥱🏃🏼♀️. [1/22, 4:52 PM] Zeenaran 😘: