
Post
Kida a ruwa Book 3 page 60
..... let him know, he will go. He said in a low voice. "Even the delegation from Garno State, sir?" Dadah raised his eyes that had changed color a little, his face was slightly pinched with a warning expression in it. "Did I stutter?" EA quickly shook his head and bowed. "No, sir. I'll handle it." "Make sure you do". "Okay Sir, I will drink ALLAH". After that, he bowed a little and turned to leave.... Then she stood up and came out in her department completely. Rayhana just found her in the general living room eating, she didn't want to pay attention to me at all, but to her surprise, she heard Rayhana say, "I'm a bride, I'm sleeping". She stopped for a moment, before she turned and looked. Rayhana smiled at her and repeated the greeting. It made Nimrah laugh, but she didn't just say to her, "You woke up safe". Then she continued her journey. Harara Rayhana followed her behind him, touching her lips. In her mind, she says that she is (The bride for one day. The bridegroom is the bride and I am packing the things for the trip. Little by little, you will come to my hand). Rayhana's surprise could not leave Nimrah's heart until she entered the department.....
60
.........Yasan EA ɗinsa ne, sai ko gashi ya shigo. Dadah bai ɗago ya kallesa ba har ya ƙaraso inda yake da faɗin, “Good Morning Sir”. Kai Dadah ya jinjina masa, sai kuma ya ɗan ɗago ido a karo na farko ya kallesa. Sanin halin ubangidan nasa da tsarinsa na son komai a nutse ya sashi ɗan rissinar da kai, cike da girmamawa ya furta, “Sir… the 1pm briefing has been confirmed,” ya ƙare faɗa a hankali. Dadah ya ɗan sake ɗago idanunsa yana kallonsa cikin nutsuwa. Sai kuma ya janye a lokaci guda ya jinjina kansa da ajiye wayar yana ƙoƙarin kunna desktop ɗin gabansa. Idanunsa akan screen ɗin ya furta “And the files I requested?” “They’re ready, sir. I’ve arranged them according to priority.” Shiru na ɗan lokaci ne ya biyo baya. Sai can Dadah ya ɗan furzar da iska kaɗan. A taƙaice ya furta, “Good.” sai kuma ya ɗan dakata, kafin cikin umarni ya cigaba faɗin, “Cancel every non-essential visit for today.” EA ɗin ya ɗan ɗago kai kaɗan, kamar yana son tabbatarwa dan yasan akwai zaman da tun jiya ya sanar masa, gashi zai yi tafiya. Cikin sake sauke murya ya ce. “Even the delegation from Garno State, sir?” Dadah ya ɗago idanunsa da suka sauya launi kaɗan, fuskarsa na ɗan tsukewa da yanayin gargaɗi a ciki. “Did I stutter?” Da sauri EA ya girgiza kai yana sunkuyarwa. “No, sir. I’ll handle it.” “Make sure you do”. “Okay Sir, in sha ALLAH”. Daga haka ya ɗan sake risinawar girmamawa sannan ya juya ya fita....
((((((@))))))))
Cikin mamaki Nimrah ta sake kallon wayarta a karo na babu adadi. Sai kuma ta miƙe ta fito a sashen nata gaba ɗaya. Rayhana kawai ta samu a General falo tana cin abinci, ko kaɗan batai niyyar kulata ba, amma a mamakinta sai jitai Rayhana ɗin ta ce, “Amarya ina kwana”. Tsayawa ta ɗan yi na sakani, kafin ta juyo ta kalleta. Rayhana tai mata murmushi da sake maimaita mata gaisuwar. Abin ma sai ya bama Nimrah dariya, amma batayi ba kawai tace mata, “Kin tashi lafiya”. Daga haka ta cigaba da tafiyarta. Harara Rayhana ta raka bayanta da shi tana taɓe baki. A ranta ko faɗi ta ke (Amaryar kwana ɗaya kenan. Ango na nanikema amarya ke naki na tattara kayan tafiya. Yarinya sannu a hankali zaki zo hannu na).
Mamakin Rayhana ya kasa barin zuciyar Nimrah har ta shiga sashen Dadah. Tun a falo ta fahimci baya nan, dan an kashe duk fitulu. Tai ɗan shiru na tunani, yanzu ta fahimci dalilin gaisuwar da Rayhana tai mata. A ranta tana raya (to kodai fushi yayi ya kirani ban ɗaga ba a farko?) ta kai hannu ta dafe kanta. Cikin damuwa ta sakko. Kiciɓus sukai da Feedoh ɗauke da basket. Dan haka ko kallon Rayhana batai ba suka wuce nata sashen Faddoh na tsokanarta da shaƙiyanci irin na ƙawaye. “Wai ya naga kamar kina a damuwa ne?”. “Feedoh, Dadah ne fa. Ya kirani ɗazun ina wanka ban ɗaga ba, na kira shi back, 2 times amma ya ƙi ɗagawa shima. Naje sashensa kuma baya nan. Ko fushi yayi?.” “A'a, to ke bakuyi sallama bane? Ai ya fita office tun ɗazun. Koda yake nama ji fa kamar su Mom na faɗin zai yi tafiya ne”. “Tafiya?”. “Kwarai kuwa, ke baki sani ba?”. Ƙasa magana Nimrah tayi, sai ma zuciyarta data fara gudu a ƙirji da sauri-sauri. Mi hakan ke nufi to? Da asuba fa ya ɗauki a ƙalla awa ɗaya da rabi a sashen nan, ko'a lokacin ai ya dace ya sanar mata zai yi tafiya. Ko kuma ma da zai tafin ya shigo ya tadata. Hakan na nufin bata da wani muhimmanci a wajensa? Yana kuma cigaba da mata kallon ƙaramar yarinya mara wayo.....? “Wai tunanin mi kike yi?”. Feedoh ta sake katse ta. Murmushi ta ƙirƙiro da girgiza kai, “Ba komai Feedoh, wani tunani na tafi ne. Ruƙayya taje sashen Mammah kuwa?”. “Bata je ba, itama naji su Mom na cewa kar bata da lafiya”. Nan take hankalin Nimrah ya tashi, ta miƙe da sauri tana faɗin, “Na shiga uku Buddy ba lafiya. Feedoh taso muje mu dubata”. “A'a ba yanzu ba, mu bari sai anjima. Dan yanzu can na fara zuwa nakai abinci. Uncle na nan kuma yace min tana barci doctor ya saka mata drip”. “Na shiga uku wai miya sameta haka? Bayan jiya lafiya muka rabu”. Yanzun kam dariya Feedoh ta ɗanyi. Cikin ƙasa da murya ta ce, “Ke inaga fa Uncle ne ya angwance. Amma banda tabbas, naga dai su Mom na ƙus-ƙus da dariya. Kinga ko idan ba wannan ba ai bazasu ma ciwo dariya ba ko”. Murmurshi Nimrah ta saki mai yalwa a karo na farko. Ta ce, “Oh ni Naja'atu Buddy an girma. Amma Uncle ya iya tsiya.” Dariya sosai Feedo ta sanya. Daga haka Nimrah ta saki jiki suna hirar su. Duk da dai can ƙasan zuciyarta hankalinta nakan Dadah da jin zafin abinda yay mata musamman batun tafiyar nan wata ƙasa batare da yi mata sallama ba. Har tana ganin maybe ma ya wuce shiyyasa data kira wayar ba'a ɗaga ba....
Da takaicin Dadah Nimrah ta yini, dan ma ana yin sallar azhar baƙin gidan sukai ta shigowa. Kowa dai yana ƙara mata nasiha. Ga su Feedoh kuma abokan shargalle. Dan wajen 2 itama Bintu tazo, hakama Mu'azz da Imam da Khalifa da suka wuto nan daga makaranta. Suna son zuwa sashen Ruƙayya amma ba dama. Dan sunje sashen Uncle Bilal bayan la'asar kamar yanda suka shirya zasu kira Nimrah ta fito a sace sai ga su Aunty Ummi, sune suka hana su. Hakan ko ya bama su Mu'azz haushi, suka koma sashen Nimrah suna ƙunƙuni. Harda tambayarta wai saboda mi aka hana su. Tace ita kam bata sani ba. Maybe Uncle Ammar ɗin ne ya hana. Daga nan ne kuma suka koma shaƙiyanci ma Uncle Ammar ɗin da gulmarsa, sai kuma aka zarce hira. Basu bar sashen ba sai gab da magriba. Feedoh da Bintu suka taya Nimrah ta gyara ko'ina, dan sunyi ciye-ciye a falon yay kaca-kaca. Suna cikin aikin akai kiran magriba...
>>>>>%<<<<<
Basa tsallake maganar Dadah a rayuwarsu. Dan haka yau duk suka shirya komawa gidajensu su duka. Tunda suma dai baƙin gidan kam tunda safe gobe zasu wuce. Gwaggo Khadijah ce kawai banda ita, bata jin daɗi su Ja'afar sukace ta bari sai an kaita asibiti tukunna. Tunda Dadah ya fita ɗazun suka sami Mammah da maganar ta hanashi wannan tafiya tashi. An kai masa Nimrah jiya yace kuma yau zai yi tafiya sai Nabeeha ta raina Nimrah ɗin ma ai. Mammah data tsaya tana kallonsu ta ce, “Ba kuna da number ɗinsa ba? Ku kira shi kawai”. Cikin waro ido Aunty Mommy ta ce, “Mammah mu kira shi fa kika ce?”. “Eh mana, ba ubanku bane, ni miye nawa”. Shiru sukai dan babu wanda ya sake magana daga nan. Sai dai sunata faman zumɓure-zumɓuren daya ma so saka Mammah dariya. Amma dai ta share su ta cigaba da sabgoginta gida cike da baƙi. Yanzu ma suna cikin shiri suna maganar, dan sun yanke abar Feedoh ta zauna da Nimrah ɗin har Dadah ya dawo. Sun ɗauki alwashin sai sun ɗora Nimrah a layin da in Dadah ya dawo sai ya rasa gane kansa. Shiyyasa zasu je siyo shiri nan da kwana biyu. Kira ne ya shigo wayar Mimi, sukai ɗan shiru ita kuma ta ɗauka tana dubawa. Yaya Imran ya bayana a screen ɗin. Sai da ta kalla su Mommy tace, “Yaya Imran ne” sannan ta ɗaga kafin suce komai. “Yaya Imran ina yini”. Ta faɗa cike da girmamawa. Ya amsa da, “Lafiya lau Mimi. Kun wuce gida ne?”. Ɗan jim tai dan tasan shida aminin nasa 5&6. Zata shuro ƙarya saboda gudun faɗa ya katseta. “Tunda kikai shiru nasan baku tafi ba. To aiko kar naji ance kun kwana gidan nan yau. Idan kina tare da wani koma gefe abu zaki yi min”. “To Yaya. Kayi haƙuri in sha ALLAHU yanzu zamu wuce wlhy”. “Idan ma baku wuce ba zan zo da bulala ai”. Murmushi tayi, tare da yima su Aunty Ummi alamar tana zuwa. “Yaya gani na fito”. “Yauwa kije sashen Haysam. Ki shirya ma Nimrah kaya bada yawa ba a ƙaramin bag. Ki sakata itama ta shirya kar ku ɓata lokaci zan jira ki idan kun gama. Kuma bance ki faɗa ma kowa ba”. Wani irin murmushi jin daɗi ne ya ratsa Mimi. Ta matse hannu a hankali tace, “Yes!” sai kuma ta kalla wayar da sauri. Ganin ya yanke kawai ta fara rawa. Kamar zata koma ta gumtsawa Auntys nata ta tuna gargaɗin ƙarshe. “Uhmm su Dadah manyan ƙasa. Naku ba irin nasu bane” ta faɗa tana dariya ita kaɗai. Su Nimrah na salla a bedroom ɗinta Mimi ta shigo. Bata bi takansu ba ta wuce wajen kayan Nimrah ɗin. Ƙaramin akwati a cikin na lefenta ta ɗauka. Ta kwashe kayan ciki ta zube a wardrobe ɗin. A lokacin ne suke idarwa. Kai tsaye tace Bintu da Feedoh su wuce sashen Mammah gata nan zuwa. Idanun Nimrah ya cika da hawaye tana kallonsu. Sai kuma ta juya ga Mimin. “Mom dan ALLAH ki barsu su kwana anan. Wlhy ba daɗi zaman ni kaɗai”. “Karki damu zasu dawo ai. Ku kuma ku wuce. Idan kunje kuce da su Aunty suyi haƙuri ina zuwa aiki Yaya Imran ya sani”. Su Feedoh na zumɓura baki suka wuce. Nimrah kam tuni ta fara sharar hawaye. Dama zuciyarta a cinkushe take da takaicin Dadah dauriya kawai take. Kasancewar su tare da ita kuma na mantar da ita. Ga su Mu'azz sunce yanzu zasu dawo zasu sayo musu ice-cream ne........✍️