Kenza eBookz
Kida a ruwa Book 3 page 55

Post

Kida a ruwa Book 3 page 55

..... and Ismat is with her. Then all the guests passed. She had to stop and listen to the words of Nabeeha who was crying for a long time before she let out a malicious whisper. On this side, she confirmed again that it was indeed her weapon. The first time she walked into the room, she sat on the edge of the bed and coughed the breath of Nabeeha who was crying inside... "If you are nice, Aunty, I will not sit and cry. Even a little girl who is not more than 16+, you will ask your husband to come here and say that you are crying. What about you? Will this path be opened in Aunty Nabeeha? Where is your brave step? Where is your strength? Where is your love? Claim to him? Do you mean that all this crying will end? You are doing it while he is there and he will meet his needs for years. Nabeeha interrupted her in a loud voice. Rayhana's hand raised the sign of surrender. "No. No, Aunty, I didn't tell you about the rabbit. I'm not going to lie down with your husband, let alone calm down on me. I'm telling you the truth, this crying is not your solution. If you say you will do it, you should prepare more tissues. I know you will cry a lot and I'll leave." "What do you want me to do wit

Standalone post1,622 words

55

........Tsayin mintina goma Rayhana ta ɗauka tana kallon Nabeeha dake kuka kamar ranta zai fita. Ta ɗan taɓe baki, dan ji take ta fita jin zafin fiye da abinda take ji. Ki shinsu take ji sosai daga ita har waccan ficikar yarinyar. Ta kuma yima kanta alƙawarin ɓata wannan daren gareta, sai dai ta ina?. Neman wannan amsar ne ke mata kaiwa da komawa tun ɗazun da taga Dada da Nimrah na nufar sashensa. Ganin Nabeehan ta bisu sai take fatan komai ya hargitse, sai dai kash babu wani jimawa Nabeeha ɗin ta dakko tana kuka. Tsaki taja da faɗin. “Wawuya sokuwa kawai”. Daga haka ta cigaba da kai kawonta na neman sabuwar mafita. A kuma hakan Dada ya sake fitowa da Nimrah suka shiga sashenta. Hankalinta ƙara tashi yayi, dan itama bata san hawaye na tsiyaya mata ba. Amma ta goge su cike da zafin rai tana faɗin, “Ni ba irinta bace sokuwa mara alƙibla. Dole ne na nema mafita ta, kuma itace zata zama makami na”. Da wannan furucin tabi bayan Nabeeha ɗin shine ta iske tana kuka. Taji daɗin ganin babu su Ismat a tare da ita. Sannan duk baƙi sun wuce. Sai da ta tsaya ta gama jin maganganun Nabeeha dake kuka na tsayin mintuna kafin ta saki murmurshin ƙeta. Dan a wannan gaɓar ta sake tabbatar da lallai itace makaminta. A karo na farko ta shiga takawa cikin ɗakin, sai da takai zaune a bakin gadon sannan ta tari numfashin Nabeeha mai kuka da sambatu a ciki.... “Da nice ke Aunty ba kuka zan zauna yi ba. Har mi akai akayi wata ƴar yarinya da bata wuce 16+ ba da zaki barma mijinki kizo nan wai kina kuka. Kuka fa? Anya kuwa wannan hanyar zata ɓulle dake Aunty Nabeeha? Ina jarumtar taki ne? Ina kafiyar? Ina soyayyar da kike iƙirarin yi masan?. Kina nufin duk a iya wannan kukan zasu ƙare? Kina nan kina yinsa yana can rungume da wata zai biya buƙatarsa ta shekaru ke kuma ki ƙare da kuk....” “Rayhana!!”. Nabeeha ta katse ta cikin ƙaraji. Hannu Rayhana ɗin ta ɗaga alamar surrender. “A'a. A'a Aunty bani fa nakar zomon ba. Dan banice acan kwance da mijinki ba balle ki huce a kaina. Ni dai gaskiya nake gaya miki, wannan kukan ba shi bane mafitarki, idan kuma kikace shi zakiyi sai ki ƙara tanadar tissues dan nasan zaki ƙarar da yawa ni kinga tafiyata”. “Ya kike so nayi Rayhana? Ya zanyi da Haysam? Kina gani Momy ma abinda tace min kawai na gyara gidana da kaina. Ta yaya kuke son nayi hakan? Wane ƙarfi garan na dawo da Haysam rayuwata bayan kun san halinsa....” “Ke ko kike da ƙarfin dawo dashi. Haba sai kace ba mace ba Aunty Nabeeha. Kina son mijinki, kina kishinsa amma baki san yaya zaki tsaida shi inda kike buƙatar ganinsa ba. Dole fa sai kin zama jaruma. Kin cirema kanki tsoronsa ki fito masa a macen ki. Dole ki tsaya da ƙafafunki ba cigaba da jiran umarnin Momy ba. Sai kace wata ƙarmar yarinya ace baki da say ɗin kanki sai na wasu sai kace ba mace ba. Wlhy idan nice a matsyinki wannan daren sai dai ayi shi a tsaye ni da su. Amma bazan zauna kishi ya kashe ni ba shi yana can yana morewarsa da ƴar cikina. Ya rage naki kiyi abinda ya dace gashi can ya goyata ya nufi sashenta da ita tana zuba iskanci tunda tasan daɗin maza tun suna ƙananu su Ammar suna gama lalube su.....” Tabbas wannan wuta da Rayhana ta kunna ta kunnu a zuciyar Nabeeha da zafin kishi ya lulluɓe jinta da ganinta ta yanda bata iya banbance abinda ya dace da wanda zai mata illa ba. Dan tuni tayi shirin barin bedroom ɗin nata a haukace. Rayhana dake dariyar ƙeta a zuciya ta riƙota. “Kinga Aunty Nabeeha kwantar da hankalinki. Ni bance kije kiyi kamar haka ba. Ita rayuwa ai komai ɗan siyasa ne. Sannan kowanne mutum da halinsa ake iya zama da shi. Kema kin san shi ba mazan da ke tsoron rikici bane balle damuwa da haukar mace. To mizai sa ki ce zakiyi hakan? Kamata yay kizo da sabon salo......” “Wane sabon salo?”. “Yauwa ƴar gari. Bara kiji na tabbatar a yanzu bawai ya nufi sashen nata dan kwanciya bane. Dan kayan dake jikinsa sune dai a jikin nasa. Hakan na nufin zai yi wanka da sabon shirin barci ko?”. “Haka ne.” “Alhamdullahi to ga maganin matsalar ki”. Tai maganar da miƙa mata key. Key ɗin Nabeeha ta kalla da ƙyau. Sai kuma cikin rashin fahimta ta ce, “Taya Key zai zama maganin matsala Rayhana?”. “Aunty daɗina dake rashin haƙuri. Yanzu dai amsa na miki bayani”. Karɓa tayi yanzu kam. Rayhana tai murmushi. “Kiyi ƙoƙari yana shiga bedroom ɗinsa ki rufe sashen nada. Wlhy sai kin gode min. Dan ƙwaila sai dai tayi barci ita kaɗai. Idan kinga result ɗin ina nan ina jiran ki da next plan dan sai dai yay barci da fillo kuma”. Nannauyar ajiyar zuciya kuwa Nabeeha ta sauke. Dan ta gama yin imanin wannan dabarar ta Rayhana kankant ce wlhy. Bata tsaya ƙara bin ba'asi ba kuwa ta fita a ɗakin tana ƙara damƙe key ɗin a hannunta zuciyarta washar da farin ciki....

(Mata ba Nabeeha hakawai ba. Duk fa mace mai zafin kishi kan saka zuciyarta da brain ɗinta toshewa har sai ta aikata abinda bai dace ba ta dawo tana dana sani daga baya. Kuma hakan baya iya canja komai daga ƙaddararta sai zubar da mutuncinta. Kishi gaskiya ne, kuma kowacce mace na da shi in har tana son mijinta. Sai dai in baki iya sarrafa naki ba bisa hanyar data dace ki tabbatar kwaɓarki ce zataita ruwa ta yanda mai zai kasa soyata, sai dai ta naɗi man da zai halaka miki zuciya ya barki a kwance).....

%=========%

“Oga akwai matsala fa wlhy”. Tamkar Oga Jush bai ji abinda Viper ɗin ya faɗa ba hankali kwance ya juyo yana kallonsa. Maimakon amsa wa kuma sai baice komai ba ya ƙarasa shigewa cikin gidan. Da sassarfa Viper yabi bayansa. Dan tun ɗazun yake zaman jiransa a gidan hutun nasa. Sakamakon kiran da yay masa domin sanar da shi tashin hankalin da suke ciki amma yaƙi saurarensa yace ya samesa anan ɗin lokacin yana wani uzuri. Kusan tare suka kai zaune cikin kujera. Dan yau ko girmamawar barin oga ya fara zama Viper ɗin bai bi ba. Sigari abu ne mai muhimmancin gaske a rayuwar Oga Jush. Da wahala yana zaune baka ganta yana zuƙa ba. Yanzu hakan ma yana zama ita ya ɗauka. Da sauri Viper ya ɗauki leta dake saman table ɗin ya matsa ya kunna masa. Kansa ya jinjina masa alamar godiya. Sai da ya zuƙa har sau uku kafin ya kalla Viper ɗin. “Mi kake cewa?”. “Akwai babbar matsala Oga. Bincike ya tabbatar da yaranmu da aka nema aka rasa suna hannun shegen mutumin nan yaron Zak-Shadow Imran. Tun daga na farkon har na biyun. Sannan bomb ɗin yau sun kama yarinyar nan da shi kafin ta tayar. A yanzu haka tana hannunsu. Ga maganar biki har yanzu bakace komai ba a kai, kuma mun samu labari daga majiya mai ƙarfi yarinyar ta tare yau a ɓangarensa zata kwana ma”. Gaba ɗaya komai ya tsaya cak daga ɓangaren Oga Jush tamkar an masa tsawa tun fara maganar Viper. Sai ma kafeshi da yay da idanu tamkar mai son ganin fuskar Imran ɗin anan kota Nimrah da akace ta tare. Fin mintuna biyu sannan ya janye yana mai kwantar da bayansa jikin kujerar ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.. “Imran! Imran Abbas.” Yay maganar tamkar mai bitar sunan dan kar ya manta. Sai kuma ya zuƙi sigarin da yawan gaske ya busa hayaƙin yay sama har yana lulluɓe fuskarsa. Wata banzar dariya ya sanya daga ƙarshe, sai kuma ya ajiye sigarin batare da ya kashe ba. Dariyar ta ɓace daga fuskarsa, sai wani irin duhu na tsantsar rashin imani ne ya maye gurbinsa. A kausashe ya furta, “Hakan na nufin kayanmu na sauran jihohin da basu isa ba na hannunsa?”. “Tabbas haka ne Oga, shi ne kuma ya ɓata mana shirin mu na gabashi a wannan satin gaba ɗaya. Ga harin da suka kaima Dagger har ya samu harbi shiyyasa kwana biyu sauran ayyukan suka tsaya”. “Mtsoww! Dagger! Dagger. Lokaci yayi da kowane aiki zaku tsaya da sunan Dagger kawai. Ku tashi sabbin yara da suka fishi karfin jini....” “Oga Dagger na ƙoƙari, samun irinsa garemu abu ne mai wahala. Bashi da tsoro sam. Sannan yasan abinda yake yi. Yana da amana da juriya, sannan baya tsallake kowane umarnin mu”. “...to sai mi? Dan ya haɗa duk wannan sai mu zauna yaƙinmu ya cigaba da gudana a ƙarƙashin Commander guda ɗaya kenan? Yanzu da ace akwai wasu rindinonin bayan nashi idan mun rasa nan zamu samu can. Umarni nake baku, sannan lokaci yayi da zaku koyama wannan Imran ɗin hankali. Daga yau zuwa gobe ina son jin sautin kuka da kururuwar mutuwar sojoji tako wace kafar media. Sannan yaranmu dake hannunsa kwana uku kacal na baku a dawo da su...” Daga haka ya miƙe zai bar falon. Da sauri Viper ya ce, “Oga ita kuma batun yarinyar fa?”. Yanzu ɗin ma ƙin tanka batun Nimrah ɗin yayi, yay shigewarsa zuwa wata ƙofa da nake ƙyautata zaton bedroom ne. Da matuƙar tashin hankali Viper yabi Ogan nasu da kallo. A zuciyarsa yana ayyana (Anya mutumin nan yasan abinda yake faɗa kuwa? Ana ga yaƙi amma yana ga ƙura). Kansa yaji ya sara masa, dan haka ya dafe shi da sauri. Dolene ma ya nema sauran aminansa su tattauna wannan matsalar tunda wannan jakin kansa ya fara toshewa da hayaƙin sigari. Mtsoww!! Yaja tsaki yana miƙewa ya fice shima.........✍️

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull