
Post
Kida a ruwa Book 3 page 59
.....to the bone". "Oh so you think I didn't open the bowl? Don't worry, I'm not in a hurry, it's not surprising that in a few months I'll bring you a dish washer that will show you everything I've eaten and put my clothes away." Tsaff got ready in a suit that smelled good for him. If he was going to leave, he would only need one bag for work. Even though he had already said goodbye to Mammah, he was going to go straight to Nabeeha's department. Since he entered the heart of Rayhana who was sitting in the living room, Ismat Kam, who was lying down, got up quickly.
59
..........Jin zai zare hannunsa data riƙe yasa ta dawo hayyacinta. Da sauri ta sake damƙe hannun. Ta ce, “Shike nan na yarda. Amma dan ALLAH ina son naji kace ka yafe min”. “Na jima da yafe miki ai, sai dai a kiyaye na gaba, dan ba lallai na yafe ba. Sannan ina ƙara baki shawarar ki riƙe girmanki, bana son wani shirme. Ki zama mai ra'ayin kanki. Zan yi tafiya ta sati biyu yau ɗin nan. Bana son jin wani abu saɓanin wanda kika faɗa a yanzu”. Wani sassanyan murmurshi ne mai yalwa ya suɓucema Nabeeha. Ta ɗan taɓe baki da faɗin, “Uhmm D. Kenan. Yo har ka gama cin amarcin ne? Kwanan amarya fa ɗaya kacal amma kace zakayi tafiya ka barta”. A mamakinta wani murmushi ya saki mai ƙayatarwa. Dan har sai da ta shagala a kallonsa. Ya ɗan ɗaga nata gira kuwa. “Mi kike ci na baka na zuba.” “A'a ai ba wani abu nace ba, kawai dai abin ne da mamaki. Ita tace daɗin naman ƴan shila ke sa a cinye har ƙarshinsa, kai kuma zaka bata kunya ta hanyar ƙin koda buɗe murfin kwanon da suke ciki balle akai ga cin har zuwa ƙashi”. “Oh haka kike tunani ban buɗe kwanon ba? Karki damu ni ai bamai gaggawa bane, babu mamaki nan da watanni kaɗan ma a kawo miki wankin kwanon da zai tabbatar miki komai na cinye na siɗe kayana”. Yana kawai nan ya miƙe abinsa. Binsa tai da kallo, da ƙyar ta iya danne baƙar maganar tasa, amma zuciyarta wani irin zafi take da tafasa a cikin ƙirji. Sai da ya shige bayi sannan ta miƙe ta fita a sashen gaba ɗaya....
Koda Dadah ya fito yaga bata a ɗakin murmurshi kawai yayi. Kamar yanda ya saba ya hau gyara jikinsa. Tsaff ya shirya cikin suit da suka masa masifar ƙyau. Ya zuba turarrrukansa masu daɗin ƙamshi. Idan zai yi tafiya sam baya ɗaukar kaya, dan haka yanzu ɗin ma laptop bag ɗinsa ce kawai sai abinda zai iya buƙata daya danganci aiki, suma duk ciki ya zuba su ya fito yana kallon agogon hannunsa. Duk da ya riga yayi sallama da Mammah tun jiya, zai shiga yanzu ma suyi sallamar, daga nan ya sallami baƙi dan duk gobe suka ce zasu wuce... Kai tsaye sashen Nabeeha ya nufa. Tunda ya shigo zuciyar Rayhana dake zaune a falon ta fara marmashewa. Ismat kam dake a kwance ta tashi da sauri. Yana ƙarasa zuwa tsakkiya ta nufoshi tare da durƙusawa tana gaishe shi kamar yanda suka saba. Itama Rayhana yitai kamar yanda Ismat ɗin tayi. A tare ya amsa musu sau ɗaya kamar yanda ya saba, batare da ya jira komai ba kuma ya shige bedroom ɗin Nabeeha. Rayhana ta sauke ajiyar zuciyarta da taji tana zafi da bugawa da sauri-sauri, har sai da Ismat ta kalleta, amma sai ta wayance da faɗin, “Ni ban san randa Yaya Haysam zai fara kallonmu da amsa mana gaisuwa tamkar ƙannensa ba”. “Kiji tsoron ALLAH Rayhana, to miye banbancin yanda yake amsa mana da su ɗin a yanzu ma?”. Harararta Rayhana tayi ta koma inda ta taso ta zauna. Ismat ta girgiza kai kawai, dan itama dai tata ta isheta. Hankalin Rayhana gaba ɗaya akan bedroom ɗin Nabeeha yake, tana faman ƙirga adadin mintuna da zuciyarta kai kace ɗakin wata kishiyarta ya shiga. Cikin sa'a kuwa bai wani jima ba sai gashi ya fito. Yanzu kam Nabeeha ɗin ce riƙe da laptop bag ɗin nasa, abin mamaki kuma fuskarta washar da murmushi kai da ka ganta kasan tana cikin farin ciki. Ba Rayhana ba hatta Ismat sai da ta tsaya kallonta galala har suka fice. Sai kuma suka kalla juna da Rayhana ɗin. “Uhmmm da alama Dadah da Aunty fa an shirya”. Cewar Ismat cikin farin ciki. Baki kawai Rayhana ta taɓe da kawar da kai tamkar bata ji ba...
Anan kam daɗi kamar zai kashe Nabeeha ganin Dadah ko kallon sashen Nimrah baiyi ba balle yace zai shiga. Tambayar kanta take yaya akai haka har suka fito. Badan tasan halinsa ba sai ta tambayi dalili. Amma dai ta shanye abinta a rai kawai tana faman dariyar ƙeta. Ganin sashen Mammah zai je sai ta doge a compound, shima bai ce mata komai ba ya wuce abinsa...
🤣🤣Wai mi Dadah yake shiryawa ne jama'a, nima fa kaina ya sani a ruɗu baifa yima Nimrah sallama ba🥶😱.
%%%%%%
Kasancewar har yanzu safiya ce ba kowa ya tashi ba, amma duk da haka hayaniyar sashen na Mammah yafi ba kowane sashe a gidan. Anan falo ya gaisa da iya wanda suka tashi sannan ya ƙarasa bedroom ɗin Mammah duk da yaji kamar maganarta a kitchen. Feedo ce kawai aɗakin ta gama gyarawa, ta zube tana gaida Dadah. Ya amsa mata da kulawa, dan duka ƴaƴan ƴan uwan nasa yana jinsu har cikin ransa ne tamkar abinda ya haifa. Feedoh ce taje ta sanar ma Mammah. Babu jimawa sai gata. “Ƴan tafiya har an fito kenan?”. “Wlhy nama so makara office Mammah”. Ya bata amsa yana kallon agogon hannunsa. Murmurshi tai da kaiwa zaune. Shi kuma ya zamo yana gaisheta. Dai-dai nan Aunty Mommy ta shigo da tray a hannu, a gabansa ta ajiye itama tana faɗin, “Dadah ina kwana?”. Maimakon amsawa sai cayay, “Yanzu Mammah barin yaran nan kikai yau ma suka kwana gidan nan?”. “Ai yau zan kora su kuwa Muhammad.” “Dadah kwana uku ne fa kawai”. Hararta yayi. Dai-dai nan itama aunty Ummi ta shigo. Sai Aunty Mimi biye da ita suna dariya. Dan labarin abinda ya faru a sashen Ammar take bata. Wai Ammar ya koma bita zai-zai ko motsi Ruky tayi sai ya kama riƙeta yana tambayar mi take so. Sam basu lura da Dada ba Aunty Mimi ta ce, “Aunty Mommy ana can ana show sashen Yaya Ammar bake”. Aunty Mommy data san ɓaranɓaramar da zata yi tai saurin yin gyaran murya da nuna musu Dadah. Muƙut Mimi ta haɗiye gulmarta suka shiga gaishe shi. Shima bai nuna ya fahimci komai ba balle ma jinsu ya amsa gaisuwar kawai. Sai kuma ya koma musu gargaɗin shiryawa su koma gida yau. Sun tabbatar masa yau duk zasu wuce in sha ALLAHU. Daga haka shima ya ajiye kuɗi masu yawa kusa da Mammah yana miƙewa da faɗin a bama baƙi. Godiya tai masa da fatan dawowa lafiya. Su Aunty Ummi sai suka nuna basu san da tafiyar ba. Cikin haɗa baki suka ce, “Dadah tafiya zakai? To Nimrah fa?”. Hararar su yayi. Hakan yasa suka fara ƴan soshe-soshen rashin gaskiya. Mammah tai murmurshi kawai da binsa da addu'a. Ya amsa mata da Amin yana ficewa ya bar su Mimi na tura baki gaba...
Baiyi mamakin sake iske Nabeeha a compound ɗin tana jiransa ba, dan ya fahimci bala'i-bala'in farin ciki take da wannan tafiya tashi. Bai ƙarasa inda zuƙa-zuƙan motocin da ake kaisa office ɗin suke ba sai da sukai sallama ya amshi bag ɗinsa. Da sauri ɗaya a cikin security guard ɗin nasa yazo ya amsa daga hannunsa bayan ya rissina ya gaishe da Nabeeha. Tako amsa masa cike da isa. Shi dai Dadah ya wuce abinsa. Tana tsaye har sai da taga fitar motocin a gidan sannan ta koma cike da nishaɗi. Badan ta masa alƙawarin daina shiga sabgar yarinyar nan ba sai taje sashenta yanzu kodan taci dariya, amma ba damuwa, tunda ana tare za'a haɗe ai...
>>>>>%<<<<<
Sai goma da wasu mintina Nimrah ta tashi da ƙyar. Sosai dai da kewar Ruky ta farka. Badan kuma tana tsoron gargaɗin su Gwaggo Alawiyya ba da sai taje sashen su Ruƙayyan yanzu nan. Batayi mamakin rashin ganin Dadah ba a ɗakin, hakama ganinta a gado dan tasan shine ya maidata can. Yanda jikinta yay mata nauyi wanka kawai take buƙata. Dan haka ta gyara gadon kamar ba'a kwanta ba sannan ta nufi bayi. Can ma sai da ta gyara sannan tayo wankan. Ta fito kenan kira ke shigowa wayarta. Baki ta tura gaba dan fushi take da kowa. Sai ta share wayar kawai ta shiga shiryawa. Sai da ta kammala tsaff cikin doguwar atamfa datai mata ƙyau, sannan ta ɗauki wayar tana shafa ciki dan yunwa take ji. Sosai ta waro idanu waje ganin Dadah ne ashe ya kirata. Da sauri ta kira shi back...
Dadah na meeting a dai-dai wannan lokacin. Dan yana isowa da meeting suka fara. Kasancewar wayar na a desk ɗin gabansu ajiye akan idonsa kiran Nimrah ya shigo. Dan ɓaro-ɓaro Little Shadow ya bayyana a screen ɗin kamar yanda yay mata saving. Koda kiran farko ya yanke na biyu ne ya sake shigowa, sai kawai ya kife wayar dan dama a silent take kamar ko yaushe. Awa biyu suka ɗauka a ɗakin meeting ɗin, bayan kuma ya fito ba office ɗinsa ya koma ba na shugaban ƙasa ya shiga. Anan ma ya ɗauki kusan mintuna talatin. Sai kusan sha ɗaya da rabi ya ƙarasa nashi office ɗin dake gyare tsaff, ga uban ƙamshi mai ratsa zuciya da sanyin ac da ba'a cika ba. Ya ɗauki wayar kenan akai knocking kuma........✍️