Kenza eBookz
Cover art for SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 11

Post

SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 11

..... she was shouting, or she came out and showed Mamman that she saw him. She was silent again, thinking all this time, what has Mamman been doing? So what is his reason for doing this? What did her brother do to him? That's what the shield did to him, or what does that mean? She sat down and was silent, thinking about what to tell Nadiya, all that happened was her silence, she was not aware of any kind of warning or advice that Yaya did not give her. She didn't know that she was deep and she was thinking for a long time until she heard Nadiya say "Alina, you saw your brother silently until half past eleven. Did he think you didn't come back?" Alina raised her head and looked at her. But she was silent and did not say a word. Nadiya went back to her room, took her phone, went to call Yaya's phone, but he didn't pick up the phone, she made a missed call, it was silent for five minutes, but there was no answer. She put down the phone slowly and was silent, studying. Alina put down the phone and came into the room, put the phone down. She looked at how Alina's body was cold and said, "Aren't you going to eat the food?" She bowed her head. "Well, come to bed, it's getting dark" Alina

Standalone post3,078 words

MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN.

SARA DA SASSAƘA... YOTA/002 AYSHERCOOL

Page 11

Aƙalla ta kai mintuna goma sha biyar a tsaye, ta kasa gaba ta kasa baya, fatanta da addurata Allah ya sanya bacci take yi, kuma duk abin nan da yake gudana mafarki ne ba gaskiya ba. Da kyar ta iya jan ƙafafuwanta ta shiga gida, tana jin yadda gumi yake ratsa ta ta ko ta ina. A tsakar gida ta tarar da Anty Nadiya, cikin yanayi na damuwa. Ta ce "Alina, ina Yayan?"

Alina ta girgiza kai ba tare da iya yin magana ba.

"To ai ke ya tafi ɗaukkowa daga makarantar fa, an ce gari babu lafiya, ba ki haɗu da shi a hanya ba?" Girgiza kai ta yi alamar a'a.

Nadiya ta ce "wataƙila saɓani ku ka yi, maybe yanzu zai dawo. Ga abincinki can, shi kuma wancan mutumin na aika masa abinci baya nan, idan ya dawo daga yawon ya zo ya aiko ya karɓa". Har Nadiya ta gama surutanta Alina bata tofa komai ba. Ta shiga ɗakinta jikinta a matuƙar sanyaye. Ta ajiye jakarta tana kallon tagar ɗakinta, ta din ga tuhumar kanta a kan dalilin da ya hana ta yi ihu, ko ta fito ta nuna wa Mamman ta gan shi. Ta sake yin shiru tana tunani tsawon wannan lokacin dama Mamman basaja yake yi? To mene ne dalilinsa na yin haka? Me Yayanta ya yi masa? Garkuwa ya yi da shi kenan, ko kuwa me hakan yake nufi?

Ta zauna ta yi shiru tana ta tufka da warwara tana tunanin me za ta gaya wa Nadiya, duk abin da ya faru ita ce sila, kasnatuwar babu irin gargaɗai da jan kunnen da Yaya bai yi mata ba.

Ba ta san ta yi zurfi kuma ta daɗe tana tunani ba sai da ta ji Nadiya ta ce "Alina, kin ga har sha ɗaya da rabi yayanki shiru. Ko tunaninsa ba ki dawo ba ne?"

Alina ta ɗaga kai ta kalle ta. Amma ta yi shiru ba ta ce uffan ba.

Nadiya ta koma ɗakinta, ta ɗauki wayarta, ta hau kiran wayar Yaya, sai dai shiru bai ɗaga wayar ba, ta yi missed call ya fi biyar shiru, amma shiru babu amsa. Ta sauke wayar a hankali ta yi shiru, tana nazari. Tana sauke wayar Alina ta shigo ɗakin, ta ajiye wayar. Ta kalli yadda jikin Alina ya yi sanyi ta ce "Ba za ki ci abincin ba?" Ta jinjina mata kai. "To zo ki kwanta dare ya fara yi" Alina ta nemi guri ta kwanta ta takure jikinta. Nadiya ta kashe musu fitila.

"Anty

"Na'am"

"To kwana za mu yi Yayan bai dawo ba?"

"Zai dawo yana nan lafiya in sha Allah, wataƙila ogansa ne ya neme shi da gaggawa"

Alina ba ta sake magana ba, kawai ta tuna lokacin da ta shigar wa Mamman ɗaki, cikin zafin nama ya ɗora pillow a kan wani abu da idan ba gizo Idanunta suka yi mata ba, tamkar bindiga ta gani, amma ta yi iya ƙoƙarinta gurin kawar da wannan tunanin a wannan lokacin. Ta sake tuna lokacin da ya je Asibiti, ita dai ta san tabbas ba gizo ba ne ba, zahiri ne abin ya faru, amma ya ce shi bai je ba. Kasancewar bacci ɓarawo ne, ba ta san lokacin da ya zo ya yi awon gaba da ita ba.

*****

Dare ya tsala, yayin da al'umma ke kwance su na hutawa, su Ramata na dokar daji su na tafiya, babu suturar kirki, wasu ƙafafuwansu babu takalma. Zaratan maza ɗauke da muggan makamai sun saka su a tsakiya. Wasu na gaba a kan babura, wasu na a bayansu, wasu kuma na biye da su a ƙafa, ɗauke da makamai masu ban tsoro. Rahama ba za ta iya ƙididdige adadin yawansu ba, tafiya suke ƙarƙshin hasken farin wata kawai. Ko ƙwaƙwƙwaran tari babu wadda take iya yi, saboda barazanar da mutanen suke yi musu. Rahama za ta iya cewa, bayan mutuwar Iro, wannan shi ne tashin hankali na biyu da ta gani a rayuwarta. Ta kalli jikinta ta kalli suturar da take jikinta, da za ta iya cewa banbancinta kaɗan da tsirara. Sai dai gara ta ta shigar da ta wasu. Tana jin yadda ƙayoyi ke huda mata ƙafa da abin da ma ba ta san mene ne ba, amma ta kasa cewa uffan. Ba za ta iya tantance adadin nisan tafiyar da suka yi ba, domin tuni ta ji ƙafafuwanta na neman bijirewa ɗaukarta saboda wahala da gajiya. Har gari ya waye ya yi tarwai tafiya suke yi tamkar fatake, maƙogwaronta ya bushe kamar zai tsatstsage. Gazawa jikinta ya nemi yi, a dole ta ja ta tsaya, ta yi ruku'u tana mayar da numfashi. "Ke! Uban waye ya ce ki tsaya, tashi ki wuce" Wani daga cikin su ya daka mata tsawa. "Ruwa" Ta furta cikin sassanyar muryarta. "A gidan uban wa ki ka ga ruwa a nan? Za ki tashi ko sai na saka bindiga na harbe ki?" Ko gezau ba ta yi ba, sai a lokacin suka haska fitila, suka lura da yadda ƙafafuwanta suke ta zubar da jini.

"Kai ku tsaya a nan. Bari mu kira Sadauki, idan babu matsala a yada zango su huta, duk sun fara galabaita"

Ya daddana wayarsa ya saka a kunnensa. "Amanar Kacalla"

"Bani labari"

"Yaran nan sun galabaita, amma mun wuce mararraba, mu na iya yada zango su huta?"

"Eh awa guda kawai, daga haka kar ku sake tsayawa sai kun dangana da inda na ce"

"An gama"

Yana gama wayar, saƙo ya shigo wayar, kasancewar a lokacin ya kunna wayar. Miƙewa ya yi da sauri bayan karanta saƙon.

***** Ba tare da sanin dalili ba ta farka daga bacci a sukwane, ta tashi zuciyarta sai bugun tara-tara take yi. Ta duba wayarta ta ga ƙarfe uku na dare. Sannu a hankali ta sauka ƙasan bene, ta buɗe ɗakin yaranta mata, ta gan su a kwance kowacce a kan gadonta tana bacci. Ta zagaya ta fita falo, ta buɗe ƙofa ta nufi boys quarter's. Ta tarar da Amir shi ma yana bacci. Sai dai ta ji jikinta ya ci gaba da rawa, ta ɗaukko wayarta ta nemo lambar Ammar, ta hau kiransa. "Hello Ummi"

"Me ka ke yi haryanzu ba ka yi bacci ba?"

Ya yi dariya ya ce "Hajjaju ni da nake gurin aiki, ai ke zan tambaya meyasa ba ki yi bacci ba"

"Dan ubanka ina tambayarka kana tamabayata?"

"Ummi aiki nake yi"

"To kana ina?"

"Mun je wani aiki ne, lafiya dai?"

Cikin dakiya take ƙoƙarin ɓoye damuwarta ta ce "Kana gida ne, ko kuma sun tura ku dawa?"

"Ummi wai lafiya kuwa? Ina lafiya fa wani aiki dai muke yi, ina tare da Mega, mun je aiki ne"

"Shikenan Allah ya tsare" Ta katse wayar ta nufi cikin gidan. Sai dai ba ta bari ta koma bacci ba, ta yi alwala ta tayar da salla.

*****

"Alina" Nadiya ta kira sunanta.

Alina ta ɗago manyan idanunta, ta dubi Nadiya.

"Ki daure ki sayo mana buredi a gurin Mamman, ki karya" Ta jinjina kai ta karɓi kuɗin, ta fita. Sai dai kantin a kulle, haka ma shagonsa. Alina ta nemi guri ta zauna ta yi shiru, har sai da ta gaji da zama, sannan ta tashi ta koma gida, ta ce wa Nadiya baya nan.

Duk yadda Nadiya ta so mazewa ta kasa, ta fita ta ƙwanƙwasawa maƙwabcinsu, ta sanar masa da halin da ake ciki.

Alhaji Sadi ya ce "Amma da mamaki, ni jiya sai bayan na dawo ake ce mini, wai yanayin unguwar kamar babu lafiya, an ga wasu mutane na ta kaiwa su na komowa, ba a san suwaye ba. An kuma sanar da 'yan sanda ba su ce komai ba. Amma bari na tuntuɓi Alhaji Sadi. Ba a jima ba, maƙwabtan da suka rage ba su fita ba duk su ka tattaru. Har su ka fara yi wa Nadiya faɗan, dan meyasa ba ta sanar tun a daren jiya ba. Nan aka fara bin diddigin abin da ya faru. Duk wani bincike da mutanen layin suka yi, babu wani gamsashen bayani, a kan haƙiƙanin abin da ya faru daren jiyan, sai cewar kawai dai an fuskanci yiwuwar samun tashin hankali a lokacin. Suka dangana har ga gurin Jami'an tsaro, sai dai 'yan sanda suka ce, babu wani abu mai kama da tashin hankali da ya faru a unguwar, kawai dai mutanen unguwar sun tayar da hankalinsu ne, amma batun ɓatan Yayan Alina za su duƙufa bincike a kai.

Alina kuwa gaba ɗaya a kwana ɗayan nan, ta yi zuru-zuru, tashin hankali ya addabe ta, ta kasa cin abinci kukan ma kuma ta kasa, ga shi ta kasa gaya wa kowa, balle ta samu sassauci. Babbar damuwarta duk ta san laifin nata ne, ita ta ƙanƙame Mamman ta janyo shi kusa da su. Daga ita har Nadiya wunin damuwa suka yi da tashin hankali. Maƙwabta suka din ga shigowa yi musu jaje, tare da fatan Allah ya bayyana Ismail.

*****

Ji ya yi an watsa masa ruwa mai zafi a jikinsa. Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, ya buɗe idanunsa a hankali. Dishi-dishi yake gani. Amma ya tattara nutsuwarsa har sai da ganinsa ya zama clear, sannan ya ɗago kansa a hankali yana ƙarewa gurin kallo. Ya motsa ya ji shi a ɗaure tamau, tamkar huhun goro. Ya sauke idanunsa a cikin na su.

"Ka farko kenan?"

Ya yi shiru yana ƙare masa kallo ba tare da ya yi magana ba.

"Ina fatan zaka sauƙaƙa mana, kuma sauƙaƙa wa kanka, gurin amsa dukkanin abin da zamu tambaye ka, ko mu nema daga gare ka"

Ya yi murmushi sannan ya ɗago kansa ya ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya, ya tsayar da kallonsa a kan Mamman,ya ci gaba da kallonsa ba tare da ya yi magana ba. Kawai ya sunkuyar da kai yana murmushi.

*****

Su na kitchen su na aikace-aikacen su, suka jiyo saukkowar Ummi daga kan bene, tamkar za ta ruso benen, cikin rige-rige, suka fito daga kitchen ɗin su na jiran jin ba'asin saukkowarta daga bene da gudu haka. "Ummi lafiya kuwa?"

"Safiyya, Ruƙayya"

"Ruƙayya meyafaru da Rukayyan?"

"Wai 'yan bindiga sun shiga har makarantar sun tafi da yaranmu. Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Ku taso mini Amir ya ɗaukko mota mu tafi"

Na'ima ce ta ƙarasa ta riƙe Ummi, ganin yadda duk ta rikice, ta ce 'Ummi ya za a yi a je makaranta a sace ɗalibai, a ina ki ka taɓa jin an yi haka?"

"Ga shi a radiyo ina ji, an sace ɗalibai hamsin a makarantar su Ruƙayya"

Safiyya ta ce "Ummi dan zatin Allah ki kwantar da hankalinki, kin san halin da ki ke ciki, ai babu wanda ya tabattar da an sace har da Rukayya ɗalibai sun kusa dubu a makarantar su. Kuma ki bari mu tabattar"

"Wane tabattarwa kuma? Radio za su yi ƙarya ne?"

"To zauna, bari a taso Amir ɗin"

Safiyya ta yi gaba tana kiran wayar Ammar.

*****

PRESIDENTIAL RESIDENT

Faruk Kankiya ne yake kaiwa yana komowa. Jikinsa har tsuma yake yi.

"Your excellency, dan Allah ka kwantar da hankalinka, komai zai zo da sauƙi"

Cikin ɗaga murya ya ce "Halilu when? Abubuwa na taɓarɓarewa za a ce komai zai zo ƙarshe ta yaya? A mulkina a shiga har cikin makaranta, a shiga makwancin ɗalibai, a kwashe yara mata 'yan makaranta. Kuma ka ce na kwantar da hankalina how? How Halilu? Gaya mini kaf tarihin duniya a inda aka taɓa haka. Sai a zamanin mulkina. Ko yaƙi ake yi ba a taɓa mata da ƙanan yara. Amma ni matan aka kaiwa farmaki. A mulkina wannan wane irin baƙin tarihi ne?"

Halilu ya yi shiru yana sunkuyar da kai, cike da tsoro da razani.

"Nan da mintuna talatin, a tattara masu riƙe da muƙaman tsaro a ƙasar nan, idan ba za su iya ba, su ajiye mini aikina"

Halilu ya jinjina kai ya fita yana jin tamkar ya ƙwato daga bakin kura da kyar.

**** Taimama suka din ga yi su na kallon duk inda ta kama su yi salla. Tsananin baƙin ciki da damuwa ya sanya Rahama kasa zub da hawaye. Wanda suke da shigar kirki a cikin su kaɗan ne, ga su a zube a dokar daji a gaban mutanen da ba muharramansu ba. "Anya ba daga rayuwata ba ne babu sa'a?" Ramata ta kalli kanta, tana ƙanƙame jikinta, zuciyarta na wani irin zafi. 'yan yaran cikinsu da basu wuce Jss 1 ba su na ta 'yan koke-koke ƙasa-ƙasa. "Yaya Baffa zai ji, idan ya samu labarin an sace ni?" Ta sunkuyar da kanta tana jin wata irin fargaba na ratsa ta.

****

Shiru ta yi tana kallon wayar hannunta, ta rasa abin da ma yake yi mata daɗi. Cikin sauri ta janyo ɗaya wayartata, ta shiga shafinta na sada zumunta ta wallafa dogon rubutu. Duk da iya ƙoƙarin da gwamanti take yi gurin kawo ci gaban ilimi, mussaman a yankinmu da ilimin yake da yake fuskantar koma baya, mussaman ga 'ya'ya mata, hare-haren ta'addanci ya fara yawa, wanda hakan yana nuna gagarumin koma baya ga yankin. #Bring back our girls". Daga haka ta yi posting ta ajiye wayar. Sadam ne ya fito daga ɗakinsa yana faɗin "Ke Laila, kina ina? Yau kin yarda gwamantin taku ta gaza ko? Saboda abin kunya da Allah wadai, an je har cikin makaranta an sace ɗalibai, mummunan abu na farko a tarihin ƙasar nan, da ya faru a gwamantinku"

"Kai kuma murna ka ke yi da hakan kenan? Gwamnati fa ba ta mutum ɗaya ba ce, ta al'umma ce kuma kowane ɓangare yana da wakili...

Saddam ya ce "Ba wani gwamanatinku ta gaza kawai malama, yanzu zan hau na wallafa rubutu a facebook na yi tagging ɗinki kuma an yi abin kunya"

Mama ce ta ja tsaki, bayan ta idar da sallar walha da kyar, saboda surutunsu, da musun da suke ta , sai rafkanuwa take yi. Kofin silva ta jefawa Sadam ta hau shi da faɗa. "Wallahi Mama na fuskanci kema yar adawa ce, duk lokacin da muke maganar siyasa da yarinyar nan sai ki goya mata baya, ki din ga kora ta. Da alama ke ma tana shaƙa miki tsari ne, aishikenan na bar muku gidan ma amma dai gwamantinku ta gaza Yasin" Mama ta kalle ta ta ce "Kar ki kula shi, ƙyale shi tun da bai san ƙaddara ba"

***** Sanye suke da uniform su huɗu a office ɗin, sai kuma ƙarami da babban ministan tsaro, sai kuma President Faruk Kankiya.

"Wannan tattaunawar da muka yi, ta zamo ta sirri, bana buƙatar manema labarai su ma san me muka tattauna. Kwanaki bakwai kawai na baku, ku nemo inda ɗaliban nan suke a dawo da su, kuma bana buƙatar ko ƙwarzane ya samu ɗaliba ɗaya. A yi ƙoƙari a tabattar da lafiyar wanda ba a ɗauka ba, a damƙa su a hannun iyayensu. Kwanaki bakwai kawai na baku. Akasin haka za ku ajiye mini muƙamai na na bawa wasu".

General Jalal ya ɗan yi gyaran murya ya ce "Mr. President tabbas wannan kuskurenmu ne, zan iya cewa sakacinmu ne ma da har wannan al'amari ya faru. Amma mu na mai baka tabbacin da yardar Allah, yaran nan za su kuɓuta. Amma muna neman alfarmarka mako guda ya yi kaɗan...

A fusace ya ce "7days Lieutenant General Jalal, 7days kawai ku ke da shi, akasin haka ku ajiye mini muƙamaina"

"Ok sir" Haka suka tashi sumi-sumi suka fice daga ofishin.

Su na fita Barwa ya ciro wayarsa ya daddana. Ya kara a kunnensa.

"Jagora barka da wannan lokaci"

"Barkanmu dai Barwa, bamu labari"

"Shugaba fa ya ɗauki zafi ba kaɗan ba, kwana bakwai kawai ya bayar a nemo yaran nan, ko su ajiye masa muƙamansa ciki har da ni"

Ya kwashe da dariya ya ce "Ƙaryar banza ce ƙiba a kunne, shi ya isa ma? Zan yi magana da Boss Ɓagwai, tun da shi ne God father ɗinsa, dole ya janye wannan maganar. Kana ganin yadda muka fara raba kan ƙasar ko? To ba a yi komai ba ma. Sai ya tattara hankalinsa a kan yaran can, za mu sake ɓallo masa ruwa, kai dai ku ci gaba da bin abin da aka tsara. Ka kwantar da hankalinka yara dai ba za su fito yanzu ba, ka zuba ido...

*****

Tuni labarin sace ɗaliban makaranta mata, kimanin hamsin ya cika gidajen rediyo da kafafen watsa labarai da na sada zumunta na ciki da wajen ƙasa. Duk inda ka buɗe babu abin da ake yi sai maganar, saboda abu ne da bai taɓa faruwa ba a tarihi.

Sai da su Rahama suka kwana guda curr, babu ko ruwa a cikin su, a kwana na biyu, aka bi su da ruwa ɗaya mutum biyu, sai buredi mai yanka-yanka kowa guda biyu. Ƙafafuwan Rahama suka kumbura sosai saboda azabar tafiyar ƙafa da suka yi. Inda suke daji ne sosai da sosai, sai dai saboda tsabar surƙuƙinsa ko rana ta take, bata wadatar dajin da wadattacen haske saboda tarin dogwayen bishiyu.

**** Alina ta yi wata irin mummunar rama, ta yi zuru-zuru saboda azabar tsoro da kuma tashin hankali. Tun safe Nadiya ta fita ta koma gurin jami'an tsaro, domin jin ko akwai wani labari. Alina na zaune ta yi zuru a tsakar gida, ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofar gidan su. Jiki a sanyaye ta sanya hula a kanta, ba tare da ta tambayi waye ba, ta buɗe ƙofar gidan. Turus ta yi bayan tozali da fuskar Mamman, kawai ta hau bin fuskarsa da kallo. Fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "'yan mata, abin da ya faru kenan? Na je gida duba jikin Innata, na dawo Alhaji yake gaya mini an nemi Yaya Ismail an rasa" Tsuruu ta yi da ido tana kallonsa, ta ma rasa me za ta ce masa gaba ɗaya.

"Ya na ga kina kallona a haka?"

Ta sunkuyar da kanta, sai a lokacin hawayen da ta gaza zubarwa ta samu damar zubar da su, zuciyarta na wani irin ƙuna da tafasa.

Cikin tausasa murya ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah za a gan shi, an je gurin 'yan sanda an sanar musu?" Ta jinjina masa kai kawai.

"Ki yi haƙuri dan Allah, ki daina kukan nan haka" Ta ɗaga fuskarta a hankali tana kallon idanunsa masu bata tsoro, a yau ta samu kallonsu da cikakken ƙwarin gwiwa, amma ta gaza furta komai. Sai dai da ta ƙara matsawa kanta ta fuskanci akwai wata ɓoyayyiyar fuska a bayan wannan fuskar da yake mu'amalantarta da ita...

Ayshercool 08081012143

1k ne a telegram 0069685771 Aisha Adam stanbic