Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 40

Post

Kida a ruwa Book 3 page 40

.....yes, seeing her is enough. Nimrah feels the weight of Mammah, she sees that she has a short smile. Then she looked at Jaafar and Lailah. But the fact that their parents were together gave her a sign that she was happy. So, if the offer is not made, the license has been lost. Full of confidence, she ended up walking in front of Dada, taking his head from the top. She kneeled in front of him and looked at him for a while, they were looking at each other and she quickly withdrew hers with a smile on her face. Dada, who was looking at her in his heart, said (Is this girl going to marry me?) and suddenly she felt her hand that was holding the cake was grabbed. She raised her eyes quickly. Seeing Dada's assurance, she threw them out. He looked calm and restrained and brought her hand to his mouth, his eyes in hers and held them looking into each other's eyes and ate the cake. He was holding her hand and put it back to her mouth and he raised his eyebrows a little to indicate that she also ate. Just like that, Nimrah opened her mouth and left the set where he left. Then he put his other hand and took away the one that Khadijah had put on her cheek and put it back on her nose.....

Standalone post1,518 words

40

.........“Yaran nan sun iya haɗa bomb”. Ma'aruff ya faɗa ƙasa-ƙasa yana ƙunshe dariya. Ja'afar ya bashi amsa da, “Dama sunan uwar daba ɗin kenan ai. Yau Dada ya shiga one chance. Bari muga zai amshi cake ɗin kuwa.” “Idan bai amsa ba ɗura zamuyi masa. Dan dole shegiyar matar can ta fita a falon nan da takaici, ta kuma tabbatar Ninah ɗinmu ce a sama”. Da ƙyar Ja'afar ya gimtse dariya... Anan kam koda Dada ya ɗago sai idanunsa a cikin na Nimrah dake fiki-fiki da nata tana kallonsa. Dai-dai Ruky ta bata mintsini tana ɗan sake turata gaban nashi. Juyowa tai zata harareta idonta ya sauka akan Nabeeha dake kallonsu da wani masifaffen yanayin ɓacin rai fuskarta kamar zata yo aman wuta. ALLAH sarki Mammah tsamm ta miƙe abinta tabar musu falon ma. Dan ta tabbatar idan tana nan Dada bazai amshi cake ɗin nan ba. Kuma koba komai ita kanta sai taji tana son Nabeeha ta fahimci irin Nimrah suke buƙata a rayuwar Muhammad, idan kuma ta kasa canja kanta tana ji tana gani Nimrah zata ƙwace komai da take ganin ita itace ta isa. Nimrah dama harda nauyin Mammah take ji, tana ganin ta wuce tai gajeren murmushi. Sai kuma ta kalla su Ja'afar da su Lailah. Amma tsabar shaƙiyancin iyayen nasu a tare sukai mata alamar tayi harda jinjina👍. To dama ba'ace tayin ba tayi bare ma an bata lasisi. Cike da jin ƙwarin gwiwa kuwa ta ƙarasa takawa gaban Dada daya ɗauke kansa tun ɗazun. Kneeling tayi a gabansa ta ɗan kallesa, suna haɗa ido ta janye nata da sauri tare da wayancewa ta lakatama Khadijah dake a hannunsa cake ɗin kamar dama ita tazo yima hakan. Dada dake kallonta a ransa yace (Kam yarinyar nan ni zata yarfa?) sai kawai a bazata jitai an kamo hannunta dake riƙe da cake ɗin. Idanunta ta ɗago da sauri. Ganin tabbacin Dada ɗin ne kuwa sai ta waro su waje. Shi ko ya fuske cike da nutsuwarsa da kamewa ya kai hannun nata kusa da bakinsa idanunsa a cikin nata ya riƙesu suna kallon juna cikin ido ya gutsira cake ɗin. Yana dai riƙe da hannun nata ya sake maida shi saitin nata bakin ya wani ɗan ɗage gira alamar itama ta ci. Kamar sokuwa haka Nimrah ta buɗe baki ta gutsira saitin inda ya gutsira ɗin. Sannan ya saka ɗayan hannunsa ya kwashe wanda ta sakama Khadijah a kumatu ya mayar kan hancinta batare da kowa ya ji abinda ya faɗa ba ya motsa lips kaɗan ya furta, “ALLAH yasa nan da wata shekarar kin zama Mummy”. Da sauri Nimrah ta waro idanu tana wawwaugawa inda kowa yake. Tare da fatan ALLAH yasa babu wanda yaji miya faɗa. Basu ji ɗin ba, amma yanda tayi duk sai suka tsargu. “Awwwwwww!!”. Ja'afar da Ma'aruff suka faɗa cike da shaƙiyanci. Kunya ta kama Nimrah sai kawai ta duƙe kanta a cinyarsa batare data farga ma da abinda tayin ba. Shi kuma kawai ya shafa kanta yana sakin wani ƙayataccen murmushin da ya bama kowa mamaki a wajen. Dan Mammah suka fi ganin yanama irin wannan murmushin mai sanyi, da armashi dake bayyana cikakken shauƙin farin cikinsa. Ja'afar da Ma'aruff suka tafa. Ma'aruff ya ce, “Oh-oh proud of you Daughter kin ciwo mana kofi”. Harara Dada ya wulla masa, sai kuma ya kauda kai yana ƙoƙarin haɗiye murmurshin dake neman suɓuce masa. Su Lailah da Shariffa kuwa aka duƙar dakai ana ƙunshe dariya. Ammar, Mu'azz Biebah kuwa hannu suka sa suna rufe fuska suma su a dole sunji kunya. Halin da Nabeeha take ciki ba'a magana, gefe ga Rayhana da Hanoon zukata kamar zasu fashe. Ismat da Amima ƴar uwarsu suke tayawa kishi.

Da ƙyar aka samu Ninrah ta ɗago a jikin Dada. Shima sai ya miƙe batare da yace musu komai ba ya saka mata Khadijah a jiki ya wuce sama. Kamar jira suke dama ya bar falon. Su Ammar suka zagayeta suna liƙa mata kuɗi. Ruky kuwa da Biebah suka rungumeta ransu fal farin ciki. Ma'aruff da Ja'afar suka sake kunna al'amarin suka hau mata liƙin suma. Ihun su Afrah da dariyar su Lailah da su Mu'azz ya ƙara kunna wutar baƙin ciki a zuciyar Nabeeha. Kawai taji kamar ta fashe da kuka. Hanoon kuwa da gudu ta bar falon itama nata kukan na tahowa. Rayhana da jikinta ke rawa ji take kamar taje ta shaƙe Nimrah. Dan yau ko makaho ya san abinda Dadan yayi a bayyane yake yana son yarinyar. Nabeeha ta yinƙura zata miƙe dan ta gama cin alwashin wlhy yau ko ita ko Nimrah sai dai wani ya mutu Amima da Ismat suka rirriƙeta. Duk da itama Ismat ɗin nata kishin akan Shariffa na cimata zuciya. Sai dai bata son suyi wani abinda ɗan sauran mutuncinsu zai ƙarasa ɓarewa. Amma tabbas yau ta sake tabbatar da akwai aiki ja a gaban ƴar uwarta. Dan wlhy babu shakka ƴan uwan Dada da yarinyar nan zasuyi amfani wajen ɗaukar fansar duk abinda Nabeeha tai musu a baya. Ko wanda bai san mike faruwa ba yaga abinda suke mata a yanzu yasan da biyu ne...

Oho suke lissafinsu, su ko su Ruky shagalinsu suke. Dan sun ma koma cin cake batare da sun nuna sun tuna su Nabeehar na a falon ba ma. Dan haka suma suka tashi suka fice zukatansu kamar zasu kama da wuta....

∆×××∆×××∆×××∆

Washe gari a bazata Dada ya gwangwaje Ruky da Nimrah da wayoyin iPhone sabbi dal a kwali ƴan yayi. Sai kuma ga su Ja'afar da laptop guda biyu suma da dama sukai musu alƙawari tun kwanaki. Wayyo zo kaga farin ciki da murna kamar zasu fasa gidan. Da ƙyar suka bar kunnen mutane ya huta.

A ranar da dare su Ja'afar suka wuce. Suda ƙasar su kuma sai satin biki idan ALLAH ya kaimu. Washe gari shima Bilal ya dawo. Sosai su Nimrah ke murnar dawowar sa. Dan kaf kawunan nan nasu babu mai taya su akan shiriritarsu irinsa. Hutun kwana biyu zai yi kafin komawa aiki. Da wannan hutun nasa Dada yay amfani ya turashi ƙauyen su Malam Ari tsohon driver. Batare daya sani ba kuma su Dabo suka bi bayansa suka samu address ɗin. Washe gari ya shirya zuwa ganin tashi ginbiyar, su Nimrah suka maƙale masa dole yaje da su. Shi dai ya daure ba kamar su Ammar ba. Dan sunyi hirarsu kamar yadda suka saba ko taɓa Asma'u baiyi ba. Su Ruky ma nata musu kai-kawo ina ya samu wannan damar. Da zai dawo ya tarkatosu suka taho harda Lolo zai ƙarasa weekend ɗinsa...

★★

Aiki ya matuƙar yima su Dada yawa. A yanzu ko lokacin shirmen gidan baida shi. Ga office ga aikin bayan fage. Su Dabo sun sami nasarar ƙwamuso masa Malam Ari. Sannan sun kwashe iyalansa dan sun fahimci akwai matsala. Waje na musamman Dada yasa suka ajiyeshi. Acewarsa sai bayan biki zai fuskance shi. Dan abu nata matsowa ga Office ma ya ɗauki zafi sosai. Ranar wata Laraba kawai a bazata aka kai wasu mugayen hare-jare a gabashin ƙasar data tada hankalin kowa musamman jami'an tsaro. Nan fa aka shiga sukar ministan tsaro da NSA. Shi kansa Dada hankalinsa ya tashi. Amma ya hana Imran yin magana da manema labarai dan ya fahimci harin tsokana ne. Wasa farin girki ai sai abu ya ƙara tsamari. Satar shanu, kidnapping mutane da zuwa a tada ƙauye babu gaira babu dalili. Abu ya kai har bomb ya tashi sau biyu a tasha da kasuwa. Dole tako wane fanni Imran ya shirya ninka tsaron jami'ai. A bayan fage Dada na aiki da su Faro. Shugaban ƙasa duk da ya fahimci shirin babba ne yanata ƙarfafa kansa da ƙarfafa su Dada. Ga ƴan jam'iyya da masu muƙamai sun masa caaa wai sai a canja Imran akan harkar tsaro dan babu abinda zai iya. Shi kuma ya muna musu ai dama Imran bai ce zai iya komai ba ALLAH shine maiyi. Dan haka suje suyi addu'a. Sannan suma aikin nasu ne bana Imran shi kaɗai ba. Wannan magana ta musu zafi, suka ƙara ƙullatarsa da komawa gefe suna masa zagon ƙasa har wasu na iƙirarin son barin jam'iyyar. Shi ko ya toshe kunensa yayi kamar bai san sunayi ba......

★★

A ɓangaren su Nimrah ma sun fara exams. Dan haka shiriritarsu ta rage a gidan. Yayinda su Aunty Mommy keta shirin hidimar biki dake ta matsowa. Duk da halin da ƙasar ke ciki da yanda su Dada sam basu da lokacin kansu na tayar musu da hankali kamar kowa. To amma ya za'ayi, dama ai ana bikin duniya ake na kiyama. Dan haka hatta gyaran jiki su Lailah da Aunty Mimi sun fara yima amare. Asma'u da Biebah na gidan Aunty Mimi. Nan kuma su Shariffa da Lailah suke kan su Ruƙayya. Aunty Mommy da Aunty Ummi suna nasu shirye-shiryen. Hakama Ummu matar Uncle Nasiru. Su Nimrah amare kuwa daga exam sai islamiyya da class ɗin Chef Yakudima 08135358038. Duk wani aiki na gidan an sauke musu shi. Ɗakin Dada ne dole Nimrah take gyarawa sai dai ba kullum ba. Dan yanzu ma yakan haɗa sati bai kwana a gida ba yana UNIT ZERO..........✍️