Kenza eBookz
Kida a ruwa Book 3 page 51

Post

Kida a ruwa Book 3 page 51

.....she took it. Then he relaxed and smiled a little. However, he did not want that in his heart. Today, he is ready to own her and return her. After everything he did, he let her drink the milk only, and finally he fixed the situation himself and told her to get up and go to bed because he was tired. Even in the situation she was in, she had to feel a little sad. But she is an easy going girl. So, none of them took her hand and followed her to the bedroom. But shame did not stop her from looking at anything. Since he sat her in the chair, she threw herself on the floor and did not allow her to do it again until he finished removing his clothes. But he offered her to go to the bath and hide her face in her legs. Yay just laughed a little as he passed by. It didn't take long for him to come out, where he left the place and here he found her. But now she's doing it too. She sympathized with him, so he did not speak and left the room to go to her room. A few minutes later, he returned with a bag in hand. The movement of the door opening and closing jolted her awake. Although everything is slow. "I'm sorry, I'm sorry". "Right, I'm not sleeping." Yay just smile. With handing over his c

Standalone post1,474 words

51

........Duk yanda Bilal yaso Asma'u taci abincin nan taƙi, ta dage akan ta ƙoshi. Naman ma sai da ya gyara zama yana faɗin, “ALLAH ɗura zan miki yanzu ko Asmah”. Idanunta ta ɗan waro da jan jikinta baya ganin yana shirin cafkota. Cikin siririyar dariyar dake kufce mata ta ce, “ALLAH da gaske nake na ƙoshi. A irin yanayin nan ƙyanƙyamin nama na nake”. “Yanayi?”. Ya faɗa yana tsatstsareta da idanu. Dole ta maida kanta ƙasa tana jinjina masa. “Bani a buɗe Asmah. Wane irin yanayi ne haka?”. Sosai taji kunya da daburcewa. Dan bata san yanda zata masa bayanin dazai gane ba kuma. Sai ma taji tana dana sanin ambaton kalmar gareshi. Jinsa gab a jikinta ya sata runtse ido. Sai kuma ta motsa kamar zata miƙe amma yay saurin riƙota. Sai ko gata a saman cinyarsa ɗare-ɗare. Mutsu-mutsun duniya ya hanata tashi, ya kuma dage akan sai fa ta sanar masa wane yanayi ne wannan dake sakata jin ƙyanƙyamin nama. Bata da mafita, dole tai dauriyar faɗin, “Idan ina fashin salla”. Shiru kamar wanda wutar kansa ta ɗauke. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya da yin ɗan murmushi. Sai dai har cikin rai bai so hakan ba. Dan yau a shiryensa yake na son mallakarta da komanta. Basar da komai yayi ya sakata ta sha madarar kawai, daga ƙarshe ya gyara wajen da kansa sannan yace ta tashi suje su kwanta ya gaji. Duk da a halin da take ciki sai da taji ɗar-ɗar. Sai dai ita ɗin yarinya ce mai sauƙin kai. Dan haka babu musu daya kama hannunta ta bishi har bedroom ɗin daya gama haɗuwa matuƙa a matsayin nashi. Amma kunya bata barta ta kalla komai ba. Tunda ya zaunar da ita a kujera ta duƙar da kanta ƙasa ko motsin kirki bata yarda ta sake yi ba har ya kammala cire kayan jikinsa. Koda yay mata tayin zuwa wanka fuska ta ɓoye cikin ƙafafunta. Yay ƙaramar dariya kawai yana wucewa ya barta. Bai wani jima ba ya fito, inda ya barta ɗin kuma anan ya sameta. Sai dai yanzu ma gyangyaɗi take yi. Tausayi ta bashi, dan haka baiyi magana ba ya fita a ɗakin zuwa nata ɗakin. Mintuna kaɗan sai gashi ya dawo da kaya a hannu. Motsin buɗe ƙofar da rufewa ya sakata ta farka. Duk da kuwa a hankali yake komai. “I'm sorry, na tadaki ko”. “Dama ba barci nake ba fa”. Yay murmushi kawai. Tare da miƙa mata kayan hannunsa. “Gashi ki canja kaya sai ki kwanta. Nasan akwai gajiya”. Hannu biyu ta saka ta amshi kayan batare data kallesa ba dan bathrobe ce a jikinsa. Ta ce, “Na gode”. Daga haka ta miƙe. Bathroom ta nufa. Bai ce mata komai ba shima ya nufi coloset ɗinsa dan yin shirin barci.

Har Bilal ya kammala komansa ya koma bakin gado ya zauna shiru babu Asma'u babu labarinta. Dubansa ya sake kaiwa ga agogon ɗakin, kafin ya maida kan ƙofar bathroom ɗin a karo na babu adadi. Sai kuma ya miƙe dan ya fahimci akwai dalilin shirun nata. Har ya kai hannu zai yi mata knocking sai kuma ya dakata. Cikin yin ɗan nazarin sakanni ya buɗe ƙofar kawai. Hakan yazo ma Asma'u a bazata. Ta ɗan zabura baya alamar a jikin ƙofar take tsaye. Suna haɗa ido ta kauda kanta tana shafa gefen wuyanta da ɗan matse ɗayan hannun nata a jikinta. Fahimtar kunya ce ta hanata fitowa ya sashi ɗan girgiza kansa. Batare da yayi magana ba ya shigo cikin bayin. Sai jitai kawai ya ɗagata gaba ɗayanta daga kan ƙasa. Sosai taji kamar ta fasa ihu dan kunya. Ta kife kanta a ƙirjinsa har ya direta a gadon bata yarda ta kallesa ba. Shi kuma koda ya diretan sai ya ƙi raba jikin nasu yama zubama fuskarta ido a yanda yake.... “Ƙyawu. Nutsuwa. Kunya. Tarbiyya duk naki ne Asma'ul-Husnah. Alhamdullahi ya rabbi daka bani Asma'u Imran Abbas matsayin sirrina. I love you so much Asmah.” Ya kai ƙarshen maganar yana hura mata iska cikin kunne. Jikinta ta ƙanƙame kalamansa na kekketa mata zuciya da ɓargo. Shi ko ya samu damar cigaba da sumbatar wuyanta, a haka ya gangara zuwa fukarta, bata ankara ba taji lips ɗinta cikin nashi.....

>>>>>>%<<<<<<

“Da kin san yanda kukan nan naki ke marmashe min zuciya Noor da kin daina. Ko kina son na tayaki nima?”. Kafaɗa Ruky ta maƙema Ammar. “To ki bari Please”. “Ni bazan daina ba sai ka kaini wajen Mammah”. Ammar ya cije lips yana wani sake ƙanƙance idanunsa da suka shige cikin. Cikin sake kwantar da murya ya ce, “Idan kinje wajen Mammah ɗin mi zakiyi?”. Kai tsaye ta ce, “Barci”. “Ni kuma ki barni da wa?”. “Sai mu tafi tare kai ma ka koma ɗakinka nacan”. “Saboda na kawo kanwa duniya Ruƙayya. Hajjaju ai bana maimaita aji”. Sosai ta kallesa yanzu kam. Sai dai suna haɗa idanu launin nasa idanun suka saka ƙirjinta bugawa. Karo na farko tai ƙoƙarin janye jikinta daga nasa. Sai dai bai bata damar hakan ba sai ma sake ƙanƙameta da yayi. Muryarsa na wani kalar sarƙewa ya furta, “My Babie ki barni na more yau ɗina Please. Shagwaɓar nan da rashin jin nan da kukema Mammah ki bani su zan ƙarɓa da hannu biyu. Sannan na matsar dake zuwa ajin girma. Na canja ki daga Auta zuwa Matar Auta.....” “Naga Boni. Uncle kana lafiya kuwa?”. Tai maganar tana kai hannu saman goshinsa alamar auna zafi. Hannun nata ya riƙo, murya a marairaice ya ce, “Bana lafiyar nan Ruƙayya. Kuma tunda kika fara zama cikakkiyar mace nake a wannan ciwon. Kullum kece mafarkina. ALLAH ALLAH nake gari ya waye na ganki. Ƙagara nake na dawo gida na gangi. Har bana son dare yayi dan nasan zanyi nisa da ganinki. Gaba ɗaya kin cinye min kurwa mata basa burgeni”. Yanzu kam Ruky ta fara dawowa hankalinta. Dan gaba ɗaya kalaman Ammar ɗin dukan mata zuciya sukeyi. Har takai jikinta na tsuma. Cikin ɗan salon daburcewa ta ce, “Uncle ina jin fitsari”. Sassauta riƙon da yay mata yayi. Batare da yace komai ba ya ɗauketa cak yay hanyar bedroom da ita. Yau kam Ruƙayya taga abinda yafi ƙarfinta. A ranta faɗi take (Wai dama Uncle Ammar haka yake ɗan duniya ne? Yau ni Ruky na shiga tamanin, Ninah kina ina za'a birkita ma Bestynki brain wlhy....) Firgigit ta dawo hankalinta jin ana tattare mata gown ɗin jikinta daga sama. Ta zabura baya tana kallonsa. “Uncle miya faru?”. “Ba fitsari kika ce zakiyi ba?”. Inda suke ta kalla. A bayi suke kuwa, har sun shigo bata farga ba tana duniyar tunani da firgicin sabon al'amari daga Uncle Ammar. Da ɗan rawar baki ta ce, “Uncle zanyi da kaina Please”. Baiyi magana ba, sai dai ya ɗan matsa. Tsoro ya sake mamaye zuciyar Ruky ta ce, “Uncle ka fita to”. “Kiyi a haka mu tafi.” “Iyeee!” “Ehhh” Ya bata amsa da irin salon da tai magana. A mamakinsa hannu ta ɗora bisa kai da faɗin, “Shi ke nan Uncle Ammar ya kama hanyar lalacewa Dadah. A gabanka fa kace nayi fitsari”. Dariya ce ta kama shi. Ya gimtse da ƙyar. “Ni ne kuma na kama hanyar lalacewa Ruƙayya?”. “To Uncle karkaga laifina. Idan ba lalacewa ba kamar ni nayi fitsari a gabanka dai. Bafa Afrah bace ba Ruƙayya ce”. Kansa ya girgiza yana murmurshi a karo na farko. Sai kuma ya gyara tsaiwa yana jingina da bangon bayin ya harɗe hannayensa a ƙirji. “Kodai kiyi mu tafi, ko kuma na fara nuna miki tuni ma na lalace ba yanzu ne zan fara ba. Zan rufe ido na ƙirga goma. Zaɓi ya rage naki.” Da alama kam Ruky ta gama shiga hannun ƴan sari. Ta kuma fahimci da gaske wannan ɗin wata sabuwar rayuwa ce ta same su. Nimrah tazo mata a zuciya. Shin itama cikin irin wannan halin take a hannun Dadah kenan? Kai shi kam bazai yi haka ba, ƙilama ya barta ta koma sashen Mammah. Hawaye suka cika mata ido. Ta ingije tunanin nata gefe ta kai duƙe jin Ammar ya kai 4 a ƙirgar tasa. Tana kammalawa ta miƙe ya kai ƙarshe. Da sauri ta saki rigar har gyalen da take ta faman rufe jiki na sulalewa ƙasa bata sani ba. Ammar ya buɗe idanunsa a kanta, kai tsaye kuma ya sauke su a ƙirjinta daya fita sosai sakamakon ɗinkin rigar daya kasance fitted gwon ne. Dan ta lafe a siririn jikinta tamkar an mata fenti da ita. Komai ya fita da fitarsa. Ammar ya haɗiye busashen yawun daya nema yanka masa maƙoshi da ƙyar. Sai kuma ya kauda idanun nasa ya kama hannunta kawai suka fito. Bai koma da ita falon ba ya zaunar da ita a bedroom ɗin, shi kaɗai ya fita. Babu jimawa ya dawo tray da abinci ke ciki. Suma su Lailah ne suka kawo musu kamar yanda suka kai sashen Bilal dana Dadah..........✍️

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull