
Post
Kida a ruwa Book 3 page 44
..... she gathered a lot to meet their family and... Around three o'clock, Aunty Momy arrived from Mammah's house. The rest of the people will be in the afternoon. Aunty Mimi and Lailah, Shariffa are the bride's head until the beautician finishes them and they are dressed in big beautiful dresses. Theirs is only four marriages with ALLAH. It's a celebration for women, except for Mu'azz, who is with Nimrah, and they are laughed at. All over their bodies. They are also photographers. They asked Ammar and Bilal to send pictures of Asma'u and Ruqayya's daughter, each with her phone, and they took Nimrah's number and added Dada's number, which they knew was on WhatsApp. They checked and there was no number. What they don't know is that there are two numbers in it except the one they don't know. Even the owner of the phone does not know who the numbers are and she has never bothered with them. They uploaded Nimrah's photos to him. He had to sit down, take a breath and untie his neck tie completely, lower the top three buttons of his shirt and pick up the phone. Don't know b.....
44
..........Washe gari tunda safe kuma aka ɗora da ƙunshi. Duk kuma dai mai saloon ɗin nan ce. Kafin Azhar an kammala tsaf. Sai yaranta da zasu ma ƙawayen amarya gobe in sha ALLAHU. Dan yau kamu gobe ƙunshi. Anan gidan Hajjo za'ai Kamu. Gobe kuma ai Kunshi gidan Uncle Nasiru. Ranar asabar Ammie da Mammah kowanne zai yi yinin biki. Lahadi ai dinnar da su Ma'aruff suka shirya, duk da Dada yaso hanawa Mammah tace ya barsu. Dan cikinsu babu abinda akayi saboda yana prison. Yanzu kam ya bari su nuna farin cikinsu daga nan kuma sai na Mu'azz. Dole yay shiru tunda anfi ƙarfinsa...
Ba ƙaramin ƙyau wajen kamu ɗin yayi ba kuwa. Mamaki ya kama su Nimrah ganin yan ajinsu na islamiyya dana boko nata tururuwar zuwa. Dan babu wanda suka gayyata. Basu san Mu'azz yayi invention ya kai makarantunsu ba. Amma da abinda zai baka dariya Mu'azz ɗin da su Imam, Khalifa ne kamar ƙawayen nasu sai su Bintu. Ita ko Biebah dama ƙawayenta tun a jiya suka fara zuwa. Na Secondary dana University. Hakama Asma'u ƙawayenta sun taru sosai gana danginsu kuma... Kusan ƙarfe uku su Aunty Momy suka iso daga gidan Mammah. Sauran mutane sai anyi la'asar. Aunty Mimi da su Lailah, Shariffa sune kan amare har mai kwalliya ta gama musu aka shiryasu cikin manyan lafaya masu shegen ƙyau. Abin nasu sai masha ALLAH amare huɗu reras. Biki ne iya na mata, sai su Mu'azz dake nane da su Nimrah har ana musu dariya yayun banza. Ko'a jikinsu sukam. Sune ma masu ɗaukar hotuna. Tsabar neman magana yanda suka turama Ammar da Bilal hotunan Asma'u dana Ruƙayya kowacce da wayarta haka suka ɗauki ta Nimrah suka saka number ɗin Dada da suka san yana WhatsApp. Dan sun duba sunga babu number ɗinsa. Abinda basu sani ba kuma akwai numbers ɗinsa har biyu a ciki sai dai wanda basu sani ba. Hatta ita mai wayar bata san numbers ɗin waye ba kuma bata taɓa damuwa da su ba. Haka suka loda masa hotunan Nimrah....
<<••>><<>><<••>>
Dada na Office aiki ya masa caa dan barowarsa office ɗin shugaban ƙasa kenan ya dawo nashi office ɗin wayarsa data shafi family ɗinsa kawai ya samu tana haske. Sai da ya zauna yana sauke numfashi da zare tie ɗin wuyansa gaba ɗaya ya rage botiran shirt ɗinsa guda uku na sama sannan ya ɗauka wayar. Dan bai sani ba ko Mammah ce ta kira shi. Ilai kuwa yana dubawa yaga miss call ɗinta sai na Uncle Nasiru ma. Mammah ɗin ya fara kira. Bayan sun gaisa take tambayarsa Uncle Nasiru ya kira shi ne?. “Yanzu nake ganin miss call ɗinku a tare na fara kiranki Mammah. Wani abu ya faru ne?”. “Dama iyayenku ne maza na Bauchi suka zo”. “Mammah iyaye kuma? Bayan Uncle Jamilu muna da wasu iyayene kuma a can?”. Murmushi Mammah tayi dan dama tasan za'a rina. Shiyyasa ta kira shi da kanta duk da hayaniya ta mata yawa. Yanzu haka tana can sama ɗakinsa dan nan ne kawai babu kowa. “Muhammad shiyyasa dama na kiraka dan nasan halinka. Tunda dai sun kawo kansu a maida komai ba komai ba ayi biki a tashi lafiya ba shike nan ba. Bana son ace wata matsala ta taso daga gareku akan dangin nan nawa dana mahaifinku. Kai ne uba, duk abinda sukaga kayi suma sauran ƴan uwanka shi zasu yi”. “To amma Mammah tunda an riga an ɗaura aure miye na wani gayya? Shiyyasa na saka aka ɗaura auren dan bana son wani damuwa”. “Koma dai miye nidai nace ayi abinda ya dace”. “Hummm shike nan. Duk yanda kike so haka za'ayi”. “To na gode idan kuka min hakan. Nasan ba gidan nan zaka shigo ba yau ma. Su Bilal ma sun tarkata yau sun koma inda baƙinsu suke har su Ma'aruff. Sai ka tarkata su ko zuwa da safe ko anjima kuje ku gaida su dan duk suna can gidan Yaya Nasiru. Yaya Zubairu ma yazo”. Jin Kawu Zubairu yazo ya saka Dada yin murmushi. Dan haka yay sallama da Mammah akan anjima zasu je. Yana yankewa ya kira Uncle Nasiru shima. Shima dai irin batun Mammah ɗin ne. Dan haka yace masa anjima zasu zo yanzu yana office. Daga haka ya yanke kiran. Zai ajiye wayar yaga notifications an tura masa hoto da number ɗin Kiddo. Yayi mamaki, dan tunda ya basu wayoyin nan daga ita har Ruƙayya bai taɓa kiran kowa ba, suma bama su san da number ɗinsa a wayoyin ba. Kamar zai share sai kuma ya ɗauka ya buɗe ta notifications ɗin. Ƙirjinsa yay wani irin motsawa sakamakon cin karo da hoton Nimrah. Tayi masifar ƙyau a cikin lafaya ɗin. Sannan ta ƙara masa girma a ido. Gashi yanda tai murmurshi da kamar tana hararar wani ya fito da hasken haƙoranta dana idannunta. Ai sai ga Dada da lumshe idanu da cije lips. Baima san ya cigaba da kallon sauran hotunan ba har wanda suke da Rukkayan sa. Duk da basa kama idan ka gansu sai ka ɗauka tagwaye ne. Sannan a kallo guda zaka fahimci akwai ƙaunar juna mai ƙarfi a tsakanin su. Hoton ƙarshe su huɗun ne duka. Su suna tsakiya gefe da gefe Asma'u ne da Biebah. Suma sunyi ƙyau sosai. Ya ɗan murmusa yana ajiye wayar. Sai kuma ya gyara fuskarsa da yanayinsa sakamakon knocking da akayi. Yasan AS ɗinsa ne ya kawo masa lunch daya buƙata. Yunwa yake ji yau ko breakfast baiyi ba, dan rabonsa da kwana gidan su kusan 5days kenan. Ya koma UNIT ZERO ya tare shi da Imran da Faro suma duk gidajen nasu dangi ƴan biki sun cike su.....
★★★★
Gidan Baffa ya cika tam da mata. Dan kuwa ga dangin su Daddy Imran, ga dangin Faro da suma suka iso. Ga tawagar Mammah. Aunty Ummi, Aunty Mommy, Aunty Mimi. Shariffa, Lailah kowa da ƙawayenta. Ita kanta Ammie ƙawayenta duk sun iso. Ga kuma dangi ƴan Bauchi da ƴan Kano. Ga abokan huɗɗa nan cikin gari. Taro fa sai ace sambarka. Karo na farko da wani abu yaso zuwama Nimrah a zuciya kan dangi. Sai dai zuciyarta tai saurin fargar da ita suma waɗan nan ƴan uwanta ne. Dan kowa na mata komai babu ko banbanci akan fuska. Kai ita bama tajin su ba jininta bane. Kawai dai zuciya da saƙe-saƙe balle kuma mutanen nan sun riga sun nuna mata abinda da bata damu da saninsa ba wato dangin nata. Sosai kamu ya ƙayatar. Ansha kiɗan kwarya. Yayinda Ruƙayya da Nimrah suka sha rawarsu da ƙawayensu. Yo mi yafi ransu ALLAH na tuba. Mutane nata dariya da faɗin waɗan nan amare biyu dai akwai rawar kai. Asma'u da Biebah kam da yake sun fisu hankali su duk sun nutsu kowace da abinda ya isheta. Sukam ƙawayen juna babu abinda suke tunawa. Su Mu'azz sun shige cikinsu ana cashewa. Dan duk ustazancin Imam yau sai da Khalifa da Mu'azz suka saka shi yay rawa. Sun ko sha liƙi wajen iyayensu yanda ya kamata. Dan Hajjo kanta sai da tazo ta liƙesu ita da tsofaffin ƙawayenta irinta. Gab da magriba aka tashi. Su Nimrah sunyi tuɓis. Suka dai samu sukai wanka sannan suka zauna ana shan hira cikin ƙawayensu. Dan kowacce amarya ɗakinta daban da ƙawayenta. Sune dai dama kowa yasan ba'a raba hanta da jini....
WASHE GARI.
Yau data kasance juma'a kuma ƙunshi. Dan haka amaren ne da ƙawayensu kawai sukai shagalinsu a gidan Uncle Nasiru. Dan tun 12 aka gama kwashesu zuwa can. Sun samu baƙi maza sosai a gidan kuwa. Sai dai da yake suna a sashen baƙi babu ruwansu da su. Hasalima basu san su wanene da wanene ba. Anan ma komai ya tafi musu yanda suke so. Akasha hotuna aka cashe. Dan yau ma su Ruƙayya basu rage komai ba. Balle ma isu-isu ne kawai. Ƙawayen Small Mom kawai suke ragawa. Na Asma'u kam ai kallon sako akema juna itace dama abokiyar faɗan tasu. Anan ma sai yamma taro ya tashi. Anan suka kwana. Washe gari asabar aka maida Asma'u gidan Daddy Imran. Biebah, Nimrah, Ruƙayya gidan Mammah. Dan yau iyaye zasuyi nasu yinin biki. Idan da da mutunci Ruƙayya wajen Nabeeha ya kamata akaita kasancewar Dada ne uba. Amma kowa yama san wata fitina ce daban. Dan tunda aka fara hidimar bikin nan babu wanda zaice yaga idon Nabeeha da ƴan uwanta a gidan. Ƙarshe ma Rayhana da baƙin ciki ke neman zubarwa a ƙasa gida ta koma, wai idan biki ya tashi ta dawo. Anan ma Hanoon ciwo kashirɓan ta kwanta dan ko taro ɗaya bata halarta ba. Mammah tayi busy da yawa bata san abinda ke faruwa ba. A tunaninta ma Hanoon ɗin na tare da Biebah ne. Shima dai Dayyan yana cikin hali, dan yanzu ba zaman gidan yake ba ne kawai saboda ya samu abokai a anguwar. Dada kuma na sane da shi kawai ya share shine dan baida lokacinsa a yanzu. Matuƙar ƙyau amare sunyi yau ma. Dan lasses ne masu ƙyau da nauyin kuɗi kowacce da kalar data dace da fatar ta suka sha. Suna katarin Mammah dan haka yau babu rawa. Sai ƙawayensu ne keta raƙashewa. Sosai yinin biki yay armashi. Dan Mammah taga mutane sai godiyar ALLAH. Wanda basu samu yi mata a bikin su Ma'aruff ba a wannan bikin sun fanshi kansu. Bayan la'asar sai ga tawagar matar shugaban ƙasa Hajiya Zainab Yusuf Tafida. Aifa dan-danan gida ya ƙara kacamewa. Dan harda tawagar wasu matan gwamnoni dana ministoci take tafe. Hummm! ƴan Bauchi da ƴan Kano sai ƴar riƙe baki akeyi. Dan kuwa yau sun sake tabbatar da A'isha da zuri'arta sunyi nisa da ƙasa sai dai kallo da nuni daga nesa. Dan amaren nan uku kowacce ƙyautar mukullin mota daga shugaban ƙasa. Ita kuma First Lady ta basu manya-manyan sarƙoƙin gwal da warwaraye. (Dan ALLAH a gayama First Lady Hajiya Zainab Tafida nima Bilyn Abdull da ƴan tawagata muna buƙata 😂🥲). Ga ƴan rakiyarta suma fa kowacce da kalar alkairin da take saukema Mammah..........✍️