Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 41

Post

Kida a ruwa Book 3 page 41

.....uk he didn't know who he was. Better than Sanda as he has a loud mouth. At Sanda Mole, he heard Nimrah taking the exam. So they put their plans on the school. But what Dagger doesn't know is that Mole has his own plan behind the scenes. Dan has already established a friendship with a man who is related to them, and they bring them food every end of the month in the places where they are. This man is the one who gave him a way to get a house in the neighboring country. A good man was found, and he himself went according to a task that Dagger was part of and saw the house. He did not come and everything had to be poured in three days. Workers were recruited and poured and then he returned. Even now that Dagger has brought up the issue of Nimrah, he is not worried since he knows that he has completed his plan as well..... >>>>>>%<<<<<< Here, Nabeeha is very concerned about the upcoming wedding. As soon as she heard what was going to be done, Nimrah would stay with her. It was hard for her to see Dada in the house. Even the Mammah did not see him. Then her mother scolded her as a result of which the First Lady also framed her. She assures her that if she wakes up, Adeel is waiting

Standalone post1,619 words

41

.........A ɓangaren ƴan Kungiyar Duhu gadai nasarar kai hare-hare da tada hankalin al'umma sun samu amma sun kasa jin farin ciki da gamsuwa saboda yanda su Dada suka matsa musu. Sai kama musu yara masu musu aiki akeyi. Tun abin baya damunsu har ya fara ɗaga musu hankali. Ranar suka kira Dagger babban yaronsu dake da mafi rinjaye yara suka masa tas. Da nuna masa idan fa ya fara gazawa zasu nema wanda zai iya. Kalamansu sun masa zafi amma ya danne bai nuna musu ba. Sai da ya koma gida ya samu Mole shima cikin nashi ɓacin ran yace masa lokacin da zasu fara nasu shirin suma yayi fa. Amma sai sun ɗakko Nimrah dan shine first target ɗin su. Ɗakkota lokaci guda kuma bazai yiwu ba dole sai Mole ya nuna mata fuskarsa da sanar mata waye shi a gare ta. Tunda yanzu babu mai basu information ɗin gidan yanda ya kamata. Gaba ɗaya Nimrah ɗin ta daina kiran Dagger, sai ma Sanda da shi Molen ke ɗan taɓawa a waya lokaci-lokaci shi da maigadi. Shi kuma maigadi tsoro na hanashi sanar da Mole wani abun duk da bai san waye shi ba. Gara ma Sanda da yake yana da bakin surutu. A wajen Sanda Mole yaji su Nimrah na zana jarabawa. Dan haka suka ɗora shirinsu akan binta makarantar. Sai dai abinda shi Dagger bai sani ba shima fa Mole na nashi shirin a bayan fage. Dan tuni ya ƙulla abota da wani mutumi dake da alaƙa dasu, dan suna kawo musu kayan abinci duk ƙarshen wata a jejunan da suke. Wannan mutumi shine yay masa hanyar samun gida a maƙwafciyar ƙasar. Aka kuwa samu mai ƙyau, da kansa yaje bisa ga wani aiki da Dagger ya sashi yaga gidan. Bai taho ba kuma sai da aka zuba komai a kwanaki uku. Aka ɗauki ma'aikata aka zuba sannan ya dawo. Ko yanzu da Dagger ya kawo batun Nimrah baiji ya damu ba tunda yasan ya kammala shirinsa shima.....

>>>>>>%<<<<<<

Anan kuwa Nabeeha ta matuƙar tada hankalinta akan batun bikin nan dake tunkarowa. Dan tunda taji abinda ake shirin yi Nimrah zata tare shike nan. Gashi ganin Dada ya mata wahala a gidan. Suma su Mammah ɗin ba ganinsa suke ba. Sai da mahaifiyarta tai mata tsawa sakamakon itama First Lady ta tsarata sannan. Ta tabbatar mata idan fa ta tada hankalinta Adeel na nan na jira. Dan yanzu ɗin ma akwai aikin da ta saka akai mata a kansa shiyyasa hankalinsa yabar kansu. Dan baya ma ƙasar yanzu haka. Abinda Hajiya Hasiba bata sani ba kuwa babu wani asirinta da yaci Adeel. Ya tafi harkar kasuwancinsa ne kawai da kuma tsarin da First Lady ta zauna ta masa batare da sanin ita Hajiya Hasiba ba. Amma dai kalamanta sunyi tasiri akan Nabeeha. Musamman data tabbatar mata akwai abinda take shiri akan Nimrah. Amma sai ta tare dan aikin yay musu sauƙi tunda yanzu tana sashen Mammah ba wani abu zasu iya a kanta ba. Duk maganar da sukai Rayhana na laɓe na jinsu. Hakama Nana, sai dai babu wanda yasan da ɗan uwansa. Wannan shine ya kawo masalaha akan Nabeeha sai dai ta saka kanta a damuwa sai rama take da duhu. Tun Ismat da Amima na lallashinta har suma suka gaji suka watsar da ita. Jiddah dama ta maida kanta gefe. Ko zuwa tai gidan suka kawo mata ƙorafi iyaka tace suyi hakuri kowa ma hakuri yake a nashi gidan. To sai ma sukai tafiya ita da mijinta yanzu haka basa ƙasar suma.....

••}{••}{{••}}{••}{••

A yau su Nimrah sukai final exams ɗinsu. Ba wani sabawa sukai da kowa ba dan haka suna kammalawa suka fito a hall ɗin cikin farin ciki. Kullum Mu'azz ke kawo su. Idan ya tashi school da wuri yazo ɗaukar su. Idan yana da lecture Biebah tazo ta ɗauke su. Dan haka koda suka fito sai suka nema waje suka zauna. Abokan jarabawar tasu nata farin ciki da shagalinsu saboda su sun san juna. Su Ruky ne kawai baƙi a cikinsu. Su dai kallonsu kawai suke, dan zasu iya rantse wa ma bayan gaisuwa doguwar magana bata taɓa haɗasu da kowa a cikinsu ba tsawon kwanakin jarabawar nan. Nimrah ta fara ƙorafi saboda barci da take ji sai ga kiran Mu'azz ya shigo wayarta. Miƙewa tai tana faɗin, “Alhammdullahi Buddy tashi yazo”. Miƙewar itama Rukyn tai tana ambaton Alhmdllh ɗin, daga haka suka fito a gate ɗin makarantar. Kansu tsaye inda motar Mammah take suka nufa, dan da ita Mu'azz ko Small Mom ke kawosu dama su ɗaukesu kullum. Kai tsaye Nimrah ta buɗe baya tana faɗin, “Barci zanyi shiga gaba dan ALLAH Ruky. Bata jira amsarta ba ta buɗe bayan ta shiga. Itama Rukyn ta shiga gaban. “Subahannallahi waye kai?”. Ruky ta faɗa tana zabura, sai dai bata kai ƙarshen maganar tata ba aka fesa mata abu. Itama kuma Nimrah anan baya ta zabura ne ganin mutum a bayan kusan lokaci ɗaya da Rukyn. Sai dai ita saɓanin Ruky ca tai, “Baba driver”. Malam Buba yay mata murmushi da faɗin, “Na'am Uwa”. Gabanta ya faɗi, sakamakon leƙo kai da Dagger yay yana kallonta shima dan shi ne a gaban. Sai kuma ta kalla Ruky da sauri. “Na shiga uku mika fesa mata?”. “Kar ki damu ƴammata na, barci kawai na sakata zata tashi bada jimawa ba”. Daga haka ya tada motar zai bar wajen. Nimrah ta sake jeho ma Malam Buba tambaya, “Baba ka koma aiki ne?”. Kai ya girgiza mata alamar a'a. “To ina kuka samu motar gidanmu?”. Kai tsaye ya bata amsa da, “Amsa mukai hannun Mu'azz”. “Yaya Mu'azz?! Ta yaya to?”. “Ki kwantar da hankalinki Uwa, yanzu zaki ji komai bari muɗan gangara”. “Ni kana rikitani Baba Driver. Miye wani Uwa? Ni sunana Nimrah ne”. Murmushi kawai yay mata baice komai ba. Shima Dagger dake kallonsu ta mirror ɗin gaba sai yay ƴar dariya. Nimrah dai ta sake rikicewa. Ga shi sunƙi amsa mata tambayoyi ko ɗaya. Hasalima sun canja hanya bata gidansu ba. Sai da Dagger ya tabbatar sun yo nesa da makarantar sannan ya samu waje yay parking. A kuma lokacin ne Malam Buba ya fara kwaye gemun sa na bogi daga fuskarsa. Ashe duk tsawon zaman da yay a gidansu gemun nan ba nashi bane. Nimrah dake kallonsa kamar sokuwa ta saki baki da hanci. Sai da ya kammala tsaf cikin rawar lips ta furta, “Baba driver dama gemun nan naka na ƙarya ne?”. Kai tsaye ya amsa mata da “Kwarai Uwa. Na saka shi ne kawai dan na samu salamar zama a gidan da kike.” “Gidan da nake? To saboda mi?”. “Ba lallai kisan dalilin ba yanzu.” Dagger ya bata amsa yanzu kam. Ta kallesa da ƙyau. Sai kuma ta ce, “Nifa kuna sake rikitani. Kai ince kasan Baba Driver ne ma ta sanadina.” Dariya sosai Dagger yayi, ya sake juyowa da ƙyau yana kallonta. “A tunaninki kenan Nimrah. Amma bari muzo miki a mutane. Da farko dai ana kirana Dagger ne. Malam Buba kuwa da kike ma kallon driver ko wanda na sani ta dalilinki ba haka bane. Malam Buba abokina ne, aminina kuma ɗan uwana. Yaje aikin tuƙi a gidan da kike ne saboda ke. Ki kalla fuskarsa da ƙyau zaki ce baki sanshi bane?”. Nimrah ta kalla Malam Buba a karo na biyu, kallo irin na ƙurulla amma sam babu wani alamar ta sanshi. Sai kanta dake wani irin mata nauyi ma. Ga zuciyarta na bugawa da masifar ƙarfi. Ba ita kaɗai ba, shi kansa Malam Buba tun buɗe fuskarsa da yayi a farko yaga babu wani reaction daga gareta na alamun ta sanshi hankalinsa ke tashe. Shiyyasa ya kasa ci-gaba da magana, dan tabbas akwai alamar tambaya..... “Ban sanshi ba! Bamma taɓa ganinsa ba”. Furuci mafi muni daya kusa wantsalo zuciyar Malam Buba ƙasa. Idanunsa sukai wani kalar juyewa. Muryarsa da jikinsa na rawa yay ƙoƙarin kamo hannun Nimrah yana faɗin. “Uwa baki sanni ba? Ni ne fa mahaifinki Maude. Babanki mijin Ummanki Hassatu. Yayan Tanimu ɗan Inna”. Kanta ne ya ƙara Mummanan sarawa. Ta kai hannu tana dafe shi da girgizawa. “Ban sanka ba, wlhy ban sanka ba n......” Tsabar yanda Malam Buba ya fahimci zai iya haukacewa da furucin Nimrah baima san ya kama kafaɗarta ya fara jijigawa ba yana faɗin, “Uwa! Ni ɗin ne baki sani ba. Naja'atu Babanki mahaifinki ne baki sani ba. Ki kalleni, ni ne mahaifinki......” Ina maimakon ma ta fahimcesa sai ta tafi luuuu ta sume masa kawai. Ya ƙwalla kiran sunanta kamar zai fasa motar. A kuma dai-dai lokacin idon Dagger ya gano masa wasu motoci biyu dake tunkaro su... “Mole! Mole akwai matsala. Ƙyale yarinyar nan muje tabbas ana bin mu”. Ina Mole bama yajin Dagger, har yanzu sai faman jijjiga Nimrah yake da kiran sunanta yana faɗa mata shine mahaifinta. Motar Dagger ya ɓalle da ƙarfi ya fice. Yay saurin duƙewa ƙasa ya buɗe inda Mole yake kawai ya fisgoshi. Amma ina yaƙi sakin Nimrah. Dagger bai san ma ya wanke masa fuska da mari ba ya fisgoshi gaba ɗaya cikin ƙaraji yace, “Kai wawa mahaukaci jami'an tsaro!!!”. Yanda marin nan ya shigesa, da yanda Dagger yay maganar cikin ƙaraji a kunensa ya sashi dawowa a hayyacinsa. Tuni ya saki Nimrah daya jawo gab da ƙofar tai yaraf. Shi kuma suka bar wajen a guje. Sai dai ina jami'an tsaron sun ƙaraso wajen har sun fara harbinsu. Dole suma suka ƙara gudu suna nausawa jejin wajen da maida murtani. Jami'an tsaron kuma suka rufa musu baya.. ƙarar wannan harbi ce ta farkar da Nimrah, dai-dai isowar ogan jami'an inda suke yay saurin kai hannu zai tarota dan yanda ta zabura gata a bakin ƙofa ta tafi ne zata faɗo ƙasa ta kai aka ɗora masa bindiga a kansa...........✍️