Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 43

Post

Kida a ruwa Book 3 page 43

..... said, "Do you know him?". Standing up, Dada seems like he won't answer questions even now. He had to go to the door and confess. "Just forget Imran. We should pass". Imran knew who his lion was, so he just let go of the conversation as he needed and they came out..... •••••••••••••••• "Wlhy since they bled me for the third time, I added them. I will kill them because of violence. Then they know that they are in trouble. I am Dagger, I am not leaving the future debt..." Mole interrupted Dagger by saying, "Oga, be quiet, son of GOD. Now this is not being given to us, we have to get you home and remove this bullet for you is the most important thing. you are bleeding even though you are tied". Dagger was struggling and kept moaning. He was sweating profusely as if he had been bathed in water. Mole is carrying him on his back even though he is heavy. Dan Dagger is a real giant and even drinks. Since they left Nimrah where they were in the desert, the police were following them. They knew the desert very well as Dada imagined, but when it was rough, Dagger accidentally got shot. From there, they found one of their hideouts and went in. That's why the children of T. Dalha did not f

Standalone post1,556 words

43

........Tsaf Dada ya gama duba bayanan da Dabo ya samo. Koda Imran ya amsa ya duba yayi matuƙar girgiza shima. Cikin kasa shanyewa ya furta, “Kenan tun a wancan lokacin Jam'i ne?”. Dada ya ce, “Hummm! Yayi wasa da hankalinmu.” “Bana wasa ba kuwa. Amma Nimrah ta gane shi kenan?”. “Banda tabbas, naga dai tanata kallonsa”. “Kai ya rabbi. Bana son abubuwa su kwaɓe a yanzu har sai an kammala bikin nan lafiya wlhy. Ni mutanen nan ma da suka ɗauke su ne naketa tunani su kuma mi suke nema? Dan bana jin na farkon ne suka sake dawowa?”. Dada dake jingine da kujera idanunsa a lumshe ya ɗan furzar da iska. “Suna da alaƙa. Amma ba'akan manufa ɗaya suke ba a kanta. Ina ƙyautata zaton driver ɗin nan ne da yaron nan da aka ɗauke su hoto a tare har ta gani”. “What! Zak.. na fara shiga ruɗani fa. Anya mutumin nan bashi da alaƙa da Nimrah kuwa?”. Karo na farko Dada yay murmushi. Sai dai baice komai ba. Hakan yasa Imran fahimtar akwai abinda ya sani game da mutumin yana ɓoyewa ne. Cikin kasa haƙuri ya furta, “Ka sanshi kenan?”. Miƙewa Dada yay kamar bazai amsa masaba yanzu ma. Sai da yaje bakin ƙofa ya furta. “Manta kawai Imran. Ya kamata mu wuce”. Imran yasan waye Zakinsa, sai kawai ya saki zancen kamar yanda ya buƙata suka fito.....

•••••••••••••••

“Wlhy tunda suka zubar min da jini a karo na uku sai na ƙarar da su. Kisan gilla zan musu na tashin hankali. Sai sun san sunyi da ɗan halak. Ni Dagger bana barin bashin gaba....” Mole ya katse Dagger da faɗin, “Oga kayi shiru dan ALLAH. Yanzu bata wannan ake ba mu samu muƙarasa gida a cire maka wannan harsashin shine mai muhimmanci. Jibafa yanda kake zubar da jini duk da an ɗaure”. A wahale Dagger yaja tsaki yana cigaba da nishi. Ga zufa ta masa sharkaf kamar an masa wanka da ruwa. Mole ke goye da shi a bayansa duk da kuwa ya masa nauyi. Dan Dagger ƙato ne na gaske dan ma yana shaye-shaye. Tun barowarsu inda su Nimrah suke suka nausa cikin jejin nan ƴan sanda suke binsu. Sun san jejin sosai kamar yanda Dada yay hasashe, amma da yake tsautsayi ya ratsa a bazata Dagger ya samu harbi. Daga nan ne suka samu ɗaya daga maɓoyarsu suka shige shiyyasa yaran T. Dalha basu samesu ba. Sai da suka tabbatar sun haƙura sun koma sannan suka fito, Dagger ya gama galabaita dan yanata zubar da jini, shiyyasa Mole ya goya shi. Sun ɗanyi nisa da tafiyar wasu matasa biyu sukazo a babura suka ɗauke su.....

∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆

Kwana biyu Nimrah na fama da ciwon kai. Dole ne ka tausaya mata dan tasha wahala sosai. Ita ko Ruƙayya tunda ta farfaɗo ta miƙe kamar komai bai faru ba. Tun daga ranar Dada ya saka musu dokar fita. Dama sun kammala jarabawa. Islamiyya ce yace a haƙura bayan biki sa koma. Hakan kuwa akayi, sai ma su Shariffa suka samu dama da nutsuwar yi musu gyaran jiki. Sai class ɗin Chef Yakudima 08135358038 da shima suka ƙara dagewa. Dan duk rashin son girkin Nimrah sai gashi class ɗin na mata daɗi saboda yanda Chef Yakudima ke treating ɗinsu tamkar ƙannenta. Ga shi dai online ne amma sun shaƙu sosai kamar sun taɓa sanin juna.

A yau ranar juma'ar data rage saura kwanaki takwas biki su Uncle Ja'afar suka iso. Washe gari asabar kayan da suka zo da su suma suka iso. A kuma ranar suma su Gwaggo Khadijah suka sauka. Abinda ya fara bama Mammah mamaki ganin zuri'ar su Yaya Babba. Dan basu taɓa zuwa inda take ba. Itace ma idan ta ɗan je takan leƙasu a gaisa. Su kansu su Dada sunyi mamaki. Amma shi dai bai ce komai ba. Su Bilal da su Aunty Mimi ne ma suka tanka. Dan da farko ma su Ja'afar ƙin kulasu sukayi. Sai da Mammah tai musu magana. Ba wannan ya sake bama Mammah mamaki ba sai washe garin Lahadi da itama wasu a danginta suka iso tare da zuri'ar Kawu Zubairu yayan Uncle Nasiru Ogan Abdul-rasheed na ɗinki idan baku manta ba. Mammah ta share hawaye, dan wannan na nufin yanzu yan uwa sun fara dawowa garesu kenan. Ta tabbatar kuma darajar tasu ta ƙara fitowa ne saboda wannan appointment da aka bama Muhammad ne. Saboda yanda ƙura ta tashi a lokacin babu wanda zaice sunan Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi da hotonsa bai shiga wayarsa ba indai yana saka data. Baiwar ALLAH babu wanda ta nunama wani abu. Kowa ta tarbeshi gwargwadon iyawarta. Tun ma ba'aje ko ina ba har gidan ya fara musu kaɗan musamman sashenta. Dan su Ja'afar sun murje ido sun hana kowa zama musu sashe sai iyalan Gwaggo Alawiyya dana Gwaggo Khadijah da Uncle Jamilu kawai. Sauran kuwa sunce su tsaya wajen Mammah ɗin ita suka sani su basu ma san su ba.

Zuwa Laraba dole wasu baƙin suka sauka gidan Uncle Nasiru. Ita Mammah harma mamakin wanda ya sanar da su bikin take. Dan tasan dai bata gayyaci kowa ba. Su ba sanarwa sukai gidan rediyo ba balle ace. Basu turama kowa invention ba. Sai daga baya ta fahimci aikin Uncle Nasiru da Uncle Jamilu ne. A ranar ne akai shirin yima amare jere. Dan haka su aunty Ummi suka ɗunguma zuwa gidan Biebah. Nan kuma aka fara ƙoƙarin tsaftace sashen Bilal, Ammar, dana Dada bangaren Nimrah da nashi bangaren.

Hankalin Nabeeha ya tashi, dan a ranar sai da Hajiya Hasiba ta yini gidan da Mamawo. Dama kwanakin nan tunda baƙi suka fara sauka duk ta ƙara hargitsa kanta. Da ƙyar ƴan uwan ke tausarta. Da tace ma zata koma gida idan an gama bikin ta dawo Hajiya Hasiba tai mata jan ido. Da yamma kuma sai ga First Lady da kanta. Ita ta zauna ta tsara Nabeeha ɗin da zantukan da suka sa ta janye batun barin gidan. Sai dai fa yanda duk ta birkice dole ta baka tausayi...

