Kenza eBookz
Cover art for SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 10

Post

SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 10

.....I am listening to you, don't you dare to break our agreement. And you said that you will take care of this part of the frog, if people are killed for me, or if someone is caught, I will rape the children of the few, to the extent that it is not necessary for me to eat. And this contract, whether it's life or death, make sure you keep your part. If you have anything, or if you are looking for me, contact Sadauki... Kit turned off his phone. ***** "Dear" Ismail called Nadiya. "Dear" "My body is giving me something" She said in a confused way "What is that something?" "Now I'm wondering who paid for Alina Hospital with my name, this proves to me that there is something on the ground" Nadiya put down the folded clothes she was doing, looked at him and said "I am also confused by this, but I don't think there is anyone who wants to follow us, because why would we be followed, I wonder if there was a mistake" He laughed and said "Mistake? It is not a mistake. Alina is going down, we will leave this town, I also saw how she concentrated on reciting the Qur'an. I just think there is a problem with our stay here."

Standalone post4,320 words

SARA DA SASSAƘA... YOTA 002 P10 AYSHERCOOL

Kangiwa ya yi shiru yana lissafa maganganun a cikin zuciyarsa.

Ya jinjina kai a hankali ya ce "Shikenan, zan je na yi shawara"

"Ina saurarenka"

Kangiwa ya tashi sumi-sumi ya fice.

Ya zuba lemo a kofin gabansa, ya ɗago kofin ya kai bakinsa yana zuƙa a hankali, yana jujjuya lemon a kofin yana kallon katafariyar talabijin din da ke cikin ɗakin.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya ɗauke ta a gefensa, ya kalli lambar bai santa ba, ya dai ɗaga ya kai kunnensa ya yi shiru bai yi magana ba. Jin an yi shiru ya sanya shi cewa "Waye a kan layi?"

"Kacalla Sumale"

Da sauri ya ajiye kofin hannunsa ya ce "Yaya ake ciki ne? Mu na ta nemanka a waya ba mu samu ba, kai fa muke jira"

"Ba na gaggawa a aikina, yaƙin sunƙuru ka ce a yi, dan haka kar ka shigar mini aiki." Cikin mamaki mutumin ya buɗe baki, jin yadda baƙauyen ɗan ta'adda yake yi masa magana gatse-gatse.

"Ba zan ci gaba da ƙaddamar da hari ko ta ina ba, nima aikina lissafi nake yi. Na kira ka ne na jaddada maka na kuma ja maka kunne, kar ka kuskura ka saɓa yarjejeniyar mu. Kuma ka ce za ka kula da ɓangaren kwaɗin nan, idan aka kashe mini mutane, ko aka kama wani zan yi fyaɗar 'ya'yan kaɗanya ne, har iyakar da bai kamata ba sai na ci. Kuma wannan kwantiragin, ko a mutu ko a yi rai ne, ka tabattar ka kula da ɓangarenka. Idan da wani abu, ko kana nema na, ka tuntuɓi Sadauki... Ƙit ya kashe wayarsa.

*****

"Masoyiyya" Ismail ya kira Nadiya.

"Masoyi"

"Jikina yana bani wani abu"

Cikin rashin fahimta ta ce "Wani abu me kenan?"

"Haryanzu ina mamakin wanda ya biya kuɗin Asibitin Alina kuma da sunana, wannan ya tabattar mini da akwai wani abu a ƙasa"

Nadiya ta ajiye ninkin kayan da take yi, ta dube shi ta ce "Nima dai abin ya ɗaure mini kai, sai dai bana tunanin akwai wanda zai din ga bibiyarmu, saboda me ma to za a bibiye mu, ni nafi tunanin ko mistake aka samu"

Ya yi dariya ya ce "Mistake? Ba kuskure ba ne, wani abu ake ƙoƙarin gaya mini da hakan. Ina tunanin Alina na yin sauka, zamu bar garin nan, shi ma dan na ga yadda ta ƙallaffa ranta a kan saukar Alqur'anin ne. Kawai ina jin akwai matsala zamanmu a nan"

Nadiya ta ce "Amma duk shekarun da muka yi, ba a samu matsala ba, sai a wannan karon? Ina zamu koma?"

