Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 38

Post

Kida a ruwa Book 3 page 38

..... That is not a crime as long as you accept it." "Yes, I really agree with him. But if you have time today, you should come and meet". "As long as you accept him, I will not see him. I will be very busy this week. I don't think I will enter UNIT ZERO, honestly." "What about these children? You should come in." "Keep taking care of them. But do not mix them with the others since they have already been treated. I also want Bilal to come back and walk." "Isn't Ammar here?". "No, Ammar doesn't listen. Don't worry, Bilal is almost back." "I understand. May God bring him back safely and give us luck".... Nabeeha's arrival there silenced Dada. Faro, who did not know the town, started teasing her with the words, "Lady, the queen of women". He said, "You don't know how to greet people, do you?". Even though she wanted to suppress her expression, her voice came out with frustration and said, "Why would he call me a lady?"

Standalone post1,555 words

38

........Dada ya fito Faro ya fito suka haɗu a compound. Cike da shaƙiyanci Faro ya furta, “Alhajin ALLAH ai nazata ma sallar a ciki zakayi yau?”. Cikin rashin fahimta Dada ya harareshi. Faro yay dariya da faɗin, “Miye na hararata daga faɗar gaskiya. Na shiga ciki akace zuciyarka na ɗakinka tare da kai. Amma bawan ALLAH ko kunyar Mammah baka ji ne?”. Yanzu kam Dada ya gane sarai. Dan haka ya girgiza kansa da faɗin, “Bani da lokacin ka. Ka cigaba ina da maganinka a hannu Haydar”. “A'a tsaya mi kake nufi?”. Gaba Dada yay abinsa batare daya sake tanka masa ba...

