Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 37

Post

Kida a ruwa Book 3 page 37

.....they are dead. She confirmed that Ruky was there more than her. She came close to him again like a mage, but she didn't touch his body but she was very close to him. Calming down his voice and shaking his head, he said, "Dada, be patient, we won't do anything more. Look at him, he looks like a slob. He is a woman who looks like a mite. We have punished him. There is no way he will take you on video and let him go. Yaya Mu'azz is like that, and he felt it in his body, let alone our parents, our parents, let alone Dada. Do you even ask us to let him go?" When she said the last word, she pushed the mouth hard and he turned his head away from looking at her, suppressing the smile that wanted to appear on his face. In his mind, he was declaring (Where it is a temptation to leave your belongings) and the names he called the children made him laugh even more. But he didn't. She didn't wait for him to ask again and said, "Of course we told him". (Innallillahi wa-inna ilaihiraji'un said in his heart. He is a soldier, he knows I am called Karara. Sometimes they themselves use it especially to trap my son, and when he is working, he touches their body. Even if he touches him, the punishm

Standalone post1,720 words

37

........“Zo nan”. Dada yay maganar a dake yana tsare Nimrah da idanunsa dake rikita lissafinta. Kamar zatai kuka ta miƙe daga inda take zuwa gabansa. Hankalinsa ya maida kan abincin da Ruky ta kawo masa, tare da jeho mata tambaya kai tsaye. “Mi kuka zuba musu a jiki?”. Zabura ta ɗanyi tana ƙwalalo idanu waje ta ce, “Dada munga idi! Su waye kuma?”. Yasan dama sai ta masa drama ɗin, dan haka ya sake haɗe fuska. “Na duba cctv footage kenan?”. “A'a dan ALLAH kayi haƙuri. Dada matsala aka samu, aljanun mu ne kawai suka hukunta shi?”. Harga ALLAH baima san yayi kasare yana kallonta ba. Yanda ya tsareta da idanu itama kawai sai dariya ta kamata. Ta ce, “Dada da gaske fa nake”. “Ni nace wani abu ne Kiddo?. Kawai dai dole na nemo malamai ai muku rukiyya ashe, yaushe kuke da aljanu ban sani ba?”. “Dada basa cutarwa, a barsu kawai ba sai anyi rukiyyan ba.” “ALLAH ya shirya min ku. Mi kuka saka musu?”. “Dada dan ALLAH bazaka dake mu ba idan na faɗa?”. “Ƙila”. Sai kuma tsoro ya kamata, tab ɗin Dada ya dake su ai sun mutu. Ta tabbatar yanzu haka Ruky na can a tsure fiye da itama. Sake matsowa tai kusa da shi kamar wata mage, sai dai bata taɓa jikinsa ba amma ta lafe kusa da shi sosai. Cikin sake kwantar da murya da shagwaɓar data gama rikita lissafinsa sai dai ya dake ta ce, “Dada kayi haƙuri bazamu ƙara ba. Kaga shi wannan mai kama da talo-talon shi ya jama macen mai kama da taɓaryar gwari. Dan shi muka hukunta. Ba yanda za'ai ya ɗauke ka a video mu barshi. Ai ko Yaya Mu'azz yay ma haka sai yaji a jikinsa balle ku iyayenmu, iyayen namu ma kai fa Dada. Ashe ma kun mana baki da zamu barshi.” yanda tai maganar ƙarshe tana tura bakin sosai ya kauda kai daga kallonta yana danne murmushin dake son bayyana a kan fuskarsa. A ransa yana ayyana (Indai Fitina ce a bar muku kayanku) shi sunayen ma data kira yaran sun fi bashi dariya. Amma dai baiyi ba. Itama bata jira ya sake tambaya ba ta ce, “Karara muka saka masa”. (Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un ya faɗa a zuciyarsa. Shi soja ne yasan mi ake kira Karara. Dan su kansu wani lokacin suna amfani da shi musamman wajen ɗana tarko, idan kuma aiki yay aiki yakan taɓa jikinsu. Dan ko shi ya taɓa taɓashi tsabar azabar da yasha sai da ya kwanta asibiti. Yanzu dan ALLAH inama suka samu kararan?) A zuciya duk yake maganar yana kallonta kawai. Ita kam sai cuɗa yatsun nata take na fama yanda ta saba. Ganin yanda take yi ya sashi basar da zancen, dan in ya tashi su biyun zai haɗa yay musu faɗa. Nimrah na jiran ya fara faɗa sai taji shiru. Sai ma gefensa ya nuna mata yana faɗin, “Dawo nan”. Yay maganar yana nuna mata kusa da shi a saman kujerar. Sosai ta waro idanun waje. Alamar taya zata iya zama a kusa da shi ita kam. Sai dai kallon daya sake wullo mata ya sata ɗan laɓe baki irin na mai shirin kukan taɓara. A karo na biyu yay mata gargaɗi da idanu. Dole ta shanye hawayen data fara ƙaƙalowa na ƙarya. Inda ya nuna matan ta zauna, sai dai a ɗofane. Amma sai ya kamata ya zaunar da ita da ƙyau har jikinta na gogar nasa. Zata fara mutsu-mutsu ya miƙo mata laptop ɗinsa jikin screen ɗin da wani hoto yana faɗin, “Kalla hoton nan da ƙyau ko zaki iya gane su waye?”. Computer ɗin ta amsa, ta ɗora a jikinta tana kallon mutanen jikin hoton daki-daki. “Lah Dada wannan kamar ni fa”. Dariya taso bashi, amma ya dake yana ɗan matsota jikinsa sosai yanda shima zaiga hoton da ƙyau, tsabar hankalinta ba wajen yake ba ta ƙara gyara zama sosai kusan jikin nata Duk a nashin. kallon yarinyar da take nuna masa yayi. Tabbas ita ɗin ce, tana sanye da boyal zani da riga, an masa ɗinkin buba da aikin wuta. Taci ɗammara da gyale tana hararar yaron kusa da ita. Yanda take farin ciki sosai ta saka shi murmushi yana kallon fuskarta. Hoton ta cigaba da kallo tana faɗin, “Dada dan ALLAH ina ka samo?”. Maimakon bata amsa sai ya ce, “Gama duba sauran ko zaki gane su”. Bata musa ba ta cigaba da kallo. Ga shi dai tabbas tasan fuskokin amma sunayen sun mata nisa. Sai da ƙyar ta dinga tsinto wasu tana faɗa masa. Tana faɗar yana rubutawa. Wanda bata gane ba kuma yana alamar jikin ainahin hoton dake cikin wani file. Ya sake nuna mata wani, nan kam harda iyayensu mata da maza. Dan harda Babanta. Fuskar Ummanta ta zubama ido. Hawaye suka shiga rige-rigen sakko mata. Shima ya jima yana kallon Umman tata, abubuwa da yawa na dawo masa. Kafin ya maida dubansa kanta. “Ba kuka ake ba, addu'arki tafi buƙata a yanzu sama da komai. Zaki iya gaya min waɗan nan duk su waye?”. Kanta ta jinjina masa. Ya ciri tissue ya bata. Hawayen ta goge sannan ya fara nuna masa kowa da sunansa. Hakan ya sashi fahimtar tafi riƙe ƴan gidansu, dan waccan hoton yaran gidan kakanninta ne, inda aka haifa Ummanta. Koda tazo kan Kawu Tanimu sai ta sake fashe masa da kuka da faɗin, “Dada dan ALLAH wacece ni? Ina duk waɗan nan suke? Nasan duk na san su. Musamman Kawu Tanimu na”. ( Alhamdullahi) Ya faɗa a zuciya. A zahiri kam cike da lallashi ya furta, “Karki damu zamuje inda suke idan lokaci yayi in sha ALLAHU. Wannan fa waye shi?”. Ya nuna mata Babanta data tsallake batace komai a kansa ba. Idanu sosai ta zuba masa, sai kawai kanta ya shiga sarawar ciwo. Da sauri ta dafe shi tana faɗin, “Wayyo Dada kai na”. Har tana neman sakar masa laptop ɗin ƙasa. Da sauri ya tareta ta kwanto jikinsa gaba ɗaya. Itama laptop ɗin ya riƙe. Saman table ɗin gabansu ya ajiye, ita kuma ya rungumeta sosai dan jikinta rawa yake. Abun kamar wasa sai ga Nimrah na neman rikice masa, sai da ya riƙe mata kai yana mata addu'a. A hankali ta fara sauke numfashi da ajiyar zuciya a jajjere, sai barci. Yanda take barci kanannaɗe a jikinsa ya sashi zuba mata idanu. Abubuwa zuciyarsa keta tuna masa a kanta, ciki harda tuna ranar farko da suka haɗu da Mamanta ɗauke da tsohon cikinta. UBANGIJI mai rahama da jinƙai. Mai tsara al'amura a yanda yaso. A lokacin inda za'ace masa abinda ke a wannan cikin abinda zai mallaka ne matsayin matar aure sai yace mai faɗar baida hankali ma. Amma shi UBANGIJI ikonsa mai girma ne. Ya ja numfashi ya fesar, tare da lumshe idanunsa a hankali. Kiran sallar magrib ya sashi miƙewa ɗauke da ita ya shinfiɗar a saman gadonsa. Fuskarsa da guntun murmurshi ya kai hannu ya shafa fuskar ta, kafin ya gyara mata hulan kanta ya wuce bayi yin alwala......