Ya ce "Alina, Saboda Alina dole mu bar garin nan, da daga ni sai ke ne, babu inda za mu je, tun da bamu takawa kowa ba, ba kuma mu zubarwa kowa ba a garin nan. Amma ba na son duk wani abu da zai kawowa ƙwaƙwalwarta cikas, kin san me nake nufi ai"

Nadiya ta numfasa tare da sauke numfashi.

Ya sake numfasawa ya ce "Wai me mutuniyar ta saƙa ne, da ulun da ta addaba mini sai na sayo mata?"

"Ina na san mata, ka san idan ta ga dama ta yi saƙar ta sayar, ko ta kyautar. Dan kai ta gado a ungo"

Ya yi guntuwar dariya ya ce "Ta saƙa wa Mamman hula ta ba shi, ya saka ta yaje masallaci da ita. Abin da nake gudu ya faru, amma zan ɗau mataki na ƙarshe a kai"

Da sauri Nadiya ta ce "A'a masoyi, kar ka...

"Shhhh" Ya katse ta yana zare mata ido, tare da tsuke fuska tamkar bai san yadda ake dariya ba.

*****

Daga nesa kaɗan yake tsaye, yana hango ƙofar gidan Malam Ɗayyabu, da rumfar almajiransa aka shimfiɗa tabarmi ake zaman makokin rasuwarsa. Duk wanda yakamata ya tambaya, da binciken da yakmata ya yi, amma babu wani gamsashen dalilin rasuwar malamin, kowa yana faɗin ya kwanta bacci lafiya kalau, aka wayi gari da gawarsa.!

Alina ce a tsaye, hannunta riƙe da takalmanta na makaranta, tana tsaye a bakin shagon yana ta sallamar mutane. Ya yi ƙoƙarin sallamarta, amma ta ce masa ya gama tukuna.

Kasancewar yamma ce, ana ta zuwa sayayya.

"Nifa na gaji da tsayuwa" Ta yi maganar tana tsuke fuska.

"To ai ke ki ka ce na sallame su, bari na ƙarasa ranki ya daɗe"

Ya sallami kowa, ya fito yana gyara zaman hularsa da ta saƙa masa. Ya saka hannu zai karɓi takalman, ta janye abin ta, ta ɓoye a bayanta.

"Meyafaru kuma?" Ya yi maganar yana kallon ta.

Ta harare shi, ta kawar da kanta gefe.

"Subhanallah me na yi?"

"Ka sallami kowa ka ƙi kula ni, kuma kana sallamar su, kana yin murmushi" Ta ƙarasa maganar tana kawar da kanta gefe fuskarta ɗauke da damuwa.

Ya yi dariya ya ce "Ni ne nake murmushin? Rigima dai ki ke ji, amma ban da ke kin ga ina yi wa wani murmushi? Ai ba na dariya murmushin ma ke kawai nake yi wa"

Ta ɗago kanta suka yi ido huɗu, kawai ta hau dariya, wanda hakan ya sanya shi ma ya yi guntuwar dariyar.

"Ɗan albarka"

"Na'am 'yar ƙwalisa"

"Yaushe za ka cire gashin nan na fuskarka ne? Ina son na ga fuskarka sosai da sosai"

Mamman ya shafa fuskarsa ya ce "Yanzu ba kya ganin fuskartawa?"

"Eh mana, gashi ya fi yawa, idan ka aske sai ka fi kyau"

Ya jinjina kai ya ce "Ai abin da Mumsy take so shi nake so, zan aske ki ganni sosai"

Ta kalle shi ta ce "Mumsy, amma dai Mamman ka yi karatun boko?"

Ya girgiza kai ya ce "Ai ba sai mutum yaje boko ba zai san wani abin ba, amma bari na din ga ce miki Inna"

"Ni wallahi ba Inna ba ce" Ta yi maganar tana dariya. Ya karɓi takalmanta, tana zaune ya goge su ya yi musu mai.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya ciro wayar ya kalla, ya kalle ta sannan ya ɗaga ya yi sallama.

Ba ta san me ake ce masa a wayar ba, ta ɗaga takalminta tana kallo, ta ga ya sauke wayar a hankali, fuskarsa babu walwala.

"Ya dai meyafaru? Ko jikin Innar ne?"

Ya girgiza kai ya ce "Maƙwabtan ƙauyenmu ne, aka yi rikici da manoma, da maharba, an karkashe mutane"

Cikin razana ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Ubangiji Allah ya taƙaita. Ko za ka je gidan to ka gani?"

Jiki a sanyaye ya ce "Sai abin da Allah ya yi"

"A'a gara ka je, irin wannan kuskuren Yaya ya yi. Ya ce mu garinmu rikicin manoma da makiyaya ake yi, ba su ɗau abin serious ba, sai da ya yi yawan da muka rasa iyayenmu, kuma aka kori wanda suka rage daga garin. Shi ne su suka taho nan, ya ce mukaɗai muka rage a gidanmu. Kafin mu zo nan a gidan su Antynmu muka zauna, har ya aure ta, ita ma aka yi ta rikici a garinsu, aka kashe musu yan uwa muka taho nan. Duk an ƙarar da danginmu, daga Allah sai yaya muke da shi." Ta yi maganar tana sanya tafukan hannayenta, ta rufe fuskarta tana fashewa da matsanancin kuka. Ya yi shiru yana nazarinta, ya jinjina kai, sannan ya yi ƙasa da muryarsa. "Ki yi haƙuri 'yan mata, bayan yaya, gani kuma, in sha Allah zan kula da ke, idan yaya ya bani cikakkiyar dama, zan ba ki kulawa fiye da yadda ya baki. Amma ban san meyasa ba ya so na ba"

Ta share hawayenta ta ce "Ba sonka ne ba ya yi ba, baya son kowa ya raɓe ni ne, saboda baya son ya rasa ni nima. Allah ya taƙaita muku yaya Mamman rashin ahali ba shi da daɗi"

"Ki daina kuka, ko ki na son ki saka ni kuka nima? Ki daina"

Ta jinjina masa kai.

"Ba ki ga hulata ba ne?"

Ta yi murmushi ta ce "Na gani, ta yi maka kyau sosai da sosai"

Ya tashi tsaye ya ɗaukko biro da takarda, ya yi rubutu a jiki, ya miƙa mata.

"Wai a ina ka iya rubutu?"

"Koya na yi" Ya ƙarasa maganar yana damƙa mata takardar.

Ta buɗe takardar tana kallo, ta ɗaga idonta ta kalle shi, ta ga ya tsare ta da ido. Kawai ta tashi tsaye tana murmushi, ta kwashi takalmanta ta yi waje. Ya bi bayanta da kallo yana murmushi. Sai da ta ɓacewa ganinsa sannan ya tashi ya shiga cikin kantin, ya ɗaukko wata wayar daban, ya danna wasu lambobi, ya saka a kunnensa.

A ƙofar gida ta tarar da Yaya a ƙofar gida a tsaye.

"Wankin takalmin ne sai yanzu?" Alina ta yi shiru tana sunkuyar da kai. Bai ce mata komai ba, ya yi gaba ya bar ta.

*****

Ana ta jarrabawa, saura guda ɗaya a kammala, Rahama na ta shirin gida. Bayan sun dawo daga night pref. Ta je ta yi wanka, ta shafa alamun ɗin ta, ta yi shirin kwanciya bacci. Tana jin Ruƙayya na ce mata, ta taso su ci abincin dare, amma ta ce ta ƙoshi, saboda wani irin bacci da take ji yau. Dogon wandon skin tied ta saka, sai vest doguwa har gwiwa, sai da ta hau kan gadonta, sannan ta cire hijjabinta ta kwanta, kasancewar lokacin yanayin na zafi ne, garin da zafi sosai.

Duk da tana jin bacci, ta janyo littafinta a jakarta, ta kunna fitilarta tana haskawa.

Tarihin gwagwarmayar karɓar 'yancin take karantawa. Gudunmawar da su Sir Ahmadu bello Dr. Nnamdi Azikiwe Chief obafemi owolowo Sir Abubakar tafawa ɓalewa suka bayar gurin karɓar wa ƙasa 'yancin kai.

Yanayin yadda mulki ya fara gudana, a wancan shekarun. Yanayin yadda sir Abubakar tafawa ɓalewa, ya zama priministre na farko, yadda ya fara gudanar da mulkinsa. Gaba ɗaya ba dukiyar ƙasar ce a gabansu ba, ƙasar suka yi ƙoƙarin ginawa da dukkanin karfinsu. Sai dai kash an yi juyin mulki a alif dubu ɗaya da ɗari tara da sittin da shida 1996 a sha biyar ga watan January. Juyin mulkin da wasu tawagar sojoji suka yi, ƙarƙashin jagorancin wani soja Major Chukuma Kaduna Nzeogwu, da wasu sojoji irin su Major Emanuel Ifeajuna. Inda aka je har gida aka tafi da shi. Daga bisani kuma aka tsinci gawarsa an kashe shi. Kisan Sir Abubakar tafawa ɓalewa ya kawo rikici a ƙasar a wancan lokacin. Daga nan General Aguyi-Ironsi ya karɓi mulkin ƙasar.

"Kash mtseww"

Ruƙayya na daga gadonta na ƙasan Rahama ta ce "Rahma lafiya kuwa?"

"History nake karantawa"

Rukayya ta yi dariya ta ce "Na zata kin daɗe da yin bacci ai. Ina mamakin abin da ya haɗa ɗalibar kimiyya da karance-karancen tarihi"

Rahama ta ce "Anty Ruƙayya zama guri ɗaya tsautsayi in ji kifi, kuma shi karance-karancen na karawa mutum ilimi. Tarihin mazan jiya nake karantawa yadda aka faro kafa ƙasar nan da samar mata 'yanci, da yadda aka fara mulki. Da an bi tafarkin da suka ɗora ƙasar tun da farko, da tuni mun fi haka ci gaba. But so sad an zubar da jini da yawa, an yi wa Sir Abubakar tafawa ɓalewa coup an kashe shi, despite all his efforts. Ba ki ji zuciyata ba" Ta ƙarasa maganar a ɗan shagwaɓe.

Rukayya ta saka dariya ta ce "Lallai ma Rahama, ita kanta Duniyar, da ƙasashen da suka kai inda suke yanzu da zubar da jini suka kafa ta. Ki ci gaba da karanta tarihin akwai abin da ya fi wanda aka yi masa ma"

Rahama ta yi guntun tsaki ta ce "Ni na karaya ma. To ina sojojin da suke tare da shi, suka bari har aka shiga aka ɗauke shi, aka tafi da shi aka kashe dan Allah?"

"Rahama kenan, ba a cin gari ai sai da ɗan gari. Galibin juyin mulki da ake yi, da sanin masu tsaronsu. Da Yaya na nan da kin sha bayani. Babu yadda a aikinsu ko kaɗan. Wataran zan haɗa ki da Yaya Ammar, ki sha labari"

Rahama ta ce "Daina bani labarin nan, zuciyata za ta karye da yawa. Sai da safe bari na yi azkar na kwanta" Ta yi maganar tana sauke ajiyar zuciya. Ta lumshe idanunta ta ɗaga hannayenta tana karanto addu'a kwanciya bacci.

*****

"Kangiwa, kana ganin yadda al'amura suke neman fin ƙarfinmu a ƙasar nan ko? Dama haka mulkin yake? Wallahi da na san haka yake ba zan yadda na karɓi ƙasar nan ba"

Kangiwa ya ce "Haba mr. President kar ka saka mu karaya mana, ka daure mu ga abin da za mu iya yi"

"An dabaibaye komai fa, yanzu kalli uban bashin da ake bin ƙasar nan. Trillion ɗari da hamsin da biyu da ɗigo huɗu fa"

"Mr. President, ƙasashen da suka ci gaba a duniya, ai duk da basussuka suka gina ƙasashensu"

"Amma Kangiwa su ƙasashensu suka gina, mu kuma wasu ne suke gina kansu. Ana maganar billion sau billions ne fa. Me da me aka yi a ƙasar na wannan uban kuɗin haka? Ga uban kuɗin ruwan da ake lafta mana. Yanzu babu ta inda za mu yi kasafin kuɗin shekara mai zuwa fa, babu komai a ƙasar nan, kai shaida ne da muka zo mulkin nan account ɗin ƙasar babu komai sai abin da ba a rasa ba"

Kangiwa ya jinjina kai cikin damuwa ya ce "Your excellency, bamu da wata mafita da ta wuce mu ranto kuɗin da zamu yi kasafin kuɗin baɗi"

"Kangiwa bashi again?"

"Mr. President bamu da wata mafita idan ba wannan ba, harajin da muke samu, ba zai samar mana da wannan kuɗin ba. Ga ɗanyen mai ya faɗi a kasuwar duniya, ga satar mai da ake yi da yake ƙara kassara mu. Ciyo bashin nan ne kawai mafitarmu"

Kankiya ya kashingiɗa yana cije lips ɗin sa, ya buɗe idanunsa da kyar ya kalli Kangiwa ya ce "Ina tausayin al'ummata. Amma kafin mu kai ga wannan gaɓar, zan zauna da shugabanin hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa. Dole a matsa tsofaffin wanda suka riƙe madafun iko, a matsa duk wanda aka kama da ha'inci, su dawo mana da dukiyar da suka sata."

Kangiwa ya yi murmushi ya ce "Wannan ma dabara ce, bari na je meeting ɗin da ka sanya ni, na ga lokaci ya yi"

Kankiya ya ce "To shikenan babu laifi"

Kangiwa na baro office ɗin, ya ja ya tsaya, ganin kiran Makama na shigo wayarsa.

Ya ɗaga yana faɗin "Ranka ya daɗe"

"Ka yi ganawar sirri da Kankiya, me ku ka tattauna?"

Kangiwa ya waiwaya bayansa, sannan ya ce "Na naɗi komai zan tura maka yanzu in sha Allah"

"Ina saurarenka"

*****

Alina zaune a ajinsu ta ajiye Alqur'aninta a gabanta ta zuba masa ido, sai murmushi take yi. Hafsa ta taɓa ta ta ce "Lafiya, murmushin me ki ka yi haka ne? Karatun kuwa ki ke yi?"

Alina ta girgiza kai ta ce "Wani abu na tuna"

"Yaya Mamman ɗin ne? Alina wai Mamman ɗin nan saurayinki ne? Soyayya ku ke yi? Ke kuwa me za ki yi da mai wankin takalmi, provision store ɗin ma fa ba nasa bane ba"

Alina ta ɓata fuska ta ce "Ce miki na yi mu na soyayya ne? Mutunci kawai muke yi"

"Kuma shi ne kullum sai kin yi zancensa, ko ya biyo ki Islamiyya ku tafi tare?"

"Wai ke Hafsa haka aka ce miki? Babba ne fa ya kusa Yayanmu"

Hafsa ta ce "Ke wallahi soyayya ku ke yi, kuma Yaya Ismail ya sani?"

Alina ta kwaɓe baki ta ce "Yaya ba ya son alaƙata da shi, amma yana yi mini kirki ne kawai"

Hafsa ta addabi Alina a kan lallai sai ta yarda soyayya suke yi da Mamman, amma Alina ta share ta.

Ko da aka tashi daga Islamiyya, su na fitowa daga gate ɗin makarantar, suka hango shi a tsaye hannunsa riƙe da wayarsa mai madannai. Hafsa ta taɓo Alina da ke sayen Agwalima, ta ce "Ga saurayinki can ya zo yana jiranki"

Alina ta ɗaga kai, ta gano Mamman yana nufo su. Hafsa ta ɗan ja baya, saboda tsoro yake ba ta.

"Nawa za a sayar mana da agwalumar nan gaba ɗaya" Ya yi maganar yana kashewa Alina ido. Sai da ta ɗan rikice, tare da kallon Hafsa ko ta ga abin da ya faru. Wani irin sassanyan ƙamshi ne yake tashi daga jikinsa, gaba ɗaya suturar jikinsa ba ta dace da ƙamshin turaren da yake yi ba. Idan ba ta manta ba, lokacin da yaje Asibiti irin wannan ƙamshin yake yi, amma ya ce mata shi ba shi ba ne ba.

"Inna mu saya duka ne?" Ya yi maganar yana karɓar ta hannunta da ta riƙe.

"Inna ko?" Ta yi maganar tana hararsa.

Ya yi murmushi ya ciro ɗari biyar a aljihunsa, ya miƙa wa mai agwaluma ya ce ya zuba mata ta 500.

"Ta ɗari biyar ai ta yi mini yawa, ta ɗari zai bani, kuma guda biyu manya"

Mamman ya ce "A ɗari za a baki biyu manya, ga wannan ƙara mata" Ya ƙara ciro ɗari biyar ya ba shi. Ta ɗaga kai za ta yi masa magana, amma ya harare ta, aka cika mata baƙar leda da Agwaluma suka tafi. Hafsa kamar ta bi Alina da gudu ta shaƙe ta, ta tsaya jiranta, ita kuma ta yi tafiyarta ta bar ta.

Ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro leda ya ce "Ungo" Ta saka hannu ta karɓa ta ce "Na waye?"

"Nawa ne" Ya yi maganar yana basarwa.

Alina ta ce "Yi haƙuri, nawa ne?"

"Mmm babu yawa"

"Na gode sosai da sosai Ɗan albarka, amma dan Allah ka daina kashe kuɗinka haka, ka ga...

"Kin raina kyautar almajiri ko?"

Da sauri ta girgiza kai ta ce "A'a ba haka ba ne, na gode sosai da sosai"

Har ƙofar gida ya raka ta, sannan ya juya ya tafi shago.

Ko da ta shiga gida, ta tarar da Nadiya kamar ita take jira ta ce "Kin dawo? Dama ke nake jira"

Alina ta ajiye kayan hannunta, ta ce "Meyafaru?"

"Leda za ki karɓo mini, da zan ƙulla tuwo. Sai da na gama tuƙawa na duba na ga bani da ita. Meye wannan a hannunki?"

Alina ta miƙa mata ledar tana faɗi. "Mamman ne ya saya mini agwaluma, sai kuma wannan ledar, da nake son ganin mene ne a ciki". Ta ƙarasa maganar tana zaro turare a cikin kwalinsa. Ta ce "Wow kin ji ƙamshinsa" Nadiya ta karɓi turaren, tana jujjuya shi tana kallon Alina. Ta ce "Amma kuwa ya yi ƙamshi sosai, je ki ki karɓo mini ledar" Alina ta karɓi kuɗin ta sake fita.

Ismail ya fito daga ɗaki ya ce "Yanzu kin yadda da abin da nake gaya miki ko?"

Nadiya ta jinjina kai, jikinta a sanyaye.

"Jibi in Allah ya kaimu, huɗun Asuba za mu bar garin nan,kar ki gaya mata ma, ba zan jira ta yi saukar ba ma" Nadiya ta jinjina masa kai. Tana jujjuya turare.

Wani matashi Alina ta hango a cikin shagon a tsaye, zai yi Mamman a tsaye, har ƙirar jikinsu iri ɗaya, sai dai ba ta taɓa ganinsa ba sai yau.

Ba ta damu da shi ba, ta shiga ta tsaya, sai dai ta ji ta a takure saboda mutumin.

Mamman ya ce "Na zo ne?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a leda baƙa ƙanana ta saka tuwo zaka bani"

Ya ce "Waye ya yi tuwon, ke ko Antynmu?"

"Anty ce, Yayanmu ya ce nata ya fi daɗi, ni jagwalgwalo nake yi"

"Ni kuma naki ya fi daɗi a bakina. Ya ki ka ga kyautar tawa, ta burge ki?"

Alina ta jinjina kai tana murmushi, ta karɓi ledar, ta miƙa masa kuɗi, ya ƙi karɓar kuɗin. Na cikin kantin na ta son ya kalle ta, amma ta juya masa baya ta fita.

Tana fita ya tuntsure da dariya ya ce "Allah wadaran naka ya yi expire"

Mamman ya tsuke fuska ya ce "Fita ka bar gurin nan ka tafi dan Allah"

"Ba zan tafi ba, ji wata riga a wuyanka kamar korarre, saboda tsabar mutuwa har ta fara gari za ta koma audugarta" Ya yi maganar yana ƙyaƙyata dariya"

Mamman ya ce "Dalla malam ware, dan Allah ka tafi"

"Kai wallahi ba zan tafi yanzu ba. Kai tsaya wai kai ne ka ke kashewa yarinya murya haka kana mata wani kallon iskanci anya kuwa kai ne?"

Mamman ya ja guntun tsaki ya ce "Bari kawai, sai shashashanci nake da yarinyar da na haife ta ko? Ni kaina kamar na yi wa kaina shegen duka"

"Ka haife ta a ina? Gyambo sarkin girma?"

Mamman ya yi tsaki ya ce "Za ka wuce ka je ka shirya abin da ya dace, ko kuma zaka ci gaba da rashin mutuncin ne?"

Da kyar yake ƙoƙarin controlling ɗin dariyar da yake yi, ya ce "Na ji. Amma sace yarinyar za a yi kenan?"

"Ina tunanin haka, sai dai yadda plan ya kasance. Ka ga a zahiri babu alamun kuɗin nan a tattare da su. Amma dai na tabattar da duk abin da yakamata na tabattar.

Matashin ya jinjina kai ya ce "Daren yau ko na gobe za mu ƙaddamar da aikin?"

Mamman ya fito ya ce "Mu je hanya mu ƙarasa"

"Amma yarinyar nan fa, kamar sonka take yi fa. Kai amma tun da aka haife ni ban taɓa ganin abin da ya bani dariya kamar yau ba. Madakin maza a cikin tsummokara yana kashewa yarinya murya Allah ya isan maza"

Ashariya Mamman ya ɗura masa yana hankaɗa shi waje, amma ya maƙale yana ƙyaƙyata dariya.

*****

Duk da nisan da baccinta ya yi, amma haka kurum ta kasa jin daɗin baccin. Banda miyagun mafarkai marasa daɗi babu abin da take yi. Wata irin hayaniya mai razanarwa ta din ga ji a saman kanta, ta kasa tantance wace irin hayaniya ce haka, kuma ta kasa farkawa daga mummunan mafarkin da take yi.

Sautin murya kawai take ji ana ƙwala mata kira "Rahama!Rahama!" Kamar daga sama ta ji an danƙota an yo ƙasa da ita daga kan gadon. Sai a lokacin ta buɗe idanunta, ta din ga jin guje-guje da iface-iface a zahiri. Hostel ɗinsu ya hargitse, sai kururuwar 'yan mata kawai ake iya ji. Tozali ta yi da wani gabjejen ƙato, sanye da kaya ya rufe fuskarsa da rawani, ga uwar bindiga a hannunsa. Ta ɗaga kai ta ga ba shikaɗai ba ne ba a cikin hostel ɗin nasu akwai wasu ma. Su na ta tarkata kan ɗaliban tamkar dabbobi. Daga ita sai shigar jikinta, ƙafafuwanta babu ko takalmi haka ya fige ta kamar abin banza kasancewar ba ta da jiki, ya yi waje da ita. Ƙarar sautin harbe-harben da ya fara tashi, ya ƙara rikita Ramata, ta gigice gaba ɗaya, sai dai ta kasa yarda da cewar ido biyu ne wannan abin yake faruwa, ta saka a ranta mafarki ne da haryanzu ba ta farka ba.

