Kenza eBookz
Cover art for SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 7

Post

SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 7

.....he feels that I hurt him. "If I had known what I would find in the country, I would not have even dreamed of seeking power. Since I was sworn in, I have not achieved anything important except the setbacks that I have faced in the country. This case is the third that has happened in recent days. We have to face it, before things get worse. In that area in the west, oil theft has escalated, and in the east, the conflict between farmers and herdsmen, and ethnic conflict. Tomorrow, God willing. He called the media and told them that he was trying to improve security. You know what you should do about it. Then arrange for me to sit with the leaders of the security forces, tomorrow at around nine o'clock at night. We will also appoint representatives to go to the affected area." ***** She was sitting on the chair, she put her phone on the small table in front of her, she was looking at the paper in front of her, she had written on her body, she was rehearsing. After her, he finally looked at the paper, he pulled away and said, "Daughter, you just saw yourself Laila" He spoke while staring at her. T.....

Standalone post4,373 words

SARA DA SASSAƘA...

YOTA /002

P7

Ganin ya ƙi magana yana ƙare mata kallo, ya sanya ta yi gaba ta bar shi a gurin, Tana ƙunƙuni, da mita ƙasa-ƙasa.

Bai san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba, ganin tsagwaron ƙarfin hali irin nata.

*****

PRESIDENTIAL RESIDENCE.

Garin ya yi shiru, ba a iya jin motsin komai, tamkar babu halitta mai numfashi a gurin. Sannu a hankali yake kaiwa yana komowa a cikin katafaren ofishin. Ya koma ya dafa kan kujera yana juya ta a hankali da hannunsa. Ya kalli agogon office ɗin, ƙarfe uku saura mintuna goma. Yana sauke idanunsa, aka buɗe ƙofar ofishin aka shigo.

"Halilu ka ƙaraso?" Ya yi maganar yana ajiyar zuciya.

Cikin girmamawa kamar ya dungura ya ce "Yes sir na ƙaraso, a yi mini afuwa, ina fatan ban ɓata maka lokaci ba?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a. Bismillah zauna"

Halilu ya ja kujera ya zauna, yana daga tsaye ya tura wa Halilu jarida ya ce "Ina fatan ka ga wannan, na san ma wataƙila ka riga ni gani?"

Halilu ya ja jaridar ya fara dubawa. Ya shafi goshinsa, da yake jin kansa na yi masa wani irin ciwo. "Da na san abin da zan tarar kenan a ƙasar, da ko a mafarki ban nemi mulki ba. Tun bayan rantsar da ni, babu abin da na cimmawa mai muhimmanci sai ma koma baya da na fara fuskanta a ƙasar. Wannan case ɗin shi ne na uku da ya faru a tsukin kwanakin nan, dole mu yi wa tufkar hanci, kafin lamuran su fi haka ƙazanta. Wancan yankin na yamma satar mai ya ta'azzara, gabas kuma rikicin manoma da Makiyaya, da rikicin ƙabilanci. Gobe in Allah ya kaimu ka tara manema labarai, ka sanar musu na ƙoƙarin ɗaukar matakan inganta tsaro, ka dai san abin da yakamata ka yi a kai. Sannan a shirya mini zama da shugabannin rundinonin tsaro, gobe da misalin ƙarfe tara na dare. Za kuma mu naɗa wakilai su je ta'aziyya gurin da abin ya shafa"

Halilu ya numfasa ya ce "Shikenan sir, za a gabatar da duk abin da ka ce, na bar ka lafiya"

Jinjina kai kawai ya yi cikin ƙarfin hali.

*****

Tana zaune a kan kujera, ta ɗora wayarta a kan ƙaramin table ɗin gabanta, tana kallon paper gabanta, da ta yi rubuce-rubuce a jiki, tana rehearsal.

Ta bayanta ya ƙaraso yaka leƙa paper, ya ja guntun tsaki ya ce 'Yar wahala, ke dai kin ga ta kanki Laila" Ya yi maganar yana dungure mata kai.

Ta ɗago tana murguɗa baki ta ce "Ba ruwanka da ni, na gaya maka ka fita daga sabga ta"

"Da ruwana da ke, ke ba ki san yanzu haushinki nake ji ba, kamar na shaƙe ki na huta"

"To sai ka kashe ni ka huta ai"

Mama ce a gefe, a kwance a kan fulo hannunta riƙe da counter, ta ɗago tana faɗin "Sadam ba ruwanka da ita dan Allah, ka ƙyale ta"

"Mama ke ki ke goya mata baya dama, kiri-ƙiri yarinyar nan, ɗan aikin nan da ta samu, ɗan abin da ake ba ta yana taimakawa, amma saboda baƙin hali, ta ja an kore ta, ta dawo wahala wai content creation. Ko uban wa ya gaya mata ɗan jarida yana ɗaukan side ya shiga siyasa oho mata"

Laila ta ce "Ni fa ba siyasa na shiga ba, tun da an kore ni, i decided to take another decision. Dama can ina content ɗina. Beside yanzu na samu cikakkiyar dama na yi abin da nake so, a hankali zan yi building pages ɗina na fara samun kuɗi"

Sadam ya yi tsaki ya ce "Aikin banza ƙiba a kunne, comment section ɗin ki ban da zaginki ma babu abin da suke yi"

"Duk da haka ba zan gaji ba, masu yaba mini sun fi masu zagin yawa. Sannan masu zagin ma taimakona su ke yi gurin pushing ayyukana. Ni fa na gama gane ka. Kuma ina yawan gaya maka, da arziki a garin wasu gara a gidanku."

"Gidanku ke a wa? Da ya ci president ɗin uban me ya tsinana miki, kullum cikin ƙona datarki ki ke a banza, da hauragiya ba a san da ke ba ma"

Laila ta yi murmushi ta ce "Mu siyasar aƙida muke yi. Ko bamu samu komai ba, muddin al'umma na amfana shikenan. Ko kowa ya watse ya bar tafiyarsa, nikaɗai zan tsaya a bayansa ƙuri'ata tasa ce"

Wani uban tsaki ya ja ya ce "Su na can su na satar kuɗin talakawa su na ci, yaran talakawa ku na nan kuna wahalar banza"

"Idan Allah ya tsayar da kai ranar shaida, zaka nuna abin da ya sata?"

A hasale Mama ta ce "Ko dai ku daina wannan musun banzan da na wofi, ko ku fita ku bar mini ɗaki. Sadam ba ka da girma sai na jikinka. Kawai ku zauna ku cika mini kunne ku hana ni sakat ni da gidana. Ko a yi mini shiru ko ku fita ku bar mini ɗaki na huta, iskancin banza kai"

Laila ta yi masa gwalo, ya galla mata harara, ya fita. Ta saita wayarta ta kunna video ta fara recording.

Mama ta ce "Malama ki yi ƙasa-ƙasa kin cika mini kunne, ko kema ki fita yanzun nan ki bani guri"

Laila ta ce "Na fuskanci videon nan ne dai ba kya son na yi, bari na tafi tsakar gida"

"Eh sauka lafiya. Haba wannan abu har ina, kai da gidanka ba zaka huta ba"

Laila ta kwashi kayan videonta, ta fito waje.

**** "Amanar kacalla"

"Allah ya bar mini kai Madugu"

"Ya ake ciki?"

"Kaya sun zo hannu, an samu shanu ɗari biyu da goma sha biyu. Ga kuma tumaki da raguna guda ɗari"

Kacalla ya numfasa ya ce "Ku kaɗa su boda, akwai tireloli su na nan su na jiranku, za su karɓa su bar ƙasar da su"

Sadauki ya ce "To ina fatan sun gyara mana hanya, saboda aka samu kuskure zubar ruwa za mu yi kan mai uwa da wabi"

Kacalla ya ce "A huce haka Sadauki, na kula da komai, an share hanya ku saka kai kawai"

"Allah ya bar mini kai ubangidana, ina sanya ran zuwanmu nan da kwana biyu"

"To shikenan, duk yadda a ke ciki mu yi magana kawai. Ka kiyaye da lokutan kirana"

Sadauki ya ce "Na kiyaye"

*****

Ɓangaren Alina ta daina gaida Mamman, ta kuma daina kai masa wankin takalmi, idan ta zo wucewa ma sai ta kawar da kanta gefe tana haɗe rai, da zumɓura baki. Yana zaune a bakin hanya, ta zo ta wuce shi za ta tafi makaranta, ta yi nisa sosai wani almajiri ya biyo ta yana ƙwala mata kira. Ta tsaya tana kallon yaron.

"Ga shi in ji wani mutum ya ce a baki" Ta kalli takardar da ya miƙo mata, ta karɓa ta buɗe. Shiru ta yi tana kallon rubutun ajamin da yake jiki.

"Na yi ba daidai ba, ba zan sake ba" Ta waiwaya ta ga yaron ya tafi, ta ɗan yi murmushi ta ninke takardar ta saka a jakarta.

Bayan an tashi daga makarantar boko sun fito tare da Hafsa, da shi ta fara cin karo a waje, a ƙofar makarantar yana jiran ta. ba ta ce masa komai ba, suka wuce shi da ita da Hafsa. Sai da suka yi sallama da Hafsa suka rabu a hanya sannan ta tsaya. Ya ƙaraso yana tsare ta da ido. Tsiwa ta so ta ɗan yi masa amma kuma sai ta kasa, idanunsa suka ɗaure ta, ta gaza cewa komai.

A hankali ya ce "Kin ga saƙona?"

"Na gani" Ta amsa tana juya masa ƙeya.

"To ya wuce?"

Alina ta jinjina kai.

Ya ɗan yi murmushi ya ce "To ki juyo mana"

Ta ɗan ɗago, amma ba ta bari sun haɗa ido ba. Ta rufe fuska tana murmushi.

Ya sake kwantar da murya ya ce "Ina fatan za a ci gaba da kawo mini wankin takalmin, kuma za a daina fushi da ni?"

Tana ƙoƙarin yin murmushi tana mazewa ta ce "Zan kawo maka ma idan na taso daga islamiyya"

Ya ce "To ya yi, yaushe ne saukar ne?"

"Mun kusa in sha Allah"

"Allah ya sanya albarka"

"Amin na gode sosai"

"Idan da taimakon da ki ke buƙata, ko inda ba ki iya ba, ki gaya mini na koya miki"

"Kai amma na ji daɗi sosai, na gode." Ya jinjina kai ta wuce gida. Ya tsaya shiru yana bin ƙofar gidansu da kallo. Yana sake nazarinta.

Kamar yadda suka yi da ita, bayan ta dawo daga islamiyya ta kai masa wankin takalmi, ta kai masa har da abinci.

Ya kalli flask ɗin Abincin ya kalle ta, ta yi shiru tana jiran ta ji me zai ce. Sai kuma ta ji ya ce "Yayanki ba zai yi miki faɗa ba?"

Ta jinjina masa kai, jiki a sanyaye ya karɓa, dan ya ga alamar idan bai karɓa ba akwai daru.

"Yaya Mamman" Ta kira sunan shi, hannunta riƙe da ƙulu tana saƙa. "Ba ka gaya mini sunan garinku ba."

Ya numfasa ya ce "Ai ko na gaya miki ba ki san ina ne ba"

"To da ka yi ciwon cikin nan ka je Asibiti ne?"

Ya amsa da "A'a"

"Meyasa?"

"Ba ni da kuɗi"

"Ka je a duba me yake damunka, idan aka rubuta maka magani sai na bawa yaya ya saya maka"

Mamman ya kalle ta ya ce "Idan zan mutu yayanki ba zai saya mini magani ba"

Ta ce "Wallahi zai saya maka in dai na kai masa. Yana da kirki fa, kawai dai saɓanin fahimta ne ku ke samu da kai da shi"

Tun yana biyewa surutun Alina, har ya yi shiru, dan da alama ita ba gajiya take yi ba. Ya gama wanke mata takalminta, ya bata abin ta. Sai dai a wannan karon ma bai karɓi kuɗin ba.

Godiya ta yi masa cikin harshen turanci tana murmushi, sai dai yadda ta lanƙwasa harshenta ta yi magana, tamkar baturiya"

Sai da ya kalle ta da mamaki, duk da makarantar da take zuwa ta boko, mai tsadar gaske ce. Amma abu ne mai wuya a ce a nan iya wannan turancin. Ya numfasa ya ce "Ina fatan dai ba zagina ki ka yi ba, tun da kin san ban iya yaren nasara ba"

Ta yi dariya ta girgiza kai ta ce "Godiya kawai na yi maka fa, yaya za a yi na zage ka ma?"

"To ai na ji turancin ma, ba irin na 'yan nan ba, kamar na turawa ki ka yi, ya aka yi ki ka iya irin wannan?"

"British Academy na yi Nusery da primary, daga baya na ce bana son makarantar, Yaya ya dawo da ni nan" Ta yi maganar tana karkaɗe gefen rigarta.

Ya yi murmushi ya ce "Lallai yaya attajiri ne, British Academy ki ka je?"

"Wai kai ma ka yi Makarantar boko ne?"

Ya yi murmushi ya ce "A'a, na san dai makarantar turawa ce, kuma tun da makarantar turawa ce, za ta yi tsada sosai"

"Aikuwa da tsada sosai, har breakfast da lunch ake bamu fa, malamanmu har da turawa, sai da muka tashi daga waccan unguwar ga nisa, ga wataran Yaya baya gari, nima dai na ce ba na son makarantar, aka dawo da ni wannan"

Ya jinjina kai ya ce "Lallai yaya ya yi ƙoƙari sosai, yana son ki yi karatu"

Ta ce "Eh mana, kuma ina yi sosai da sosai ba"

Sannu a hankali, wata irin shaƙuwa ta din ga shiga tsakanin Alina da Mamman mai wankin takalmi. Wanda har ta kai Alina ta saka masa kwanon abinci, a gidansu safe rana dare, duk abin da aka dafa sai ta zuba ta kai masa. Tun tana ɗan jin ɗar-ɗari, saboda jarabar Yaya Ismail, har ta rage jin tsoron. Hatta alaƙarta da Hafsa sai da ta ja baya, saboda Mamman. Ba ta taɓa zaman mintuna ashirin ba ta yi zancensa ba. Idan ta taso daga Islamiyya, sai ta tsaya a gurinsa, su yi hira ya jiye mata hadda. Wataran kuwa a ƙofar makarantar take tarar da shi su tafi tare.

Nadiya nata bacci, ta yi juyi kawai ta ga Ismail a zaune a kan gado. Ta kai hannu ta shafa bayansa ta ce "Masoyi ya dai na ganka a zaune, kai ba salla ba meyafaru ne?"

"Alina" ya ba ta amsa a taƙaice.

"Me ta yi kuma?"

Ya ja numfashi ya jingina da allon gadon ya ce "Alaƙarta da mutumin nan ce ba na so ko kaɗan, alamu sun nuna na yi sake shaƙuwa ta shiga tsakaninsu, na kuma fuskanci idan na matsa, za ta iya jin haushina. Na fuskanci yadda magana ɗaya biyu a gidan nan sai ta ce Mamman, hatta yadda take rawar jikin kai masa abinci duk ina ankare da ita, kallonta kawai nake yi"

Nadiya ta tashi zaune ta ce "Masoyi, ko muna so fa ko ba ma so, dole Alina a ce ana sonta, kuma dole a aurar da ita, yawan hana ta kula samari da ka ke yi, kar ya zame mata matsala fa a gaba. Sai dai kuma idan abin da nake so tsoro ne zai faru"

A kausashe ya ce "Za ki fara ko? Sau nawa zan gaya miki ki daina ɗarsa wannan shirirtar da a ranki? Alina yarinya ce ƙarama fa, soyayya kuma barazana ce ga mutum mai ƙallafa abu a rai kamar ta. Idan Alina ta kamu da soyayya za ta sha wahala, kuma ban shirya bawa ƙasƙantaccen mutum kamar wannan auren Alina ba, dan ni gaba ɗaya ban yarda da shi ba, yanayinsa gaba ɗaya na marasa gaskiya ne, ina nan ina bibiyar lamuransa, ta ƙarƙashin ƙasa zan yi maganinsa sai ya bar unguwar nan. Sannan dole ni zan nemawa Alina wanda ya dace da ita, saboda gudan abin da ka iya zuwa ya dawo"

Nadiya ta numfasa ta ce "Maganganun ka gaskiya ne, amma Alina ba soyayya take yi ba, kawai dai jininsu ya haɗu ne. Ina saka ido sosai da sosai nima a kanta"

Kawai ya yi dariya ya kwanta, ya ce " za kuwa ta baki mamaki, za ki ce na gaya miki. Na saka masa ido ta kowace fuska yanayinsa da ƙirarsa ta marasa gaskiya ce, amma ina nan ina bin diddiginsa"

Alina ce tare da Mamman, tsaye a ɗan madaidaicin shagon provision ɗin da Alhaji Sadi ya buɗe masa a cikin layin, ya ce ya din ga zamar masa a ciki.

Cikin washe baki Alina ta ce "Allah ya sanya maka albarka, ya sanya daga wannan ka buɗe plaza ƙatotuwa, kamar rabin unguwar nan"

"Amin 'yar ƙwalisa" Ya yi maganar yana dariya.

Ta ce "Ɗan albarka"

"Na'am"

"To yanzu shikenan ka daina wanke mini takalmina, wa zai din ga wanke mini kenan"'?"

Ya din ga kallon idanunta, har sai da ta sunkuyar da kai ta daina kallonsa.

Can ya ce "Na daina gyaran takalmi, ko wankin takalmi,sai naki kawai" ya yi maganar yana kallonta. Ta yi dariya tana rufe fuska.

Can kuma ta ɗago ta ce "To ka gaya wa mamanka ta yi maka addu'a, an buɗe maka shago?"

Ya jinjina kai ya ce "Tun jiya, na kuma ba ta labarinki, ta ce na gaishe ki. Ta kuma gode da ciyar da ni da ki ke yi"

Ta faɗaɗa murmushinta ta ce "Ka ƙi bani ita mu gaisa, ina son ta yi mini addu'a, na ji ya ake ji"

Cikin rashin fahimta ya tattara hankalinsa a kanta, ya ce "Kamar yaya kenan?"

Ta yi shiru jikinta a sanyaye ta ce "Ban san mamanmu da babanmu ba, Yaya ya ce mini dai ni kama ta ɗaya sak da mamanmu, shi kuma da babanmu yake kama"

Mamman ya ce "Ban fahimce ki ba, sun rasu ne?"

Ta gyaɗa kai.

"Oh Allah, ki yi haƙuri ki din ga yi musu addu'a, Allah ya gafarta musu" Maimakon ta amsa sai ya ga ta fashe da kuka.

Sai ya rikice ya yi ƙasa da murya ya ce "Ki daina kuka dan Allah, ki rufa mana asiri kar a ce ko wani abin na yi miki ma, ki yi haƙuri mu yi musu addu'a" Ta jinjina masa kai tana share hawayenta.

"Yauwwa kar ki saka yaya ya zo ya zane mu"

Ta saki murmushi ta ce "Haba dai, ba zai zane mu ba, sai dai ni ya zane ni, kuma nima ɗin baya dukana ai"

"Hmm ke ba zai zane ki ba, amma ni fa"

"Kai ma ba abin da zai yi maka"

Suka ci gaba da hira cike da shaƙuwa.

***** 'yan boarding su na cikin walwala da farinciki, kasancewar yau ranar visiting ce, makaranta ta cika ta batse da iyayen da 'yan uwan yara. Tun da Rahama ta ga azahar ta wuce ba ta ga Baffa ba, ta fitar da ran za a zo mata. 'yar kwanarta Anty Ruƙayya ce, ta janyo ta cikin 'yan uwanta, suke ta hira kamar tare aka zo musu. Dan tun Rahama na jss 1 Ruƙayya ke bayar da labarinta a gidansu, idan an zo visiting ko hutu ma su na haɗuwa da 'yan uwan Ruƙayya. Maman Rukayya na son Rahama, mussaman da ta ji labarin, daga ƙungurmin ƙauyen da babanta ya ya sadaukarwar kawo ta makaranta, kasancewarta 'yar boko. Maman Ruƙayya ta ce "Rahama ni wannan kunyar taki ta yi yawa, ko dai a cikin yayyen Ruƙayya wani ki ke so ne?"

Rahama ta sunkuyar da kai tana murmushi.

"To matso nan mu ci abinci tare, ke dole ma a yaran nan zan yi miki miji. In dai Baffanki zai ba mu ke. A ba wa Abdallah ko Ammar"

Kamar ta nuste, haka ta ɗan cakali Abincin nan, saboda Rahama akwai gudun Duniya da abin hannun mutane. Ga su Rukayya kuma masu kuɗi ne sosai da sosai. Idan za a zo mata visiting sai an yi nata na package ɗin. Har Baffan Rahama 'yan gidansu Ruƙayya sun sani.

Mami ta miƙa wa Rahama wayarta da take ringing. Ruƙayya ta ce "Waye"

"Karɓi ki duba mana"

Ruƙayya na ganin sunansa, ta yi murmushi ta koma gefe ta ɗaga.

"Yaya Mubarak"

"Na'am shalelen, ashe su Mami sun ƙaraso, na so zuwa ayyuka ne suka yi mini yawa sosai, kin san yayyen nan namu, sai su cinye mutum idan bai yi abin da suke so ba"

Ta yi murmushi ta ce "Take your time ka yi aikinka a hankali, kawai idan ka samu time ka zo na ganka"

Mubarak ya ce "Wanne dole ne, dan ba zan iya shafe wata uku ban ganki ba, zan zo in sha Allah." Sun yi hira sosai kafin su yi sallama.

Yana zaune a cikin mota, ya kwantar da kujera, ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan ɗaya, ya ɗora a saman sitiyari yana ɗan kaɗa ta, hannunsa ɗaya riƙe da waya yana magana.

"Wallahi Ummi ce ta sako ni a gaba, wai sai an zo wa yarinyar nan visiting, daga zuwana gidan na ɗan huta, dan dai ba yadda zan yi ne"

Daga cikin wayar mai amsa wayar yake magana, cike da kamala, da har kamalar tasa take nuna isa isa. Yayinda nauyin muryarsa ya sanya in da da wani mutum a cikin motar bayan shi zai iya jin abin da yake faɗa, duk da wayar ba a hansfree take ba.

"To mene ne a ciki dan ka je wa Ruƙayya visiting, I wish ina da little sister da za ta ga gata"

Na cikin motar ya kwashe da dariya ya ce "Ta ga gata, ko ta ga gwale-gwale, kai da gidanku gidan maza ne, Ummi ce kaɗai mace, da kuna da ƙanwa azaba za ta sha ne kawai"

"Alfa zan zage ka wallahi"

Alfa ya ce "Ware, gidan nan naku imaninku da sauƙi wallahi, ku kanku ganawa kanku azaba ku ke yi" Ya yi maganar yana ƙyaƙyata dariya.

Tsaki wancan ya ja ya ce "Stupid"

"Kai tsaya, ga su can ina ga sun gama tafiya za mu yi, zamu yi waya anjima take care"

"Take care like? Mace ne ni da za ka wani ce mini take care?"

"Zan zage ka fa, ma yi waya dai. Don't care, stay wrecked tun da baka da mutunci"

"Am wrecked already ai" ya katse wayar yana ɗan tsuke fuska.

Ummi ce ta fara ƙarasawa gaban motar ta ce "Ammar ba dai baƙin hali ba, for more than 5 months bana tunanin kun haɗu da yarinyar nan, ka fito ka gana da 'yar uwakka amma ka ɗauki motar ka tafi gantali ta zo baka nan"

Ya kalli Rukayya, ta risuna ta ce "Yaya Ammar Ina wuni, ya aiki?"

"Lafiya kalau, ya karatu?"

"Lafiya kalau Alhamdillah."

"To a mayar da kai a yi karatu da kyau idan ana son a ga daidai." Ta yi murmushi ta ce "In sha Allah thanks"

"Ina wuni" Rahama ta faɗa daga bayan Ummi a tsorace.

"Lafiya sannu" Ya yi maganar yana sake mayar da hankali kan wayarsa.

Ummi ta ce "Wannan wace irin amsa ce? Haka ka amsawa 'yar uwakka? Ka daina irin haka. Ita ma ƙanwarka ce ai"

Ya jinjina kai ya ce "To hajjaju, tuba nake." Ya ciro kuɗi ya miƙa wa Ruƙayya kuɗi ya ce "Ga shi nan ki ƙara, a kula da karatu sosai"

"Ita ɗayar me ta yi maka?"

Ya ce "Wa?"

"Ban sani ba" Rahama kuwa tuni ta juya za ta tafi, amma Ummi ta kira ta, ta saka Ammar ya ba ta kuɗi ita ma. Sai dai da fari ƙin karɓa ta yi, sai da Ummi ta haɗe rai.

Su na tafe a hanya Ummi na yi wa Ammar faɗa."Ammar ba ka kyautawa abun da ka ke yi, yaran nan ƙannenka ne, su na sonka su na ƙaunarka, su yi ta murna idan za ka zo, amma ka yi ta wulakanta mini yara dan baka da kirki?"

Ammar ya na kallon hanya ya ce "Ummi kin san raini ne ba na so, amma nima ina murnar ganinsu ai"

"Ƙarya ka ke yi, kuma dan wulaƙanci har da baƙuwa, yadda ka amsawa Rahama gaisuwar da ta yi maka ya bani haushi"

Ammar ya waiwaya ya ce "Wace Rahama?"

"Yarinyar da suka zo da Ruƙayya mana, Junior ɗin ta ce, wulaƙanci ba shi da daɗi ai"

"To Ummi, ban san yarinya ba sai na din ga washe mata baki kamar wani shashasha"

"Kai ubanka, ina yi maka magana kana kawo mini useless excuses ɗin ka"

"Allah ya baki haƙuri"

"Amin. Baƙin hali ba abin yi ba ne Ammar, ba a san inda rana za ta faɗi ba"

Ƙasa-ƙasa ya ce "A yamma mana Ummi" jin ta yi shiru ya ɗan waiwaya ya ga tana hararsa ya kawar da kansa ya ci gaba da tuƙinsa.

Rahama a ƙasan zuciyarta ta ji babu daɗi rashin zuwan Baffa, tare da rashin sanin dalilin da ya hana shi zuwa. Da daddare da suka koma Hostel, kowa yana ta murna, Rukayya na ta ƙoƙarin ganin Rahama na walwala amma da ta hau kan gado sai da ta yi kuka.

*****

Dattijo ne a ƙalla mai shekaru hamsin da takwas, yana zaune a kan buzu, hannunsa riƙe da Alqur'ani bugun warsh, yana karantawa. Opposite ɗin sa wata irin ƙatuwar rumfa, shimfiɗe da tabarmi da alluna a jijjingine, almajirai sun tafi bara.

Sallama ya yi wa dattijon, ya nemi guri ya zauna a gefensa. Dattijon ya kai aya, sannan ya amsa sallamar suka gaisa.

Ya dubi dattijon ya ce "Malam Ɗayyabu ko?"

"Eh nine"

"Dan Allah tambaya na zo na yi maka, kai malamin Alqur'ani ne. Ma'abocin Alkur'ani kuwa za a same shi da gaskiya da tsoron Allah. Kuma yanayin dattakunka, ya sanya mini yarda da komai zai fito daga bakinka, gaskiya ce"

Malam Ɗayyabu ya jinjina kai ya ce "Wannan gaskiya ne, in sha Allah yadda ka kyautata mini zato, ina sanya ran gaya maka gaskiya da yardar Allah"

"Akwai wani matashi da ya tare a unguwarmu, ya ce shi ɗalibinka ne, ya yi sauka a hannunka, daga baya kuma ya sake dawowa garin nan, neman kuɗi. To ina son tabattar da hakan daga gare ka ne, saboda yana ɗan bibiyar 'yar uwata ne, ina tsoron wani abin da ba a so ko fata ya faru, na ga yakamata lallai na bibiya"

Malam Ɗayyabu ya ce "Wannan gaskiya ne, ka yi kyawun kai, mussaman zamanin nan da ya lalace. Amma ka ga tun ban fi shekara ashirin da biyar ba, nake harkar ɗalibai, dan haka wanne daga cikin ɗaliban nawa?"

Ya ce "Sunansa Mamman, ban san sunan garinsu ba, amma ga hotonsa".

Ya yi maganar yana ciro wayarsa ya ɗan daddana, ya miƙa wa malam Ɗayyabu. Hoton Mamman ne a zaune yana wankin takalmi, Alina na gefensa a kan dakali tana magana. Malam Ɗayyabu ya karɓi wayar ya yi shiru yana kallon wayar, ya numfasa ya ce "Wannan ce yar uwar taka?"

"Ba a kanta mu ke magana ba malam, wannan mutumin da ya ce shi ɗalibinka ne, nake magana a kai"

Malam Ɗayyabu ya yi shiru ya zuba wa hoton ido.

"Malam ka yi magana mana" Ismail ya yi maganar yana kallonsa.

Malam Ɗayyabu ya ɗago kai yana kallon Isma'il.

Ismail ya ce "Ina ƙara tuna maka, ka dubi girman mai littafin da yake gabanka, ka gaya mini gaskiya"

"Ɗalibina ne" Ya yi maganar yana gwama numfashi.

Ismail ya yi shiru yana nazartar fuskar malamin.

"Ka tabattar ɗalibinka ne?" Ya jinjina masa kai yana ɗan zazzare ido.

"Idan akasin gaskiya ka gaya mini, mai Alqur'anin nan ba zai bar ka ba"

"Me zai sanya dattijo kamar ni, ya yi maka ƙarya, alhalin baka sanni ba ban kuma sanka ba? Mamman ɗalibina ne, sai dai ya sauke ya haddace, dan haka ya kai munzalin da zai zaɓi abin da yake so, kuma ina da yaƙinin mutumin kirki ne, ba zai cutar da kowa ba"

Ismail ya jinjina kai ya ce "Gaskiya ne,na gode sosai da sosai Malam" Suka yi musabiha, ya tashi ya tafi. Yana tafiya jikin Malam Ɗayyabu ya yi sanyi, wani irin gumi ya fara tsatstsafo masa, ya kalli Alqur'anin da yake gabansa ya furta "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, da wani bakin zan nemi gafarar Allah"

'yar ƙaramar wayarsa da ke cikin aljihunsa ce ta fara ringing, ya ciro ta, yana kallon yadda kira yake shigowa babu suna kuma babu lamba.

Hannunsa na rawa ya kara wayar a kunnensa.

"Aikinka ya yi kyau, idan aikin naka ya ci gaba da kyau, shikenan ka tsira, idan kuma aka samu matsala salin alin zamu ɓatar da kai"....

Ayshercool 08081012143