
Post
Kida a ruwa Book 3 page 56
..... who prayed yesterday and kept the hijab for her. He started the prayer, so she greeted him on the ground because she remembered today that she was asleep in his body. The thing that she has never seen in her life or in her dreams. GOD is the one who does what he wants when he wants, so Nimrah has to stop talking today. He grabbed her hand and brought her close to him, he just stole her body and hugged her as if he was going to turn his muscles into one thing. "This is how to greet a husband, not from afar, Babie". Her head rested on his body and she felt this hug deep in her body, she was feeling a strange phenomenon in her body. She said, "Uncle Ammar, you are embarrassing me". The first time he laughed and buried his head in her neck. In the mood of seizing his affairs, he began to kiss her face. See his warm breath blowing on her. It's like a game for women, she shrinks her body and wants to pout and get a chance to connect their lips together. She let out a deep sigh while her body began to tremble like last night's fear and the fact that it was new to her... "Uncle Please stop". Ruqayya fell into a trembling voice and extreme tension. Dan g.....
56
..........Barci sosai Ruƙayya ta sha bayan tabbatar da da gaske babu abinda Ammar zai mata. Saɓanin shi daya ƙare da ciwon ciki saboda kasancewarta a cikin jikinsa. Dan har gabannin asuba idonsa biyu, sai wajen 3:30 ɓarawo ya ɗaukeshi. Sai yayi kamar ya saɓa alƙawari ko ɗan rage zafi yayi sai zuciyarsa ta gargaɗesa akan yabi komai a hankali ta saki jiki da shi. Idan ba haka ba yace zai yi yanda yake so tun a wannan dare lallai zaiga abinda baya so a kwanakin da zasu biyo baya. Haka ya daure har ya samu barcin ya ɗauke shi. Ana kiran salla kuma ya farka. Sosai cikinsa a ƙulle yake, har takai ya gagara tashi sai da aka fara shiga salla yay ƙarfin hali cicciɓawa. Dama tuni ya zame Ruƙayya daga jikinsa saboda halin da yake ciki. Wanka ya fara yi da ruwa masu zafi, sannan yayo alwala. Samun ta tashi ya sashi sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Je kiyo alwala muyi jam'i bazan iya fita massalaci ba”. Bata kawo komai a ranta ba tace masa to tana miƙewa. Babu jimawa ta fito ta sameshi har ya saka masu sallayun jiya ya kuma ajiye mata hijjab. Shine ya jasu sallar, sun idar ta gaida shi kanta a ƙasa saboda tuna yau fa a jikinsa tai barci. Abinda bata taɓa kawoma rayuwarta ba ko a mafarkinta. UBANGIJI kenan mai yanda yaso a lokacin da yaso, ai dole ma Nimrah tasha labari yau. Hannunta ya kamo ya matso da ita kusa da shi, sai kawai ya sata a jikin nasa ya rungumeta tsam kai kace zai maidata cikin tsokarsa ne su zama abu ɗaya. “Haka ake gaida miji, ba daga nesa ba Babie”. Kanta ta sinne a jikinsa tana murmurshi da jin wannan runguma har cikin ɓargonta, gaba ɗaya wani baƙon al'amari take ji a jikinta. Da yanayin kunya da tsoro-tsoro na rashin sabo ta ce, “Kai Uncle Ammar kana bani kunya”. Karan farko yay dariya yana wani cusa kansa cikin wuyanta. Cikin yanayin ƙwacewar al'amarinsa ya fara kaima fuskarta kisses. Ga nunfashinsa mai ɗumi yana busa mata. Abin na mata kamar wasa tana ƙanƙame jiki da son zillewa harya samu damar haɗe lips ɗinsu waje ɗaya. Wata wawuyar ajiyar zuciya ya saki yayinda ita kuma jikinta ya fara tsuma irin na daren jiya na tsoro da kasancewar abin sabo a gareta... “Uncle Please ka daina”. Ruƙayya ta faɗa cikin rawar murya da matsanancin tashin hankali. Dan gaba ɗaya Ammar ya birkice mata daga Uncle Ammar data sani zuwa wani sabon Ammar. A wahale yana ƙoƙarin sake haɗe lips ɗinsu data ƙwaci kanta da ƙyar ya furta, “Bazan iya ba. Bazan iya barinki ba Ruƙayya, idan nayi hakan zan cutu. Please forgive m....” A cikin bakinta ya ƙara faɗar kalmar, a haka ya sungumeta camak kamar zasu zube a ƙasa saboda yanda yake tangaɗi ya maida su saman gadon. Hankalin Ruƙayya ya sake tashi saboda abinda Ammar yake mata yanzu ya shafe duk wanda yay mata daga daren jiya zuwa yanzun. Duk fa rashin jin su basu kai inda Uncle ke shirin kaita ba yau, kai ko hanyar sani ma basu da ita. Barsu dai da shirmensu da kallon soyayya a matsayin soyayya kawai da ido yake gani kuma ya sani. Iyakar abinda suka sani shine karatun Islamiyya da abinda addini yazo da shi, shiko a karance nuni ne ba zahiri ba kamar yanzu da take gani daga wajensa. Jinta a yanda Ammie ta sillota duniya ya sake gigitata. Ta fashe da kuka tana ƙanƙamesa da ƙoƙarin ɓoye jikinta dan karya gani, sai dai kuma ta makaro, dan Ammar bai iso wajen ba sai da ya shirya. Duk da kuwa idanunsa a rufe suke na shiga ruɗanin da yake ciki, hakan bai hanashi more ganin nasa ba. Kafin ya ɗora da sabon karatu ga Ruƙayya mai ban tashin hankali da ruɗani a gareta a wannan safiya mai ɗunbin tarihi da zukata bazasu iya su manta ba....
...★Ammar dai ya tabbata angon wannan safiya mai albarka. Yayinda hajiya Ruƙayya ta shaida babu abin bautawa da gaskiya sai ALLAH. Kuma ANNABI MUHAMMADU MANZON ALLAH ne. Dan kuwa ta jero kalmar nan ta shahada yafi sau shurin masaƙi, a nata shirme isowar mala'ikan ɗaukar rai da ƴan rakkiyarsa kawai take jira. Yayinda sunan Mammah dana Nimrah da Small Mom da Mu'azz suka zama na biyu da tafi ambata. Uncle Ammar ya sha yakushi harda cizo batare da ya ceci kansa ba. Dan haka daga ita har shi babu wanda bai jigata ba ta yanda zai iya tabbatar da eh lallai First Morning, ya tabbata a first morning ɗinsa, dan ba'a kirashi a first night ba. Ata kuɓuta ɗinma bakin bai mutu ba, sai dai muryar ta shige ta yanda baya iya jin kalmomin ALLAH zai saka mata sai ta haɗashi da Dadah da take jerawa. Amma dai yana jin ƙunƙunin sarai a kunensa har takai sai da yay wahalallen murmurshi a bayyane. Sai kuma ya rungumeta yana bata wasu sabbin sumbatar na lallashi da ban haƙuri. Ai ko ta sake daddagewa ta fashe masa da kukan da muryar da bata fita. Ganin bazai barta ɗin ba ta sake kai masa cizo. Ba shiri ya saketa yana mirginawa gefe da sanya dariyar da bai shirya zuwanta ba. Sai ko dariyar ta bama Ruƙayya haushi. Tai ƙoƙarin janyo filo danta mammaka masa sai dai babu ƙarfin yin hakan. Dole ta haƙura ta sake fashe masa da kuka kawai da iya iyawarta. Ammar na dariya a hankali yana riƙe gefen inda ta cije shi, amma idanunsa suna kanta. Yanda take kuka tana kudindine jiki kamar mai jin sanyi ya motsa wani abu mai taushi a zuciyarsa. Dariyar ta ragu a hankali har ta zama murmushi mai cike da tausayawa. A hankali ya matsa kusa da ita, ba tare da yin yanda zata firgita ba. Ya ɗora hannunsa kan filon da kanta yake kai yana kallonta cikin nutsuwa da wani shauƙi mai ƙololuwar girma.. “Ruƙayya…” .....ya kira sunanta cikin murya mai laushi. Har yanzu hawayen nata basu tsaya ba, sai dai ta ɗan juyo inda take jin muryarsa, amma bata yarda ta kallesa ba sam. Ammar ya sauke numfashi a hankali, tare da sake matsar da jikinsa kusa da ita sosai. Cikin muryar raɗa ya furta, “Ki dube ni, please.” Kafaɗa ta maƙe masa alamar taƙi. “Mi yasa?”. Ya faɗa yana ɗora hannunsa kan gashinta daya barbaje. Shafa shi ya fara yi kaɗan-kaɗan, hakan yasa ta ɗan ɗaga idanunta jajaye da hawaye ta kalleshi, idanu suka haɗa, da sauri ta janye natan tana tura masa baki. Sai ya ƙara matsowa kaɗan yana murmurshi, amma wannan karon a hankali sosai, kamar wanda yake tsoron karya sake tunzurata. “Kiyi haƙuri ki yafe min kinji. Ban so ki wahala haka ba Noor”. ya faɗa cikin murya mai cike da nadama. “Ni ma kaina ban san yaushe zuciyata ta kai ni nan ba.” Ya miƙa hannu ya goge mata hawayen da suka gangaro kan kumatunta da yatsunsa cikin tausasawa. “Kin bani farin ciki a wannan safiyar fiye da yadda zan iya faɗa da baki, Ruƙayya. Tun jiya zuciyata ta cika da wani abu da ban taɓa ji ba. Ina jin kamar ALLAH ya bani wata ni’ima da ban cancanta ba.” Ruƙayya da tai shiru tana sauraron sa, kukanta ya fara raguwa kaɗan kaɗan, dan tana jin fita da saukar kalamansa masu tasiri a gareta tamkar busar sarewa. Ammar ya fahimci kalamansa na tasiri, dan haka ya ɗan sunkuyar da kai yana kallonta da yanayi mai taushi. Cikin sake kashe murya ya cigaba da faɗin, “Dan ALLAH ki yafe min daga wahalar dake ɗin da nayi.” Ya ɗan yi murmushi da kifa fuskarsa akan tata ya haɗe goshinsu waje guda. “Ni dai Uncle Ammar ɗinki ne har yanzu. Ba zan taɓa zama wanda zai cutar da ke ba.” Hannunsa ya sake kaiwa a kanta cikin kulawa kamar yadda ake lallashin yaro. “Ki kwantar da hankalinki, Ruƙayya. Babu wani abu da zai faru da ke sai wanda zai saka ki cikin aminci da farin ciki a zaman mu, nayi alƙawarin zan riƙe amanar Dadah. Nayi alƙawarin zan tabbatar miki da ni mai sonki ne da tsananin ƙaunarki tun kina ƙanƙaniwarki. Zanyi aiki tuƙuru da zuciyata, da kwanji na wajen sauke haƙƙokinki. Koda ban baki farin ciki ɗari bisa ɗari ba a dukan rayuwa, zan kamanta da jarumtata domin tabbatar miki Abdul-rasheed Abdul-rasheed Shehu naki ne ke kaɗai a duniyarki. In sha ALLAH sai na sakaki a jerin matan da suka ce NAMIJI ɗan goyo ne. Daga yau ki rubuta ki ajiye Abdul-rasheed mijin kan-tace ne kawai a gareki.....” Karo na farko Ruƙayya ta saki ɗan murmurshi saboda kalmarsa ta ƙarshe. A hankali ta kai masa ƙaramin duka a ƙirji da faɗin, “Kai Uncle, mijin kan tace kuma?”. Shima ƙaramar dariya yayi. Tare da sake rungumeta sosai. “Eh mana Noor, mijin kan tace kuwa. Na gode da safiyar nan, na gode matuƙa da ƙirgen da bashi da adadi. I love you” ya faɗi furucin ƙarshe a hankali cikin da kunnenta tare da rungumeta tsam-tsam.” Ajiyar zuciya mai nauyi Ruƙayya ta sake saukewa tare da numfashi a hankali, zuciyarta tana sauka kaɗan kaɗan daga tashin hankalin da ya mamaye ta. Sai kawai ta rungume shi itama tana cusa kanta a gefen wuyansa hawayenta na sauka a jikinsa............✍️
Kuyi hakuri da wannan. Iya pages ɗin dake ƙasa kawai kenan. In sha ALLAHU zan yi typing a weekend ɗin nan sai mu shiga sabga gadan-gadan ba wasa. 😀