★★★

Kuce min ina amare su Nimrah suke? Suna gidan Baffa su duka huɗu. Dan dole a yau aka maida su can. A can Hajjo ta buɗe musu batun an ɗaura musu aure tun randa aka kawo kuɗi. Yanda Ruƙayya ke zaro ido da su Asma'u da ita kanta Small Mom ɗin tasu ba ƙaramar dariya ya bama Nimrah ba. Ta dinga tsokanar Ruƙayya har sai da ta sakata kuka. Dan ita fa duk abin nan da akeyi ta dauka kawai ana mata tare da Nimrah ne saboda tana aminiyar amarya saboda wauta. Ganin kuma tana kuka sai jikin Nimrah yay sanyi ta koma lallashinta itama tana hawayen. Sai da Hajjo ta ce. “Kai kuji min yara da shashancin. Kuda ma kuke ƴan gata. Mutum yay aure a gidansu gaku ga uwarku, ga sauran iyayenku. Sannan kuna tare. Ai idan ma da me yin kuka uwarku Habiba ce. Ni nama taɓa ganin auren gata irin naku? Idan da haka mata ke samu babu su ai babu kukan aure.” Wannan magana ta Hajjo ta kawo musu nutsuwa, dan kuwa tabbas sun yarda su ƴan gata ne. Ana haka sai kuma gasu Feedo ma sun iso, tuni suka sake mantawa da komai suka koma shiriritarsu. Balle ma harda baƙin Bauchi ƴammata kamarsu-kamarsu. Gobe idan ALLAH ya kaimu alhamis kamu, dan haka a yau da daddare sai ga Mu'azz da akwatinan kayan da zasuyi amfani da su su duka. Dan ranar aka kawo lefen Biebah. Itama Asma'u an kawo nata nan gidan Hajjo tun jiya. Nimrah da Ruƙayya kuwa nasu na wajen Mammah, dan bama a buɗesu ba ance kowacce za'a kai mata sashenta idan masu jere sun kammala gaba ɗaya dan har zuwa yau suna kan aikinsu. Gaba ɗaya amaren babu mai ganin angonta sai ta waya. Dan Ammar ma dai ya dage, bare yau yana kira Ruky ta saka masa kuka. Jiyay gaba ɗaya ya rikice, gashi baya kusa suna hotel ɗin da zasu sauke abokansu shi da Bilal. Dan su manyan gayyar Dada da Faro basu san ya suke ciki ba. Kai su bama ganinsu ake ba, suna can sabgar aiki tasha kansu. Dan ko Imran yanda yaga sunyi busy ɗin nan sai da yace Dada ya taimakesu da aka ɗaura auren nan a waccan ranar da yanzu suna nan a birkice. Yanzu kuwa sun barma mata sabgar sukuma suna mai fishesu. Nimrah daba taɓa waya tai da Dada ba dama ko'a jikinta. Kai ita haka ma ya mata, dan rabon ma data ganshi tun randa ta samu lafiyar ciwon kan nan nata, abin mamaki kuma bata sake tuna wani Malam Buba ba balle abinda ya faɗa mata na cewar shi mahaifinta ne. Sosai ɗinkuna nasu duk sunyi ƙyau, dan su duka huɗu an musu na bikin ne na musamman ba'a cikin kayan lefe aka ɗauka ba. Zuwa yamma mai wanke musu kai tazo gida. Dan komai da za'ai musu home services aka ɗauka saboda tsaro. Da yake kwararriyar mai aiki ce tasan aikinta sosai gata aminiyar Aunty Mimi ce kuma tana da ma'aikata sosai da suma suka san aikinsu zuwa dare an gama gyara su. Amare sun ƙara fitowa. Dama ga gyaran jikin ya sakasu sun ƙara ƙyau matuka, dan kayan SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. duniya ne. Turare kam ai ko daga nesa ka doso su sai kaji yanda ƙamshinsa ke tashi Masha ALLAH.........✍️