Kenza eBookz
Kida a ruwa Book 3 page 54

Post

Kida a ruwa Book 3 page 54

.....that's why he is wlhy. What I understand is that Nimrah still looks like a little girl. I am afraid that he will lie and take the date to go to the sheikya there". I am wlhy Aunty would you agree to let us go and find Mammah now she just stopped him". This is not the solution, since Mammah did not prevent him, it is possible that the trip is important. Aunty Ummi smiled for the first time as she looked at Aunty Mommy who was speaking. "God has prepared you, Mommy, is there any reason why you are sleeping?". "Humm Aunty, why are you talking about God, I have hair, three marriages are a joke". He started praying and took her to sleep again when he came back from the mosque. He also looked at her. Then he gently put her on the bed and put the duvet on her. He was also asleep.

Standalone post1,521 words

54

........“Amma gaskiya ban san randa zakiyi hankali ba Mimi. Jibafa yanda kike shigo mana ɗaki kamar wata su Ruƙayya, lafiya kuwa?”. “Humm Aunty Mommy ina fa lafiya. Lissafin mu naji yana neman rikicewa. Dada ne fa naji yanama Mammah sallama wai tafiya zai yi gobe ashe.” “Tafiya?”. “Wlhy kuwa? Da safe ma.” “Ita kuma Nimrah ɗin fa?”. “To waya sani Aunty Mommy. Kunga dai da alama duk abinda mukai ya tafi a banza kenan. Ina Aunty Ummi?”. “Gani nan ina alwalar barci, mi naji wai kuna magana?”. “Wai Dadah take magana zai yi tafiya gobe fa Aunty”. “Kamar ya tafiya? Wanda aka kaima Amarya yau ne kuma zai yi tafiya, to ko tare zasu tafi ne?”. “Wlhy Aunty babu wani tare. Ni dai a yanayin da naji suna maganar da Mammah shi kaɗai ne. Ni wlhy ji nake kamar nayi kuka, wannan shegiyar matar tasa ma ai sai ta mana dariya taci nasara. ALLAH idan Dada yay mana haka ya kwafsa mana...” “Hummm muguwar kwafsawa ma kuwa Mimi. Yanzu Aunty Ummi miye abin yi? Kinyi shiru?”. “To Mommy mizan ce. Lamarin Dadah ne sai shi wlhy. Ni abinda na fahimta har yanzu kallon ƴar ƙaramar yarinya yake ma Nimrah. Ni tsorona ma karya ɗauki kwanan yau ɗin ya kaima shegiyar can”. “Da Dada ya gama damu ashe. Ni wlhy Aunty da zaku yarda muje mu samu Mammah yanzu ta hana shi kawai”. “Mimi kenan, kamar kin manta akan wa ake magana. Wannan ba shine mafita ba, tunda Mammah ɗin bata hanashi ba zata iya yiwuwa tafiyar nada muhimmanci ne. Ni wlhy dana san abinda zanji kenan yau bazan kwana gidan nan ba”. Murmushi Aunty Ummi tayi a karo na farko tana kallon Aunty Mommy mai maganar. “ALLAH ya shirya ki Mommy, to ashe dan wani dalili kika kwana?”. “Humm Aunty wlhy magana ta ALLAH dan nayi gashi ne, amare uku wasa ne”. Dariya sosai Mimi ta sanya Aunty Ummi na tayata. Dan harga ALLAH yanda Mommy ɗin tayi dole abin ya baka dariya.......

>>>>>>%<<<<<<

A inda ya barta tai salla anan barci ya sake ɗauketa har bata san lokacin daya dawo daga massalaci daya fita ba. Guntun murmushi yayi kawai shima yana binta da kallo. Sai kuma ya duƙo tare da ɗagata gaba ɗayanta a hankali ya nufi gadon da ita. Koda ya kwantar da ita ya gyara mata duvet shima kwanciyar yayi a gifenta bayan ya zame jallabiyar jikinsa. Shima dai barcin ne a idonsa sosai. Dama ga gajiyar aiki na kwana biyu da suke ciki, ga kuma wadda ya ƙirƙirar musu a daren jiya shi da ita.... Sosai suke barci har basu san rana ta ɗaga ba, sai da kiran da akai masa a waya ya dameshi. Da ƙyar ya kai hannu ya ɗauka daga bed side drawer ya duba mai kiran. Ganin yayarshi ce ya sashi ɗagawa da ƙyar yana mata sallama. “Ya rabbi, ai ban san barci kuke ba na tashe ku Haydar”. “Ba komai Didi mun tashi ai”. “Ni ɗin ce dai na tada ku. Dama abinci ne na aiko muku da shi tun ɗazun su Sumayya nata knocking sunce sunji shiru”. “Wlhy ban jisu ba sam, bara na duba. Sannu da ƙoƙari mun saki aiki da safe”. “Ba wani aiki a ciki. Habibah ta cancanci fiye da haka a garemu. Ka gaidata idan ta tashi sai zuwa yamma zamu shigo su Gwaggo suyi muku sallama, dan tafiyar safe zasuyi gobe in sha ALLAHU”. Dai-dai yana ficewa daga bedroom ɗin ya ce, “ALLAH ya kaimu sai kunzo.” daga haka suka sallama ya yanke kiran. Koda ya buɗe ƙofar falon Sumayya yarinyarta ta uku ce tsaye. Budurwa ce dan yanzu haka tana lavel 2 a University. Cike da girmamawa ta risina tana gaishe shi. Ya amsa yana bata hanya alamar ta shigo. Koda ta shigan ma sake gaishe shin dai tayi, kafin ta gabatar masa da abincin. Ba kuma ta zauna ba tai masa sallama dan Mamanta ta mata gargaɗi akan su dawo da wuri....

Tunda ya shigo bedroom ɗin Biebah dake tafiya a hankali zata bayi ta tsaya cak. Sai dai bata kalla inda yake ba har ya ƙaraso gabanta. Rungumota kawai yayi jikinsa yana sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Miyasa baki jira nazo na kaiki ba?”. Kanta ta sake duƙarwa sosai. Da ƴar shagwaɓa ta ce, “Ai zan iya yanzu”. “Ban yarda ba. Bayan gashi kina tafiya a hankali kodai nayi ɓarna?”. Matuƙar kunya taji ta sake mamayeta. Ta kasa cewa komai. Murmushi yayi mai yalwa. Batare da shima ya sake yin magana ba ya ɗauketa cak zuwa bayin.. Da ƙyar ta yadda ya ƙara taimaka mata ta gasa jikinta dake mata mayuƙar ciwo, dan har ga ALLAH bai zo gareta da wasa ba. Duk da a farko ya fara da taka tsantsan da tausayawa sai kuma komai ya ƙwace masa. Yanzu kam ta dage akan zata iya sanda zasu fito. Sai ya ƙyaleta amma ya kamo mata hannu. A gaban mirror ya zaunar da ita tare da sumbatar gefen fukarta ya juya bayin dan yin nashi wankan. Sai lokacin ta ɗan ji hawaye sun ɗan ciko mata ido na tausayin kanta. Idan har ita dake kusan 26years zatai irin wannan jigatar a hannun Yaya Haydar su Nimrah fa ƴan 17. Musamman ma Nimrah a hannun Dada da yafi Haydar ɗinta komai na jikin jarumai. Duk da shima ba daga baya ba, amma Dada ya fishi tsayi da cika ido gaskiya. Gara-gara Ruky Ammar da ƙuruciya, duk da shima ɗin dai a tsaye yake dan mazan gidansu kam sai Masha ALLAH a wajen ƙira da cikar mazantaka ta zahiri. Koda yake sai ma fa Dadan ya tausaya ma Nimrah ita Rukyn ta wajigu a hannun Ammar ɗin..... “Tunanin mi kike?”. A ka faɗa cikin kunnenta. Firgigit ta dawo hayyacinta tare da kallonsa. Sai kuma tai saurin kauda kanta ganin daga shi sai towel. Cikin ɗan rawar lips ta ce, “Ba komai”....

★<>★<>★<>★<>★

A ɓangaren Asma'u kam a iya abinda Bilal kawai yay mata taji a jikinta, dan har sai da ta sanya masa kuka da magiya sannan ya barta. Sosai tai barci a tsorace duk da tasan dai abinda take tsoron bazai faru ba saboda halin da take ciki. A kunnenta ya fita sallar asuba bayan yayo wanka daga bayi. Ta matse sosai bata nuna ta farka ba har sai da ya tafi. Sauri-sauri ta tashi ta gyara gadon. Bata jira ba ta fice duk da bata da tabbacin akwai wani bedroom ɗin bayan wannan. Sai dai tana fatan yiyuwar hakan dan tasan baza'a barsu da bedroom ɗaya ba...

Koda Bilal ya dawo yaga bata ɗakin murmurshi kawai yayi. Baiyi yunƙurin binta ba ya haye gadon ya sake kwanciya, koba komai dai ai ya rage zafi. Sai gashi bai tashi farkawa ba sai kusan tara. Yayi mamakin barcin da yayi, duk da yasan dama hakan zai iya faruwa dan daren jiya bai samu na kirki ba. Wanka yay ya kimtsa jikinsa sannan ya fito. Tun daga corridor ɗin kuwa wani ƙamshi mai saka nutsuwa ya mamaye hancinsa. Koda ya ƙarasa fitowa a falon sai yaji nutsuwa na ƙara saukar masa. Fes an gyara ko'ina fiye da yanda yake a jiya. An saka ƙamshi da yake ji tun fitowar tasa. Motsin plate da yaji ya sashi kai dubansa ga hanyar kitchen yana kaiwa zaune cikin kujera. Dai-dai Asma'u na fitowa. Tayi ƙyau sosai cikin atamfa da taima jikinta ɗas. Plates ne a hannunta da kofuna. Kasancewar ba lura tai da shi ba cikin sanyinta ta nufi dinning da kwanikan. Gaba ɗaya a kasalance take ga kewar gida na damunta. Ta ɗan yi nisa a tunani har bata san mi take yi ba balle isowarsa wajen. Sai da ya riƙe plate ɗin sannan ta ɗago da sauri. Cikin ɗaga gira yay mata alamar miye. Kanta ta sunkuyar tare da girgizawa alamar ba komai. “Badai girki kikayi ba Asmah?”. “A'a daga sashen Mammah aka kawo”. Ajiyar zuciya ya sauke. Sai kuma ya rungumeta a haka yana gyara plates ɗin. Kafin ya zaunar da ita shima ya zauna yana faɗin, “Dama da yunwa na tashi kamar Mammah ta sani. Kinga zuba kafin na fara miki kuka ma”. “Kuka fa dai?”. Ta faɗa tana ɗan waro ido waje. Cikin kashe mata ido ya ce, “Irin wanda kikai min jiya ma kuwa. Kona fara ki gani?”. Daga haka ya rufe bakin nata dan ta kasa sake cewa komai. Shi ko ya dinga mata dariya da zolayarta da kukanta na daren jiyan da ba komai akai ba illa sharar fage. Hakan ya ƙara hanata sakewa cin abin kirki. Daga ƙarshe sai ya koma bata da kansa, shine ma ta ɗan samu taci. Suna kammalawa ya taimaka mata suka gyara wajen. Zata wanke kwanikan da suka ɓata ya tayata. Bayan sun kammala ne sun fito yace suje gaida Mammah da Dadah. Jitai kamar tace a'a saboda kunya. Dan gani take kamar kowa zai iya gane miya faru a daren jiya a goshinta. Babu dai yanda ta iya taje ta ɗakko mayafi, sai yace mata wasa yake Mammah tace kar taga kowa a sashenta yau ta yafe. Ajiyar zuciya ta sauke kuwa da har ya saka shi dariya sosai ya cigaba da tsokanarta..........✍️

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull