Kenza eBookz
Cover art for SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 6

Post

SARA DA SASSAKA HAUSA NOVEL PAGE 6

.....you are on their ears.... *** It is usually at night when the body of a person is lying down and it is at this time that the soul rises and enters the world and wanders, this is the reason why when you meet a person in reality, you start to think as if you know him, and you lose where you have seen him before. This is the reason why your soul meets the night on the road. Others say that it is the Spirit that rises above the body. Since Batty has been begging Mado for her life, he has to pay, because he is very fat, his blood and his good meat will taste good in your mouth. This is the reason why she followed the night to see if she can achieve her goal this time, this is the first time she feels that she can't tolerate what she feels about Mado. She sneaked into Moddibo's house and found Mado's room. She climbed over the roof of the room and cried to him in his deaf ear because of a noise coming from inside. In a panic Mado woke up hearing what happened as if in a dream, he jumped up and stood up while turning around and met Moddibo who was standing, Mado went towards his father saying "Didn't you hear?" He shook his head. "Didn't you hear the mage cry?" "I heard my name...

Standalone post564 words

"Na tsani haihuwa, me ya saka ta saki jiki duk ta haife ku kamar wata dabba, uwarku bata da amfani ita da dabba ɗaya suke a wajena. Jaka ce, daƙiƙiyya mara amfani"

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"

Iftihal ta furta tana fashewa da kuka, tana jin kamar zuciyarta ce zata fito waje.

Daada ya sake kallon Innti take durƙushe ya ce "Wallahi Tani ta fita armashi da garɗi, ta sani bana son haihuwa me ya saka ta haife ku har haka? Ku duka tsinannu ne ba za ku yi albarka ba. Allah wadaran....," a zabure Innti ta miƙe tana girgiza kai kafin ta ce

"Kar ka aibata mini zuri'a Daada, kar furucinka ya zame musu Harshen wuta, ka yi wa girman Allah Daada...," bai bari ta ƙarasa ba ya ɗauke ta da mari ya nuna ta da manuniyya "Na faɗa, Allah Ya tsine musu dake dasu gabaɗaya, zuri'ar da bata da wani amfani kema ba ki da amfani bare su, sai sun watse sun bi duniya. Allah ya tsine musu, Allah ya farraƙu gabaɗaya na huta"

"Allah Ya tsine maka dai Daada da kai da Tani Allah Ya tsine muku" muryar Ana ta sauka akan kunnuwansu....

*** Dake yawanci sai dare yayinda gangar jikin mutum ke kwance yana samun nutsuwa a wannan lokacin ne kuma kurwa take tashi ta shiga duniya ta dinga yawo, wannan dalilin ya saka idan ka haɗu da mutum a zahiri sai ka fara tunanin kamar ka san shi, kuma ka rasa inda ka taɓa ganinsa. Hakan ya faru ne dalilin kurwarku data haɗu da daddare a hanya. Wasu kuma na cewa

Ruhi ne yake tashi yabar gangar jiki.

Tunda Batty ta yi arba da Mado ta ji ranta ya biya, domin yana da kitse sosai jininsa da namansa masu kyau ne za su yi daɗi a baki. Wannan dalilin ya saka ta biyo dare ko za ta iya cimma burinta a wannan karon, wannan ne lokaci na farko da take jin ba zata iya haƙura da abin da take ji ba akan Mado ba. Har cikin gidan Moddibo ta kutsa kai cikin sa'a ta samu ɗakin Mado ta haye rufin ɗakin ta shiga rera masa kuka a cikin kunne mara daɗin ji saboda wani amo da yake fita a ciki

"Mado... Mado... Mado..."

Haka magen ta dinga kiran sunansa.

A firgice Mado ya farka jin abin ya yi kamar a mafarki, ya zabura ya miƙe tsaye yana juyawa ya ci karo da Moddibo yana tsaye, Mado ya nufi wajan mahaifinsa yana faɗin

"Baka ji ba?"

Ya girgiza kai. "Baka ji kukan mage ba?"

"Sunana na ji ana kira" Moddibo ya kalli Mado, a wannan lokacin da Mado ya nutsu zai iya hango ƙwayar idanun Batty a cikin idanun Moddibo zai fahimci Batty ce bawai mahaifin nasa ba. Moddibo ya miƙa hannu kamar zai riƙo Mado sai kawai ya kai hannun zuwa wuya Mado ya shaƙe masa wuya, Mado ganin Mahafinsa ne sai bai shiga ramawa ba, ya dinga kokawar ƙwace kan shi amma ya kasa, sai da aka kai Mado ƙasa baya ko motsi kafin Moddibo ya bar ɗakin daidai nan magen ta yi sauri ta fice daga cikin gidan gabaɗaya.

Read the complete chapter 6 on ArewaPen.

Akwai chapter 1&8 ma idan kuna son more chapter drop a message under da chapter.

Follow my account on ArewaPen Like the book

Happy reading 🌹 Share the link 🤲🏻

Bright pens 08164069385