Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 36

Post

Kida a ruwa Book 3 page 36

..... they ate something. Even when he asked them about Afeef, he did nothing but cry for help. Hanoon was also unable to answer. When it came to Nimrah, she said that she did not lose anything. And she didn't take a bath. Then she confused the doctor's mind again. Her hair didn't touch anything on her body. In the end, he blurted out that it was her strong blood that's why hers was not as strong as theirs. He will give her an injection like them and she will tell her that the medicine will be wasted since it is not as good as theirs. Her itch has also started to subside. The medicine was gone, it was said that they should be taken to a room to lie down so that they can sleep. Nimrah did not take any medicine. Full of strategy, she turned Ruky over and brought her water in her hand. So even when they went to the room, they closed the door and danced.... GOD has prepared 🥱. Today, Afeef realized that GOD is the same as Hanoon😂🏃🏼‍♀️. \••••\••••\••••\••••\ Five minutes left, Dada returned home. His mind is all there. No wealth from the Asr prayer left the office. He did not find anyone in the hall. Then they went to Kulu to prepare Faro's food in the guest room. Biebah is in the room

Standalone post1,761 words

36

.........“Muguwa, wlhy dama na zargi ƙarya kike. Kai Trouble Queen kin iya munahinci”. “Bazaki gane ba Trouble Buddy, dole fa sai da haka. Idan ba hakaba kin san halin Mammah tsaff zata ramfomu. I sauri bani kaya na canja mu koma kada a cigaba babu mu kallo ya wuce”. Kwantar da hankalinki ai ina mana video. Tafawa sukai Nimrah na rungume Ruky. “Sai dake abokiyar ɓuruntu. Dole mai bakin uwa yasha bulalarmu”. Haka suka cigaba da shaƙiyancin su kafin a canja riga a fito. Sai dai yanzu Nimrah ta rage nata soshe-soshen wai taji dama-dama data cire rigar. A wannan halin su Ja'afar suka iso gidan. Sai kuma ga doctor da suka kira shima ya iso. Nan fa doctor ya fara duba Afeef da yafi jin jiki. Abinka da fata fara jikinsa yay burɗin-burɗin kuma jazur kamar borin jini. A haka ma na Hanoon yafi nunawa saboda bayan farin ta tana ƙarawa da mai ita. Shi dai doctor bai gane komai ba sai hasashen Allergy ne kawai. Maybe ruwan da sukai wanka da shi ne. Nan fa kowa yace badai ruwa ba. Sai dai ko wani abu suka ci. Koda ya tambaye su shi Afeef Banda kukan a taimakeshi babu abinda yake yi. Itama Hanoon ta kasa bada amsa. Sai da aka zo kan Nimrah ne tace ita bataci komai ba. Kuma batai wanka ba. Sai ta sake rikita tunanin doctor. Gashi ita bai maga komai a jikinta ba. Ƙarshe sai ya ɓige da wai jininta ne mai ƙarfi shiyyasa nata bai ƙarfi kamar nasu ba. Zai mata allura kamar su ta wayance ita dai a bata magani kawai tunda bai kai nasu ba. Nata ƙaiƙayin ma ya fara sauka. Maganin kuwa ya bata, akace a kaisu ɗaki su kwanta dan zasu iya yin barci. Nimrah bata sha magani ba. Cike da dabara ta juyema Ruky data kawo mata ruwa shi a hannu. Dan haka koda suka je ɗaki ƙofa ma suka rufo suka hau rawa....

ALLAH ya shirya🥱. Yau dai Afeef ya gane ALLAH ɗaya ne shi da Hanoon😂🏃🏼‍♀️.

\••••\••••\••••\••••\

Biyar saura wasu mintuna Dada ya dawo gida. Dan hankalinsa duk yana nan. Babu arziƙi daga sallar Asr ya baro office ɗin. Bai samu kowa a falon ba. Sai su Kulu dake kai-kawon shirya abincin Faro a falon baƙi. Biebah na ɗaki tana shiri. Mammah ma bata fito ba tai zaman azkar bayan sallar la'asar. Afeef da Hanoon suna can suna barci wahala. Nimrah na ɗaki a zuwan barcinta take, sai dai hirarsu ma suke sha da Ruky hankali kwance, sai dai dole ake ƴar ƙasa-ƙasa kar asiri ya tonu. Mammah ta amsa sallamar Dada tare da bashi izinin shigowa. Cikin kasa ɓoye mamakinta ko zama bata bari ya ƙarasa yi ba ta ce, “Yau dai ka dawo da wuri ALLAH yasa lafiya?”. “Mammah kece kika tayar min da hankali. Duk da su Ma'aruff sun min bayanin doctor ya duba su”. “Nima na rikice a ɗazu ɗin ne. Yara duk sun rikice kamar masu aljanun susa”. “Mi doctor ɗin yace to?”. “Wai ƙila wani abu suka ci da jikinsu baya so. Amma ita Nimrah ma da sauƙi. Hanoon da Afeef ne suka fi jigatuwa kam. Duk suna can suna barci ya musu allura”. Karan farko Dada yay ɗin jim cikin nazari. Sai dai baice komai ba ya miƙe yana faɗin, “Bari na gansu”. Miƙewa itama Mammah tayi suka fita tare. Ɗakin su Nimrah ne kusa da nata. Dan haka nan Mammah ta fara nufa yana biye da ita. Tana taɓa ƙofar da yake kunnen su a wajen yake Nimrah ta baje, Ruky ta yayimo blanket ta rufa mata. Ta koma gefenta ta zauna tana ɗaukar littafi batare data duba inama ta buɗe ba. Sai da su Mammah sukai sallama ta gyara fuska alamun tana cikin damuwa ta amsa, ganin harda Dada ƙirjinta ya buga. Yawu ta haɗiya masu nauyi tana ambaton sunan ALLAH da miƙewa. Sai kuma ta rissina tana gaida Dada da tunda ya shigo idonsa akan littafin hannunta ya fara sauka. Koda ya amsa mata sai karaf ta ce, “Mammah bari na kawo ma Dada ruwa naga yanzu ya shigo”. Bata jira amsar su ba ta fice. Dada kawai ya girgiza kai murmushi na son ƙwace masa, amma sai ya basar yana maida hankalinsa ga Nimrah da Mammah ta yayema bargo sai wani nishi-nishi take. Kallonsa da Mammah ta ɗago tayi ya sashi ƙarasa takawa gaban gadon sosai, ya wani zubama mutuniyar ido. Tsaff kuwa suka shige cikin nata. Yanda take fiki-fiki da su tana narke fuska tamkar zata saki kuka sai taso bashi dariya itama. Bai dai dara ɗin ba ya kauda nashi. Dan fuskar tasa ma a tsuke take tam. Nimrah aka sake narke murya ita a dole mai ciwo ana gaishe shi. A taƙaice ya ce, “Ya kike ji?”. “Dada na samu sauƙi. Sai dai bakina ɗaci. Jikin kuma har yanzu yana zafi. Ga barci ina ji yaƙi zuwa”. Yanda ta jero zantukan yasa Mammah ƙara rikicewa. Ta fara salati da faɗin, “Sai ya sake kira mata likita ya dawo a kuma dubata ko ya kaisu asibitin tunda su Ja'afar sun koma kasuwa. Ga su Bilal babu wanda ya dawo.” “Mammah relax, normal ne zata daina ji. Badai ya basu magani ba?”. “Muhammad bazaka gane ba yaran nan sun sha wahala wlhy”. “Tunda an basu magani wahalan ya ƙare ai. Ta kwanta ta rufe ido barcin zai zo.” Ita dai Mammah badan ta gamsu ba suka baro ɗakin. Na su Biebah suka shiga. Anan kam kallo ɗaya yayma Hanoon dake barcin wahala ya san ga asalin mai jiyyar nan dai. Da yake barci take Biebah ce kawai data gaida Dadan tai masa bayani akan Hanoon ɗin nanma suka fito. Daga nan yace Mammah basai ta haura sama ta wahala ba ta bari zai duba Afeef ɗin shima. Dan haka shi kaɗai ya shiga ɗakin Mu'azz ya duba Afeef dake barcin wahala a tuɓe an ware masa ac kamar Hanoon yayi ɗai-ɗai a gado. Dada dake ayyana (JIKI MAGAYI AI) A zuciyarsa ya fita zuwa nashi ɗakin. Sai a lokacin murmushin da yake ta riƙewa ke fita a fuskarsa, dan tun a kallon farko da yayma Ruky ya gane basu da gaskiya, saboda book data riƙe ma ƙasa ne a sama, itama uwar dabar langyaran nata ya san na bogi ne. Yaran nan sai a barsu kawai. Wanka ya shiga. Bayan ya fito yana shiryawa ya kasa shanye tambayoyinsa. Waya ya ɗauka yay kiran Mammah yace ta saka Ruƙayya ta kawo Nimrah ga wani magani zai bata saboda ɗacin bakin itama ta samu tai barci. Mammah bata kawo komai a ranta ba ta aiki Hinde dake zuba mata shayi ɗakinsu Nimrah. Hinde na isar da saƙon Mammah aka shiga yar kallan kallo tsakanin Nimrah da Ruky, sai dai ba damar ƙin zuwa. Ga Hinde taƙi tafiya dole suka shanye maganar bakunansu, Ruky ta kama Nimrah tana sake jangwaɓewa kamar gaske suka nufi upstairs ɗin. Dariya taso kama Kulu dake hangensu ta ƙofar kitchen. Anya ta taɓa ganin yara masu rashin ji irin waɗan nan biyun? Maza sukafi irin wannan iya shegen, amma su sun ma fi wasu mazan...

Ruƙayya tai knocking, Dada dake zaune a cikin kujera ya basu izinin shigowa. Har suka ƙaraso inda yake bai ɗaga kai ya kallesu ba, yanata rubuce-rubucen sa kamar ma bai san da su ba. “Zaunar da ita kije ki haɗa min abinci”. Yay maganar tasa cikin ishara ga Ruƙayya. Kamar dama abinda Ruky take fata kenan tsilim ta nufi ƙofa. Nimrah kamar zatai kuka ta bita da kallo. Sai dai babu damar magana. Mintuna kusan biyu da fitar Ruky Dada yayi kamar ya manta da Nimrah, sai ta hau gyangyaɗin ƙarya. Abinda bata sani ba duk motsinta akan idanunsa ne, dan ta gefe yake kallonta yana aikinsa. A bazata ya furta. “Sai yanzu barcin yazo kenan?”. Fiskewa tai kamar bataji ba. Ta cigaba da gyangyaɗin har kamar zata tuntsura. Ɗagowa yay a karo na farko ya zuba mata idanu, tasirinsu ya sata jin rikicewa. Tai wani laɓai-laɓai da fuska tana kawo numfashi mai nauyi irin ta farka ɗin nan. Suna haɗa ido ya ɗage maga gira sama. Kame-kame ta fara da faɗin, “Dada barcin ya fara zuwa, naje na kwanta dan ALLAH?”. Bai amsata ba saboda dawowar Ruky datai knocking da sallama. Izinin shigowa ya bata. Ruky na ajiye tray ɗin abincin a table ɗin gabansa, cikin shagwaɓa ta ce, “Dada Mammah tace na koma yanzu zan kaima Uncle Haydar da yazo ruwa shima”. Nuni yay mata taje, dan baya son ma yayi magana koya kalleta ya sake rikitata. Dan ya fahimci a halin da take ciki. Tun bayan gama tantance halayensu ya gane uwar dabar tafi na'ibar tata dakewa idan suka aikata abu. Tuni Ruky ta fice abinta tanama Nimrah Addu'ar fitowa lafiya itama....

★★★

A dai-dai wannan lokacin kamar yanda Ruky ta faɗa Faro ne ya iso gidan. Dan tunda aka ɗaura auren nan bai zoba aiki ya musu yawa a UNIT ZERO. Weekend yaso zuwa hakan bai samu ba. Shekaran jiya waccan kuma Biebah ta marairaice masa wai suna sunan baby. Yau ma ɗan lokacin da yaga yana da shi yace bari yay amfani da shi, saboda in har suka kama yaran nan bakwai da suke fako da Ojo baya jin za'a sake gane kansu kuma. Sai da ya fara shigowa ya gaida Mammah cike da jin kunya. Ita ko kowa nata ne. Bata nuna tama gane ƙunshe-ƙunshen da yake ba ta ce, “Idonka kenan Haydar?”. “Mammah ayi haƙuri, ayyuka ne sukai yawa a office. Ranar naso shigowa na gaida su Gwaggo Habibah tace kun fita gidan Baffa”. “Shike nan na haƙura. Ya wajen tsoffin? Duk da Hajiya muna waya dan taso shigowa sunan nan tace ƙafa ta sata gaba”. “Wlhy ƙafa ke damunta. Amma ina shirin suje Egypt a dubata tunda nan ɗin sai cin kuɗi ake ba wani canji”. “Ai asibitocin ƙasar nan sai addu'a. Na kuɗin ma dai gasu nan ne. Gara kuje can ɗin, ni bagashi na samu sauƙi ba sosai.” “Haka Haysam ke gaya min, shiyyasa ma yace a kaita can itama”... Sun ɗan taɓa hira kafin ya miƙe yana tsokanar Ruky data sakko daga sama tana gaishe sa. Dariya take da ɓoye fuska. Ya tambayeta Nimrah da Mu'azz. “Yaya Mu'azz na school. Ninah kuma na sama ɗakin Dada”. Faro yay dariya a zuciyarsa saboda maganar ƙarshe. A zahiri kam yace, “To ki gaida min su”. Kanta ta ɗaga masa. Daga haka ya fice domin komawa falon baƙi yaga ta inda ginbiyar tasa zata ɓullo ita kuma. Dan tunda ya shigo ko mai kama da ita bai gani ba..........✍️