Kenza eBookz
Kida a ruwa Book 3 page 53

Post

Kida a ruwa Book 3 page 53

.....I'm afraid". "Afraid again? What about me?". She seemed like she didn't want to say anything. Then she went there and said, "Hajarah Ilyas once told us about her friend who went to her wedding. After they were taken to her house, they were alone with one of her husbands. She told him to take one chicken for her and said that they must pray from here. Um... Um..." She couldn't finish. Harga GOD forbid Ammar burst out laughing. But he just frowned a little more. He said, "What about me? Oh right, when you go to school, do you have friends?". "Wlhy no, we don't. She also told this story to Mufeeda who were sitting in the same chair, and we were in front of them. Ninah and I were in front of them. Rasama said that he was like that. He was just looking at her and she was shedding tears. He then folded and put her back to where she was. He took off her hijab himself, and suddenly he started to take off her clothes.

Standalone post1,603 words

53

........A ɓangaren Ammar ɗura ta gaske yayma Ruky da nama. Sai da ta saka masa kuka zatai amai sannan ya barta. Gaba ya sakata sukai brush tare da yo alwala. Gaba ɗaya sai taji jikinta yayi sanyi, zuciyarta ta raunana musamman data tuna wani labari da wata ƙwarsu ta Tahfiz mai suna Hajarah ta basu, itama wai wata ƙawarsu ce datai aure a ƙauye ta basu. Zuciyarta ta ƙara tsargawa, har bata san ta fara roƙon ALLAH a sallar ba kada Uncle Ammar ɗin yayi mata irin na ƙawar Hajarah ɗin, idannunta suka cika da ƙwalla. Suna idar da sallar shashshekar kukanta tazo masa har cikin kunne. Da sauri ya waigo yana kallonta cike da mamaki da tashin hankali. “Ruƙayya baki da lafiya ne?”. Kanta ta girgiza tana ƙara fashewa da kuka. Yay ƙoƙarin riƙota ta noƙe. Sai ya sake jin hankalinsa ya tashi. Cikin lallashi ya furta, “Shike nan bari kawai nima nayi kukan to”. “Ni dai a'a”. “To ya kike so Ruƙayya. Yau fa rana ce mai muhimmanci da daraja a garemu. Kodai baƙya sona har yanzu?”. “Ni ina sonka mana, kawai ina jin tsoro ne”. “Tsoro kuma? Nami to?”. Ɗan jim tai kamar bazata ce komai ba. Sai kuma zuwa can ta ce, “Hajarah Ilyas ta taɓa bamu labarin ƙawarta da sukaje bikinta, bayan an kaita gidanta an basu su kaɗai mijinta daya sakata taci kazar daya kai mata dole yace suyi salla daga nan kawai yay mata.... Um... Um...” Ta kasa ƙarsawa. Harga ALLAH kaɗan ya hana Ammar fashewa da dariya. Amma dai ya dake tare da ɗan ƙara tsuke fuska. A dake ya ce, “Yay mata mi? Oh dama idan kukaje makaranta zancen banza kuke da ƙawaye?”. “Wlhy a'a bama yi. Shima wannan labari take bama su Mufeeda da suke kujera ɗaya, mu kuma muna gabansu shine mukaji ni da Ninah”. Rasama abin cewa yayi shi kam. Sai kallonta kawai yake tana sharar hawaye bil haƙƙi. A ransa ya ce dama ance masu baki ragwayene. Bai ƙara tabbatar da ƙuruciya ce zagaye da yaran nan ba sai yau. Dada nacan na fama da ƴar uwar ɗayar. Tunaninsa ya kawar. Batare da yayi magana ba ya miƙe a wajen yana kwashe abin sallar da yake kai. Sai da ya ninke ya ajiye ya dawo inda take ya ɗagata itama. Da kansa ya cire mata hijjab ɗin, yaja hannunta zuwa bakin gado, a bazata kawai taga ya fara ƙoƙarin cire mata rigar jikinta. Rawar jiki ta fara masa, ya harareta da mata alamar ta nutsu. Tunda take bata taɓa jin tsoronsa irin yau ba a rayuwarta, tana ji tana gani ya canja mata kayanta zuwa wasu kayan barci masu ƙyau dake a saman gadon. Ya sata ta zauna shima ya fara ƙoƙarin canja nashi. Hannu tasa ta rufe fuskarta, sai da har ya kammala ya hawo gadon tare da kamota jikinsa cikin muryar raɗa da tsokana yana faɗin, “Matsoraciyar amarya zomu kwanta to”. A firgice ta buɗe baki zatai nagana. Ya ɗora yatsarsa saman lips ɗinta yana mata wani kalar kallo. Da yanayin maganar raɗa yana lumshe idanun da buɗewa a kanta ya furta, “Barci zamuyi kawai Babie. Manta da batun angon ƙauye naki mai haƙurewa ne har sanda zaki sallama masa”. Ba komai ta fahimta ba a maganar tasa, amma sai ta samu kanta da sauke ajiyar zuciya tana lafewa a jikinsa daya rungumeta. Daga haka yaja duvet ya rufesu....

✨★✨★✨★✨

(Ki zama mai dasa ƙauna da yarda a zuciyar mijinki ba mai yaƙin karɓar ƴanci koda da takobin harshe ba. Bar ganin Muhammad da zafi a zahirinsa. Ni nake gaya miki mai sauƙi ne da taushi a ainahinsa. Indai kika bi dukkan shawara da dabarun dana baki na zama da shi, lallai zaki zama mai cin riba da karɓar zuciyarsa a tafin hannunki Nimrah. Ni uwa ce a gareku ke da shi, zan zama mai fata a gareku na cin ribar wannan zaman naku. Tabbas ke amanarsa ce, ya jaddada haka a gareni har babu adadi, ya kuma bani tabbacin riƙe wannan amanar da muhimmanci mabayyani. Dan haka Nimrah, nima a yau zan baki amanar Muhammad, dan ALLAH ki zama bangon jingina a gareshi a duk lokacin da ƙarfin iskar rikicin duniya ke neman saka ƙafafunsa rawa. Ki zama ruwa mai Kore masa ƙishi a duk lokacin da wasu suka turashi rana. Ki zama murmurshi mai riƙe zuciyarsa a duk lokacin da aka shirya ganin kukansa. Ki zama irin matar da ko miji baya so saita shiga aljanna saboda biyayya da kiyaye dokokin ALLAH akan bautarsa. Nasan har yanzu ke yarinya ce ɗanya, ba komai zaki fahimta daga zantukana ba. Amma ina fatan zaki rubutasu a zuciyarki ki ajiye su zama abin bita da tunawa a cikin rayuwar aurenki. Idan lokacin da zaki fahimcesu yayi ko bana raye zaki fahimta. Karki damu da yawan shekarun Muhammad ko ƙarancin shekarunki ke, da wannan ƙaracin shekarun naki ma da ƙuruciyar da yake kallonki ciki zaki iya samunsa fiye da zatonki. Ina son koda kin fahimci abu ko kin sanshi ki cigaba da zama a yarinyarki a wajensa, a kuma wadda bata san komai ba. Wannan makamin naki Nimrah sai yafi kowane makami tasirin mallake Muhammad a wajenki cikin sauƙi. Dan sai kin koma dinga mamakin shi ɗin ne? Ko ba shi bane?. Ina addu'ar ALLAH ya ƙara tasirantar da soyayyarki a zuciyar Muhammad ki kasance Mata abokiyar rayuwa da farin cikinsa ta har abada.......) Tunanin Nimrah ya yanke sakamakon turo ƙofar da shigowar Dada ɗakin. Hannu tai ƙoƙarin kaiwa da sauri ta share hawayenta. Bata juyo ba harya iso inda take gaban mirror ɗin ɗakin. Ya tsaya a bayanta yana kallonta ta cikin mirror ɗin, sai dai baya ganin fuskarta saboda duƙar da kanta da tayi. “Naja'atu Nimrah”. Ya kirayi sunanta da wani irin sauti mai zurfi. Har cikin ƙashi taji tasirin fitar muryar tasa kuwa. Dan haka ta ɗago fukarta a hankali ta kalla mirror ɗin suka haɗa idanu. Cikin sauri ta maida nata ta rissinar, sai kuma ta amsa da, “Na'am Dadah!”. Ɗan ƙara matsowa yayi jikinta gab, ya cire hannayensa duk biyu dake cikin aljihun wandonsa ya ɗora saman kafaɗunta. Juyo da ita yay gaba ɗayanta tana fuskantar sa, hakan ya bata damar jingina jikinta da jikin Mirror ɗin. Sai dai yanzu ma taƙi yarda ta kallesa. “Kuka kike yi?”. Tambayar tazo mata a bazata. Dan batayi tunanin zai saurin gane hakan ba. Nimrah yarinya mai wayo, sai tai saurin girgiza kanta da sakin murmushi ta ɗago ido tana kallonsa, sai kuma ta ɗan tura baki gaba. “Dadah ni ba kuka nake ba. Kawai ina tunani ne”. “Tunanin mi Kiddo keyi alhalin tana a hannun Muhammad Haysam Abdul-rasheed Shehu ɗari bisa ɗari a yau”. Sosai kalamansa sukai mata daɗi. Murmushi tayi mai yalwa, sai kuma ta saka duka hannayenta ta rufe fuskarta. “Dadah ai bakai murna da kasancewata a hannunka ɗin ba”. Sosai ya ɗan waro idanu na mamakinta. A ransa ko yana ayyana (Yarinyar nan fa wayonta zai shanye hasashena a kanta) a zahiri kam hannun data rufe fuska yay ƙoƙarin janyewa da faɗin, “Kiddo waya sanar dake haka?”. “Dadah babu wanda ya sanar dani, kawai nice na gani. Kaga a film idan aka kawo mutum wa mutum sai kaga abokai sun rakoshi, zasu zo da kayan daɗi, sannan zasuyi addu'a. Daga nan sai.....” Tai shiru ta kasa ƙarasawa. Sai ma tai saurin juya masa baya ta koma yanda ya shigo ya sameta a farko. Murmushi mai haɗe da ƴar dariya ta suɓuce masa. Ya duƙo sosai tare da dafe gefe da gefen jikin mirror ɗin. Hakan yasa shi mata rumfa jikinsa a nata sosai sai dai bai sakar mata nauyi ba. A cikin kunne ya raɗa mata. “Hakan na nuna min lallai Kiddo ta fara girma. Yanzu dai na fahimci nayi laifi. Idan aka kawoma ango amarya ya kamata ya mata tarba ta musamman ni kuma ban yi ba.” “Lah Dada ni dai bance ba?”. Ta faɗa tana dariya da ƙoƙarin fita a jikinsa. Shima dai murmurshinsa ne ya ƙara faɗaɗa har haƙoransa na bayyana. Tsaye ya tashi sosai yana riƙota da hannu ɗaya. Itako sai kaucewa take tana neman ɓoye fuskarta. Da wannan damar ya sakata jikinsa ya rungume. Aiko tai luff abinta tana shaƙar nutsatstsen ƙamshin turarensa. Shi kuwa yana shafa kanta zuwa bayanta. Idanunsa a lumshe... “In sha ALLAHU zan gyara wannan kuskuren nawa Kiddo. Zan zo da kaza gobe idan ALLAH ya kaimu. Ke ma sai ki shirya da shiri irin na amarya. Kinga sai Imran ya min rakkiy.....” Da sauri ta ɗago cikin zare ido tace, “Dadah! Daddy fa kenan?”. Cikin irin yanayin datai maganar shima ya bata amsa idanunsa dake a shanye cikin nata ya ce, “Eh mana. Ba shine abokina ba. Kinga kawai sai kiyi fiska abinki tunda matsayin abokin Ango zai zo ba Daddy ba”. “Tab! Dada bazan iya ba ai da kunya”. “Ba wata kunya Kiddo, to nima ba Dadah bane? amma gashi na zama Ango”. Dariya ta ƙyalƙyale da shi. Ta ce, “Kai Dadah wai ango. Ni dai ba ruwana gaskiya”. Hancinta yaja kaɗan. “Nima nasan babu ruwan Little Shadow ai”. Kanta ta sake kifewa a jikinsa tana murmurshi. Sai kuma ta ɗago tana faɗin, “Dada zanje na kwanta ina jin barci”. Ya riga ya gama shiryama kansa yanda zai tafi da ita dai-dai da tunaninta. Dan haka ya ce, “Okay! Na raka ki?”. “Lah Dadah ai bana jin tsoro fa”. “Nima nasan Little ɗin Dadah ba matsoraciya bace. Amma muje na raka ki dai”. Bata wani damu ba suka fito. Hannunsa riƙe da nata suka sakko. Yayi zaton zatace sashen Mammah zataje. Sai yaga saɓanin hakan. Ya kuwa ji daɗi har cikin zuciyarsa........✍️

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull