Kenza eBookz
Kida a ruwa Book 3 page 58

Post

Kida a ruwa Book 3 page 58

...the mran?". Even though Scythe was angry with Mr. Specter's scolding, he only sighed in frustration. He directly said, "I told you that marriage is scary for the married man, let alone Imran? We should first return our thoughts to our bodies. For centuries we have been repeating the same thing every session. But this man in every movement has a new style in it. Every time we brought the girl before us and opened her eyes to the things that were our secret, instead of influencing her with our plan, things turned upside down, if what we told her had an effect on her, why would she trust him?..." For the first time, Viper said, "The truth of Scythe is what I want you to understand, don't think that we are using a girl and that this man is the one who used us on her. In the meantime, we have noticed that things have started to get messy. Then Oga fought to say everything, even on the occasion of the ceremony." "Well! I just think that there is something that Oga is planning." "But he should inform us of our concern, leaving us in the dark is pointless since it is a problem that affects everyone". "Pray for him until he returns. I am going to visit my madam who is sick". Praying for

Standalone post1,502 words

58

..........Yanda ɗakin yay shiru zaka tabbatar da magana ma ta gagaresu yau ɗin. Dan an gama kaiwa ƙarshen goge musu hadda a wannan gaɓar. Ga Oga Jush baya ƙasar ma shi, dan a daren shekaran jiya bayan maganarsa da Viper ya tsallake yabar ƙasar batare da sun san dalili ba. Basu kuma bi ba'asi ba balle damuwa tunda sun san haka yake. Ya riga ya maida shigowa ƙasar da fita tamkar ɗakin barcinsa da falo. “Kowa yayi shiru mazaje. Miye abin yi?”. Scythe ya katse shirun nasu hannunsa dafe da kansa. Kallonsa duk sukayi kawai, sai dai duk sun gagara cewa komai a yanzu ɗin ma. Sai zuwa can Mr Specter yaja tsaki mai ƙarfi, cike da isarsa ya furta, “Ni inaga mu jinkirta Oga ya dawo, sai mu sake zama da shi muji ko akwai wani shiri da yake ne.” “Hummm, jira. Jira dai koda yaushe, kanafa jin bayanin Viper akan zaman ƙarshe da yay da shi. Nifa gaskiya al'amarin nan ya fara bani tsoro....” A fusace Mr Specter ya katse Scythe da yay maganar. “Miye abin tsoro anan? Auren da dama kasan da shi ko shi Imran ɗin?”. Duk da Scythe yaji haushin tsawar da Mr Specter yay masa sai yay murmurshin takaici kawai. Kai tsaye ya furta, “Ni nace maka aure ya ban tsoro ko mai auren balle wani Imran? Ya kamata mu fara dawo da tunaninmu jikinmu. Shekaru aru-aru abu ɗaya muketa maimaitawa a kowane zama. Amma mutumin nan a kowane motsinsa da sabon salo a ciki. Duk yaushe muka kawo yarinyar gabanmu muka buɗe mata idanu da abubuwan da suka kasance sirrinmu, maimakon muga tasirin namu shirin a kanta sai abin ke juyewa, idan har abinda muka gaya mata ya mata tasiri miyasa zata amince ta tare da shi?...” A karo na farko Viper ya ce, “Gaskiyar Scythe abinda nake son ku fahimta kenan nima, kada fa ya zama muna tunanin munyi amfani da yarinya ace mutumin nan shi ne yay amfani da mu a kanta. A tsakanin nan fa mu lura abubuwa sun fara tufƙa da warwara ne. Sannan Oga yaƙi cewa komai hatta akan bikin nan da akayi”. “To! Ni dai ina ganin kamar akwai abinda Oga ke shiryawa ne fa.” “Amma ya kamata ace ya sanar damu muma, barinmu a duhu baida wani ma'ana tunda matsalace data shafi kowa”. “Miyi masa uziri har ya dawo. Ni inaga zan wuce Madam ɗina bata da lafiya”. Addu'ar samun lafiya sukai mata, Mr Specter na fita Viper ya dubi Scythe. “Mutuminka shima bai ɗauki abin nan da muhimmanci ba Scythe, nifa zuciyata ta fara shiga kokwanto akan tafiyar nan”. Alamar shiru Scythe yayma Viper, daga haka ya ɗakko musu wata hirarma. Sai abin ya ƙara ɗaure zuciyar Viper tamau. Amma dai bai sake cewa komai ɗin ba....

============

Anan ɓangaren Ammar da kansa ya gyarama Ruƙayya jiki tare da gasata cikin ruwa masu zafi duk da tanata bore. Sai dai kamar jira zazzaɓi keyi tun a bayin ta fara rawar sanyi. Kafin wani dogon lokaci jikinta ya ɗauki zafi sosai. Hankalinsa ne ya tashi, yama rasa miya kamata yayi. Sai kawai yay kiran Aunty Mimi. Babu jimawa ta iso sashen, shi yazo ya buɗe mata ƙofa. Daga sama har ƙasa Aunty Mimi ke kallonsa, hakan ya sashi haɗe fuska da faɗin, “Wai miye kike kallona?”. “Oh tijara zaka min ma? Lallai ma Yaya Ammar ɗin nan ALLAH sai na koma”. Tai maganar zata juya. Da sauri ya riƙo hannunta ya rufe ƙofar. “Yi haƙuri wasa nake miki ƴar ƙanwata. Kinga zo muje ciki wlhy Baby najin jiki”. Da ƙyar Mimi ta iya danne dariya suka ƙarasa har bedroom. Zaune ya kai bakin gadon kusa da Ruky yana janye bargon. Tai ƙoƙarin riƙewa tana sakar masa kuka. “I'm so sorry Baby, kinga ga Mimi na kira mik....” Baima ƙarasa faɗa ba tai saurin kallo inda Mimi ke tsaye tana mata kallon tausayi, dan yanda idanun sukai luhu-luhu zaka san tasha wahala da kuka sosai. Kukan ta sake fashewa da shi tana faɗin, “Mom”. Mimi takai zaune kusa da ita itama, hannu takai saman kanta ta shafa. Cike da kulawa ta ce, “Be brave, Ruƙayya. Kuka bazai canja komai ba, kuma bazai bada lafiya ba kinji. Yanzu mike miki ciwo?”. “Kaina da jikina duka. Mom dan ALLAH kuce ya bari muje wajen Mammah. Ni dai banzan zauna nan ba nafi son can”. Murmurshi Mimi tayi a karo na farko. “Rukayya zama gaban Mammah kuma ai ya ƙare, sai dai na wankan jego. Kinga kiyi haƙuri kiyi zamanki anan, sashen Mammah cike yake da baƙi. Ki bar wannan kukan haka nan yana ƙara miki ciwon kan”. Ta ƙare maganar tana share mata hawayen. Sai kuma ta maida hankalinta ga Ammar daya zuba tagumi yana kallon su da saurare. “Yaya Doctor ya kamata a kira ta duba ta. Dan jikinta da zafi sosai. Ta shiga ruwan zafi ne?”. “Da ƙyar ta yarda, ruwan ma ba wani zafi sosai dan na farko catai yayi zafi ta ƙara ruwa”. “A'a Rukayya dole ne shiga ruwan zafin nan. Shine zaisa kiji daɗin jikinki. Kaga kira Doctor ɗin bari na sake haɗa wani ruwan”. Ammar ya sauke ajiyar zuciya yana miƙewa. Bayi ta nufa, a ranta tana addu'ar ALLAH yasa Dadah ma bai basu kunya ba.....

✨✨✨✨✨

Daga gaisuwa Nimrah ta ɓibgire da barci a jikin Dadah. Sai jin saukar nunfashinta yayi a hankali. Koda ya leƙa fuskarta yaga barcin take da gaske sai ya murmusa. Miƙewa yay tare da ɗagata camak ya dire a saman gadon. Hijjab ɗin jikinta ya cire sannan ya ja mata bargo. Daga haka ya fice a ɗakin. Yana fitowa a sashen Nabeeha na fitowa a nata itama. Gabanta ya faɗi sosai, ta zuba masa idanu zuciyarta na zallo. (Karfa mutumin nan a sashen yarinyar nan ya kwana. Wannan wane kalar abin kunya ne ni Nabeeha) Tai maganar a zuciyarta tsoronta na bayyana a fuska. Dada kam yama wuce abinsa nasa sashen sai ka rantse ma bai ganta ba ne. Bayansa tabi da kallo hawayen da take riƙewa na ƙoƙarin ciko mata ido, tabbas tana tsananin son Haysam, duk duniya babu namijin dake birgeta take kuma jin ya isa a kira shi namiji tamkarsa. Haysam nada wasu sirrika da macen aurensa ce kawai ta sansu. Dole ne a wannan gaɓar ta ajiye makaman yaƙinta, tayi duk yanda zatai su shirya, dan in ba haka ba akwai babbar matsala. Al'amarin yarinyar nan na ɗaga mata hankali, dan bata taɓa ganin macen da Haysam yake kallo da irin kallon da yake ma yarinyar ba. Mayafin abayar dake kanta ta saka ta share hawayen tas. Kafin ta nufi sashen nasa. Baya a falon, dan haka ta wuce bedroom kai tsaye. Knocking tai da sallama a lokaci ɗaya, bata jira izini ba kuma ta tura kawai ta shiga. Yana zaune a bakin gado da waya a hannu alamar wayar yayi ko zai yi. Suna haɗa ido ya ɗauke nasa, yanzu ma bata nuna ta damu ba ta ƙarasa inda yaken, kusa da shi gab ta azauna a bakin gadon. “D. Ina kwana”. Yanda ya ɗago ya kalleta zai baka tabbacin ba haka yay tunanin ji daga garetan ba. Itama ta fahimci hakan, shiyyasa tai murmurshi ƙarfin hali tana sake ɗan matsawa jikinsa da kamo tattausan hannunsa a cikin nata. “Kayi haƙuri ka amsa min gaisuwa ta. Sannan ka yafe min abinda ya faru jiya dama wanda kake kallona da shi shekaru da yawa. Haysam kasan duk duniya babu abinda nake so sama da kai. Sannan babu macen da zata so kishiya musamman irin tawa ƙaramar yarinya da zan iya haihuwar wanda ma ta fita. Haysam ka fahimce ni”. Shiru Dadah kamar bazai ce komai ba. Harma ta fidda ran zai yi maganar sai kuma yayi. “Nabeeha ai ke da kanki kika jawoma kanki kishiya. Abinda ya faru ya faru ya wuce, amma tabbas da'a lokacin kin amshi Nimrah matsayin ƴa da a wannan matsayin take har abada. Amma kika nuna min ke mai taurin kai ce, sannan baki da ra'ayin kanki sai abinda akace kiyi...” “In sha ALLAHU zan zama fiye da yanda kake so a yanzu Haysam. Dan ALLAH ka saket...” Wani kallon kin haukace ma yay mata, dole tai shiru batare data ƙarasa faɗar abinda tai niyya ba. Tai ƙasa da kanta dan bazata iya jurar kallon nasa ba. “Baki shirya canjawa ba kenan.” “Wlhy na shirya Haysam, da gaske na shirya zama dakai na har abada. Kuma zan kasance a yanda kake so”. “Hummm! Idan ko har haka ne to dole ki cigaba da kallon Nimrah matsayin MATAR HAYSAM”. “Shi ke nan naji na amsa. Sai dai ina roƙon alfarma ɗaya a gare ka. Ka samar min wani gidan zan koma, ita sai ta zauna anan”. Dadah yay murmurshi mai faɗi. Sai kuma ya ɗan girgiza kansa da faɗin, “Look Nabeeha, ki daina ɗakko abinda bazai yiwu ba. Kin sani har abadan bazan zauna inda babu Mammah da ƙanne na ba.” Nabeeha ta haɗiye yawu masu zafi. Kenan duk shirinta bamai yiwuwa bane ba. Miyasa Haysam bazai fahimceta bane ba..........✍️

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull