Kenza eBookz
Cover art for Kida a ruwa Book 3 page 47

Post

Kida a ruwa Book 3 page 47

.....a dangerous trap in the life of the Boss above her. That's why I'm ready to return to his world, and I promise to give my life to support this fight." "We are also with you in the battle, Haysam's son deserves more than that for us. Now what is the next step?" "Then I think that you delayed more and revealed your face to him, you just continued to give him personal information as you started. If only these people would understand that you are alive and suffering, our lives would be better." He smiled with many meanings. Before he congratulated himself by saying, "That's right, Sir. But don't forget that we have died in the human world. What are you afraid of on this shore? You are a soldier, the soldier also raised ZAK-SHADOW". His heart dropped and he said, "That's what I understand. Now we have to go next? But before that we should seek Baba's advice". "This is correct. But before that I will send him this information first. Then you pushed the Messenger of God, God gave us the opportunity to see him soon.." I bowed to him. After that, they said goodbye and he left the place. They met in a hidden place, and he was going in to hide his true identity. That's why...

Standalone post1,497 words

47

.........“Kana nufin lokacin da zaka bayyana kanka ga Zak-Shadow yayi kenan?”. “Tabbas yayi, kuma ya kamata ace nayi hakan saboda wannan shine dai-dai lokacin daya dace. Abinda ya sakani jinkirtawa ya riga yaje hannunsa. Matarsa ita ce babban MAKAMIN da mutanen nan suke riƙe da shi a kasa ta kowanne ɓangare....” “Hummm kana ganin dan ta koma hannunsa zai iya tsira? Ka sani na sani mutanen nan nada ƙarfi matuƙa. Dan sun binne mutanen kirki da yawa irin Zak-Shadow a ƙasar nan dama wanda suka fishi gwagwarmaya. Shi kansa UBANGIJI ne bai kawo ƙarshensa ba a hannunsu shiyyasa suka kasa kaisa ƙasa badan yafi ƙarfinsu ba”. “Nasan da haka sosai Sir, kamar yanda kace UBANGIJI kuma ai magana ta ƙare. Abinda nake so ka fahimta bana fatan su sami nasarar kai masa hari ta hannun AMANARSA. Dan ita ɗin amanarsa ce......” “ƘALUBALENSA kuma a yanzu ba”.. Mutumin ya faɗa cikin katseshi da takaici da damuwa”. “Bazan yi musu da kai akan ita ɗin ƘALUBALENSA bace Sir, dan inada tabbacin a yanzu babu wani tarko mai haɗari a cikin rayuwar Boss sama da ita. Shiyyasa nima na shirya dawowa cikin duniyarsa, kuma nayi alƙawarin bada rayuwata wajen tayashi wannan yaƙin.” “Mu ma muna tare da kai a cikin yaƙin, dan Haysam ya cancanci fiye da hakan a garemu. Yanzu miye mataki na gaba?”. “Zan cire fuskar bogi, sannan zan fito na daina laɓewa a baya.” “Sai nake ganin kamar ka ƙara jinkirtawa da bayyana masa fuskarka, ka dai cigaba da bashi bayanan sirri kamar yanda ka fara. Dan in mutanen nan suka gane kana raye da wahala rayuwarmu tayi tsaho”. Murmushi yayi mai ma'anoni da yawa. Kafin ya jinjina kansa da faɗin, “Haka ne Sir. Amma karka manta ai mun jima da mutuwa a duniyar mutane. Har mi kake tsoro a wannan gaɓar? Kai ɗin fa SOJA ne, sojan ma rainon ZAK-SHADOW”. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi. Ya ce, “Haka ne na fahimta. Yanzu sai muje next kenan? Amma kafin hakan ya kamata mu nema shawarar Baba”. “Wannan shine dai-dai. Amma kafin hakan zan fara aika masa waɗan nan bayanan. Sai ka turama Baban saƙo ALLAH yasa ya bamu damar ganinsa da wuri..” Jinjina masa kai yayi. Daga haka suka sallama ya baro wajen. Dama a wani ɓoyayyen waje suka haɗu, yana cikin shiga ne ya ɓoye ainahin kai shiyyasa baka isa gane waye shi ɗin ba kai tsaye.....

•••••••••••• •••••••••••••

Sosai damuwa ke shimfiɗe a fuskar Faro dake kallon Biebah tun bayan ficewar su Dada. Sai da yaji ƙarar rufe gate alamar sun fita gaba ɗaya sannan ya sauke ajiyar zuciya. Karo na farko ya ɗaura hannuwansa duka biyu a saman kafaɗarta. Sai ta sake duƙar da kai sautin kukanta na ƙara fitowa. “Kukan nan bai isa haka nan ba Biebah? Nima fa yayanki ne. In sha ALLAHU zan yi ƙoƙarin maye miki gurbin su Haysam, koda ba ɗari bisa ɗari ba zan kamanta kinji”. Kanta kawai ta iya jinjina masa, shima bai matsawa kansa da sai tayi maganar ba ya sakata a jikinsa kawai ya rungume ta. Abinda tafi buƙata kenan a yanzu, dan haka ta lafe tana shashshekar kuka da jan ajiyar zuciya. Bayanta ya cigaba da shafawa a hankali, har sai da ya tabbatar ta rage nauyin zuciyar tata sannan ya kama hannunta suka zauna a cikin kujera. Mayafin jikinta ya yaye, dan haka ta sake sunkuyar da kanta taki yarda ta kallesa. A karo na farko yay murmurshin da har tana jin fitar sautinsa. Sai kuma ya matso sosai yana leƙen fuskarta data sunkuyar. Yanda yay ɗin ya bata kunya, tai ƙoƙarin kauda kanta gefe ya kamo fuskar cikin hannunsa. “Na zata kunyar ta ƙare ai kuma ko Habibiya. Kin manta yau a gidan Haydar kike? Amarya mai capacity kenan da Babban yaya da kansa ke kawota gidanta”. Murmurshi ta saki tare da kife kanta cikin hannunsa dake riƙe da fuskar tata. Shima ya sanya dariya yana matsota sosai jikin nasa ya sake rungumeta. Suna a haka akai kiran sallar magrib. Badan yaso katsewar yanayin ba ya kamata ya miƙar yana faɗin, “Muje na rakaki ɗaki na je massalaci”. Babu musu ta miƙe, haka suka nufi inda bedrooms ɗin suke. Ya tsaya a farkon corridor ɗin yana kallonta. Cikin magana ƙasa-ƙasa ya ce, “Ina zan kai amarya?”. Kanta a ƙasa ta ce, “Koma ina”. Fuskar sa da murmurshi har yanzu ya ce, “Shike nan bari na kaiki ɗakina, dan yau baƙuwata ce ke”. Batace komai ba, shima bai sake magana ba ya kama hannunta suka nufi ƙofar dake can ciki a ƙarshen corridor ɗin. Ɗaki ne babba, an zuba masa kaya masu ƙyau, babu kuma tarkace a cikinsa sam. Ga ƙamshi da tsafta alamar yana samun gyara da kulawa. A kaikaice ta ƙare masa kallo, ya zaunar da ita a bakin gadon ya nufi bayi batare da yayi magana ba. Babu jimawa ya fito jikinsa da ruwa alamar yayi alwala. “Naje massalaci”. Ya faɗa yana nufar ƙofa. Ta amsa masa da “A dawo lafiya”.

★Bayan fitarsa itama alwalar ta tashi tayo. Ta gabatar da salla. Koda ta idar bata tashi a wajen ba ta zauna zugum cike da damuwa da kewar gida. Musamman ma su Ruƙayya da a koda yaushe suna nane da ita. Sai Mammah uwa abar alfaharin kowane ɗan halak. Hawaye ne suka cika mata idon, bata bari sun zubo ba ta maida su ta haɗiye. Karatun Alkur'ani ta fara dan ɗebema kanta kewa har aka kira sallar isha'i. Tashi tai ta gabatar, tayi har shafa'i da wutri. Bayan ta idar tana zaune tana addu'a ya shigo. Kyakkyawan basket ɗin hannunsa ya ajiye a gefenta shima ya nema waje ya zauna a ɗaya daga kujerun ɗakin. Tai addu'a ta juyo tana masa sannu. “Yauwa Baby. Ga abinci nan Hajiya ta aiko”. Kanta a ƙasa ta ce, “ALLAH ya saka da alkairi”. Sai kuma ta miƙe ta ɗauki Basket ɗin zuwa inda yake. Kallon da yake mata ya sakata kasa kallonsa, murya a ƙurya ta ce, “Ina kitchen yake?”. “Ke da gidanki kike tambayar kitchen? To na hutar dake zauna mi kike buƙata na ɗauka miki? Dan yau ke baƙuwata ce”. Murmushi tayi, shima ya miƙe yana nasa murmushin ya fita. Babu jimawa ya dawo da plates da cups, sai spoons. Ta zamo daga kujerar da take zaune ta buɗe abincin ta zuba masa komai. Zata miƙe ya riƙota, kusa da shi ya zaunar da ita har jikinta na gogar nasa. Abincin daya ɗiba ya kai bakinta. Zata fara nuƙu-nuƙu ya ce, “Ɗura kike so kenan?”. Kanta ta girgiza masa, cike da kunya ta fara amsa. Idan yaci sai ya bata a haka suka cinye abincin da gasashen naman. Ta fara gyara wajen yana tayata. Sun fito tare har kitchen ɗin da yay mata matuƙar ƙyau, dan har sai da ta tsaya tana kallo. Sai kawai jitai an ɗauketa gaba ɗayanta. Babu shiri ta kama dariya da roƙon ya sauke ta amma yaƙi sai da ya kaita har bedroom ɗinsa, a bedroom ɗin ma a cikin bathroom. Sabon brush ya buɗe mata ya saka marclen a jiki ya bata. Ita dai a kunyace ta amsa. Koda suka kammala sai yace suyi alwala...

Sun gabatar da sallolon nafila, yay musu addu'a sosai tare da dafa kanta. Sannan ya ɗora da nasiha, tare da sake maimaita mata abinda yake saurin saka shi a fushi da wanda ke saka shi a farin ciki. Itama yace ta sanar masa. Kasa magana tai, sai bai matsa mata ba ya barta. Shi ya fara miƙewa ya sake shiga bayi. Tana nan zaune kusan mintina talatin sai gashi ya fito ɗaure da towel. Da sauri ta duƙar da kanta, shi kuma dan neman magana yazo har inda take ya kamata ya miƙar. Duk yanda yaso ta kalleshi taƙi kallonsa. Sai ma jikinta dake neman fara rawa. Sai yay murmurshi kawai, cikin raɗa ya furta, “Baby sarkin kunya. Yanzu fa miji nake ba Yaya Haydar ba”. Ita dai batace komai ba, sai ma sake duƙe kanta da tai. Ya sake murmusawa da faɗin, “Tunda bakin ya mutu shike nan. Jeki kiyi wanka to kizo ki kwanta ki huce wannan gajiyar bikin da kuka kwasarma kanku”. Koda ta jinjina masa kai sai ta nufi hanyar fita. Riƙota yay. “Haba Biebalo ina zuwa kuma? Ga bathroom anan. Har kayan barci kina da su anan ɗakin, kin san duk inda Haydar yake kema kina a wajen”. “Yaya zanje can nidai”. “Bazan ce a'a ba. Amma idan muka je can ɗin nine da kaina zan miki wankan kin yarda?”. Karo na farko ta ɗago a rikice tana kallonsa. Sai dai tama kasa furta abinda ke bakinta. Shi kuma ya fuske ya tsareta da idanunsa da ke a juye. Har sai da taji kallon na sake tsumata da ratsa mata jiki sannan tai saurin barin wajen ta nufi bathroom ɗin nashi kamar yanda ya buƙata tun farko. Sai dai babu abinda zuciyarta keyi sai dukan tara-tara, dan tunda take da shi bata taɓa ganin kalar abinda ya gani a cikin idanunsa ba yanzu........✍️