
Post
Kida a ruwa Book 3 page 35
..... Nimrah laughs that Mammah has Small Mom with her. They are just not now. Mammah just laughs. {×××}{×××}{×××} No matter how Hanoon are careful with Ruky today, it seems that their evil will move. Ever since Afeef was released from the sky, they were looking at him and shouting. He ignored them until he got up and left the room. "You will kill your father. Bare feet like those of the middle class." Ruky said as she followed him with a bang. In the midst of Nimrah, she also said, "It is like a bird that is called a bird. It should be felt in his body today." Ruqayya said, "I personally want him to feel it first. Do you have a plan?". "There is. Come and hear...." She whispered to Ruky everything in her ear. They laughed. With applause. At that time, Biebah was coming out of the kitchen. Then they got tired. Dan didn't want her to understand anything, let alone stop them. The stranger did not understand. They are also working on fixing the guest room for her, today Faro will come. She also does things in the kitchen. Biebah was surprised when they got up and did not do this work. But then she lost everything and did not turn back. They came out and Hanoon said to Afeef, "Brother,
35
.......Yanzu saura Ruƙayya da Ammar. Duk da tasan Ammar na matuƙar son Ruƙayya, amma ita bama ta fahimci ina aka dosa ba, Ammar ɗin kuma da alama ya kasa faɗa mata. Tana fatan ALLAH ya daidaita su suma kamar yanda Bilal da Asma'u suke. Dan a yanzu itama babban fatanta su gama jarabawar nan kawai kowa ya tare ɗakin mijinsa ta samu nutsuwa. Hatta Nabeeha duk iskancin nan nata Mammah addu'a take mata ta shiriya kodan samun zaman lafiya a gidan, jinin Yaya Nasiru bazai taɓa zama abin ƙi a gareta ba har abada. Dan Nasiru ya wuce abin da zasu yarda. Wannan nasiha ta Mammah ta kawo masalaha su Ruky suka nutsu a ɗaukar lassing ɗinsu. Dama dai Alhamdullah a ɓangaren karatu basu da wasa. Ga Mammah ta musu register a online class ɗin Chef Yakudima. Dan ta aikoma Mammah alƙawarin data ɗauka na kayan snacks masu daɗin tsiya daya saka Mammah sake gamsuwa da aikinta. Ba'a nan Mammah ta tsaya ba, takan zaunar da su cikin hikima tana musu nasihohi da suka shafi aure. Wani lokacin Ruky kan dinga yi ma Nimrah dariya wai da ita Mammah take da Small Mom. Su dai ba yanzu ba. Ita dai Mammah takan yi dariya kawai.
{×××}{×××}{×××}
Duk yanda su Hanoon suke taka tsantsan da su Ruky yau da alama muguntar tasu zata motsa. Dan tunda Afeef ya sakko daga sama suke kallonsa suna ƙus-ƙus. Tun bai kulasu ba har yay tsaki ya tashi ya bar falon. “Zakaci ubanka. Shegen ƙafa kamar na ƴan tsaki.” Ruky ta faɗa tana raka shi da harara. Tsakin Nimrah taja itama da faɗin, “Ai garama ƴan tsaki kamar dai wani tsuntsu da ake kira zalɓe. Ya kamata yau yaji a jikinsa.” Ruƙayya tace, “Ni kaina ina son ya fara ji a jikin san. Kina da wani plan ne?”. “Akwai kuwa. Zo ki ji.......” Ta gwargawaɗama Ruky komai a kunne. Dariya suka sanya. Tare da tafawa. A lokacin Biebah ke fitowa a kitchen. Sai suka gimtse. Dan basa son ta gane komai balle ta hana su. Bako ta gane ɗin ba. Sai ma aiki data sakasu na gyara mata ɗakin baƙi dan yau Faro zai zo. Shima take yima abu a kitchen. Yanda suka tashi ba musu yin aikin nan ya bama Biebah mamaki. Amma sai batace komai ba ta juya ta koma. Sun fito sai karaf a kunensu Hanoon na cema Afeef, “Bro bakayi wankan bane?”. Ƙaramin tsaki yaja yana bata amsa da, “Banyi ba, wannan Mumun yaron ashe ya birke makunar water higher kafin ya fita. Shine na ɗan kunna ruwan yayi zafi a ɗakin su Dayyan na ɗibo acan Dad ya kirani na kawo miki waya”. Kallon juna Ruky da Nimrah sukai. A take kansu ya kawo haske. Komawa sukai da baya. Wuff suka shige ɗaki Nimrah na faɗin, “Ga dama ta samu ma ai basai anje da nisa ba”. “Kamar ya?”. Cewar Ruky yana waro idanu. Nimrah bata bata amsa ba. Sai ɗan goran dake ɓoye ta ɗakko tare da leda. “Da wanne za'a fara?”. “Kai jama'a. Hot pepper kin fini bala'i fa. Yanzu dan ALLAH wa kika saka ya samo miki abin nan?”. “Hahhh kina wasa dani. Kulu na saka shekaran jiya da zata gida. Wannan kalkashine kwanansa biyu kenan a jiƙe. Wannan karara ne”. “Miye karara?”. “Banza kefa haihuwar birni ce baki san komai ba. Wani abu ne mai shegen ƙaiƙayi. Idan aka sakama mutum sai ya koma kamar ya haukace”. Dariya Ruky ta sanya babu alamar tausayi. Ta ce, “Yayi yanzu ya za'ayi?”. “Muje ki gani”. Da sanɗa suka fito a ɗakinsu suka haura sama. Sun san Mammah barci take yanzu. Dan in tai sallar Azhar takan ɗan kwanta. Small Mom da su Kulu hankalinsu nakan aiki a kitchen. Uncles duk sun fice. Mu'azz ma na school. Dayyan kuwa basu san ina yake ba. Ɗakin Mu'azz da Afeef yake zaune suka nufa. Ɗakin kaca-kaca. Shiyyasa kullum Mu'azz cikin ƙorafi yake yanzu. Sai da suka rufe kofar sannan suka shiga Bathroom. Shi da ɗan sauƙi a gyare yake, sun san kuma Mu'azz ya gyara kafin ya fita. Sun san shower gel ɗin da Mu'azz ke amfani da shi. Dan haka suka ɗauki ɗayan da suka tabbatar na Afeef ne. Tsabar mugunta yana da yawa fa a ciki amma suka tatse rabi a wata robar sabulu da babu komai ciki suka haɗa da kaf kayan wankan bayin suka ɓoye sannan suka zuba karara a sauran suka ajiye. Sosansa ma suka ɗauka suka barbaɗa. Sun fito a bayin kayansa da ya ajiye kan gado alamar su zai aka suma suka barbaɗa sannan suka fice. Suna sauka Afeef ke hawowa. Suka sha mur kuwa. Tare da fara waƙar habaici ta ado gwanja. Har sunayi kamar zasu buge Afeef. Bai dai kulasu ba ya kauce musu hanya. Sai dai a ransa ayyanawa yake sai yaci uban yaran nan kwannan nan. Aikin Small Mom suka tafi yi, sai dai kunnensu ɗaya na nan sashen duk da falon a jikin babban falo yake. Sun ko kammala shara Ruky na saka turaren wutar SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Ita kuma Nimrah na fesa air freshener a labule suka jiyo ihun mutumin nasu. Wata muguwar dariya suka sanya. Sai da sukai mai isar su suka shanye kamar basuyi ba suka fito a guge babban falo.... Mi zasu gani. Afeef tsirara jiki duk kumfa, dan itace ma ta rufa masa asiri. Sai soshe-soshe yake yana ihu kamar zai fasa gidan. Mammah da su Biebah tuni sun fito. Hakama Hanoon dake waje ta shiga da gudu jin ihun ɗan uwanta. Hankalin Mammah ya tashi bata ma san ta cire hijjab ɗin jikinta ta ƙudindine Afeef dake birgima a ƙasa ba ya rasa ina zai sosa. Da ƙyar Mammah ta ɗaura masa hijjab ɗin nan a ƙugu. Tsabar yaran nan sun ƙware da su aketa jajen miya sameshi? Sune ƴan cewa bari su duba ɗakin nasu. Suna shiga kuwa sauri-sauri sukaje suka juye sauran shower gel ɗin suka wanke robar suka juye wanda suka rage suka maida inda suka gani suka fito suna faɗin su basuga komai ba. Sun duba ko'ina kuma. Abu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Dan hatta su maigadi dasu Lailah sun shigo. Ga Afeef na neman ƙara yaye hijjabin Mammah ana dannewa. Ke Hanoon mai ɗan uwa ta tafi sama ɗakko kaya wai a saka masa. Aiko cike da mugunta Nimrah ta bita. Na saman gadon nan da suka zubama kararan ta nuna mata. Sam Hanoon bata ma gane dawa take tare ba, ta yayo suka sakko. Tana warware riga itama ya zazzagu a jikinta. Da yake bai fara ba bataji komai ba ta yaɓama Afeef riga taja zip. Tab ɗin, ai tamkar an yayyafama wuta gas haka Afeef ya ƙara haukacewa. Sai kuma Hanoon ɗin ta fara zabura itama. A take sabon zance ya tashi. Hanoon ma ta fara susa tana ihu da tsalle-tsalle. Ganin haka kan Nimrah ya kawo wuta, tunda da ita akaje ɗaukar riga ai ya kamata tai pretending ko. Sai itama ta fara kamar gaske. Ruky tai zuru tana kallonta. Tun tana kokwanto ta fara yarda da tunanin tsautsayi ya haɗa da Trouble Queen kenan. Ita ko Mammah ta sake rikicewa. Batama san ta ɗauki waya ta danna ma Dada kira ba....
<<•••••••>><<•••••••>>
Dada na Office ɗin shugaban ƙasa a dai-dai wannan lokacin suna magana kiran Mammah ya shigo masa. Ya ɗan zubama wayar ido tare da tsayawa da maganar da yake yi. Hakan yasa shugaban ƙasa kallonsa. Shima ya ɗan ɗago zai nema excuse dan bazai iya ƙin ɗaga wannan kiran ba sai dai in a sume yake ko tsananin yaƙi kawai ke hanashi ɗaga wayar Mammah. Kafin ma yace komai shugaban ƙasa ya jinjina masa kai alamar ya amsa. Ya ɗan sauke numfashi yana miƙewa ya koma gefe yana ƙoƙarin kiranta. Dan nata har ya katse. Sai kuma gashi ta sake kiran ma. Hakan ya bashi tabbacin babu lafiya. Tun sallamar Mammah yasa zuciyarsa motsawa, ya dai dake ya amsa tare da gaishe ta. Bama ta amsa masa gaisuwar ba ta fara masa bayanin abinda ke faruwa. Harga ALLAH jin sunan Nimrah a ciki ya saka hankalinsa tashi. Amma sai bai nuna ba ma a hakan cikin dakewarsa ya ce, “Wani abu ne ya taɓa su Mammah?”. “Wlhy bamu sani ba Muhammad. Shi Afeef ma zance ko daga cikin ruwa ne. Sai kuma naga Nimrah da Hanoon ma daga ɗakko masa riga sun fara”. “Ki kwantar da hankalinki Mammah, bari na kira su Ja'afar yanzu suzo sai a kaisu asibiti ko'a kira doctor ya duba su.” “To dan ALLAH maza kira su Muhammad”.
Koda ya katse kiran sai da yay jimm kamar mai nazari. Sai kuma dai yay kiran layin Ma'aruff. Suma suna kasuwa suna faman lissafi dan a satin nan zasu bar ƙasar kawo kaya kiran Dada da umarninsa ya riskesu. Dole suka ajiye komai suka fito dan wucewa gida....
★★★★
Tsakanin Nimrah da Ruky kar ta san kar ne. Tun ba'ayi nisa ba Ruky ta gane ƙarya Nimrah take. Da ƙyar ta iya gimtse dariya ta lallaɓa ta ɗauki wayar Biebah ta kunna recording ɗin video. Abu ya kai yanzu Afeef susa harda cokali. Da wuƙa ma ya rarumo aka ƙwace. Ya koma bango, ganin bazai masa ba ya koma ya ɗakko cokula. Riga dai tuni ya saluɓe ya watsar. Hijjabin Mammah kam sai da aka tsawatar masa. Amma ya gwada son cirewa yafi sau babu adadi. Ita Hanoon da farko iya wuyanta ne da hannaye. Sai da ya kacame ta gudu ɗaki wai zatai wanka. Aiko tana zuboma kanta ruwan nan tun a bayin ta ƙara haukacewa. Da ƙyar ta iya ɗauro towel. Ganin haka Mammah ta hana Nimrah zuwa yin wanka, sai kaya da tace Biebah ta kaita ta cire. Caraf Ruky tace bari ta kaita. Suna shiga ɗaki Nimrah ta fashe da dariya.........✍️