Bayan an idar da salla sun fito Faro kema Dada bayanin yaran nan duk sun zo hannu fa. Sannan ya fara aiki akan Garba. Dada ya jinjina kansa yana ɗan furzar da iska. “In dai Garba ya faɗa tarkonmu Ojo ya gama zuwa hannu Haydar. Yanzu damuwata musan ta yanda zasu rarraba kayan nan da yaran suka ce”. “Nima hakan na damuna sosai. Amma akwai wani jami'in farin kaya na yarda da aikinsa gaskiya. Ko zamu shigo da shi tawagar nan ne?”. “Hakan ba laifi bane in dai ka yarda da shi.” “A, na yarda da shi gaskiya sosai. Amma in kana da lokaci yau da sai yazo ku haɗu”. “In dai ka yarda da shi basai na ganshi ba. Dan satin nan zan yi busy da yawa. Bana jin ma zan shigo UNIT ZERO gaskiya.” “Yaran nan fa? Ya kamata dai ka shigo”. “Ku cigaba da kula da su. Amma kar ku haɗasu da waɗan can tunda su an fara treating ɗin su. Driver nan ma Bilal nake so ya dawo dan yayi tafiya”. “Ba Ammar na nan ba?”. “No, Ammar baya ji, zai iya ƙwaɓa aikin. Karka damu Bilal ɗin ya kusa dawowa”. “Na gane. ALLAH ya dawo da shi lafiya ya bamu sa'a”.... Isowar Nabeeha wajen ya saka Dada yay shiru. Faro da bai san dawan garin ba ya fara tsokanarta da kalmar, “Uwargida sarautar mata”.. “Hummm!”. Kawai tace masa. A take ya fahimci ya ɗebo da girma. Sai kawai yayma Dada sallama ya wuce masaukinsa. Nabeeha bata gaida shi ba, dan haka bai sake bi takanta ba. Sai da ya wuce Dada da yaƙi kallonta da alamar ɗaci a muryarsa ya ce, “Ke baki iya gaisuwa wa mutane ba ko?”. Duk da yanda take son dinga danne yanayinta sai da ta ɓata fuska, muryarta na fita da takaici ta ce, “Miyasa zai kirani da wani Uwargida”. Idanu ya zuba mata a karo na farko. Abu biyu ya saukar mata a lokaci ɗaya. Tsigar jikinta ta tashi, sannan wani shakkarsa ta tsarga mata. Ta sani shi baya son raini, ba'a kansa kawai ba. Ko ga wani kayi, wanin daya tabbatar ya girmeka sai ya nuna maka ɓacin rai. Sai dai idan wancan ɗin ya zubar da nasa girman ne... “Kayi haƙuri ina son muyi magana ne”. Nabeeha ta faɗa muryarta na rawa. Tamkar Dada bai jita ba, yay ƙoƙarin barin wajen. Da sassarfa ta tari gabansa, cikin danne shakkarsa dake son rinjayarta da aro jarumtar dole kawai ta rungumesa ta sakar masa kuka. Kasa motsawa Dada yayi, sai dai yabi compound ɗin da kallo dan son tabbatar da babu mai ganinsu. Ita ko wani bugawa ƙirjinta yayi, saboda jin ƙamshin turaren da tunda ta dawo take jinsa a jikin Nimrah da Ruƙayya. Tabbas turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Duniya ne. Suna da turare wuta da khumra kaloli har uku: black humra, white humra, brown humra. Akwai oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima. white, black, and brown. Akwai man kitso, da kayan gyaran jiki masu gyara fata da sanyata laushi da santsi kiyita glowing abinki hajjaju. Tsagaitawa tai da kukan nata, ta ƙara zuƙar numfashi da ƙyau. Jin tabbacin ƙamshin ne fa ya sata saurin jan jikinta baya. Ya bita da kallo, itama nata idanun ta ɗago tana kallonsa, zuciyarta na tafasa a cikin ƙirjinta. Tana da kishi mai zafi, kuma ko yaya ya taso mata bata iya haɗiyewa. Tsaf ya karance wutar bala'in da ke ci a cikin idannunta. Sai dai bai san akan miye ba. Bai kuma yi magana ba har sai da ta buɗe nata bakin ita tayi. “Saboda kana samun biyan buƙatar ka a wajen tatsitsiyar yarinyar da ka haifi wadda ta fita ma kake wulaƙantani Haysam. Ka kasa sauke nawa hakkin amma ita kana tare da ita ko kunyar ƙannenka baka ji? Kaƙi taka inda nake duk da halaccin da nai maka na jiranka tsahon shekarun da bani da tabbas na dawowarka. Kana zaton bazan iya barinka ba saboda ina sonka ko?......” Kuka ya sarƙeta ta kasa ci-gaba da magana. Sai jiri da take ji kamar zata faɗi. Kanta ta dafe, da jan ƙafa tabar wajen ganin yaƙi yay magana. Wani irin zafin tsanarsa take ji a ranta. Tana son mijinta, tana masa kishi mai tsananin gaske da ita kanta har tsoron kanta take ji. ALLAH wani lokacin har ji take kamar garama ace ya mutu idan ta tuna yarinyar nan matarsa ce... Koda ta wuce Dada ya kai mintuna biyu a wajen kafin ya wuce ciki dan kalamanta sun masa zafi. Bai samu kowa a falon ba sai su Afrah. Hankalinsu kuma na kallon cartoon har ya wuce basu ganshi ba.

Da sauri Nimrah dake daga balcony ɗin upstairs tana kallonsu tabar wajen, hawaye share-share a fuskarta. Wani ɗan lungu ta samu ta maƙale, har sai da ta ga shigarsa ɗakinsa ta fito ta sauka downstairs. Itama bata kula su Abees ba ta shige ɗakinsu. Ruƙayya dake zaune a tsorace ta tashi zaram tayo kanta tana tambayarta dukanta Dadan yayi? Maimakon amsa sai kawai ta rungumeta ta fashe da kukan. Ruky tai matuƙar daburcewa, itama tata muryar na rawa alamar zatai kukan ta ce, “Dan ALLAH ki daina kuka Ninah, ki faɗa min miya miki?”. Yanzu ma bata iya bama Ruky amsa ba, sai da ta tabbatar kukan ya saka zuciyarta rage nauyi sannan ta sanar mata abinda ta gani tsakanin Dada da Nabeeha. Ruƙayya ta dalla mata harara. “Shine kuma abin kuka kamar wata sakarai. Ninah wai miyasa akan matar nan kike son zama wata lusara ne?”. “To ni ya kike so nayi? Kawai fa kaina ya kama ciwo ya barni a ɗaki barci ya ɗauke ni sai yanzu na farka. Na leƙa ta window ɗin ɗakinsa na hangota ta fito a sashen ta, shine na fita balcony ashe shine tsaye tare da Uncle Haydar......” “Kema gashi kin faɗa ita ta kawo kanta. Ninah itafa matarsa ce. Banda ma sun sami matsala daba wannan maganar ake ba. Ni ba wannan kishin irin nata nake so kiyi ba, kishi irin na kwatar ƴanci zamuyi. Dan haka al'amarinsa da matarsa yama daina damunki. Mu zauna mu tsara abinda ya dace kin fahimta”. Kai ta jinjina mata, itama sai ta rungumeta tana faɗin, “Uhmmm my Trouble Queen na tsoron kishiya. Wlhy kin fara son Dada”. Karamin dundu Nimrah tai mata a baya. Ruky ta sanya dariya.....

(+++)+(++++)+(+++)

Anan kam Biebah na zubama Faro abinci shi ko ya zuba mata idanu. Komai tayi ƙyau take masa. Ji yake a ransa anya zai iya dannewa kuwa. Shifa sai yanzu ma yake ji kamar Haysam bai kyauta masa da batun a ɓoye auren nan ba. Koba komai inda ta sani ai ya ɗan rage zafi. Amma yanzu komai yayi zata iya kallonsa a baibai ne. Haka dai dole ya shanye maitarsa yaci abincin. Yana kammalawa kaɗan suka ƙara taɓa hirar ya miƙe akan zai wuce. Tayi mamaki, dan kafin yazo yace mata sai irin tara ɗin nan zai tafi. Dan haka ta kallesa cikin damuwa da ƴar shagwaɓa ta masoya. “Yaya amma cakai bazaka tafi da wuri ba. Miyasa ka canja kuma?”. Gaba ɗaya sai lissafinsa ya nema ƙwacewa da salon nasa. Ya haɗiye busashen yawu, tare da runtse idanunsa da launinsu ya canja. Tsawon sakanni kafin ya buɗe ya ɗan tako kusa da ita gab har sai da ta motsa zata ja baya saboda kusancin nasu. Yay wuf ya taro ƙugunta. Ta waro idanunta sosai, sai kuma lips ɗinta ya kama rawa tana son yin magana. Yatsarsa ya saka a lips ɗin nata yana sake kusanta fuskarsu gab da juna. Hakan ya sake daskarar da jinin Biebah data shiga tsilla-tsilla. Shi ko ko'a jikinsa. Saima nasa idanun da suka rine sosai ya riƙe natan da shi. Miryarsa na wani kalar komawa ƙasan maƙoshi ya furta. “Idan kika hanani tafiya zan aikata ba dai-dai ba. Dan wannan sojan naki bai san ya taɓa ya bari ba”. Yana kai ƙarshen zancen ya wani irin janta ya saka a jikinsa gaba ɗaya yay ma bayanta zobe da hannayensa. Idan Biebah bata suma ba a wannan lokacin to ina tabbatar muku numfashinta ya tafi yawon duniya na wucin gadi. Dan numfashinta bai dawo da ƙarfinsa ba sai da ya sumbaci idanunta, tai wata zaburar da ya saka shi sakin dariya. A rikice ta kwace jikinta kawai ta nufi hanyar fita. Yana kiranta amma ko waiwaye. Ya ƙara ƙarfin dariyarsa yana cizar lips. Dan harga ALLAH dariyar ta bashi. Ga wani shauƙi dake ɗawainiya da shi. Ai dolensa yay nisa da Biebah har tarewar nan. In ba hakaba ya rantse sai ya aikata ba daidai ba. Dama a yanayin mai son yin kuka an jefe shi da kashin awaki yake a halin yanzu.........✍️