Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 26
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 26: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 26. Ummani tayi wani lakato tana dubansa kafin tace,"Amma kuwa banda…
4,480 words
Ummani tayi wani lakato tana dubansa kafin tace,"Amma kuwa banda na san waye mijina wallahi sai in ce mutumin nan siyeka yayi da kuɗi, yanzu tsakani da Allah sai ka bar Babangida ya auri ƴarka? Kenan kaima a wannan shekarun naka tsofe tsofe zaka iya zuwa neman auren ƙaramar yarinya ƴar cikinka ta kusan nawa? Ko da ike zamu ce ta tadda muje".
Abbaa ya buɗe ba ki da mamaki ƙarara yana dubanta yanda duk ta mayar da maganar gaske. "Ka saki baki kana kallona, to ni dai ba dani za'ai wannan zalunci ba, yarinyata da sauran ƙuruciyarta don tana bazawara ba zai yiwu a laƙaƙa mata auren tsoho ba, daga nan har hizba wallahi, mene wani Babangida daga ya ɗan taimaka mana sai ya wani kwaso ƙafafunsa na marasa kunya yace ya zo neman auren ƴar cikinsa".
Abbaa yace,"Babangida kai tsaye ma babu Alhajin".
"Yo wanne Alhaji bayan ya zubar da girmansa, neman aurar ƴar cikinsa fa yake yi kuma daɗin abin kunyar ma aminiyar ƴarsa".
Ganin fa ta haƙiƙance har tana ɗaukan fushi da shi sai mita take yi yace,"Kinga ke ba ki tsaya kin gama jin bayanin da zan miki ba kawai kin hau kan wata maganar, Aure fa ɗan su suka zo nemawa ba kansa ba".
Ƙyam Ummani ta tsaya ko ƙyafta ido babu. "Ɗansa?". Sai kuma ta dawo ta zauna tana cewa,"Kar dai kace min yaron nan Khalid me hankali, ka san ƴaƴansa maza biyu ɗayan kurma ɗayan kuma shi ne lafiyayye".
Abbaa yace,"To ai bama a nasa ƴaƴan ba ne, ɗan Yayar matarsa ne yaron nan Salim da suka nemi aurenta tun tana budurwa".
Ummani ta ware ido akansa ƙwaƙwalwarta na auna maganarsa kafin tace,"Wai kana nufin yaron da ya kawo kuɗi suka dawo suka karɓa?".
Abbaa ya jinjina kai yana Faɗin,"Ƙwarai shi fa".
"Abbaa sojan nan fa da kace min babba ne da gwamnatin tarayya yake aiki".
"Shi dai Sa'a".
Nan Abbaa ya shiga bata Labarin duk abunda ya faru tsakaninsa da su Baban Safiyya, Ummani bata jira ƙarashen zancen ba ma ta rangaɗa guɗa a hankali. Ta ɗaga hannu sama tana faɗin,"Allah gatan bawansa, Allah mun gode maka, Allah maji roƙon bawa".
Bakin Abbaa buɗe yake kallonta, mamaki sosai ya kama shi, kar dai abin da ke ransa ne a nata ran itama? Kawai sai yaji tana ƙara faɗin,"Bayan wuya sai daɗi, kuma wani hanin ga Allah baiwa ne, Rabo daga sarkin da ba ya zalunci, bijahi rasulillahi wannan yaron alkhairin Sa'ida ne".
Abbaa yace,"To ke wai kin san yaron nan ne da kike ta farin ciki haka".
"Abbaa ya ba zan yi farin ciki ba, ɗan gidan manya mutane fa, to ni dai wallahi ba don kuɗi ko matsayi ba zaɓin Allah na ke ta nemawa yarinyar nan kuma ina da yaƙinin Salim shi ne Allah ya zaɓo mana, domin kuwa tunda ta fito zaurawa ke ta sintiri akanta ban ji ina farin ciki da zuwan wani ko naji sha'awar ta ƙara yin wani auren ba sai da wannan batu ya afku". Tayi maganar baki dukka a buɗe kamar zai yage saboda murna.
"Yanzu a wacca matsaya ku ka kwana da su? Na san halinka Allah sa suma ba ce kayi su kama gabansu ba, don ni dai ban sani ba Abbaa ko kwaɗa Sa'ida zamu yi muci ba".
Yay murmushi yana cewa,"Ba haka ba ne Sa'a, aurenta na baya ne har yanzu abinda ya faru bai gushe min ba, shiyasa na ke ta jin tsoro ban san da wa zan kuma haɗata ba".
"To ya za'ai na faɗa maka ba dukka aka taru aka zama ɗaya ba, adu'a zamu ta mata ya bata wanda yafi wancan".
"To yanzu dai na ce musu su turo yaron ya same ni zuwa jibi idan Allah ya kaimu saboda bana so a saka wasa a lamarin, sai dai ita ɗin bamu sani ba ko ta amince".
"Kai rabu da ita yanzu ai ba shashasha bace da hankalinta ta san inda ke mata ciwo, a bayan ma ƙuruciya ce ta hanata gane wanda ya kamata ta aura".
****"Maman Nana ni zan wuce". Na faɗa a sa'ilin da na ke ɗaukan jakata ƴar ƙarama na riƙe a hannu. Maman Nana tace min,"To Sister Sa'ida sai Allah ya kaimu, ki gaida gida ki gaida su Ummani".
Na amsa mata yayin da Khadija ke tsokanata da cewa,"Wai ke don Allah ko ki ɗan gwada soliderity watarana ki ce za ki kwana".
Ina murmushi na ce,"To madam indai za ki bar min albashinki na watanni biyu ni kuma zan dinga haɗawa da aikin ki".
"Ehh lallai da ya ke ni bani son kuɗin".
Ina dariya kamar yanda kowa yay na ce,"A'a to ke fa kin je saudiya, ni kuma so na ke nayi nayi na kwashe iyayena na kaisu su sauke farali, kinga idan na samu ƴar 380 duk wata ai tuni zasu wuce umra".
Maman Nana tace,"To Allah dai ya cika buri, ki yi maza kinga Ummani ta bani amanarki yau kin yi dare".
Nace,"Wallahi fa kinga Yaya Imam ɗin ne ma har yanzu bai kira ni ba, ɗazu ya kira nace masa Dr yace in tsaya saboda waccan matar da akai wa operation to ina ga ko tunani yake bamu gama ba".
"To ki kira shi mana". Na ɗan karayar da wuya ina cewa,"Wallahi Maman Nana bana son takura mi shi, komai yake yi yanzu hankalinsa na kaina, Abbaa ne ma yaƙi ya bari na ke komawata ni ɗaya ni banga wani abu a ciki ba".
Suka haɗa baki wurin cewa,"Gata ne suka miki wallahi, mace yar tsaro ce sai da kulawa, ki gode Allah da ya ba ki iyayen da idon su yake akan ki".
"To bari naje, ni na manta ma daga yau nayi off ni da shigowa sai laraba".
Khadija da tsokana tace,"Dama kullum ana ba ki na goron albishir ai dole kike son zuwa aiki kullum".
Sauran pure water ɗin da ke hannuna na jefa mata. Da haka na fito daga Nursing station ɗin, Metrom na zaune muka yi sallama da ita, har na fito compound ɗin asibitin sai gata ta biyo ni tana ƙwala min kira da cewa,"Kinga ajiyar ki kin mance nima zan manta kuma".
"Sauri na ke ta yi kinga ƙarfe tara ta kawo kai, na gode".
Wasu hulunan sanyi ne da safuna Sister Hauwa ke siyarwa daga turkey ake kawo mata, shi ne na siya mana ni da Ummani da Safiyya, da yake safunan ma har da na maza sai na siya har Abbaa da Kaka. Ina tafe zuciyata nata tunanin in kira Yaya Imam ko na ƙyale shi, har dai na fito bakin gate, tunda bai kira ni ba na tabbata wani babban uzurin ne ya riƙe shi, iyaka koƙari suna yi akaina, Abbaa zai rako ni kullum sai mun ci rabin hanya yake komawa, in dai kuma nayi evening to ya sakawa Yayyuna duty yau idan wannan ya ɗauko ni gobe wannan ne zai ɗauko ni.
Ina tsaye bakin gate na buɗe jaka ina laluben wayata sai naji gate man na ce min na matsa za'a wuce. Nayi gefe ce na ke ma ko Dr ne zai tafi sai naga ba motarsa ba ce. Na ɗaga waya na kira Yaya Imam yace,"Kin ganni na taho mashin ɗin nawa ya samu matsala yanzu haka ina wurin masu gyara, kiyi haƙuri gani nan zuwa kin ji".
Nace,"'To Yaya kana ta wajen ina? Na gaji ne wallahi yunwa ma na ke ji".
Yace,"Zan taho yanzu yi haƙuri".
Na kashe wayar ina sanyawa a jaka, na fara tafiyata ni ɗaya cikin tsoron da ya fara kama ni, kafin na gama fita a layin ne Allah ya taimake ni na samu me adaidaita sahu na kuwa yi saurin tsayar da shi, na faɗa masa inda zai kai ni yace na bayar da ɗari takwas. Na shiga ina faɗin Allah ya sauke mu lafiya, ban manta da adu'ar zama cikin mota ba, a koƙarinsa na tayar da babur ɗin motar da ke gefenmu tayi masa horn, na ɗan leƙa na kalla sai naga motar da ta fito daga asibiti ce ɗazu.
Mutumin da ke cikin motar ya fito ya ƙaraso yana cewa me adaidaitar,"Ina kayi?".
Yace masa,"Cikin gari nayi can wajen gidan sarki".
Yace,"Ok to nima can ɗin nayi motana ne kaga ya samu matsala, samun bakaniken da zai zo ma yanzu aiki ne".
Na ɗan saci ido na kalle shi jin yanda yake hausar gwari, kananun kaya ne jikinsa blue riga me dogon hannu da baƙin wando, yasa bakin gilashi da face mask da sam ba zaka gane fuskarsa ba, zubinsa ma ba na hausawa ba ne duk da fuskarsa a ɓoye take. Zan fito ya fara shiga sai naji yace,"Noo shige daga ciki".
Na matsa ciki ya shigo, ƙamshin turarensa ya daki hancina sai naji zuciyata ta motsa, kuma ban aune ba na tsinci gabana da faɗuwa sosai, yatsun hannuna har ji nayi suna rawa, sai da muka yi nisa sosai a tafiya kana na kira Yaya Imam nace masa ba sai yaje ba nama taho, ya gama min faɗansa ya kashe wayar. Ni dai na yita mamakin mutumin ganin bai sauka ba duk da cewa bai faɗi inda za'a kai shi ba, muna tafen ma me adaidaitar ke daɗa tambayarsa yace masa no worry muje kawai idan anzo inda zan sauka zan faɗa maka.
Me adadaitar yake ce masa,"Yallaɓai ko dai baƙo ne kai a garin".
Na jiyo sautin karamin murmushin da yay kawai ba tare da yace komai ba. Muka iso unguwarmu ina ta ma me adaidaitar kwatance har muka zo ƙofar gida, idona ya hasko min Abbaa tsaye a ƙofar gida hannayensa sarƙe a baya, ban san lokacin da na furta,"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, shikenan na kaɗe".
Mutumin ya juyo yana kallona me adaidaitar ma ya juyo, duk da banga ƙwayar idon da ke cikin gilashi ba na san dai ayar tambaya ce a cikinta dangane da furucin da nayi. Me adaidatar yace,"Hajiya akwai matsala ne?".
Ai kuwa kafin na buɗe baki Abbaa ya doka min tsawa da cewa,"Ba za ki fito ba ne".
Na haɗiye dunƙulallan yawu, mutumin ya fita nima na fito sai rawar jiki na ke yi, na ciro kuɗi na bawa me adaidaitar na wuce zan iya cewa ina jin yanda ƙwayar ido ta manne a jikina. Muryar Abbaa tuni ta cika kofar gidan da faɗansa akan tahowar da nayi ni kaɗai, ga layin yay tsit ƙarfe tara da arba'in a lokacin, faɗi yake da uban dare na kamo hanya na taho ina matsayin mace, da ba zan iya jiran Imam ɗin ba me yasa ban kira Yashaik ko Al'amin sun je sun taho da ni ba. Hannu ya kawo zai buge ni nayi saurin shigewa cikin gidan, Ummani ma na tsakar gida na shiga tace,"Ya za ki mana haka, ba dole ayi miki faɗa ba ga wayarki anata faman kira ba ki ɗaga ba".
Idona a waje nace,"Wallahi banji kiran ba na sakata a silent".
Abbaa ya shigo yana ci gaba da faɗin,"Idan kika kuma tahowa ke ɗaya sai ranki yayi mugun ɓaci, kuma faɗa min gidan uban wa kika tafi?".
Jikina ya kama ɓari na shiga wallacewa ina faɗin,"Allah Abbaa babu inda na je".
"Ƙarya kike yi in ba haka ba me ya hana ki ɗaga waya? Kin san Allah zan soke fita aikin nan? Ba dai kin yi karatun ba kin samu na tsira da mutunci, to aikin ba dole ba ne zan hana ki".
Tuni na durƙusa ƙasa hawayen idona na neman sakkowa nace,"Wallahi Abbaa babu inda na je, kayi haƙuri don girman Allah".
Uwa me tausayin ƴaƴanta tuni ta shiga bawa Abbaa haƙuri da tausarsa akan yay ƙasa da murya dare yayi, cikin gida ana jinsa haka maƙota ma duk suna ji. Ya watsa min wani mugun kallo da cewa,"Ba zan ɗauki sakarci irin haka ba, kike jira duk dare za'a zo a ɗauke ki, amma wallahi kika ƙara kuskuren tahowa ke ɗaya daga ranar kin gama aiki".
Yana faɗa ya shige ciki, nima na miƙe na wuce ɗakina, Ummani na leƙowa tace,"Abincinki yana ɗakina".
Ko takalmi ban iya cirewa ba na zauna ina goge hawayena tare da danasanin tahowar da nayi. Ko kayan ban cire ba na tashi na fita zuwa ɗakin Abbaa, sai da na tabbatar ya haƙura ya daina fushin kana nayi masa sallamar sai da safe na wuce ɗakin Ummani na ci abinci. Wajen sha ɗaya har na rufe ido naji wayata na ringing, da sauri na tashi na rarumota gudun kar Abbaa ya jiyo ƙararta, nifa mahaifina is very strict, bai ƙi ya zo ya ƙwace wayar ba, ban ɗaga ba sai da naga kiran yay yawa har sau uku sannan na ɗaga ana huɗun.
Nayi sallama aka amsa, shiru for some seconds sai aka ce,"Nurse Sa'ida ce?".
Na ce,"Ehh ita ce". Na faɗa ina jin muryan kaman na santa duk da cewan muryan namiji ne.
Sai aka ƙara cewa,"Sorry don Allah na kira ki da daddare, ɗazu na zo asibiti ne Dr Samuel yake bani number na ki yace duk sanda na zo na dinga nemanki, domin ke ɗin ƙwararriya ce wacca ta san makamar aikinta".
Babu shakka na san muryar sai dai ba zan ce ga inda na santa ba ko kuma ta wacece ba, a hankali yaci gaba da magana yana ce min yana fama da ciwon baya ne da ƙafa ko zan taimaka na recommending masa maganin da zai sha yanzu kafin zuwa da safe yaje asibiti. Na zage na buɗe murya ina ta kora masa bayani da tambayan ya yake ji, kusan minti goma haka sai naji ya katse ni da tambayan,"Babu dai wani damuwa ko?".
Na ce masa,"A'a babu, duk sanda kake neman taimako irin haka zaka iya kira na".
Sai ya sake cewa,"Thank you so much, but still ba ki cikin wani matsala dai ko?".
With confusion na ce,"Babu komai, kawai na dawo daga aiki ne yanzu na gaji ina so zan yi bacci". Na faɗa ina sauke wayan daga kunnena na kashe bayan ya cika ni da godiya.
Daga can ɓangaren Salim ya sauke ajiyan zuciya, sai yanzu ya samu relief jin muryanta ba cikin yanayi na damuwa ba kamar yanda ya tsammata, kenan babu wata matsala saboda sosai ya damu da yanayin da yaga Abbaa a ɗazu, ya san dole zata sha faɗa kam, don faɗan da Abbaa ya dinga mata a lokacin ji yay kaman ya fito ya ba da haƙuri, shi kansa ji yay ba zai iya barinta ta tafi ita ɗaya ba a wannan daren shiyasa ya aje motarsa ya shiga napep ɗin domin ya san idan yace ta zo ya rage mata hanya ba yarda zata yi ba.
Ya sauke a jiyan zuciyayana aje wayarsa, tare da jingina kai a gadon ta gefen ƙwayar idonsa kuma yana kallon Kudrat da ke gefensa tana bacci.
******Bayan kwana biyu yau tun tashina Ummani tace da na gama komai na gyara ɗakin Al'amin akwai baƙin da za'a yi anjima. Ban tsaya tambayarta ba ni dai ina gama wanke wanke na shiga na gyara tass, na sanya turaran wuta me bala'in ƙamshi da nasa ordarsa daga meduguri. Gidan duka ya ɗauka har Ummansu Hindatu sai da ta leƙo tana faɗin kamar gidan haihuwa ko sabuwar amarya.
Ummani tace na shirya zan rakata unguwa, nayi wanka na saka rigar bubu sai ce tayi lallai sai na sauya in ɗauko abayata da na siya kwanaki mana. Na ce an gama ranki ya daɗe, haka na ɗauko na saka na zauna zaman jiranta sai ƙorafi na ke ina Ummani ki zo mu tafi kin san ba wuri ɗaya kike zuwa ba, an ta shige shige kenan yanzu za ki ga yamma tayi.
Tace kar na dameta in ban rakata Yasmin zata rakata. Ban ƙara magana ba na fito da keken ɗinkina tsakar gida na hau ɗinka kayan wasu da za'a kaiwa bauchi. Lokacin yaro ya shigo yana cewa ana sallama da Abbaa, na tashi na leƙa ɗakin na faɗa masa, babu jimawa ya fito ya fita, can ya kuma dawowa yace da ni na ɗauko masa tabarma. Da kaina na kai soro na shimfiɗa kana na dawo ciki.
Abbaa ya leƙa daga waje, tsaye ya hangi Salim jingine da motarsa hannayensa harɗe saman ƙirji, cikin kamilalliyar shigarsa ta cofee ɗin yadi da ɗinkin irin na yare, shigarsa tayi masa bala'in kyau. Abbaa dai murmushi ya suɓuce masa, tun asubahin yau ko kuma yace tun a lokacin da yay sujjada ga ubangiji a cikin dare yana me neman zaɓinsa akan lamarin Salim da Ƴarsa yaji fargaba ya barsa yayin da ƙwarin gwiwan aurama Salim ƴarsa ya shige shi, kuma a yanzu da idanunsa ke kan yaron sai yake jin yana samun salama a cikin ransa dangane da lamarin.
Yaywa Salim izinin shigowa, ya tako cikin tafiyarsa ta namiji me cikar zati da kamala ya shigo soron lokacin Abbaa har ya zauna akan tabarmar, ya cire takalma ya nemi waje ya zauna, zaman nasa ma har sai da Abbaa yace masa tukunna don da tsugunawa yayi cikin jin nauyin zama a inda surukinsa ke zaune. Ya gurfanar da kansa gaban Abbaa kamar me neman gafara, da girmamawa da ladabi ya sake gaida Abbaa a karo na biyu, Abbaa ya amsa ƙwayar idonsa ƙyam akansa tun a ɗazun.
Abbaa yay nisa tare da sauke numfashi ya kira yi sunansa. "Salim ka ke ko?".
"Ehhh Abaa".
"To ya kake ya aiki?". "Alhamdulillahi Abbaa, fatan na same ku lafiya". "Lafiya lau, Salim ko za ki iya faɗa min dalilin zuwanka wurina?". Da wani ƙwarin gwiwa da jarumta irin tasa ta sojan gaske yace,"Abbaa na zo gare ka ne da ƙoƙon baran ka bani amanar rayuwar ƴarka Sa'ida...".
Abbaa ya katse shi,"Amana dai Salim? Ka kuwa san amana?". "Na sani Abbaa, ni musulmi ne cikakke, kuma ina da yaƙinin zan riƙe amanar shiyasa na ce aba ni ita". "Salim amana tana da girma, wutar Allah na cin wanda bai riƙeta ba". "Bana fatan na kasance cikin sahun maciya amana Abbaa, ka yarda da ni zan riƙe amanar da zaka bani tsakani da Allah".
Abbaa ya sake cewa,"Kai ka turo iyayenka kenan ko kuwa sun yi zuwan kan su ne?". "A'a Abbaa ni naje musu da maganar". "Amma me yasa baka fara zuwa da kan ka ba? Ko kuma kana ganin kawai don mahaifanka sun zo sai na ce musu na baka ƴata? Shin ka taɓa neman soyayyarta ne?".
Ya ƙara yin ƙasa da kai kafin a hankali yace,"Bamu da ƙarfin ikon da zamu zo kai tsaye mu ce zamu ne abu a bamu ta yanda muke so, na fi so ne a duk sanda wani babban lamari ya shiga gabana na fara saka manyana a ciki, musamman sha'ani me girman gaske irin wannan. Sa'ida kuma ban taɓa tunkararta ba, kawai dai na san da cewa in har iyaye suka amince min na nemi soyayyarta da sannu...".
Sai yay shiru bai iya ƙarasa faɗin abin da zai ce ba. Abbaa yace,"Da sannu me? Yi min bayani ina jinka".
Ya sarƙe yatsunsa da ƙyar ya iya cewa,"In har ta bani dama na shiga sahun manema aurenta da sannu zan koyar da ita so...". Sai kuma ya canja kalamin da cewa,"Da sannu zata aminta da ni".
Abbaa ya jinjina kai sannan yace,"To amma kai da kake da iyali mene naka na son ƙara aure Salim? Ba ku zaman lafiya ne ko kuwa dai lamarin wasu mazan na son wulaƙanta matayen su ne?".
Abbaa yay maganar wajen bugun cikin Salim ɗin. A hankali kuma cikin natsuwa Salim yace,"Babu ko ɗaya Abbaa, ina dai da sha'awan ƙara aure ne domin ko addini ya bamu damar yin hakan, idan har muna da iko kuma zamu yi adalci zamu iya ƙara aure. Sannan zaman lafiya iyaka gwargwado akwai shi tsakanina da iyalina, bani da nufin na ƙara aure don na ci mutuncin iyalina, ba zan ƙara aure don na cutar da wani ɓangaren ba, lamarin aure abinda Allah ya nufa shi ke kasancewa". [2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR05FT5* Idona da ke kallon fuskarsa sai naga kamar ya haska min da ƴar ƙaramar damuwa, na tsinkaye shi da ci gaba da faɗin. "Kina son sanin tarihina tun daga tushe?". Bai damu da jiran na amsa mishi ba ya ɗora da faɗin,"Mahaifina haifaffen garin Anambra state ne ɗan ƙabilar Igbo, Asalin sunansa na yare Kaodinakachi, sunan mahaifinsa Chibuzo Ibrahim Ude, sunan matarsa Isioma Debare kuma ƙabilar su guda, sai dai ita kirista ce bayan ta aure shi ne ta musulunta. Mahaifina shi ne na uku a ƴaƴansu, kasuwanci ya kai shi garin Oyo, a can garin ya haɗu da mahaifiyata Kafayat Oluwa Sunmola, ita kuma yoruba ce, soyayya me ƙarfin gaske ta shiga tsakaninsu wanda har su ke tunanin rayuwa ba tare da junansu ba. All tribes have an issue with each other ba wai tsakanin Igbo da Yaruba ba ne kawai, ƙalubalen farko da suka fara fuskanta a soyayyarsu shi ne ta ya zasu tunkari iyayensu da batun aure, duba da irin yaƙin da ke tsakanin ƙabilu biyun musamman idan aka zo ga ɓangaren sha'ani na aure. domin galibin iyayen ƙabilar Igbo ba sa goyon bayan ƴaƴansu maza su auri mace a wajen ƙabilarsu, an sha gumurzu kafin iyayen mahaifina su yarda ya auri mahaifiyata, sai dai duk da hakan sai ya kasance mahaifiyata bata jin daɗin auren saboda tsangwamar da Kakata ke mata, su ƙabilar Igbo in basa son abu to basa so, idan kuma suna so babu wanda ya kai su so, ta kai ta kawo har iyayen suka yi fushi da mahaifina suka kore shi daga gida, sai Baban Mahaifiyata ne ya ba su wuri, shi yaci gaba da tallafar al'amuran mahaifina tamkar ɗan cikinsa har ta kai ga matakin da ya shiga ya fita ya samar masa aikin soja, dalilin wannan karamci da halacci mahaifina ya sakaya sunan sirikinsa a jikin sunansa, madadin Sadiq Chibuzo Ibrahim sai yake amfani da Sadiq Ibrahim Oluwa, duk wasu takardun aikinsa da wannan sunan yake a amfani kuma da shi duniya ta sansa, sai bayan an haife ni ne aka samu fahimtar juna tsakanin mahaifina da iyayensa har suka yarda ya koma garesu tare da matarsa, lokacin da suka koma Anambra state an yaye ni sai aka bar ni wurin Maman Mamata, suka tafi da Yayana Chibuzo me sunan Kakanmu. na taso cikin soyayya da kulawar Kakana shi yasa nima na ke amfani da Salim Sadiq Oluwa kamar mahaifina madadin Salim Sadiq Chibuzo, sunana na yare Onochie don ko a garinmu da wajen aiki duk haka ake kira na. Papa mutum me mutunci sosai da sosai, ba ya nuna banbancin ƙabila don ko lokacin da Baban su Safiyya yaje neman auren Mamanta wato ƙanwar Mahaifina shi yay conviecing Kakana amma da ba za su taɓa bawa bahaushe auren ƴarsu ba".
Ya numfasa kafin yaci gaba,"Mahaifina babban soja ne, kuma nima soja ne aikina yafi kai ni cross river da Ebonyi, a baya da na zo gare ki da batun aure ne a matsayin saurayi, amma a yanzu ni ɗin me iyali ne, nayi aure da matana ɗaya Kudrat, tare da yarana uku Rofi'at, Isioma da kuma Foridat, ni da su dukka muna zaune a barrack ɗin Edo state".
Sai yay shiru ya ɗago yana kallona, nima shi ɗin na ke kallo da tsantsar mamaki, so na ke na auna bayanan da yake min domin kuwa na kasa fahimtar dalilin yi min su, ina ce zuwa yay kawai mu gaisa? Then why this information all of a sudden?
"Abbaa ya faɗa miki dalilin zuwana wajen ki?".
Kamar doluwa nayi saurin girgiza kai. Numfashi ya sauke ya gyara zama sosai tare da cewa,"Ki yi haƙuri da irin ƙarfin halina, haka na ke ni duk wani babban lamari nawa bayan Allah nah to manyana na ke fara sanyawa a ciki, kar ki ce na zaƙe da yawa kawai ina turo iyaye su nema min aure ba tare da na fara fuskantarki ba na nemi soyayyarki. No kawai zan fi samun ƙwarin gwiwa ne da sakewa idan ya zama na tunkare ki da amincewar iyayenki...Kwana biyu da suka wuce iyayena sun zo sun yi magana da mahaifinki...A yau kuma Abbaa ya bani damar in nemi yardar ki, amincewarki ita ce amincewarsa, ni da ke yanzu dukka ba yara ba ne balle a tsaya ɓata lokaci, musamman ma dai ni da na doshi hamsin da ƴan kai....".
Mamakin furucin ƙarshe ya doke wancan mamakin da tunani na, ban san lokacin da na waro ido waje kamar zasu faɗo ba ina kallonsa baki buɗe, a raina na maimaita hamsin fa! Ta gaske ko ta wasa?. Ashe a fili nayi furucin sai naga yay dariya yana tsefe gemunsa kamar wani saurayi ɗanye shagaf yace,"Kin ganni da jikin yara ko, shekaruna basa nunawa a jikina ne, shekarun tsufa fuskar yarinta, kuma hakan ai yafi ko?".
Ya faɗa yana ɗaga min gira dukka biyu, ni dai na san wannan mutumin na gabana bai kai hamsin ba, to me ma abin so a shekarun da yake kai kansa inda bai kai ba? Na ɗauke kai a hankali kuma naji ya ambaci sunana da harafin jaaa, ƙofofin gashin jikina suka buɗe na lanƙwashe yatsun ƙafafuna. "Sa'idaaaa! Ina son ki, ina miki irin son da ba zan iya misaltawa ba, da ƙyar na haƙura a wancan karon, amma a wannan karon bana jin akwai wasu adadin kalmomi na ban haƙuri da zasu yi tasirin da zan iya barwa wani soyayyata, ki yarda da ni ina faɗa miki abinda ke ƙuryar zuciyata ne, na miki alƙawarin kulawa, soyayya da ƙauna a cikin gidana...please ki ɗago ki kalle ni".
Ya faɗi hakan ni kuma sai na kasa wani motsi illa ma sadda kai ƙasa da na ƙara yi, sai ya miƙo hannu zai ɗago haɓata nayi saurin janyewa ina girgiza masa kai alamun kar ya fara. Sai ya sauke hannu yana faɗin,"Sorry! But please ki sanya idanunki cikin nawa domin ki yarda da abin da na ke faɗa miki ki kuma bani amsar tambayar da zan miki".
Da ƙyar na tattaro courage na sanya ƙwayar idona cikin tasa da ta kashe min jiki a lokaci guda. Ina ƙoƙarin janyewa sai yay saurin haɗe hannaye yana faɗin,"Please". Sai na fasa, shi kuma yace,"Za ki iya auren ƙabila? Za ki iya auren me mata? Kar ki tunani ta yanda za ki fara rayuwa a cikin ƙabilar da ba taki ba, family na suna da sauƙin kai, suna da mutunci, za su karɓe ki kamar ta su, ba su da matsala kuma ina tabbatar miki da ba za ki samu wata matsala tare da su ba, babu ta wani ɓangare da za ki fuskanci ƙalubale na banbancin yare".
Ganin na bada dukka attention ɗina sai ya gyaɗa min kai da cewa,"Uhmm ki ba ni amsa, ni ba zan tilasta miki ba, amma dai zan so ki bani dama, ki bani damar da zan kafa gwamnatin soyayyata a zuciyarki, ina da ƙwarin gwiwa ta wannan fannin".
Idanuwana suka cika da ruwan hawaye sai dai ba su samu nasarar gangarowa ba, a sanyaye na ce,"Wataƙila baka san wacece a gabanka ba ne...".