Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 33

Post

Kida a ruwa Book 3 page 33

..... forget him. Mommy, son of GOD, do something. I don't want to see Aunty Nabeeha in this situation. That's why I didn't want you to answer this man in the first place, Adeel's son is not the type of men in our country who understand the language of marriage." "I personally feel sorry for Auta, but on this side, Adeel slipped in front of me and didn't buy it. I'm at a loss as to where I'm going to discuss his matter." "Mommy, let the First Lady speak to us, since you know him well, I am sure that if you speak to him, he will understand. Wlhy koni I am afraid that Dada will know the truth of this conversation. Dan didn't really believe that Aunty didn't give Adeel a chance. And we don't know the plan that Adeel is planning since she has come to the house". Hajiya Hasiba was silent and studied Amima's words..... ★★★ On the part of the First Lady, she was cutting the phone between her and Nana, her best friend, who was in the car from Hajiya Hasiba's house. She laughed and said, "Anya, among your children, is there anyone who loves you like Nana? Privilege and jealousy. If you ask this girl or her mother to say goodbye to you, she will do it." Baki Firt Lady was a bit shy. But she

Standalone post1,701 words

33

........Harara Amima ta wulla mata, cike da wulaƙanci ta furta, “Ke wai wace irin jakar yarinya ce? Kashemu kike son yi, kin saka abu a wuta kinzo kin shige ɗaki uwar uban mi kike yi?”. “Aunty kiyi haƙuri dan ALLAH. Wlhy bayi na shiga ne”. Mangari Amima ta kai mata, duk da kuwa ba girmarta tai ba. “Bayani zaki tsaya min ko zuwa ki duba dan ubanki”. Da gudu Nana ta wuce kitchen ɗin, Amima taja tsaki tana nufar ɗakin Nabeeha. Mamakin ganin Momy tunda safe ya kamata. Ta dai ƙarasa shiga tana gaisheta da kallon Nabeeha dake kuka ga idannunta sunyi luhu-luhu alamar bata samu isasshen barci ba. Zama tai cikin tashin hankali tana dafa ta, dan tabbas Amima nada rashin kunya da rashin mutunci, amma tana da son ƴan uwanta. Musamman ma Nabeeha tana sonta sosai fiye ma da Rayhana da suke uwa ɗaya uba ɗaya. “Aunty yanzu saka abin nan kikai a ranki har haka?. Kalla idanunki fa. Dan ALLAH ki kwantar da hankalinki, na tabbatar Dada zai dawo gareki. Kuma idan ya tabbatar miye a zuciyar Adeel zai hukunta shi. Momy dan ALLAH kiyi wani abu. Bana son ganin Aunty Nabeeha a wannan halin. Shiyyasa tun farko ban so kuka amsawa mutumin nan ba, dan Adeel ba irin mazan ƙasarmu bane da suke gane yaren aure.” “Ni kaina nayi nadama Auta, dan kuwa a wannan gaɓar Adeel ya zame min gaba kura baya sayaƙi. Na rasa ta inda zan taro al'amarinsa.” “Momy kima First Lady magana mana, tunda ta silarta kika sanshi na tabbatar idan tai masa magana zai fahimta. Wlhy koni ina tsoron Dada yasan gaskiyar zancen nan. Dan ba lallai ya yarda Aunty bata bama Adeel dama ba a kanta. Kuma bamu san makircin da Adeel ɗin ke shiryawa ba tunda har gashi yazo gidan”. Shiru Hajiya Hasiba tai cike da nazarin kalaman Amima.....

★★★

A ɓangaren First Lady tana yanke waya tsakaninta da Nana babbar aminiyarta data ɗakkota a mota daga gidan Hajiya Hasiba tai ƴar dariya da faɗin, “Anya a kaf cikin yaranki akwai mai sonki kamar Nana? Gata da kishin tsiya. Yarinyar nan ko uwarta kikace ta sallama miki zatayi fa”. Baki Firt Lady ta ɗan taɓe. Sai dai fuskata da murmushi ta ce, “Na sani. Dan ki duba randa na fara ganin videon ta a TikTok nasa Ilu ya kawo min ita, yana mata magana ko musu batai ba. A washe gari ya saya mata ticket tazo. Da ƙyar na samu ta koma gida bayan ta min sati, haka kuma ta cigaba da damuna da massages har sai da na sa ta ƙara zuwa daga nan ta maƙale taƙi ta koma. Ita kanta Hasiba yanzu haushinta take ji”. Cikin ƙyalƙyalawa da dariya Hajiya Caras ta ce, “Mutuniyar kina basu wuta. Amma nikam miyasa bazaki ƙyale Hajiya Hasiba da ƴarta su huta bane?”. “Hummm.... kema kin san bana wasa da ɗaukar fansa. Duk wanda yay min kan kara zan masa na itace. Ai tunda Hasiba ta nuna min ƴarta tafi ƙarfina zama ta iya rabuwa dani a kanta, wlhy sai ta tabbatar tayi dani ƴar halak. Kima shirya a satin nan zamu je wajen mai tukunyar tsafi, dan na fahimci ƙullin dake kan Adeel ya fara hucewa game da Nabeehar. Sannan ina son yamin aiki akan Nabeeha, dan anzo gaɓar da da kanta zata kawo min kanta. Kuma a gaban Hasiba zan yi yanda nake so da ita, dan wannan alwashina ne, sai na kasance da yarinyar nan. Sannan saina kunnama Hasiba wuta tsakaninta da Adeel da bazata iya kasheta cikin sauƙi ba”. “Bazan hanaki ba aminiya. Sai dai kiyi a sannu dan kin san wanene mijin yarinyar nan. Ya fimu hauka wlhy tsaf zai ƙarar damu”. “Bani da matsalar komai da shi sai ta son matarsa. Amma idan yace zai shiga gonata dai-dai nake da shi. Dan a tafin hannuna yake shima, da yawan masu neman kurwarsa ƴan hannun damata ne. Ko last abinda ya faru nina basu rahoto akansa. Duk da yarinyar da sukai amfani da ita naso ta mutu dan ɗaukar fansar Zahir da suka nema illata min tasha da ƙyar, kuma ban haƙura ba, inada wani sabon shiri, suma yaran sai na girgiza duniyarsu.” “Lallai Hasiba na cikin one chance kenan. Dan naji ranar kina faɗin da taimakon ta aka fita da yarinyar ma a gidan”. “Tabbas haka ne. Dan ni suka bama aikin na sakata. Na gaba ma idan ya taso itace zatayi”. Dariya sosai Aminiyar tata ta sanya, tare da faɗin, “Aminiya wanda bai sanki ba ya shiga ukun sa, musamman ace ya shiga komarki a gaɓar da yake kallon bashi da masoyiya kamar ki, shiyyasa Hasiba ke ban tausayi. Dan a yanzu duniya ji take bata da kamarki, bata sane kece makashiyarta ba”. A tare suka tuntsure da dariya harda tafawa. First Lady ta ce, “Itama ita tajama kanta. Data bani muradin raina tun farko da tasha daɗi. Dan na ɗauketa da muhimmanci amma ta watsan ƙasa a ido ita a dole mai ƴa, mu ko bamu san zafin haihuwa ba ai ko”. “Ai gashi nan ta jama kanta.” Hajiya Caras ta faɗa tana saving recording ɗin hirar tasu da duk tayi batare da First Lady ta farga ba. Dan sun riga sun iso katafaren gidan su da suka dawo bayan sun sauka a mulki.....

🥱🥱Hhhhmm nama rasa abin faɗa. Hajiya Hasiba wannan fa shi ake kira idan bakai sharar massalaci ba zakayi ta kasuwa.

∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆

Ƙarfe biyar aka maido Dada gida kamar yanda aka ɗaukesa. A lokacin su Nimrah na sashen su Lailah da aketa shirye-shiryen suna. Dan haka basu san ya dawo gidan ba ma. Sai su Mammah kawai dake hira a falo da su Gwaggo Khadijah. Uncle Jamilu yana gidan Uncle Nasiru. Uncle Tasi'u kam ya tafi yau da safe maganganun Dada na cigaba da ragargaza zuciyarsa. Duk da yanda yake a gajiye sai da ya zauna suka gaisa da gwaggonin nasu. Sukai masa addu'ar ALLAH yasa an fara shiga office a sa'a. Dan da safe sanda ya fita basu haɗu ba. Ya miƙe zai haura sama Mammah ta masa zancen abinci. Duk da yana buƙatar abincin agogo ya kalla. Dan sauri yake zai ƙara fita tun yana office Faro ya tura masa saƙon an kama uku a cikin drivers ɗin nan. “Mammah bar abincin nan zan sake fita ne. Idan na dawo zanci. Yanzu kam ina sauri Haydar na jiran mu, yanzu zakiga Imran yazo”. Daga shi har Imran ɗin tausayi suka bata. Sunje wani aikin yini guda ba kuma hutu za'a fita wani. Batace komai ba, dan haka shima ya wuce sauri-sauri dan yana son watsa ruwa. Tashi tai da kanta ta nufi kitchen ta shiga haɗa abincin nasa fiye ma da cikinsa a basket, ta fito da shi falo ta ajiye. A mintuna talatin kaɗan ya ɗara sai gashi ya fito cikin sabuwar shiga. Sai dai daga sama har ƙasa baƙaƙen kayane, amma marasa nauyi. Yanda ya sakko yana gyara bindiga a jikinsa ya saka Mammah kauda kanta. A ranta tana musu addu'ar kariyar UBANGIJI da fatan nasarar kammala wannan aiki mai haɗari lafiya. Kaɗan ya rage yay karo da Hanoon data taho akan sani. Dan ta fito a bedroom ɗinsu ita da Biebah ta hango shi yana sakkowa shine ta taho da sauri. Ko kallon inda take baiyi ba yay wucewarsa, zama ka rantse bai ganta ba ne. Suma su Mammah bai tsaya a wajensu ba yay musu sallama ya fice dan Imran har ya zo. Rashin su Nimrah a falon yasa Mammah tace Hanoon tazo ta bishi da basket ɗin abincin. Aiko daɗi kamar zai kasheta. Jikinta har rawa yake tazo ta amsa tabi bayansa. Sai dai yanda yake tafiyarsa har ya mata nisa. Ba arziƙi ta haɗa da gudu. Ta iso dai-dai yana buɗe ƙofar gefen driver zai shiga. “Dada gashi inji Mammah”. Muryarta ta shiga kunnesa. Bai juya ba sai da ya shiga motar, yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kai. Itako ta tsare shi da idanu fiki-fiki. Imran yay ɗan murmushi. Tare da faɗin, “Saka a baya.” Ba haka taso ba. Dan haka jiki a sanyaye ta buɗe bayan ta saka. Imran ya tada motar zasu fice cike da tsokana ya furta. “Humm wai kaga kallon da yarinyar nan ke maka? Kodai ƴar gida za'ai mutumina?”. Wani kallo Dada ya watso masa. Dan haka Imran ɗin ya kwashe da dariya. Dai-dai suna fita a gate ɗin gaba ɗaya. “Ai gaskiya na faɗa. Kaga Soja a waje soja a gida. Girman ka ne wannan babban kai, saura ta huɗu”. “Hummm”. Dada ya faɗa. Imran yasan iya amsar kenan. Dan haka ya cigaba da tsokanarsa. Sai da ya tabbatar ya kaisa bango sannan ya barsa suka koma maganar Office. Sun iso UNIT ZERO ana kiran magriba. Sai suka tsaya sukai salla a farkon anguwar sannan suka ƙarasa gidan. Da su Dabo suka fara cin karo ata ɗayan sashen da aka gyara dama dan ajiye mutane. Cike da girmamawa suka fara gaishesu. Imran kawai ya amsa. Gogan hannu kawai ya ɗaga musu. Sun ƙaraso wajen da aka shirya cells da yawa da ƙarfuna. Na can ƙarshe da ihu ke fitowa suka dosa. Faro na tsaye daga ƙofa hannuwa a aljihu fuskar nan babu ɗigon fara'a. Sai wasu jami'ai biyu cikin baƙaƙen kaya fuskar su a rufe idanun su da yankan baki kawai kake iya gani. Suna sakama mutane uku dake a kujera shocking a jiki, shine suke ihu. Isowar su Dadan ya saka Faro fitowa. Kauda kai Dada yay daga kallon matasan yaran ya maida kan faro. Dai-dai Imran na faɗin. “Wai sunƙi magana ne?”. Faro ya jinjina kansa yana furzar da huci. “Sunƙi. Sun dage akan aiki kawai aka basu basu san masu kayan ba. Sannan basu san minene a motocin ba. Sannan sunƙi faɗa mana inda sauran suke. Sai nake ga kamar da gaske basu sani ɗin ba.....” “Ƙarya suke yi. Koda basu san su waye ogannin ba sun san mi suka ɗakko. Sannan su dukkansu yara mutum ɗaya ne. Da ace ba mutum ɗaya ya basu horo ba, dole su samu saɓanin magana.” Dada ne mai maganar. Batare da ya jira amsawarsu ba ya tura ƙofar ya shige. Binsa da kallo Imran da Faro sukayi. Sai kuma suka bi bayansa suma cikin wajen.......✍️