Kenza eBookz
Kida a ruwa Book 3 page 57

Post

Kida a ruwa Book 3 page 57

..... Aysam, Rayhana. And of course, I should have tried the same decision as I tried the others, a little bit different from yours as a whole. So just go, go and pray for me, thank you for your efforts, let me try my hand at this point as Momy said, it's time for me to fight for myself". She went to the bathroom and saw Rayhana's hair standing there, her heart pounding on her chest....... Aheel is a lucky girl. There are no signs that this will change. Today, she is a bride who is proud of her husband. Even if her husband doesn't like her, he takes care of her like a queen At the same time, she wiped them with her hand, then she touched her mouth and said, "You will change Dadah." You have to change the way I want and need my husband. I love love, I am.....

Standalone post1,757 words

57

.........Rayhana na cikin ƙyalƙyala dariyar mugunta sai ganin Nabeeha tayi ta dawo. Cikin sauri ta shanye dariyar tana kallon ta. Sai kuma cikin dauriya ta ce, “Naga kin dawo Aunty?”. Murmurshi Nabeeha tayi, tare da miƙama Rayhana key ɗin. Ƙasa amsa tayi, sai ma kallonta da take ita da key ɗin. Hakan ya saka Nabeeha ɗora mata key ɗin a hannu tana faɗin, “Rayhana babu amfani rufe Haysam, dan idan nayi yau gobe ma nayi zan iya jurar cigaba da yi ne har ƙarshen rayuwarmu?.” “Amma Aunty....” “Rayhana!”. Nabeeha ta katseta ta hanyar ɗaga mata hannu. Sai kuma ta dafata tana mai ƙoƙarin shanye hawayen dake ƙoƙarin ciko mata ido. “Rayhana mutane da yawa sun bani shawara daban-daban a wannan daren, na gwada wasu a ciki amma banga wadda keda hanyar ɓillewa da ni ba, sai guda ɗaya tak. Kin san daga bakin wa ta fito?”. Kai Rayhana ta girgiza mata. Nabeeha tai murmurshi tana barin wajen. Sai dai taku ɗaya biyu ta tsaya cak, hannayenta ta harɗe a ƙirji, batare da ta juyo ba ta cigaba da faɗin, “Haysam, Rayhana. Kuma tabbas ya kamata ace na gwada tashi shawarar shima kamar yanda na gwada na sauran, dan tasha banban da taku gaba ɗaya. Dan haka kije kawai, kije ki min addu'a, nagode da ƙoƙarin ku, ku barni nima na gwada nawa a wannan gaɓaar tamkar yanda Momy ta faɗa, lokaci yayi da nima zan yi yaƙin kaina”. Tana kaiwa nan ta wuce bathroom tabar Rayhana datai sumar tsaye anan zuciyarta na hanƙoro a ƙirji.......

★==========★

Da kallo Nimrah tabi bayan Dadah dake ficewa, wasu irin hawaye masu zafi suka ciko mata idanun. Tabbas gaskiya kowa ke gaya mata, Dadah yana mata kallon ƴar yarinya ne sa'ar su Aheel har yanzu. Babu kuma wasu alamu dake nuna zai canja hakan anan kusa. Dubeta a yau ita amarya ce a ranar da kowace mace ke jin alfahari, take samun kulawa da tattali na musamman a wajen mijinta. Ko miji baya sonka a randa aka kaika gidansa yakan maka abubuwa ne tamkar sarauniya kodan amfanuwa da baiwar, amma ita Dada sai yay mata tarba irin ta uba da ƴa. Murmurshi mai ciwo ya suɓuce mata tare da hawaye a lokaci guda. Hannu takai ta share su, sai kuma ta ɗan taɓe baki da faɗin, “Zaka canja Dadah. Dole ne ma ka canja a yanda nake fata da buƙatar mijin aure na. Ina son soyayya, ina son kuma a nuna min soyayya. Tunda har ka kasance a cikin ƙaddarata koda ace ina tuhumarka da wani laifi dole ne ka bani wannan soyayyar nima naji yanda ake ji. Dan wlhy bazan yarda na zama cikin ƴan rakkiyar mata ba. Sannan matarka bazata yankeni nasha zafi a banza batare da na amshi sakamako itama ta amshi na ba. Ni da kai da ita dolene mu zuba”. Tana kaiwa ƙarshe ta kaɗa kanta zuwa bathroom. Wanka tai da alwala ta fito. Ta gabatar da shafa'i da wutri ta haye gadonta ta kwanta kewar Ruky na dawo mata. Sai kuma ta hau murmurshi da tunanin ko yanzu yaya Buddyn tata ke ciki da Uncle Ammar? Da wannan tunanin barci mai nauyi ya kwasheta kasancewar akwai gajiya sosai a jikinta, sannan duk yanda abu yakai ga damun zuciyar Nimrah bata cika zafafa shi da tsananin da har zaka iya karantar shi a zahirinta ba...

....★ Da asuba kamar yanda Dadah ya saba, ya fito domin tafiya massalaci. Kai tsaye sashen Nimrah ya nufa, dan yasan ita kaɗai ce ba lallai ta iya tashi ba. Sai dai bashi da tabbacin bata rufe sashen nata ba. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya jin yana murɗa handle ɗin ƙofar ya buɗe. Ganin fitulun falon a kunne yanda ya barsu jiya bata kashe ba ya sashi ɗan girgiza kai. Bedroom ɗin ma ya sameshi a buɗe, sai dai nan kam babu haske sai da ya lalubi makunnar ya kunna. Can ya hangota a gado cikin bargo ta rufe har kanta, dan ta ƙure uban ac ɗakin yay mugun sanyi. Ya ƙarasa takawa har gaban gadon. Zama yay gab da inda yake ƙyautata zaton kanta ne, sannan ya janye bargon. Wani irin harbawa zuciyarsa tayi a cikin ƙirji sakamakon inda idonsa ya fara sauka. Yay saurin janyesu yana maidawa kan fuskarta dan tana a kwance ne a rigingine. “Nimrah.” Ya faɗa yana ɗan shafa fuskar tata datai masa fayau. Babu alamar zata motsa, sai ya ɗan fara bubbuga mata fuskar yana cigaba da kiran sunan ta. Karo na farko ta motsa tana yamutse fuska. Da ƙyar ta buɗe idanun da sukai wani kalar shanyewa tamkar wadda tasha wani abun maye. Tai walai da su ta maida luuu zata sake lumshe abunta. Harga ALLAH sai da Dadah yaji wani al'amari mai girman gaske. Dan hatta maƙogwaransa sai da yay wata kalar yin sama da sauri ya dawo har sau biyu. Ga shi ita kuma tama sake gyara kwanciya ne abinta. Yanzu kam baiyi magana ba, sai kawai ya kamata cak ya tayar zaune cike da dakewa da kamewa tamkar komai bai faru ba. Nimrah da giyar barci ke ɗiba cikin ƙunƙuni ta ce. “Small Mom please ki barni zan tashi ɗan anjima. ALLAH ina jin barci”. Ya fahimci tama manta a inda take ne, ga shi tana gama faɗa ta sake ƙoƙarin komawa zata kwanta. Dole ya tallafota sosai ya jikinsa, ita ko saita samu damar shige masa jiki, dan kanta ta kwantar a ƙirjinsa ta zagayo da duka hannyenta bayansa kawai ta cigaba da barcinta hankali kwance. Yayinda Dadah ya ɓige da riƙe numfashinsa na sakanni dan abin yazo masa a matuƙar bazata. Ya tabbatar Kiddo ta kusa ƙarasa tona masa asiri inda aka cigaba da tafiya a haka. Dan data san tarzomar da take tasarwa da tuni ta shiga hankalinta. Shirin tada salla da ake yi ya saka tunaninsa katsewa, cikin furzar da iska ya shafa kanta dake ƙirjinsa zuwa bayanta. Sai da yay ɗan gyaran murya kafin sake kiran sunanta. Amma yarinyar nan bata da alamar sake buɗe idanun ma ko irin na ɗazun. Ya tabbatar ya riga da ya rasa raka'ar farko, gashi ya zama wajib a gareshi sake alwala. Camak ya ɗauketa ya miƙe da su tsaye, sai dai tana jingine a jikin nasa. “Kiddo kina son kuwa na samu salla yau?”. Yay maganar yana ƙoƙarin ɗagota daga jikinsa ya tsayar da ita akan ƙafafunta. Yanzu kam dole ta buɗe idanun, sai dai kana gani kasan barci ne taf a cikinsu. Ganin Dadah saɓanin Small Mom ya sata ware su sosai. Sai kuma duk ta nema daburcewa, ta ɗan kalla jikinta dake sanye da ƴar fingilar riga best da wandonta iya cinya, bamma tasan ta daka tsalle ta koma bayansa ba, tare da faɗin, “Naga Boni.” Dadah da abin nata ya bashi dariya ya gimtse da ƙyar. Juyowa yay ƙoƙarin yi da nufin mata magana kawai ta rungume shi ta baya, dan da ya sake ganinta gara ai hakan. Yanzu kam sai da ya ɗan murmusa, sai kuma ya kai dubansa ga hannyenta data zagayo kan cikinsa. Nasa ya ɗora akai cikin basarwa kamar bai fahimceta ba ya furta, “Tunda kinsa na rasa salla je kiyi alwala muyi anan”. “Ni wlhy Dadah zaka ganni”. Ta faɗa cikin shagwaɓa tana sake ƙanƙamesa. “Tunda baƙya so na ganki ya kike so ayi?”. “Ka rufe idonka to”. “Ashe ni naga Bonin ma. Shike nan na rufe”. Sai da ta ɗanyi jimm na sakanni sannan ta sake sa, ta ɗan leƙo da kanta dan tabbatar da ya rufe ɗin. Sai suka haɗa ido. Da gudu ta nufi bayi. Kansa ya girgiza kawai yana murmurshi. Ya tabbatar zata sake ɓata masa lokaci, sai kawai ya nufi wardrobe ɗinta ya buɗe, cikin sa'a ya samu abaya a kusa. Ɗauka yay ya bita bayin, yay knocking da faɗin, “Buɗe ki ƙarɓa wannan ki saka karki sake makarar damu”. Kaɗan ta buɗe ta miƙo hannunta da lalle yayma ƙƴau sosai. Abayar ya saka mata, cikin gargaɗi ya ce, “Kuma 3 minutes na baki”. Mintuna ukun ma basu gama cika ba ta buɗe bayin ta leƙo. Ganin ya juya ma ƙofar bayin baya ta fito sum-sum tana sake jan ɗan kwalin abayar ya rufe mata fuska sosai. Komai baice mata ba shima ya shige bayin kawai. Bai wani jima ba ya fito yana gyara hannun jallabiyar jikinsa alamar alwala yayo. Ita kuma harta shimfiɗa abin salla guda biyu, sai dai nashi ya zama nata gaba kaɗan. Sannan ta saka hijabi yanzu. Yanda take faman sinne kai yasa baiyi magana ba kawai ya hau kan sallayar ya tada salla bayan ya juyo ya kalleta domin tabbatar da tsaiwarta tayi.. Karo na farko da Nimrah taji sautin ƙira'ar Dadah. Jitai tana neman narkewa. Daga ita har Ruƙayya suna bala'in son karatun Uncle Bilal saboda ALLAH ya bashi murya, a yau sai taji aiki gamai ƙareka. Dan jitai kamar karma su idar da sallar, sai dai babu yanda ta iya. Ya ɗaga hannu yana addu'a Nimrah kawai taji son tsokanarsa. Fuskarta da murmurshi ta ɗan matso kusa da shi, duka hannyenta biyu ta saka cikin nashi hannun tai kamar ta ɗiba abu. Da mamaki ya juyo ya kalleta, sai tai saurin matsawa baya murmushinta na ƙara faɗaɗa ta shafa addu'an a fukarta. Sosai abin nata ya bashi dariya dan ya fahimci wai addu'ansa ta kwaso. Wani mitsitsitsin murmushi yayi tare da kamo hannun nata duk biyu ya shafa a fuskarsa shima. Dariya sosai ta sanya tana ɓoye fuskarta. Shima dai bai iya hana murmushinsa fita ba, dan abinda tai ɗin kawai ji yay ya sakashi nishaɗi. Koda tai ƙoƙarin janyewa a jikinsa bai barta ba, sai ma riƙeta yay da ƙyau yana faɗin, “Kiddo baƙya ji ko. Kin hana ni zuwa massalaci kin kuma kwashe min addu'a”. Siririyar dariya ta saki da saka hannyenta ta rufe fuska irin na mai jin kunya. A haka tace, “Dadah ina kwana”. Shiru yay bai amsa ba, har sai da ta janye hannunta daga kan fuskar ta ɗan kallesa, ganin ita yake kallo tai saurin sake duƙarwa. A tunaninta ko baiji bane sai ta sake maimaitawa. Yanzu ma bai amsa ba, ya dai miƙa mata tattausan hannunsa alamar suyi musabaha. Hannun ta zubama ido itama, wani abu mai nauyi da armashi na ratsa zuciyarta. A hankali ta saka nata a ciki. Sai kawai ya jawota gaba ɗaya jikinsa ya rungume. “Haka ake gaida miji daga yau Little Shadow”. Ba ƙaramin nauyi kalmar nan ta miji take mata ba, musamman a bakin Dadah, sai taji kamar ƙasa ta buɗe ta shige ciki. Shi kansa ya fahimci hakan, kuma yana saka shi jin nishaɗi............✍️

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull