Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 45

Post

Kida a ruwa Book 3 page 45

.....yes do it, he also wants to do it for Dada's son to get to know the people better. They were invited and very important people, including those who had never joined them before. After the afternoon prayer, when they were there, Mammah interrupted their party and broke into Uncle Nasiru's house. But when Ja'afar, Ma'aruff, Bilal, Ammar were together they preceded Dada. But they refused to go in and waited for him in the compound. It didn't take more than fifteen minutes for the hair to arrive. It was Yusuf who led it. A son from another place also told them to take it out. Yusuf finished standing and they ended up there. Bilal opened the door where Dada was sitting. He was on the phone so he was late to come out. Dan had to waste about five minutes before he came out. The four of them all joined him and hugged him until they were not interested in Yusuf. They miss him enough that they don't see him for days and it's hard for them to see him. He also misses them very much. When he provoked Ammar and Bilal, he saw that they started to flirt. Send me Jafar and Ma'aruff, they will do it if they don't laugh. With this amusement on their faces, they went to Uncle Nasiru's guest room

Standalone post1,888 words

45

..........Wajen biyar suka bar gidan zuwa gidan Daddy Imran. Shima acan an bama Asma'u key ɗin mota da tata sarƙar. Duk da biki ne da bana ƴan siyasa ba sai da aka samu munafukin daya kai batun wannan ƙyautuka a media. Oho suma suka san sunayi. Su dai masu bikin shagalinsu kawai suke yi Alhamdullah.

(((((★)))))

A jiya Dada bai samu damar zuwa gidan Uncle Nasiru ba saboda abubuwa da suka taso musu. Dan suma Ammar da Bilal a ranar sukai bachelorette party ɗinsu su da abokansu. Jiya kuma juma'a sukai walima. Yau asabar ɗin ma akwai party da zasuyi da daddare da ƙyar Dadan ya samo su da yammar nan. Dan Ma'aruff da Ja'afar sun biye musu su kansu ba ganinsu yake ba. Shi ko ko event ɗaya bai halarta ba dan babu ma hakan a tsarinsa. Yo shi baima san mi da mi suke yi ba. Dan ko dinnar daga shi har Faro babu mai maganar zuwanta. Akwai dai walima da zasuyi shima dan shugaban ƙasa ya dage ne kawai a gobe lahadi daga 2 na rana zuwa 6 na yamma in sha ALLAHU, acewarsa tunda babu daurin aure ya dace ayi ɗin, shi kuma yana son ayi ɗin ma dan Dada ya sake sanin mutanen ma da ƙyau. An gayyaci kuma manyan ƙasa sosai harda wanda ma su huɗɗa bata taɓa haɗasu ba.

Bayan sallar la'asar lokacin da can su Mammah keta shagalinsu anan su kuma gidan Uncle Nasiru sukaima tsinke. Sai dai da yake Ja'afar, Ma'aruff, Bilal, Ammar suna tare sun riga Dada zuwa. Amma sai suka ƙi shiga suka tsaya jiransa a compound. Basu wuce mintuna sha biyar ba sai gashi ya iso. Yusuf ne ya tuƙoshi. Dan daga wani waje ma suke yace su zarto nan ɗin. Yusuf na gama tsayawa suka ƙaraso wajen. Bilal ya buɗe inda Dada yake zaune. Waya yake dan haka ya samu jinkirin fitowa. Dan sai da ya ɓata kusan mintina biyar kafin ya fito. Su huɗun duk suka haɗashi suka rungume har suna bama Yusuf sha'awa. Su ko kewarsa ce ta ishe su kwana nawa basu ganshi ba ya musu wahalar gani. Shima kewar tasu yake ji sosai. Dan har sai da ya tsokani Ammar da Bilal wai yaga har sun fara ƙyallin angwaye. Aiko mi Jafar da Ma'aruff zasuyi in ba dariya ba. Da wannan nishaɗin akan fuskokinsu suka doshi falon baƙin Uncle Nasiru da takalma suke birjit. Dada ne a gaba su huɗun suna take masa baya kamar wani boss da securitys ɗinsa. Tunda sukai sallama falon yay tsitt. Sai masu ƙarfin hali ne suka amsa a cikinsu. Dattijan tsoffi ne kusan goma sha uku. Uncle Nasiru, Zubairu, Jamilu. Sai Uncle Tijjani (Yaya Babba kenan daya ce zai auri Mammah bayan rasuwar Babansu) sai ƙaninsa mai bi masa Uncle Yusha'u, sai autansu Uncle Mudan daya je saudia ya tare tsahon shekaru, baifi watanni biyu kenan da aka dawo da shi ba. Uncle Ayuba cikon na huɗunsu shine ya rasu tare da Abdul-rasheed in baku manta ba. Sai Uncle Tasi'u da basu san ma da zuwansa ba, ashe shima jiya yaso. Sauran kuwa duk dangin bangaren Mammah ne na wajen mahaifi da kuma na bangaren Inna. Sosai zaratan mazajen na Mammah biyar ras suka girgiza zukatan su Yaya Babba. Dan babu wanda bai daburce da ganinsu ba. Balle ma Dada ya haɗe fuskar nan tashi babu wasa a cikinta. Abinda ya ƙara firgitasu cike da girmamawa ya gaishe da Uncle Zubairu da Uncle Nasiru da Uncle Jamilu. Amma su sai ya haɗasu a kuɗin goro yace. “Barkan ku”. Yanda yayi kuma haka ƙannen nasa suma sukayi. Daga haka ya samu kujera ya harɗe hankalinsa akan Uncle Zubairu dake masa magana. Suma su Ja'afar suka samu wajen zama kusa da shi hankali kwance duk suka harɗe. Ko kura tasan gidan mai babbar sanda. Ba boss ɗin kawai ba, hatta su Bilal ɗin kwarjininsu ya cika musu ido. Dan ko makaho ya laluba waɗan nan lafiyayyun zaratan samarin yasan nera ta zauna musu. Sannan hankalinsu a kwance yake duniya nayi da su. Kunya, nadama, dana sani suka shiga rige-rigen sauka musu a zuciya. Da ace sun riƙesu a lokacin da suke buƙatar taimakonsu matsayinsu na yara marayu da yanzu dasu ake cin wannan duniyar da tsinke. Amma son zuciya da sheɗan ya rinjayesu suka runtse idanunsu. (Mutane da yawa suna kallon yau ne a rayuwar bayin ALLAH musamman yara marayu a lokacin da aka tafi aka barsu da ƙarancin shekaru. Sai kaga an kasa ƙyautatawa da kulawa da su ana kallonsu a nauyi matsala mai girma. Shi kuma UBANGIJI shi yasan gobe. Shi yasan su waye bayinsa kuma a goben. Shiyyasa sai kaga ALLAH ya ɗaukaka yaran a shekarun girmansu kuma ƴan uwansu suzo suna nadama da koke-koken banza da wofi da nadama. Su kuma yaran zukatansu sun riga sun bushe da abinda akai musu, masu sauran imani ne ma ke iya musu irin wannan kallon naba wulakanci babu kuma girmamawa irin na su Dadan. Mutane sai mu kula, mu kuma gyara, sannan mu dinga tunawa muma ba ƙarfinmu ko wayonmu ko iyawarmu ce tasa muke rayuwa da namu yaran ba. Idan ka kula da maraya, kaima watarana sai su kula da kai da taka zuri'ar). An bar su Yaya Babba dai da murmushin yaƙe da kalar zance. Uncle Tasi'u kam da abin duniya ya ishe shi sai dai kaga yayi zugum abinda dariya abin tausayi. Daga sallar magriba suka baro gidan. Kai tsaye gidansu suka nufa duba Mammah. Sai dai sun samu gidan har a lokacin cike yake da mutane. Bama su san inda zasu gano Mammah ɗin ba. Amma fa securitys ba'a magana. Dan harda na farin kaya da su kansu su Mammah basu ma san dasu ba a kwai su a gidan nan har gidan Daddy Imran. Hatta su Bilal a masaukinsu akwai jami'an tsaro basu sani bane. Dan su Dada basu bari anyi taron bikin nan ba sai da suka shirya. Dole suka haƙura da batun ganin Mammah dan bata ganuwa. Dada ya koma UNIT ZERO dama su Faro jiransa suke. Su kuma suka nufi masaukinsu inda suma abokansu ke jiransu harda su Ja'afar ɗin. Sai dai har cikin rai Bilal da Ammar suna son ganin amaren su ko yaya. Amma lamari yaƙi saita waya. Har mamakin Dada suke da jinjina ƙoƙarin sa shi da Yaya Haydar, har gulmarsu sun sha yi ma....

Abinda basu sani ba su sun fisu iya kamewa ne saboda girma. Musamman ma Dada da baka iya gane ainahinsa ba. Dan ko Imran yana matuƙar jinjinama dauriya irin ta Zak-Shadow ɗin nasa. Babu yanda za'ace Dadan baya cikin buƙata. Shekaru kusan tara ba wasa ba ne. Balle ma su maza ba komai ke iya dakushe wannan yanayin a garesu ba cikin sauƙi. Garama mata wata ko cikin damuwa take zakaga komai ya fita kanta. Duk wanda ya kalla Dada yasan mutum ne mai cikakkaiyar lafiya kodan yanda yake gudanar da komai nashi cikin zafin nama da jarumta. Sai dai nutsuwarsa da kamewa ke ɓoye ainahinsa har takai bai san yabi hanyar saɓama UBANGIJI domin kwaranye ƙishinsa ba. Ya san dai komai lokaci ne, sannan jarabawa ce. Ko Nabeeha na bashi tausayi, amma yana buƙatar ganin ta dawo hankalinta kafin shi da ita su fuskanci juna. Zai iya barinta da ƴan uwansa suyitayi matsalarsu ce. Amma dole ta koya girmama masa mahaifiyarsa. Dan duk duniya baida kwatankwacin ta koda a misali ne. Duk yanda yasan halayen mahaifiyarta marasa ƙyau koda wasa bai taɓa mata kallon banza ba balle yin maganarta da wani, ita miyasa bazata gane tashi uwar ba abar wasanta bace. Koma dai miye ai yanzu ya shirya mata kuwa. Jira yake kawai a kammala bikin nan su koma muhalli guda ɗaya...

°•••°•••°•••°•••°

Yau data kama Lahadi shagali biyu ne zai gudana. Walima da rana, dinnar da daddare. Dan haka tunda fa gari ya waye duk da gajiyar da aka yini a ciki haka aka sake dasa wata hidimar. Amare dama an yanke sai gobe idan ALLAH ya kaimu kowacce za'a miƙata ɗakinta. Dan haka su Biebah suka samu damar yin barci sosai. Basu tashi ba sai kusan sha biyu. A taron walima ba wata kwalliya za'ai musu ba, dan haka da kansu sukai kwalliya da shirinsu cikin atamfofi. Sannan aka kawo musu alƙyabbu masu shegen ƙyau da tsada suka saka. Ba ƙaramin ƙyau sukai ba kuwa. Dan zaka iya cewa ma sun shafi gidan sarauta ne. Lailah tazo tai musu turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. A lokacin itama Shariffa ke shigowa da wani abu a babban kofi sai ƙananun kofuna uku. Zubawa tai ta bama kowannensu. Maganannu biyu suka tsaya kallo batare da sun sha ba. Lailah dake kallonsu ta ce, “Ninah da Ruƙayya wai mi kuke jira ne?.” Kamar Nimrah zatai kuka ta ce. “Mamy wlhy abun nan fa akwai matsala. Jiya ciwon ciki ya sakani da daddare. Hakama Ruky yau da asuba taita ciwon ciki ko?”. Tai maganar ƙarshe tana kallon Ruƙayya. Kai ta jinjina itama. Sai kuma ta ce, “Mamy wai minene?”. Shariffa ta hararesu da faɗin, “Ƙaniyarku ce. Dalla kusha ku bani. Ba ciwon ciki ba ciwon ƙashi yake saka ku ƙarewa”. Lailah dai dariya take ƙunshewa. Hakama Aunty Mimi dake bakin ƙofa tsaye. Dan ta fahimci shiriritar yaran nan baisa sun gane mike damunsu ba. Amma tunda sun ce ciwon ciki kawai a barshi a hakan. Ganin suna ƙus-ƙus Shariffa ta fahimci zasu iya zubarwa. Dan haka tazo gabansu ta tsaya tace su sha a gabanta. Aiko a gaban nata suka sha kamar zasuyi kuka. Sai suka bama Biebah tausayi. Dan ita kanta da take babban abubuwan nan da ake basu sun dameta bare su....

Ana idar da sallar azhar aka fara kwasar mutane zuwa wajen walimar. Amare kam sai wajen biyu saura ma. Dan tare aka zo ɗaukar su tare da Mammah. Bilal zai jasu, dan haka Ammar ya maƙale a kusa da shi. Aiko tunda suka fito ƙamshin su ya buɗaɗe compound ɗin. Ji Ammar yay kamar yaje ya rungume Ruƙayya, ya dai daure ya cije da ƙyar. Mammah na lure da shi, ta girgiza kai kawai. Shima Bilal sai ya zungureshi yana nuna masa Mammah ɗin. Ammar ya ɗan waro idanu yana shafa ƙeya. Bilal ya kauda kai yana dariya ciki-ciki. Tun daga nan Ammar ya kama kanshi. Amma harga ALLAH daga shi har Bilal ɗin kamshin turaren su Ruƙayyan ɗaga musu hankali yake. Sai da suka fara tafiya su Nimrah suka gaishe su. Bilal dake kallonsu ta mirrorn gaba ya ce, “Wai ya naga duk kunyi laushi ne? Mammah yaranki ko basu da lafiya ne?”. Ƙaramar dariya Mammah tayi, yayinda Nimrah da Ruky suka ƙara lafewa jikinta. Sai Biebah ce ta ce, “Yaya bazaka gane ba”. “Ganar da ni Auta. Dan ke gani nai ma kin rame min a ido fiye da su”. Hawaye suka zubo mata. Sai kawai Ammar ya hau dariya da faɗin, “Wai kuka kike?”. Kanta ta sake duƙarwa, da lafiya-lafiya ne sai ta rama. Dan shi da Aunty Mimi sam bata raga musu kasancewar su sakonta. Bilal bai ƙara magana ba, sai idanunsa da suka kaɗe. Shi kansa Ammar ɗin dauriya ce kawai amma har ya fara jin kewarta tunma da aka fara bikin nan. Motar tai shiru dan suma su Nimrah sun koma jikin Biebah suna hawayen ne. A haka suka iso wajen.........✍️ [1/30, 5:31 PM] Zeenaran 😘: 46