***** Fafur Hafsa ta ƙi kula Alina, cikin damuwa Alina ta ce "Dan Allah Hafsa ki yi haƙuri, wallahi na zata kin tafi ne"

"Eh mana tun da an saya miki agwaluma, ana kallonki ana kashe miki ido kin makance"

"A'a ban makance ba"

Hafsa ta ce "Wallahi kin makance da ƙauna"

Shugaban makarantar ne ya shigo ajin nasu a ɗan rikice yana faɗin "Subhankallauma wa bi hamdik, ashhadu alla ila ha illa Allah, Astagfiruka wa a tubu ilaik. Maza kowa ya tashi ya tafi gida, kar wanda ya tsaya wasa ko ya tsaya a wani gurin"

Cikin rashin fahimta ɗaliban suka mimmiƙe, su na mamakin mene ne dalilin tashinsu a daidai wannan lokacin, da bai kamata a tashe su ɗin ba. Su na fitowa harabar makarantar, suka tarar da 'yan sauran azuzuwa su na fitowa, su na fita dan haka su ma suka fita. Yanayin yadda mutane ke ta kaiwa su na komowa, ya nuna akwai matsala. Kowane dalibi ya kama hanyar gida, ga babu wuta, Hafsa suka yi sallama da Alina ta tafi gida.

Nadiya ce take kallon Yaya ta ce "Masoyi fita za ka yi?"

"Alina zan je na ɗaukko daga makaranta, hankalina ba zai kwanta ba"

"Amma da ka kira waya makarantar, ina tsoro"

Bai ma tsaya sake tanka mata ba, ya yi waje yana sassarfa.

Tun da Alina ta doso layinsu, ta ga wasu irin zabga-zabgan ƙarta na kaiwa su na komowa. Jikinta ya yi sanyi ƙalau, ta bi ta wani lungu ta zagaya ta baya ta shiga layin nasu. Security light ɗin da ke ƙofar gidan Malam Sadi, ta haske sashi mafi yawa na layin. Ga wata mota sienna a tsaye a cikin layin nasu, an yi parking ɗin ta. Daga inda take tsaye take kallon ikon Allah, Yaya ne ya fito daga cikin gida, ya yi turus bayan ganin ƙarti a tsatstsaye a layin, wasu na facing ƙofar gidan sa. A aljihunsa ya zura hannu, amma cikin zafin nama wani ya haska masa wani abu mai kama da bindiga, take ya durƙusa a kan ƙafafuwansa yana karkarwa. Mamman ta gani ya zare tsummar rigar jikinsa, daga shi sai wata baƙar shirt da dogon wando. Ashe wannan tsummokaran ne suke ƙara ɓoye girmansa. Ƙara ƙura ido take yi, domin tabattar da shi ɗin ne ko wani daban? Ya ƙarasa gaban Ismail ya sunkuya daidai fuskarsa, yana yi masa magana, daga inda take tsaye ba ta iya jin me yake ce masa.

"Ka ga inda wasan ya kawo mu ko?"

Ismail ya yi murmushi ya ce "Gaskiya ne, sai dai ba zai ƙare a nan ba, yanzu za a fara, kai kuma ka zuba ido ka ga inda zamu ƙarƙare. Ka saka a ranka yanzu ne aka buɗe shafin farko.

Jikin Alina wata irin rawa yake yi, ƙafafuwanta suka yi sanyi, jikinta ya jiƙe sharkaf da gumi.

Abdallah ya miƙa wa Ammar hannu, ya miƙo masa igiya, ya banƙare Ismail ya yi masa wata allura a dokin wuyansa, a take jikinsa ya saki. Ya yi masa wani irin ɗauri tamkar zai karya shi. Ya saɓa shi ya jefa a bayan mota ya zagaya ya shiga motar aka ja motar suka bar layin.

1K NE A TELEGRAM VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC. MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN. Ayshercool 08081012143