//★//★//★//★//★//

Tun kafin ta iso falon ƙamshinta ya iso hancinsa. Turaren nan nata na rikita masa lissafi tun ba yanzu ba. Yana dakewa ne kawai kada ai abin kunya. Amma yau sai yake jin kamar ma bazai iya hakan ba. Biebah da bata san yanayi ba tai sallama a ƙofar falon. Koda ya amsa da bata iznin shiga kanta a ƙasa ta shigo. In dai haƙuri ne da rashin son hayaniya shi shaida ne akan Biebah ɗinsa. Ta ɗakko halayya da yawa na Mammah. Rashin kamaninta da su Haysam baisa ya taɓa kawoma ransa ba mahaifinsu ɗaya ba. Sai a jiya da Haysam ɗin yay masa bayani da kansa. Ya kuma tabbatar masa mahaifin Biebah ɗin na nan a raye. Hasalima ya ƙara bunƙasa da dukiya, kuma bai ƙara samun haihuwa ba har yanzu. Wannan abu ya ɗaure kan sa sosai, dan shima ana faɗar sunan ya sanshi. Dan mutum ne daba ɓoyayye ba. Lallai akwai baban al'amari a tsakanin wannan ɗiya da mahaifinta, ga shi kuma wani ikon ALLAH tana bala'in kama da shi, ya tabbatar koshi yaga Biebah a yanzu ba asiri ba komi ke kansa sai zuciyarsa ta girgiza. Dan kamanin bana wasa bane ba fa.... “Yaya sannu da zuwa. Kayi haƙuri na saka jira”. Furucin Biebah ya katse masa tunani. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke da sakin murmurshi. “Ba komai, ai amarya bata laifi”. Bata wani kawo komai a ranta ba tunda tasan dai bai wuce akan saka rana ba. Sai tai ɗan murmurshi kawai tana sunkuyar da kai. “Ina Baby na?”. Ta faɗa cikin son ture wancan zancen. Ɗiyarsa take kira Babynta. Wannan kuma yana cikin abinda ya saye zuciyarsa da shi sosai. Ya nisa kaɗan yana gyara zama. “Babyn ki na lafiya. Duk da yau kwana biyu banje na gansu ba nima. Aiki yamin yawa sosai. Amma koda nake fitowa ɗin nan munyi waya”. Tai murmurshi tana jinjina masa kai. “Masha ALLAH. Ya jikin Hajiya?”. “Alhamdulillah da sauƙi itama.” Ruwan data zuba ta miƙa masa. Ya haɗa da hannun nata ya riƙe. Hakan ya sata daburcewa dan bai taɓa mata hakan ba koda da kwatance. Kallonsa ta ɗan yi ta janye idanunta dan haka yay murmurshi da faɗin, “Kowa kin tambayi ya yike amma ni banda ni. Anya akwai amana a wannan sabgar Biebalo.” Kanta a sunkuye tana murmurshi ta ce, “Ai kai na ganka kana lafiya”. “Tab sama-sama dai. Bakiga duk ma na rame ba”. Ɗagowa tai ta kallesa fuskarta na nuna damuwa. Ta ce, “Miya same ka?”. “Ƙaunar Biebalo da tsananin buƙatar ta a kusa dani mana”. Ya faɗa kansa tsaye yana ja mata hanci. Wata muguwar kunya data rufeta bata ma san ta furta, “Kai Yaya na banu”. Dariya yayi sosai. Dan yanda tai ɗin dole ta baka dariya. Sai da yasha ruwan ya ajiye kofin sannan ya gyara zamansa da faɗin. “Da gaske nake fa. Shiyyasa ma kikaga inata dojema zuwa gidan nan. Dan nasan bazan iya kauda idanu na ba.” Ita dai yau gaba ɗaya yana neman rikitata da kalamansa. Abinci ta buƙaci zuba masa. Yace ta barshi sai yaje salla ya dawo magriba ta kusa. Ta jinjina kai tana miƙewa ta koma kujerar nesa da shi kaɗan kamar yanda ta saba. Bai hanata ba ya cigaba da janta da hira har aka kira sallar magriba sannan ya miƙe ya shiga bayin cikin falon ɗaura alwala...........✍️