
Post
Kida a ruwa Book 3 page 32
..... their spirits are just right here, Dada has praised the head officer. It seems that today there are no words around. Jamin quickly turned around and understood the boss's language. Soon they brought back a man wearing a black suit as well. He will not pass the time of Ja'afar. When they arrived there, he greeted them respectfully and explained what he was going to do. "Your life is long, on the order of the President, we have come to take responsibility for your security and your escort to the Office." His eyes widened and he looked at the officer, sending a servant of GOD without a plan to lower himself. His heart was beating very fast. In his mind, he said, (Tab wlhy I can't. That's right, this man is full of people. I'm in this field, it's not mine so I can dig myself). In fact, he could not raise his head to look at Dada for the second time, and he also did not speak and went to the gate. As soon as they reached Ammar, they had to follow them too. Of course the manager did not lie. The hearts are cars that even those who don't know cars think they were bought with a lot of money. Here are some brave heroes waiting for the night. When they came out, they all calmed down ag
32
.........Sun fito compound da Sanda ya gama sharewa tsaf, dan yana tsaka da banruwan fulawa ne ma ya hangosu ya ɓuya. Sai maigadi ne ya zo da sauri yana gaishe da Dada. Sannan suka gaisa dasu Ammar. “Alhaji dama tun ɗazu baƙi suke jiranka.” Da mamaki Dada daya ɗan zuba masa ido ya furta, “Baƙi?”. “Eh wlhy suna wajen gate. Sai dai daga gani jami'an tsaro ne. Amma fa da wasu zuƙa-zuƙan motoci suke baƙaƙe wulik kamar na shigar shugaban ƙasa”. Dada baiyi magana ba, sai ma juyawa yay ya kalla Bilal. Bilal ya fahimci abinda yake nufi, dan haka ya miƙama Ammar briefcase ɗinsa ya nufi gate, sai kuma akai sa'a ma jami'an dake a gidan tun dawowarsa sai ga shugabansu ya shigo. Tare suka dawo inda Dadan yake da Bilal, yay gaisuwa. Kai kawai Dada ya jinjina masa. Cikin ƙara gyara nutsuwarsa ya cigaba da faɗin, “Sir! Masu rakkiyarka ne daga fadar shubagaban ƙasa. Idan ka amince zan shigo da shugaban su”. Kallon juna Bilal da Ammar sukayi suka kashe ido da jinjina. Sai kuma suka gimtse murmushin fuskokinsu dan dai-dai nan Dada ya jinjinama jami'in kai. Da alama yau babu ƴan maganar a kusa. Da sauri kuwa Jam'in ya juya, dan ya gane yaren Boss ɗin. Babu jimawa suka dawo da wani mutumin dake sanye cikin baƙaƙen suit shima. Bazai wuce sa'an su Ja'afar ba. Sai da suka iso wajen yay gaisuwa irin ta girmamawa sannan yay bayanin dake tafe da shi. “Ranka ya daɗe, bisa umarnin Shugaban Ƙasa, mun zo ɗaukar nauyin tsaronka da rakkiyarka zuwa Office.” Birkitattun idanunsa ya zubama jami'in, aiko bawan ALLAH babu shiri yay ƙasa da kansa. Zuciyarsa kuwa sai bugawa take da sauri-sauri. A ransa ya furta, (Tab wlhy bazan iya ba. Dama haka mutumin nan yake da cika waje. Ina wannan filin ba nawa bane dan zan iya tona kaina). A zahiri kuwa ya kasa ɗago kai ya kalla Dada a karo na biyu, shima kuma baiyi magana ba ya nufi gate abinsa. Da sauri su Ammar suka bisa kuwa, dole suma suka take musu baya. Tabbas maigadi baiyi ƙarya ba. Zuƙa-zuƙan motoci ne da ko wanda bai san mota ba yasan an saye su da kuɗaɗe masu nauyin gaske. Ga wasu baradan jaruman tsaye masu jiran kota kwana. Suna fitowa duk suka sake nutsuwa, sai kuma sukai caaa suna miƙa gaisuwa. Hannu kawai ya ɗaga musu.. Wanda ya masa bayani a cikin gidan nan ne dai ya buɗe masa motar tsakkiya da saurinsa. Dada yay ɗan jimm yana karanta addu'ar hawa abin hawa kamar yanda ya saba koda tashi ce sannan ya shiga ya zauna. Jami'in ya maida ya rufe. Sannan ya zagaya gaba ya zauna ta gefen mai zaman banza, cikin waɗancan kuma wani ya buɗe mazaunin driver ya shiga. Matsowa su Bilal sukai suka masa bye, ya jinjina musu kai yana lumshe idanunsa. Suma sauran jami'an duk sun shiga sauran motoci biyun. Daga haka suka harba kan titi. Kasa haƙuri su Ammar sukai sai da suka koma cikin gidan kaima su Mammah rahoto. Dan Ammar ma harda video ya ɗauka dama. Kuma ya ƙudiri aniyar ɗorashi a media dan zukatan maƙiya su buga.....
^^^^^^^^^^^^^
A ɓangaren Daddy Imran ma hakan ce ta faru. Yayi shirinsa tsaf cikin Suit masu duhu Ammie tai masa rakkiya compound da shirin shiga motarsa, Asma'u dake riƙe da briefcase ɗinsa na roƙonsa bin Ammie kasuwa dan za'ai sunan Aunty Lailah gobe, shi kuma yace a'a tanata shagwaɓa. Gefe Khalifa na mata dariya, Lolo kuwa na ɗakinsa yana shirin makaranta. Isowar mai wankinsu ya katse faɗan Khalifa da Asma'u. Ya gaishesu sannan yake sanar muku baƙin dake gate. Mamaki ya kama Daddy Imran sosai, amma sai yace maiwanki ya shigo da Ogansu yaji lafiya. Saɓanin na Dada shi nashi sojoji ne, duk da dai a wanda ke waje akwai wasu jami'an harda ɓoyayyu ma. Yanda akaima Dada bayani anan shima haka akai masa. Yasan hakan normal ne dama, amma yayi tunanin sai sun fara zuwa office a yau sannan za'a basu waɗan nan damammakin. Dole yay sallama da iyalinsa yana sake jaddadama Asma'u karta fita ko'ina. Daga haka aka buɗe masa mota suka wuce fadar shugaban ƙasa.
)))))))★((((((((
Tsakanin isowar motocin Dada dana Daddy Imran babu nisa. Sai dai da yake a faɗar shugaban ƙasar ma kowa da fanninsa sai basu haɗu ba. Kai tsaye motocin ɗaukar Dada sun nufi sashen ofishin shugaban ƙasa ne. Wani babban jami’i Chief of Protocol ya tarbe shi. Dan motocin na kammala tsayawa jam'in nan yay wuff ya fita a gaban mota kamar sauran suma yazo ya buɗe sashen da Dadan yake. Sai da yaja fin mintuna biyu, dan sai da ya karanta addu'oi sosai tare da ƙarema wajen kallo sannan ya sauke ƙafarsa ta dama dake sanye cikin haɗaɗɗen takalminsa. A take ƙamshin turarensa ya isa hancinansu, duk da suma ƙamshin nasu turarrukan sun shiga nashi hancin. Cike da girmamawa Chief of Protocol ya miƙa gaisuwa. Tare da faɗin, “Ranka ya daɗe Sir. Shugaban Ƙasa ya bayar da umarnin a raka ka kai tsaye ofishin ka.” Kai kawai ya jinjina masa kamar na baya, dan tun maganarsa da Mammah a gida bai sake magana da kowa ba. Wannan kuma salon takun manya ne. Jami'an da suka ɗakkosa har yanzu basu ji muryarsa ba, dan haka suka fara tunanin wai kodai bebe ne mutumin nan?. Babu mai basu amsa dan haka sukai gum, saboda kwarjininsa kawai da cikar kamala da kamewarsa ga nutsuwa da gizago ya sakasu jin shakkarsa, tare da yarda da batutuwan mutane a kansa. Dan a weekend ɗin nan babu sunan daya kai sunan sa dana Imran yawo sai na shugaban ƙasa. Yanda Chief of Protocol ke gaba, sai jam'in nan dake nuna shine shugaban wannan tawagar a tare da shi, Dada na bayansu, bayansa kuma sauran jami'an nan ne ke take masa baya dole abin ya birgeka. Dan kamar an tsara su ne, suna sauke ƙafa da ajiyeta a tare kaida ka gani kasan rakkiyar ta babban kai ce. Gashi suna tafiya ne ta cikin dogon corridor mai sanyi, shirun da babu hayaniya. Tun fitowarsa motar ƴan median fadar ta shugaban ƙasa suka dasa musu camara kuma. Dan dole ne a saki labaran shigowar Chief Of Staff na farko office ga ƴan ƙasa. Ko'a jikin gogan naku. Takunsa yake cike da ƙasaita da mazantaka. Fuskar nan ciɗin-ciɗin yau ta asalin sojan sa a fagen yaƙi. Ga hotunan tsoffin shugabanni da suka cika bangon dogon corridor ɗin suna kallonsa kamar suna tantance shi da masa barhaban. A ƙarshe aka tsaya a gaban wata ƙofa dake ɗauke da baƙin allon rubutu da kalar gold. CHIEF OF STAFF TO THE PRESIDENT. Shine a rubuce ɓaro-ɓaro ga mai kallo. Chief of Protocol ya danna wani maɓalli dake a bango a take ƙofar ta raba kanta biyu. Makeken Ofishin mai girman gaske ya bayyana a idanunsu. A tsaftace yake, ga ƙamshi na tashi mai ainahin saka nutsuwa. Matuƙar tsaruwa wannan office ya tsaru. Dan kuwa komai na cikinsa yana tabbatar da ƙarfin ikon mamallakinsa . Dada ya tsaya na ɗan lokaci yana karanta addu'oi. Kafin ya saka ƙafarsa ta dama batare da ya daina ambaton ALLAH ba. Dan shine cikakken sarki gagara misalin masu misali. Mai cikakken iko da rahama ga jinƙai ga bayinsa. Shike bada dama ga wanda yaso a sanda yaso. Shike daka girma da cikar kamalar bawa a idanun ƴan uwansa bayi badan ya kasance mafifici a garesu ba. Ba'a farautar ɗaukaka ko girma da kuɗi ko ƙarfin ƙwanji. UBANGIJI ne kawai ke badawa kamar yanda ya bama wannan bawan nasa Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi. A hankali ya kai zaune cikin kujerar da aka gyara masa idanunsa a lumshe bakinsa na cigaba da ambaton UBANGIJI da neman agajinsa. Dan tabbas yanzu ne wasan zai fara. Farawa irin ta KARE JINI. BIRI JINI. A yanzu yaƙine na kwatar ƴanci da neman tsira. Kuma duk zasu fara ne ta silar wannan kujera....
★A can ma Daddy Imran ya shiga nasa babban ofishin dake da ƙarfin faɗa aji akan tsaron ƙasa. Shima dai an shirya shi da girma da aji tamkar na Dadan. Dan tsarin da akaima offices ɗin duk mai hankali ya tabbatar da gayya shugaban ƙasa yasa akayi su. Ga tsaro mai tsaurin gaske dake tabbatar ma maƙiya koda zasu iya keta wannan alfarmar sai da ƙarfin ikon ALLAH. Sannan The two shadows sun iso FILIN YAƘIN. Yanzu ne za'a banbance MAZAJE DA MAZARE......
=============
Fitar Dada babu jimawa Hajiya Hasiba ta iso gidan. Su su Nabeeha ma ko barci basu tashi ba. Sai Nana daketa kai-kawon gyara da girka breakfast. Dan in bata kammala da wuri ba su Rayhana suka tashi sunta cimata mutunci kenan. Har ƙasa Nana ta durƙusa ta gaida Hajiya Hasiba da kallo ɗaya zakai mata kasan a firgice take. A taƙaice kawai ta amsa mata. Kanta tsaye kuma ta wuce ɗakin Nabeeha. Tana maida ƙofar ta rufe Nana ta ajiye tsintsiyar hannunta ta shige ɗakinta. Waya ta ciro a ƙugunta tai kiran First Lady. Sai da ta kusa tsinkewa aka ɗaga. Tai murmurshi a bayyane tana faɗin, “Ranki ya daɗe barka da safiya”. Yanda ta maƙale murya cike da iyayi ya saka First Lady lumshe idanu daga can cike da shaiɗanci, itama sai ta sake maida murya ƙasa ta amsa mata. Nana tayi murmushin cin nasara. Tare da ƙara gyara murya. “Mommy ga mutuniyarki fa tazo gidan yanzun nan. Kuma kamar wadda take a ruɗe ta shige ɗakin Nabeeha”. First Lady tai murmurshi. “Karki damu da ita Adeel ne ya kunnota. Ai muna tare da ita tun jiya”. A take fara'ar Nana ta ɓace daga fuskarta. Cike da jin kishi ta ce, “Oh ai na zata baki sani bane ba dama. Bari naje na cigaba da aiki”. Sarai First Lady ta fahimci halin da Nana ke ciki. Dan haka ta sake sauke murya ƙasa cike da lallashi tana mata magana. Har sai da Nana tai murmurshi ta cigaba da bata labarin abinda ya faru jiya da yamma akan zuwan Adeel ɗin. Bugun ƙofar da ake mata ya sata zabura tai sallama da First Lady ɗin ta ɓoye wayar ta fito........✍️
🤭🤭🤭🤭Ahema kwartis ce.
[1/23, 4:59 PM] Zeenaran 😘: