Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 42

Post

Kida a ruwa Book 3 page 42

..... But then Nimrah was taken away and she was going to spill. Together, Dada and the crowd jumped up to stop her. But within an hour, Dada had already held her. For the first time, he gave him a serious look. With a warning in a low voice. "She is a married woman". "I'm sorry sir!". The officer said while shaking his head, but all the signs of a smile wanted to hide from him and appear with him. Dada had already taken his head so he didn't notice. Then Faro looked at him full of suspicion and surprise. He knows very well who T. Dalha is. He is a good man, let alone blame him for a purpose. He didn't say anything, he is currently working. Dada already took his head away from them and lifted me up and put him in the car. For the first time his eyes fell on Ruqayya that Nimrah was showing him. After putting her to rest, he went around to where Rakayyan was too. At one glance, he understood the hair that they cut on purpose, so he didn't touch it and put the cover back and closed it. At this time Yusuf's team is approaching the inside of the cave. Dada did not stop and handed Faro his car key. He returned to the car and gave her the key. From Faro, T. Dalha stared at the car, before

Standalone post1,642 words

42

..........“Waye kai?”. Jarumar muryar Dada ta daki cikin kunnen sa. Numfashinsa daya riƙe a maƙoshi ya sauke a hankali jin ba waɗanda yake zato bane. Sai ma wani ƙaramin murmushi da ya ɗan saki kaɗan. Dai-dai nan Faro da yanzu motarsu ke isowa suka ƙaraso wajen suma. Dan shi Dada a mashin ɗinsa yazo. Mashin ɗin kuma sam baya ƙara dama, shiyyasa shima baiji zuwansa wajen ba. Faro daya riga ya sanshi sosai yana isowa wajen ya furta, “T. Ɗalha”. “Yes Sir!”. Jami'in ya faɗa dan shima kai tsaye ya gane muryar Faro kamar yanda ya gane ta Dada a maganar farko da yayi. Dada ya ɗan harari Faro dake kallonsa yana wani murmushin neman magana. Sai kuma ya janye bindigarsa daga kansa ya maidata cikin jikinsa ya matsa ya kama Nimrah da kansa. Nimrah na riƙe da kanta dake sara mata kamar zai fashe ta shige jikinsa lips ɗinta na rawa alamar son yin magana amma ta kasa. Sai ma hankalinta da kamar ya rabu biyu. Dada ya fahimci kallon ƙurullar da take ma mutumin, dan haka shima ya juya yana kallon sa. Amma sai jiri ya kwashe Nimrah ta tafi zata zube. A tare Dada da jam'in suka zabura zasu tareta. Sai dai cikin sa'a Dada ya riga shi riƙeta. A karo na farko kuma ya watsa masa kallo mai nauyi. Tare da jefa masa gargaɗi cikin kausashiyar murya. “Matar aure ce”. “I'm sorry Sir!”. Jami'in ya faɗa yana duƙar da kai, sai dai gaba ɗaya alamun murmushi yake son kufce masa ya bayyana a tare da shi. Shi Dada ya riga ya ɗauke kansa dan haka bai lura ba. Sai Faro daya zuba masa ido cike da tuhuma da mamaki. Yasan waye T. Dalha sosai. Mutumin kirki ne balle ya zarge sa akan wata manufa. Bai dai ce komai ba dan yanzu ana kan aiki ne. Dada da tuni ya ɗauke kansa daga garesu dama ɗagata yay cak ya saka a mota. Karo na farko idanunsa suka sauka kan Ruƙayya da Nimrah ke nuna masa. Ƙarasa kwantar da ita yay ya zagaya inda Raƙayyan take itama. A kallo ɗaya ya fahimci sumar da ita sukai da gangan, dan haka bai taɓa ta ba ya maida murfin ya rufe. A wannan lokacin tawagar su Yusuf ke ƙarasowa wajen cikin kaki. Dada bai tsaya ba ya miƙama Faro key ɗin mashin ɗinsa. Motar ya koma yay mata key kawai yabar wajen. Daga Faro far T. Dalha da kallo sukabi motar, kafin Faro ya dawo da kallonsa akan T. Dalha ɗin cike da tuhuma. T. Dalha ya kauda kai yana murmurshi. Cike da basarwa ya ciro waya a jikinsa yana faɗin, “Bari na taɓa yaran nan muji sun kama su”....

_____________

Kai tsaye Dada gida ya nufa. Koda ya samu waje yay parking sai ya ɗaga waya yay kiran Ammar dan ya tabbatar yanzu suna gidan basu kai ga fita sallar juma'a ba, dan da ɗan sauran lokaci kaɗan. “Fito ka sameni a compound”. Ya faɗa a taƙaice yana yanke kiran. Babu jimawa kuwa sai gashi ya fito sanye cikin jallabiya. Dada shima ya fito yana nuna masa gaban motar. Ajiyar zuciya Ammar ya sauke mai ƙarfi, dan tun ɗazun cikin tsananin tashin hankali suke duk da an kawo Mu'azz gida tuni. Kuma Alhamdullah babu wani mumman rauni a tare da shi, shima sumar da shi kawai sukai suka ajiyesa gefen titi suka ɗauki motar. Ganin Ruƙayya kamar babu rai sai da gabansa ya faɗi. Amma sai Dada ya katse shi da faɗin, “Kallonta zaka tsaya ko ɗaukarta?”. Ƙeya yaɗan sosa. Kafin ya ranƙwafa ya ɗauketa yay ciki. Sai lokacin Dada ya kama Nimrah ya fiddota itama. Hannunta na riƙe cikin nashi ɗayan kuma ta riƙe kai suka shiga falon. Mammah dake tattaɓa Ruƙayya da Ammar ya shinfiɗe tayo kansu a rikice ta kama Nimrah ɗin tana jera mata tambayoyi. Da ƙyar Nimrah ta iya furta, “Mammah basu mana komai ba ki kwantar da hankalinki”. Ajiyar zuciya kuwa ta sauke. Dada dake kallon su ya ɗan furzar da numfashi. Kusa da Mammah da duk hawaye suka cikama idanu ya zauna yana amsa gaisuwar su Shariffa da duk suka sake nutsuwa waje guda cike da girmamawa a gare sa. Ya maida kallonsa ga Mu'azz dake kwance. “Sun maka wani abu ne?”. Kai Mu'azz ya girgiza masa. Muryarsa da damuwa ya ce, “A'a Dada. Abu kawai suka fesa min daga nan na rasa hankalina.” “ALLAH ya kiyaye gaba”. Ya faɗa a taƙaice ce yana miƙewa. Su kuma suka amsa da amin....

Likita aka sake kira ya farfaɗo da Ruƙayya. Nimrah kuwa addu'oin Mammah taita mata a haka barci ya kwashe ta. Dukansu aka maidasu ɗakin Mammah mazan gidan suka fita salla. Sosai abin nan ya tsaya ma Mammah a zuciya. Ji take anya baza'a matso da tariyar nan ba yaran nan su koma ƙarƙashin mazajensu. Ita fa harga ALLAH wannan ɗauke-ɗauken na ɗaga mata hankali matuƙa. Yau badan ALLAH yasa Muhammad yayi dabarar saka abu a wayarsu da motar ba da basu san kuma mizai faru ba. Dan ba lallai yanda Nimrah ta tsira a ɗaukar farko a yanzu ace duk sun tsira ba. Waɗan nan wane irin ibilasan mutanene haka?. Bata da mai bata amsa, dan haka ta haƙura ta zauna tana ta kallon su Ruƙayyan kawai. Addu'a kam yau sun shata kala-kala.....

<<••>><<•>><<••>>>

“Bafa a samu mutanen nan ba Zak.. Ni nama fara tunanin ko aljanu ne?”. Dada dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya yana sauraren Faro dake maganar ya ɗago idanunsa a karo na farko yana kallonsa. Sai dai yaƙi yace komai akan maganar da Faron yayi tsahon lokaci. Har ma ya fidda rai da samun amsar sai kuma ya amsa masan. “Suna da maɓoya ne kawai ta wajen. Shiyyasa suka kai motar suka ajiye a wannan gurin saboda kota ƙwaɓe”. “Wow! Tabbas maganarka na kan hanya. Ya akai kammu bai kawo wuta ba ne. Dan yaran T. Dalha dama sun tabbatar sun harbi wani a cikinsu a ƙafa.” “Shine kuma suka baro jejin?”. Dada ya faɗa cikin alamun ɓacin rai. “Relax Haysam, ka musu uzuri. Dole su dawo da baya tunda basu san shirin mutanen ba. Gashi babu wani makaman kirki a hannunsu, wlhy bindugunsu duk sun saki fa. Kasan fa ƙasar yanda take”. Shiru Dada baice komai ba. Amma alamu sun nuna ya gamsu da zancen Faro ɗin. Dan suna a haka Imran ya shigo. Hannu duk ya basu suka gaisa, kafin ya zauna. Bayanin yanda komai ya faru Faro ya bashi. Mamakin tsagerancin mutanen nan ya tsaya masa a rai. Shima zai fara faɗa akan dawowar Jami'an tsaron da basu zauna a jejin ba har sai sun gano inda suke Faro yay masa irin bayanin da yay ma Dada. Shiru yay dan ya fahimta. Sai kuma zuwa can ya furta, “Dole ne a sabuntama Jami'an tsaron kasar nan makamai na zamani in har ana son aikin nan ya tafi yanda ake buƙata”. “Tabbas wannan shine abinda ya dace. Dan mutanen nan sunada makaman da suka fi na jami'an tsaron. Ka duba fa kaɗan daga kayan da muka fara samu nasu yanda suke.” “Wannan gaskiya ne Haydar. Amma shi wannan T. Dalha yake ko? ya akai yasan da wannan shirin nasu haka?. Kaga fa yama rigaku zuwa”. “Nima wannan tambayar nata min kai-kawo a rai. Amma nasan T. Dalha jami'i ne mai gaskiya da sanin kan aiki. Dan wannan halayyar tasa ce ta ɗagashi da sauri a aikin jami'an farin kaya. Shine ya jagoranci aikin kwashe iyalan driver ɗin can fa”. “Oh Masha ALLAH dama shine?.” Kafin Imran yaba Faro amsa Dada ya furta. “Ina buƙatar bincike a kansa”. Bai jira amsar su ba ya miƙe abinsa ya nufi ɗakin sirri. Da kallo duk suka bishi, sai da ya shige Faro yay murmushin da yake ta riƙewa. Cike da gulma ya kalla Imran. “Hummm mutuminka fa kishi ke ɗawainiya da shi.....” ya kashe abinda ya faru ya sanar masa. Imran yay ƙaramar dariya da faɗin, “ALLAH ma ya taimakesa ba'a karya hannun ba. Amma fa gaskiya nima ina buƙatar ganin T. Dalha ɗin nan. Dan akwai abinda ya kamata mu sani a kansa. Kace fa Nimrah nata kallonsa?”. “Sosai, dan har kamar htna son yin magana ma”...

★Dada kam koda ya shiga ɗakin sirri wasu hotuna ya shiga tattarowa. Tare da wasu tsoffin files yana bincike. Kafin ya koma gaban computer. Tun ma bai nisa ba ya samu abinda yake so. Ya zubama bayanan daya tattara idanu, mamaki sosai na kamashi. Yaya akai tun a wancan lokacin basuyi wannan tunanin ba? Sannan miyasa shi ma ya ɓoye musu?. Maimakon samun kansa da neman amsa waya ya ɗauka tare da file ɗin ya fito. Ya samu Imran kawai a zaune sai Dabo. Faro ya fita. Hannu kawai ya ɗagama Dabo dake gaishe shi. Sai kuma ya miƙa masa file ɗin hannunsa yana faɗin, “Bincika min cikin hukumar ƴan sandan farin kaya yaushe wannan mutumin ya fara aiki”. “Okay Boss”. Dabo ya faɗa yana amsar file ɗin. Waya ya sake ɗauka shima yay kira. Bugu biyu aka ɗaga masa. Daga can akai sallama cike da girmamawa. Tare da gaisuwa. A taƙaice ya amsa. Sai kuma ya cigaba da faɗin. “Hassan zan turo maka wani suna yanzu ina son bayanansa gaba ɗaya a cikin jami'an ku yake”. “In sha ALLAHU Sir. Ka tura kawai”. Komai Dada bai sake cewa ba ya yanke kiran. Dukkan abinda ya faɗa ya turama Hassan ta email. Yana ajiye wayar Dabo ya ce, “Sir! Ga shi na samu komai”. Ƙaramin Murmushi yayi, dan yasan Dabo shegen kansa ne indai akan kutsen bayanan sirrine ko shi daya koya masa a yanzu ya dama shi ya shanye. Shi kansa Imran sai da ya murmusa da faɗin, “Anya Dabo ba kune matsalar ƙasar nan ba? Dan wataran brain ɗin mutane zaku dinga shiga ta na'ura”. Dariya Dabo yayi da faɗin, “Sir mu mun isa. Wannan ma dan aikine kawai”..........✍️