
Post
Kida a ruwa Book 3 page 52
..... let's go inside the wall together and rest with the little watchers Kiddo". He ended the conversation by grabbing her hands that were still covering her face with them and he would withdraw. Then she came to his body again and laughed and said, "Naga Idi Dadaaah na". "Together we will see him my Little Shadow". The smell of the phone was very strong in her body. The ringing of her phone interrupted her, but she refused to look at him because of her pride Every time he is in such a situation, he finds himself in a big fight and he can suppress himself. He knows that a woman is a great woman for her husband, no matter how small she is, but she feels pity for him, especially if he looks at her like a witch.
52
.........Nimrah najin su Nabeeha sun gama fita a ɗakin tai ƙoƙarin miƙewa. Dan tunda Dadah ya rungumeta babu abinda zuciyarta keyi sai duka da sauri-sauri. Ga kunya da kwarjininsa sun mamayeta. Sarai shima yana jin yanda zuciyar tata ke harbawar, dan haka ya ɗan sassauta mata riƙon ta samu damar fita a jikin nashi. Sai dai idanun nasa na'akanta. Hannu ta saka ta rufe fuska murmushin da batai niyya ba na suɓuce mata. “ALLAH Dada idan kana min irin kallon nan sai na dinga jin kunya, da wani abu mai nauyi, kamar bango ya buɗe na shige ciki na ɓuya nake ji”. Tsabar yanda ta bashi dariya baima san ya saki murmushin da har ya bayyana haƙorasa ba, sannan sautinsa ya bayyana zuwa cikin kunneta. Hannu ya kai saman kanta ya shafa, sai kuma ya matso da fuskarsa gab da tata a saitin kunnenta har tana jin sautin numfashinsa dake fita a hankali a dokin wuyanta. Yanda take matse jiki ya sashi fahimtar tasirin kusancin nasu a tare da ita, dan haka ya sake matse mata waje da faɗin, “Shike nan, kawai mu shige cikin bangon tare mu huta da ƴan sa ido Kiddo”. Ya ƙare maganar da kammo hannayen nata da har yanzu take rufe da fuskarta da su zai janye. Sai ta taho gaba ɗaya ta sake faɗawa jikinsa tana dariya da faɗin, “Naga Idi Dadaaah na”. “A tare zamu ganshi Little Shadow na”. Sake ƙanƙameshi tai duniyarta na sake juyawa da birkicewar mamaki mai haɗe da wani shauƙi na musamman, tsoro da al'amarin Dadan a yau. Yayinda ƙamshinsa ke matuƙar tasirantuwa a cikin hancinta da jijiyoyin dake riƙe da wayarin ɗin jinin jikinta a kowace gaɓa. Ringing ɗin wayarta ne ya katse yanayin nasu, da wannan ta samu damar raba jikinsu dake manne da juna. Sai dai taƙi yarda ta kallesa saboda kunya da girmansa da take ji har ƙololuwar kanta. Ga wayar tata ya ɗauka kafin ita ta ɗauka. Sai dai bai ɗaga kiran ba har ya yanke. Idanunsa ya maida a kanta, ta sake sunkuyar da kan tana cuɗa yatsun hannunta waje guda. Duk sanda take a irin wannan yanayin yakan tsinta kansa cikin al'amari mai girma da sai yayi babban yaƙi yake iya danne kansa. Yasan baiwar mace mai girma ce ga mijin aurenta komai ƙanƙantar ta, amma ita tausayi take bashi, musamman idan ya kalleta figit a gabansa ba jikin kirki kamar kazar mayu, kodan an haifeta a gabansa ne ta girma a gabansa shiyyasa ya kasa yarda har yanzu ta wuce ƴar shekara bakwai ɗin nan.. “Zan iya gayyatar Little Shadow ta min rakkiya?”. Ya katse yanayin nasu da wannan furucin. Da yake fitar take so batare data kawo komai a ranta ba ta miƙe fuskarta na washewa da murmushi. Cike kuma da zumuɗi ta bashi amsa da, “Eh Dadah muje”. Komai bai ce ba ya miƙe shima. Kafin yay wani yunƙuri har taje ƙofa. Ya girgiza kansa kawai a ransa yana ayyana kalmar (ƙuruciya mai daɗi). Oho batama san yana yi ba, dan tuni harta fice, a bakin ƙofar ya sameta tsaye. Nan ma baiyi magana ba sai hannunta daya kamo cikin nashi. A tare suke tafiyar tamkar an jeranta takun nasu akan sawayen su.
Da sauri Rayhana ta saka tafin hannunta ta danne bakinta saboda kuka dake ƙoƙarin kubce mata. Wani irin kishi mai zafi na tafarfasa mata ƙirji. Ita kaɗai tasan mi take ji akan Dada. Dan haka a karo na farko take jin yaƙinta ba'a kan Nabeeha bane kawai harda Nimrah...
..★Sosai Nimrah ta saki baki da hanci da ido tana kallon ƙayataccen falon da Dadan ya shigo da ita. Ba shakka falon ya matuƙar ƙawatuwa da ababen more rayuwa da ƙyale-ƙyale mara hayaniya. Hannunta dake riƙe a nasa ta janye tana faɗin, “Wooow!! Amma falon nan ya haɗu”. Sai kuma ta juyo tana kallon Dada dake ƙoƙarin ɗaga kiran daya shigo masa a waya da ya ciro a aljihu. “Dada falonka ne?”. Yanda tai maganar kai tsaye tana tsatstsare shi da idanu ya sashi kallonta shima cikin ido. Dai-dai yana saka wayar a kunne kuma. Sake buɗe baki tai zatai magana ya ɗora yatsarsa saman lips ɗinta alamar tai shiru. A lokacin Nabeeha ke shigowa falon kamar wadda aka jeho. Su duka kallonta sukai, sai dai shi daga kallo ɗayan ya janye nasa idanun tare da janye yatsarsa daga kan bakin Nimrah. Saman kujera ya kai zaune. Da wannan damar Nabeeha dake ƙarasowa wajen ta bangaji Nimrah da gangan. Kasancewar abin yazo ma Nimrah a bazata sai ta tafi gaba ɗaya zata faɗi... Ta gama sallamawa sai ta kai ƙasa, dan haka ta runtse idanu tana mai ambaton sunan ALLAH. Jinta a jikin mutum ya sata buɗe ido da sauri. A cikin idanunsa dake kallonta suka shige, yayinda lips ɗinsa da suka ɗan bushe ke motsawa a hankali cikin ambaton sallama daga abokin wayarsa daya kasance Yusuf. Gashi dai Yusuf ya katse kiran daga can saboda sun gama. Amma Dada ya kasa janye wayar a kunnensa sannan ya gagara janye idanunsa dake cikin na Nimrah da itama take kallonsa tamkar wadda aka tsaida. Yana zaune sa ne a inda ya zauna da suka shigo, kasancewar Nimrah na tsaye ne ata kusa da kujerar sanda Nabeeha ta bangajetan sai tayo inda yake, shi kuma sai kawai ya samu damar tarotan ta faɗo jikinsa, rabinta kuma na'a kujerar ne. Iska ya shiga hura mata cikin idanun a hankali. Ai ko taja wata nannauyar ajiyar zuciya data saka tsigar jikinsa tashi, jikinsa yay sanyi ƙalau ta yanda har Nimrah ta miƙe bai farga ba. Sai da Nabeeha ta furta, “Iskancin banza da wofi” sannan. Karo na farko Nimrah ta dubi Nabeeha, sai dai kafin ta furta abinda tai niyya Dada ya katseta ta hanyar kiran sunanta. Hararar Nabeeha tai sannan ta juya tana amsawa. iPad ɗinsa ya miƙa mata. “Kaimin shi wancan ɗakin, ki jirani a ciki”. Amsa tai tabar wajen duk da ta fahimci abinda yake sonyi, ta harari Nabeeha ta yanda bazai gani ba ta wuce....
Sai da Dada ya tabbatar Nimrah ta shige sannan ya maida dubansa ga Nabeeha dake cika tana batsewa. Yanda ya tsareta da idanunsa masu bulala ga mara ji ya saka zuciyarta tsargawa. Duk yanda tai ƙoƙarin dakewa bisa huɗubar su First Lady dama ƙawayenta akan ta daina nuna tsoronsa sai taji bazata iya ba. Fuskarta ta maida gefe kawai. Shima kuma sai ya miƙe cike da ƙasaita ya tako zuwa gabanta. Tsayuwa yay irin ta jarumin soja, ya zuba hannayensa duka a aljihu still dai yana cigaba da kallon nata. Ita kam fuskarta na gefe gudun zuciyarta na ƙara ƙarfi. Sun kai mintuna biyu a hakan, har sai da ya fahimci yanda take neman fara tsuma sannan ya fara magana cikin golden voice ɗinsa da take matuƙar so da bege. “Nabeeha har yanzu kina da sauran kima na matsayin mata mai hakki a gareni. Zan baki shawara ta farko kuma ta ƙarshe. Karki kuskura, ki biye ruɗin zuciya da na zuga da rashin mafaɗi ki ƙetara zuwa layin dake kin san ba tsarina bane. Ita ɗin yarinya ce ƙarama, zata koya ne daga kowanne irin darasi da zaki ɗorata a kai. A baya na faɗa miki banda kawaici a kanta saboda ita ɗin amanata ce. Bar ganinta haka da ƙaracin shekaru tana da kaifin basirar fahimtar komai yanda aka zo mata da shi, sannan bata barin saita kwana. Ina son ta kalleki a matsayin Aunty matar Dadan su, ba kishiya ba abokiyar raba shimfiɗa a ɗakin miji. Abu ɗaya ne tak kuma zai baki wannan darajar da kimar a wajenta. Shine ki kame kanki. Ki zama mai riƙewa ni zan kama miki. Idan kuma kikaƙi hakan kika cigaba da biyewa masu koya miki waɗan nan abubuwan shirmen da rashin hankalin zaki rasa abu biyu ne a lokaci guda. Idan kunne yaji....” Bai ƙarasa faɗa ba ya nuna mata hanya tare da kaucewa daga gabanta. Sai yanzu ta ɗago tana kallonsa idannunta share-share da hawaye. “Haysam ni zaka wulaƙanta saboda ka auro ƴarinya ƙarama da a haife ka haifeta?”. “Ita ɗin halattacciya ce a gareni koda har yanzu tana a shekaru bakwai ɗin da aka ɗaura aurena da ita. Kasancewarta tare da ni a yanzu shine amsar da zata sake gamsar dake ita ɗin MATAR AURE NA CE, BA ƊIYAR DANA HAIFA BA kamar yanda kika ce. Daga cikarta kwanaki bakwai a shinfiɗata ki shirya zaman sabuwar rayuwar aure dan akwai yiwuwar daga wannan ranar alƙawarin dana ɗaukama kaina akan hukuntaki ya cika. Zaki iya tafiya”. “What? Kana nufin saboda yarinyar nan ka wofantar da ni daman?...” “Shiiii!!”. Ya faɗa yana ɗora yatsarsa saman lips tare da ɗan sake rankwafowa gaf da fuskarta sosai. Idanunsa a cikin nata cikin rada ya cigaba da faɗin, “Karki lalata min yarinya da hayaniyar nan taki. Sannan kina cinye min lokacina, bayan kin san ni ɗin a wannan daren ANGO nake”. Ya sake nuna mata hanya, fuskarsa na sake haɗewa fiye da yanda take. Tasan halinsa, dan haka ta saki kukan da take riƙewa tana nufar ƙofar fitar da ɗan gudu. Da kallo ya bita yana wani murmushi mai sanyi. Yanda ta buga ƙofar ya taɓe baki da ɗage kafaɗu alamar ko'a jikinsa. Daga ƙarshe ma yabar falon zuwa bedroom ɗinsa daya aika Nimrah...........✍️