Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 46

Post

Kida a ruwa Book 3 page 46

.....the preaching from the mouth of the great Muslim scholars is cooling people's bodies again. He also asked the bride to enter their attention directly on married life in Islam and the lectures were held. Afternoon prayer time was suspended. After the prayer, a new lecture was started, and at 5 o'clock there was a prayer and the dinner started again. Alhamdulillah everything went smoothly and smoothly. A lot of great people attended this party. Hair was shown on live tv. Apart from those who post on phones. However, for the first time, Nimrah's pictures were out. When people talk about Zak-Shadow marrying a young girl. Women began to tell his wife that it was permissible for him to wait eight years for him to come back and marry her. People don't know the truth but they are able to organize the conversation and respect it. For the issue of the president's arrival, there are also a few names. Oh, the one they are doing, there is no sign that he has time for them... They return home after the evening prayer and start preparing for dinner. Isha is being distributed and people are passing by here as well. While the bride and groom are there, they are decorated and decorated for the

Standalone post1,769 words

........Sosai wajen yayi ƙyau, komai kuma a nutse a tsare. Ɓangaren mata daban na maza daban. Kasancewar itama Asma'u sun iso aka dawo da ita wajen su Biebah. A motar aka barsu Mammah ta shige. Sun kai kusan mintina goma sannan Aunty Mommy tazo tafiya da su. Wajen yayi tsitt kamar yanda aka buƙaci shirun domin fara addu'a. Dan haka hankalin kowa ya dawo kan amare da suka shigo. Sai dai fuskokinsu rufe da hular alƙyabba su duka huɗun, Dada yaji daɗin yanda akai musu shigar mutunci kuwa. Har wajen da aka tanada domin su akai kaisu. Kujeru huɗu daga gefe ta ɓangaren mata. Dai-dai lokacin kuma ake isar da batun zuwan shugaban ƙasa da kansa ba saƙo ba. Tare da iyalansa gaba ɗaya. Mutane sun ƙara tabbatar da lallai akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin su Dada da Shugaban ƙasa a yau, dan haka ƙus-ƙus ya fara tashi a wajen har sai da aka buƙaci shiru. Sosai tsaro ya ƙaru a wajen, bayan sun zauna akai addu'a sannan Imam ya fito yay karatun Alkur'ani. Sosai zukata suka ƙara nutsuwa, kafin a fara gudanar da wa'azi daga bakin manyan malamai musulinci daya sake sanyaya jikin mutane. Ya kuma saka amare ƙara shiga hankalinsu dan kai tsaye akan rayuwar aure a musulinci taken lectures ɗin suka gudana. Lokacin sallar la'asar yay aka dakata. Sai da aka yo salla aka ɗora wata sabuwar lecture ɗin kuma dai, zuwa 5 akai addu'a aka fara liyafar cin abinci kuma. Alhamdullahi komai ya gudana cikin nutsuwa da dattako. Dan sosai manyan mutane sun halarci wannan walima. Gashi an nuna a gidajen tv live. Banda masu posting a wayoyi kuma. Sai dai a karo na farko hotunan su Nimrah sun fita. In da mutane suketa ka-ce-na-ce akan wai Zak-Shadow ya auri yarinya ƙarama. Mata suka fara faɗin matarsa tai masa halaccin jiransa shekara takwas ya dawo ya saka mata da kishiya. Mutane basu san gaskiyar magana ba amma sun iya tsara zance da girmamashi. Ga batun zuwan shugaban ƙasa wajen shima sunata yan-yan, akai. Oho shi wanda suke yi dan shi ɗin ma babu alamar yana da lokacin su.....

Ana dawowa gida sallar magriba akayi aka kuma fara shirin dinner. Ana idar da isha'i aka fara wucewa da mutane nan ma. Yayinda amare ke can ana tsara musu ado da kwalliya na amaren girma. Kai daga gani kasan fitar ta musamman ce. Babu wanda ya saka ran zuwan Dada wajen nan da Faro. Dan haka ma akace ayi angunan bogi. Wai Ma'aruff ya zauna tare da Biebah. Nimrah kuma Ja'afar. Mammah naji ta ce, “Babu ruwanta su da Muhammad, gara su fara kiransa su sanar masa idan ya amince to. Aiko sunata darurar kiran nasa suka dai daure. Sai da wayar ta kusa tsinkewa ya ɗaga. A lokacin fitowarsa a wanka kenan ma. Cikin kame-kame da in inar rashin dalili Ma'aruff ya sanar masa. Yay shiru kamar bazai amsa ba. Hakan yasa Ma'aruff fahimtar sun taro match. Amma ya daure dai bai kashe wayar ba. Dada yay gyaran murya, sannan ya furta, “Ku kun zama manyan banza kenan ko Ma'aruff? Kunsa Mammah ta takura na barku kuyi shine kuma zaku sake kawo wani abun..” “Dada kayi haƙuri mun tuba. Kawai mun san ko munce kazo bazaka zo bane. Kuma Yaya Haydar ma idan baka zo ba shima nasan bazai zo ba......” “Shi ke nan su Bilal ɗin basai suyi ba ya wadatar”. Dada ya faɗa cikin katse shi, yana gama faɗa kuma ya yanke wayarsa. Ja'afar ya ce, “Hummm dama bana faɗa maka ba Twiny, Dada fa wlhy kishin tsiya ne da shi. Da zakuji ta tawa suma su Bilal su haƙura. Amaren kawai su zauna ba dole sai da anguna ba. Idan ba hakaba kaɗan daga aikinsa yace kada ma aje da Ninah wajen”. “Wlhy Dada daya gama damu”. Cewar Bilal kamar zai kuka. Dariya su Ja'afar ɗin suka sanya kuwa. Ma'aruff ya ce, “To inaga kawai abi shawarar Twiny ALLAH. Dama da yaya ya amince ayi dinnar ɗin nan. Kada mu ƙureshi kuma kun san dai Dada ƙaniyarmu zamu ci a ƙarshe”. Hakan yafi basu masalaha, dan haka duk suka amince. Suka kira su Aunty Ummi suka sanar mata. Itama ta gamsu, dan wlhy tasan badan Mammah ta saka baki ba ma bazai bari ba. Daga haka aka kwashi amare zuwa wajen dinner daya gama cika ya tumbatsa. Ga uban tsaro har ba'a magana. Yanda aka tsara amaren ma kawai babu angwaye sai ya kawo wani sabon salo daya burge mutane. Gashi sun sha ƙyau har sun gaji. Gaba ɗayansu material ne a jikinsu dogayen riguna, sai dai kowacce da kalar nata da kuma irin ɗinkin da take so. Kasancewar an tsara wajen da iya adadin mutanen da ake buƙata komai a nutse. Bayan addu'a ƙawayen su Nimrah da suka shirya kalolin rawa suka fara gudanar data farko tare da su Mu'azz. Ba ƙaramin ƙayatarwa abin yayi ba. Sai kuma mawaƙan da sukai waƙoƙin biki suma suka fara baje kolinsu. Sannan ƙawayen Asma'u suka gudanar da tasu rawar. Su dai na Biebah sun ɗauki girma. Su Feddo sun sake yin rawa ta biyu, kafin ai taƙarshe harda amare. Sosai abin ya ƙayatar da jama'a. Su Uncle Ja'afar sai liƙe yaransu suke da kuɗi. Bilal yana fakar ido ya rungume Ma'u, Ammar na ƙyalla ido ya gani yace, “Wlhy nima bazaka barni a baya ba. Haba ai nayi haƙuri jama'a”. Shima ya kama Rukyn sa ya kanainaye. Mi su Lailah zasuyi ba dariya ba. Sai da Ma'aruff yay musu ƙulli a baya kowa ɗai-ɗai suka sake su. Nimrah nama Ruky dariya da shaƙiyanci ita ko ba baki. Dan gaba ɗaya jikinta yayi sanyi tun lectures ɗin ɗazun. Ita kanta Nimrah ɗin ƙarfin hali ne kawai. Asma'u kam ai bama a magana, kodan ita da Biebah zasu bar gida ne zuwa wasu gidajen. Garama Asma'u gida za'a kaita dan bayan gidan Baffa basu da wani gida abin alfahari sama da gidan Mammah. Sosai dinner ta ƙayatar itama sai sambarka. Kamar yanda Dada ya saka doka ƙarfe sha biyu a aka tashi. Dan sha biyun ma na cika sai ga kiransa a wayar Aunty Mommy. Cikin rikicewa ta ce, “Dada ALLAH mun tashi, dan yanzu haka ma su Yaya Ma'aruff sun wuce da su Ninah gida. Muma muna ƙarasa sallamar baƙi ne kawai. Ajiyar zuciya ya sauke yana ajiye wayar. Faro da Imran suka kallesa sukai murmushi. Dama tun ɗazun sai ƙananun tsaki yake musu....

_______________

Sai muce Alhamdullah biki kam ya kammala. Dan washe gari aka karasa zuwa gidan Biebah aka ƙarasa komai. Dada yace duk mai zuwa yaje yaga ɗaki dan shi da Imran zasu kai Biebah ɗakinta. Wannan ba sabon abu bane. Dan tun daga kan Aunty Ummi, Mommy, Mimi shi da kansa ya kaisu ɗakunansu tare da Imran. Sai suma su Ja'afar dake yin mota ɗaya subi bayansu. Kuma anayi la'asar suke tafiya. Iyaye da yayye sun zagaye Biebah da aka gama shiryawa. Aka fara kaita gaban Uncle Nasiru da Uncle Jamilu, Zubairu, Tasi'u sukai mata nasiha. Sannan aka kaita ga Mammah. Addu'a kawai tai mata dan ita kam duk wani faɗa da nasiha tama yaranta shi. Suma su Gwaggo Khadijah sukai nasu. Sannan aka ƙarasa da ita gaban Dada da Imran, sai su Ja'afar dake tare da su har zuwa Ammar ƙarami. Sosai idanun Dada sun juye. Duk lokacin da zai kai ƙannen nan nasa gidan aure kobai fito ya faɗa ba kallo ɗaya zaka fahimci damuwa a tare da shi. Yanzu ma koda Biebah ke durƙushe a gabansu ya zuba mata idanu ne kawai. Sai kuma ya kai hannu ya kamo nata. Hakan yasa ta matso jikinsa sosai ta ɗora kanta a ƙafarsa. Kanta ya shafa a hankali yana murmushin ƙarfin hali. “ALLAH yay miki albarka. Yanda kikai mana biyayya kema UBANGIJI ya baki yara masu albarka da zasuyi miki. ALLAH ya zaunar dake gidanki lafiya kamar sauran ƴan uwanki. Habibah na yarda da mijin da kika zaɓa da kanki ɗari bisa ɗari kamar yanda na yarda dana ƴan uwanki a baya. Kema na yarda da tarbiyyar da muka baki, kije kiyi haƙuri. Shi aure ibada ce. Rayuwa ce ta rabi farin ciki rabi jarabawa. Babu wani bawa da zai iyama ɗan uwansa bawa yanda yake so ɗari bisa ɗari na yau da goben rayuwa. UBANGIJI ne kawai mai wannan ni'imomin a gare mu. Dan haka idan kinga kuskure daga Haydar ki yarda shi ɗin mutum ne kamar ke. Dole yay dai-dai kuma dole yayi kuskure. Ku zauna ku gyara a ɗakin ku basai kin kawo mana ba. Ga ƴan uwanki nan su duka ukun tunda na kaisu gidajen aurensu ban taɓa zama shari'a tsakaninsu da mazajensu ba ko sau ɗaya. Kuma ni shaida ne kin fisu haƙuri. Badan mun gaji dake ba zamu kaiki wani gida, idan so samu ne naita ganinku a kusa dani ina jin daɗi da farin ciki, amma hakan bazai yiwu ba, wannan shine gatan da zamuyi muku muma muyima kammu. Kar ai sakaci da ibada, yanzu ne ma lokacin da za'a ƙara dagewa kinji”. Kanta ta jinjina masa tana sake fashewa da kuka. Ya kauda kansa gefe yana dauke guntun hawayen da suka taru masa ta gefen ido. Daga nan shima Imran ya sake mata tashi nasihar. Kafin su Ma'aruff, Ja'afar, Bilal, Ammar. Daga haka akai addu'a sannan Dada ya miƙe riƙe da hannunta. ALLAH sarki Small Mom, da gudu su Nimrah da Mu'azz sukazo suka rungumeta, dama suna ɗaki sun haɗe kai sunata kuka. Bintu taje ta kirasu yanzu. Idanu kawai Dada ya zuba musu yama kasa magana. Sai Daddy Imran ne ke lallashinsu. Dan su Ja'afar ma sharar ƙwalla suke. Wato kowane ɗan uwa fa a irin wannan ranar yakan ji wannan damuwar ta rabuwa da ƴar uwarsa. Musamman wannan zuri'ar da suka shaƙu suke matuƙar son junansu. Ƙarshe dai da ƙyar Mammah tazo ta janye su Ruƙayya tai ɗakinta da su. Su kuma suka fice Biebah na jikin Dada...

//★//★//★//★//

Ashe wasa farin girki. Sai da suka kai Biebah gidanta daya gama haɗuwa Dada ya kama hannun Faro ya saka na Biebah a ciki. Ya jaddada masa amana ya bashi, idan kuma yaci wlhy bazai taɓa yafe masa ba. Ya tabbatar masa a cikin kaf ƙannensa Biebah itace zuciyarsa. Kar ya bari ya taro faɗan da bazai iya karewa ba. Faro yay murmurshi da tabbatar masa zai kamanta in sha ALLAHU. Dan shima Biebah ƙanwace a garesa ai. Shima Imran ya sake jaddada tashi amanar. Su dai su Ja'afar sun barma zuciya saboda matsayin Haydar yaya. Amma yasan kosu kaɗai sun ishe shi gayya idan ya taɓa Biebalo. Zasu tafi fa Biebah ta riƙe Dada tanata ku

[3/25, 12:07 PM] Zeenaran 😘: