
Post
Kida a ruwa Book 3 page 30
.....them at the same time. Pushing the conversation, he said, "What is going on with these children?". Also, Daddy Imran just released the conversation. Then he handed him some papers to keep beside him. "Everything is finished. GOD wanted me to go today when there was a problem. Tomorrow they will close the registration." "Dama Auta said it. It's now since we're done Alhamdullah. When will they start the exams?" "There is no distance in two weeks." "GOD is why we have a destiny to reach. Did Haydar call you?". "Hmm, don't you think I'll forget. He called me and informed me that they found out where the drivers are, and they suspect that the one we know is their Ogan, he is no more than Ojo. However, they are not sure. Soon the officers in white will go out for an operation with Dabo". "I don't think there is any doubt." "Did you work in secret?". Dada let out a broad smile but said nothing. Imran, who was muttering, also said with a nod, "Your devilishness scares me, Haysam." Dada didn't say anything here either. So Imran said again, "Mr. Buba is back?". Kai Dada shook him no. "Are you sure this man is a hypocrite? Now where do we start?". "Don't worry, they will come easily. Now
30
...........“Malam duk kabi ka rikita yaro da wannan kallon naka sai tsuma yake kamar mai tsutsar basir. ALLAH kai mugu ne”. Hararar Daddy Imran Dada yayi, tare da faɗin, “Kai ai duk duniya ba wanda ka raina sama dani. Ni ubansa ne da zai yi tsumar jiki a kaina? Tunda ni mugu ne kai ne na'ibina ai”. Dariya Imran ya shiga tuntsurawa. “ALLAH Serious a rikice yake. Ko Ammar ya sha jinin jikinsa ne shiyyasa yace suje.” “Su suka sani, amma tun wuri ka dakatar da shi zuwa gidan nan inba haka ba kuma huumm.....” “A'a yi haƙuri mu gara ka barshi yazo mu samu abinda muke so. Amma fa yanda Nabeeha ta razana yafi komai ɗaure mun kai, shima yanda yake kallonta kamar sun san juna.” Dada dake kallonsa ya ɗan ciza lips. Ga hannunsa ya dunƙule alamar fushi. Imran daya fahimci halin da yake ciki ya sauke numfashi da faɗin, “Relax! Zak... Mubi komai a sannu, in sha ALLAHU zan sabunta bincike akansa. Dan tabbas ina ji a jikina ba business ya kawo shi ƙasar nan ba kawai.” Idanu Dada ya lumshe tare da buɗesu a lokaci guda. Cikin ture zancen ya ce, “Ya ake ciki da yaran nan?”. Shima Daddy Imran sakin zancen yay kawai. Sai kuma ya miƙa masa takardu da ya ajiye gefensa. “Komai ya kammala. ALLAH ma yaso naje yau ɗin da an samu matsala. Dan gobe zasu rufe registration ɗin.” “Dama Auta ta faɗa ai. Yanzu dai tunda anyi Alhamdullah. Yaushe zasu fara exams ɗin?.” “Babu wani nisa nan da sati biyu ne”. “ALLAH yasa muna da rabon kaiwa. Haydar ya kira ka ne?”. “Humm kaga zan manta ba. Ya kirani yana sanar min kamar sun gano inda drivers ɗin nan suke fa, kuma suna zargin wanda muka sani ne Ogan su, bai wuce kuma Ojo ba. Sai dai basu tabbatar ba, gadai jami'an farin kaya zasu fita operation tare da Dabo”. “Ni bana jin wani shakkun shine.” “Kayi aiki a ɓoye kenan?”. Murmurshi mai faɗi Dada ya saki amma bai ce komai ba. Imran dake murmurshin shima da jinjina kai ya ce, “Aljanancin ka na bani tsoro Haysam.” Dada bai ce komai ba nan ma. Dan haka Imran ya sake faɗin, “Malam Buba ya dawo ne?”. Kai Dada ya girgiza masa alamar a'a. “Kenan ta tabbata mutumin nan munafuki ne? Yanzu ta ina zamu fara?”. “Karka damu, zasu zo hannu cikin sauƙi. Yanzu haka akwai jami'an da nake son ya kasance kan aikin.” “Hakan yayi, sai office. Kasan dai ba fashi dole gobe idan ALLAH ya kaimu mu fara shiga”. “Humm wato Janar ko....?”. Dariya Imran ya sanya. “To ya muka iya, ya riga ya ɗaure mu, kuma tsarin yayi. ALLAH ya ɗora nasararmu akan tasu kawai....” “Amin ya rabbi to”....
💦💦💦💦💦💦
“Momy wlhy na shiga uku.....” “Kamar ya kin shiga uku Nabeeha? Ba sallama ba gaisuwa sai zance shiga uku. Nifa matsalata dake rashin hankali”. “Momy dole nake faɗar haka, Adeel ne fa a gidana.....” Wani kalar rikitowa Hajiya Hasiba tai daga samon gadonta. Sai kuma ta kalla First Lady dake kallonta dan suna tare ne a saman gadon. Ɗauke kai First Lady ɗin tayi, itama Hajiya Hasiba sai ta haɗiye busashen yawin dake neman yanka mata maƙoshi. Cikin tsargawar zuciya ta furta, “Adeel! Nabeeha ya akai Adeel yasan gidanki? Miya kawo shi kuma?”. Nabeeha ta share hawayen dake mata gudu. “Momy ban sani ba. Tare da wannan ƙanin Haysam ɗin suke Ammar. Kuma Haysam na nan dan yanzu haka a wajensa na baro shi. Wlhy Mammah ina son mijina, ina son rayuwar aurena. Idan na rabu da Haysam mutuwa zanyi. Ki taimakeni Momy, ki taimakeni kada Adeel ya lalata min aure na”. “Ki kwantar da hankalinki. Zuwa anjima zan kiraki. Shima kuma zan samesa a masaukinsa kinji.” “Mammah hankalina bazai taɓa kwanciya ba sai naga Adeel ya bar ƙasar nan na har abada”. “Kar ki damu zai barta. Ki saurare ni”. Ƙitt ta yanke kiran, Nabeeha ta zube ƙasa hawaye na cigaba da zuba mata. Wani makirin murmurshi Rayhana dake laɓe ta saki. Dan tabbas wannan shine babban makaminta a yanzu. Dan haka yanzu wasan zai fara......
✨✨✨✨✨✨
“Alhamdullahi Mammah na samo number ɗin Chef Yakudima fa, kin ganta 08135358038. Abin ma farin cikin kwanan nan zata fara Ramadan class ɗinta.” Mammah tai murmurshi tana kallon Biebah. Itama tace, “Alhamdullah, lallai abin yayi dai-dai. Ki mata magana muji yaya tsarin yake. Dan in so samu ne ma ni su dinga zuwa gidanta tana musu practical. Sai dai bamu san yaya tsarin nata yake ba, sannan bamu san ko anan garin take ba. Online class take ko practical ɗin? Duk bamu sani ba”. “Ai Mammah kawai a kirata sai muji yaya tsarin yake. Amma gaskiya bana jin ƴar garin nan ce. Sai dai kiran nata zai sa mu tabbatar.” “Hakan yayi kira tan muji.” Kai tsaye Biebah tai kiran number Chef Yakudima, duk da batai tunanin zata ɗauka ba. Sai dai abin mamaki bugu ɗaya ana biyu na uku ta ɗaga. Cike da fara'a da girmamawa tai sallama. Biebah tai murmurshi tana amsa mata, sannan suka gaisa cikin mutunta juna. Ba Biebah kawai ba, hatta Mammah taji daɗi, dan yanda Yakudima tai ya tabbatar da tasan kima da mutuncin jama'a, haka kuma ake buƙatar duk mai huɗɗa da mutane ya kasance. Koda mutum yazo maka da fuskar rashin tarbiyya, kai maida masa aniyarsa ka mutunta shi sai UBANGIJI ya haɗashi da dai-dai shi a nashi kasuwancin. Dan ko maganar banza da izgili kazo kayi ga bawa saboda wani dalilinka ki sani ka sani ALLAH bazai barka ba wlhy, kuma sai ka biya wannan bashin a randa ake biyan bashin haƙƙoƙi da ayyuka. Cikin iya huɗɗa da mutane Chef Yakudima ta furta, “Sister sai dai ban gane mai magana ba”. “Eh, bazaki sanni ba gaskiya. Sunana Biebah. Na samu number ɗinki a wajen wata friend ɗina Bilyn Abdull. Dan naci wani snacks masu shegen daɗi a bikin Anniversary ɗinta shine nake tambayar waye yayi mata. Ta sanar min kece. Da nazo da shi gida Mamana ta yaba itama sosai”. “Masha ALLAH ina godiya sosai. A faɗama Mama in sha ALLAHU zataga saƙo kuwa a satin nan”. “A Mama na godiya. Dama muna da ƴammata ne guda biyu, muna son su shiga class ɗinki sai dai bamu san yaya tsarin yake ba. Sannan kina practical ne ko Online class?”. “Ina yin practical da, amma yanzu na ɗan dakata saboda wani shirye-shirye da nake kai. Sai online class, dan yanzu haka ma zamu fara Ramadan class in sha ALLAHU”. “Shike nan faɗuwa tazo dai-dai da zama. Yaya tsarin yake?”. “Ina koyar da abinci kala-kala na gida dana waje da arab, girki kala kala dawa Morocco zuwa Saudia. Sannan ina bayar da dessert for business da nayi a gida. Ina koyar da Mocktail’s wanda zakiyi a gida da business. Zan iya baku handles ɗina na media sai ku duba wasu ayyuka na”. “To Masha ALLAH babu damuwa. Ki tura min links ɗin handles ɗin naki. Tare da tsarin shigar dan faka-faka ba wasa muna son su fara ne amare ne. Dan haka komai a taɓa musu dan ALLAH. Idan muka dai-dai ta saina tura miki number ɗin da zaku yi aikin da su.” “Yanzu kuwa in sha ALLAHU. Na gode sosai dana kasance zaɓinku.” Murmurshi Biebah tayi tamkar tana gabanta. Suna yanke kiran sai gashi ta mata magana ta WhatsApp. Handle ɗin ne ta tura mata na...
TIKTOK https://www.tiktok.com/@chef_yakudima_?_t=8oUfeR16r93&_r=1.
YOUTUBE https://youtube.com/@chefyakudima?si=xm2CHdXFnwbUTb7r.
INSTAGRAM https://www.instagram.com/chef_yakudima?igsh=MTg5NnlqcmJ3emJqNA%3D%3D&utm_source=qr.
Ƴan uwa wannan tagomashin alkairi bana Ƴaƴan Dada bane kawai. Kuma fa zaku iya garzayawa faka-faka waɗan nan links ɗin domin ganema idanunku. Sannan ƙofa a buɗe take gareku domin koyon girke-girke daga Chef Yakudima. Girke-girke ne na zamani dana gargajiya, harma dana ƙasashen ƙetare. Zata fara Ramadan class in sha ALLAHU kwanan nan. Kada ku bari ayi babu ku. Girki babbar kima ce ta mace. Duk da an haifi kowace mace da wannan baiwar mu sani wani fa dabgen sai ka koya yanda ake sarrafa shi. Abinci yana ɗaya daga cikin makamin mallake mai gida batare daya shirya ba. Garzaya kar ayi babu ke. Dan bana mu tashi kan masu gidajen nan da kayan daɗin Ramadan class na Chef Yakudima 08135358038 akan farashi mai sauƙi. Biyan buƙata ai yafi dogon buri masoyan Bily. Karki bar kanki a tukunya. Kullum daga shinkafa, sai taliya da tuwo a gidanki. A'a Hajiya Balki ai an wuce wannan ƙarnin tuni. Mata sun gane yanzu. Idan kuma kin tsaya kallon ruwa lallai kwaɗo zai miki ƙafa, dan kina ji kina gani mijinki zai koma bin gidajen abinci. Daga haka a barbaɗesa kuma😝, to ni dai ba ruwana🥱, na nuna muku hanyar da zata fishe ku. Wato Ramadan class na Chef Yakudima, bama sai Ramadan ba, ko yaushe ajinta na koyon girki abuɗe yake. Nima dai Bilyn Abdull banga ta zama ba. Dole naje domin sake damƙe Bawan ALLAHn nan Malam Audu a hannuna🤤. Chef Yakudima zo mu saka labule🚶.
×××××××××××
“Ruky dan ALLAH ga abincin nan ki miƙama Uncle Ammar. Yace a bama Mu'azz ya kai masa kuma ban ganshi ba”. Kallon Mammah Ruƙayya tayi, dan tasan in har Uncle's ɗin nasu na ɗaki bata aiken su ciki. Dama shara ce ta safe ke kaisu. Idan har ka gansu da yamma ko da rana to su suna falo ne suka aike su ɗakko abu ko basa gidan Mammah ta aikesu, mafi yawancin lokaci ma sunfi saka Mu'azz. Jin batace komai ba, kuma bata miƙe ba Mammah ta kallesu, dai-dai itama Kulu ta buɗe baki zata sake magana sai tai shiru. “Amsa ki kai masa”. Cewar Mammah tana kallon Ruƙayya. Mamaki sosai ya kama Ruky, amma babu musu tsakaninsu da Mammah dan haka ta miƙe ta amsa ɗin...........✍️
Jama'a, karfa ku bari ayi bikin shagalin girke-girken online class na Chef Yakudima babu ku😘💃.
Ga Ruky kuma za'a fara aikin lada🤣. Bari muga ya za'a kwashe🥱. A barku haka ko a ƙara biyun🏃🏼♀️💃?.
[1/22, 5:28 PM] Zeenaran 😘: