Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 27
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 27: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 27. "Akwai wata Sa'ida bayan ke ne a cikin gidan nan?". Na girgiza…
4,448 words
"Akwai wata Sa'ida bayan ke ne a cikin gidan nan?". Na girgiza masa kai da cewa,"Ba haka na ke nufi ba".
"To ya kike nufi?". "Ni bazawara ce ba badurwa ba, kuma ina tunanin ka zo da zummar samun waccan Sa'idar ne ba wannan da yanzu ke a gabanka ba". Na faɗi hakan ina rumtse ido sosai tare da jin wani ciwo a ƙasan raina.
Sautin murmushinsa ya fito sannan yace,"A alqur'ani ko hadisi faɗo min inda aka haramta auren bazawara, na san kina da ilimin hakan, ni kuma in har kika kawo aya ko hadisi zan tashi na bar gabanki kuma ba zan ƙara dawowa duniyarki ba".
"Babu". "To kuma kike ce min ke bazawara ce, mene da hakan?". "Saboda maza basa son auren bazawara". "Saboda bazawara bata darajar da za'a aureta kenan? Ko kuma ita abar ƙyamace da bata cancanci a sota a aureta ba? Look Sa'ida na san da cewa ke bazawara ce, kuma a haka na ke son ki kuma a haka zan aure ki kuma zan zauna da ke a hakan, ke na ke so, ke ɗin dai, hasalima idanuwan Salim basa miki kallon bazawara so kar ki ƙara furta min wannan sunan".
Sai kuma yay ƙasa da murya yana cewa,"Wallahi tallahi Sa'ida ina sonki ina ƙaunarki, ba da cuta ko yaudara ba, da gaske na ke miki aurenki zan yi don Allah ki ba ni dama".
Kawai sai na fashe da kuka sosai har ina kifa kaina a saman cinyoyina, domin kuwa kalamansa sun faman ciwon da ke zuciyata, Ta ya zan yarda da irin kalaman da Nazifi yay min? Ta ya zan kuma gasgata wani namijin har na yi kuskuren aurensa? Sai kawai na mike ina jin wani ɗaci da ƙunci sun mamaye ni, gani na ke kamar da gangan ya zo yana min wannan maganar, kamar saboda yaci mutuncina ne, to ai ni kuma har abada na rufe babin aure.
Kukan nawa sai ya rikita shi, inda shima yay saurin miƙewa yana ruƙo gefen rigata. A rikice yake tambayata,"Me ya saka ki kuka Sa'ida? Ni na faɗa miki wani abun mara daɗi ne? Don Allah ki yi haƙuri kin ji".
Nayi ƙoƙarin fizge rigata ashe ruƙon da yay mata da kyau, don haka na ɗago cikin kukana me ban tausayi na ce,"Ka sakeni, kuma don Allah kar ka ƙara dawowa gare ni da maganar aure, tsammanina ka zo ne mu gaisa matsayinka na Yayan Safiyya, ashe na tafka babban kuskuren zama ina sauraronka".
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Ya ambata tamkar wanda ya haɗu da wani ibtila'in. "Ka sake ni ka matsa ka bani hanya". Na faɗa a tsawace ina sake fashewa da kuka. Salim ya shafo kansa yana furzar da iska me zafi daga bakinsa. Tabbas da ina da damar da zansa hannayena na tunkuɗe shi daga gabana babu abin da zai hana ni aikata hakan. Kawai sai na tsinci muryarsa a marairaice yana cewa,"Don darajan Allah kar ki min haka, ni ba zan iya yafewa kaina ba idan ya zama ni ne silar wannan hawayen na ki, idan na faɗi wata kalma ne mara daɗi a gareki ki haƙuri ki yafe min kuskure ne ban san na aikata ba".
Kai na girgiza ina cewa,"Ni baka min komai ba, kawai dai ka rabu da ni kar ka ƙara min zancen aure".
Sai kawai ya tsare ni da ido da murya me bala'in sanyi da ban tausayi yace,"To mene laifina da ba za ki so ni ki aure ni ba? Ko ina da wani aibu da ban sani ba? Idan ina da shi ki faɗa min nayi alƙawarin zan gyara, kuma ni ban tilasta miki sai kin aure ni ba idan ba ki da ra'ayina zan ƙyale ki, ba zan miki dole ba amma kar ki zubar da hawaye ta dalilina, ba zan yafewa kaina ba".
Ajiyar zuciya ya sauke yana matsawa daga gabana, wayarsa da hularsa ya ɗauko ya dawo gabana yana cewa,"Ki yi haƙuri ki yafe min".
Yana faɗin hakan ya juya zai fita, na bi bayansa da kallo, ba tare da sani ba sai na tsinci kaina da cewa,"Ni kawai auren ne bana so da maganarsa, ina jin haushin duqk wata fuska da zata tunkare ni da batun aurena, na rigada na yiwa kaina alƙawarin ba zan kuma yin aure ba...".
Na faɗi hakan kuka na daɗa cin ƙarfina. Ban ankare ba naji ya kama hannuna wanda sai da naji tasirantuwar wani abu a jikina, ya jani ya zaunar da ni a bakin katifa. Ya durƙusa gabana yana dubana da kyau sannu a hankali ya fara cewa,"Bana so naji dalilin da yasa kika ɗau alwashin hakan, bana so naji ko kaɗan, sai dai hakan da kika ƙudurta ba mafita ba ce kuma ba hanya me kyau kika zaɓarwa kan ki ba, idan kika ce ba za ki kuma aure ba means ba ki son auren kenan and kar ki manta aure sunnar ma'aiki ne me ƙarfi, shi yace kuyi aure ku hayayyafa domin nayi alfari da ku. Ki manta da abubuwan da suka faru a baya ki fuskanci gaba domin shimfiɗa sabuwar rayuwa me kyau".
Sai yay shiru bai ce komai ba. Ni kuma nace,"To lallai sai nayi aure ne zan yi farin ciki? Lallai sai nayi ne rayuwata zata inganta?".
"Kina da amsar dukka tambayoyin ki a wajenki, sai dai ba za ki iya bawa kanki amsar hakan ba har sai kin sanyaya zuciyarki kin yi watsi da ƙudurin da kika ɗauka".
Sai ya miƙa hannu ya tsiyaya kunun aya a kofi ya miƙo min. Na karɓa kawai na riƙe ba tare da na kafa baki ba. Hawaye ya silalo saman kumatuna nace,"Ko da ka aure ni ba zaka iya zama da ni ba, zaka tsane ni ne, danginka ma ba za su so ni ba, zan zama abar ƙi da hantara a cikin gidanka da danginka".
"Saboda mune azzaluman farko?". Da sauri na girgiza masa kai,"A'a ba haka na ke nufi ba".
Naga ya haɗe rai yana cewa,"To me kike nufi?". "Saboda bana haihuwa, kuma babu namijin da zai iya rayuwa da mace me irin lalurata...".
Ya katse ni,"Wacce irin lalura kenan?". Na kalle shi,"Rashin haihuwa mana, ko kana sona yanzu daga baya zaka daina sona idan ban haifa maka yara ba, suma ƴan uwanka zan fuskanci ƙalubalen hakan daga gare su, kuma matarka ma zata dinga min gori".
Ina faɗin hakan ya zauna daga tsugunen da yake. "Au haba! Ashe haka aka yi?". Ya tanƙwashe ƙafa ya amshe kofin hannuna ya kafa baki ya shanye kunun ayar. Ya sauke yana yin gyatsa kana ya kalle ni kaɗan yace,"Ina son kukun aya sosai, wannan yayi daɗi matuƙa, ki cewa Ummani ɗanta ya na godiya Allah ya ƙara mata lafiya, and i hope kema kin iya me daɗin hakan?".
Ƙura masa ido nayi kafin na ɗan harare shi, sai shima naga ya galla min harar ido kamar zai zazzago ka rantse macece, kawai sai na tsinci kaina da yin dariya kafin na sha mur. "Ehh ai gwara ki sani ba ke ɗaya ke da ido ba, harara ce kowa ya iya ai".
"Ina maka zancen serious kana ɗauka da wasa, kuma na san ko Abbaa ya faɗa maka bana haihuwa don haka kar ka dage akan sai ka aure ni ba zaka yi farin ciki ba".
"Yau ba ki je aiki ba kenan? Ko duk zumuɗin zuwana ne da son ganina ya hana ki fita, to a albashinki ni babu ruwana, kar ki zo daga baya kina min ƙorafi an cire miki kuɗi".
Yay maganar da son shashantar da wancan zancen. Na tsinkaye shi da ƙara cewa,"Yanzu dai yaushe su Baba za su dawo ayi maganar sa rana? Ba na so ayi taking long, a yanda na tsara cikin satin nan su dawo a bada kuɗin aure a tsayar da rana wata guda, shima don na san za kice sai kin yi ƙaƙalen shirye shirye ne, to kafin dai mu shiga january na ke so na mallakeki ki zama matar lieutenant Salim".
Ɓata rai nayi ina masa wani kallo na ce,"To ni nace maka ina sonka ne da har kike lissafin ayi aure".
"Manta da wani so me wuyar dama shi ne mu fahimci juna kuma mun fahimta".
"Da yaushe ɗin muka fahimta?". "Ehhh kin fahimci ni mugu ne mara mutunci me wulaƙanta mace me tozaratata me cuzguna mata, ni kuma na fahimci ke ba kya haihuwa kuma an rubuta a goshinki ba za ki taɓa haihuwa ba, shikenan sai me ya rage kuma? Sai aure idan muka je can sai ayi ko wacce wacce".
Yanda yake zaro magana kamar bahaushen gaske, kuma magana ta masu karfin hali da zaƙewa, Na kauda kai gefe ina jin haushin ma maganar tasa, bai damu ba yaci gaba. "Safiyya ce babbar ƙawarki zan je na tambayeta sizes ɗin kayanki, tare zamu je haɗa lefen ko na haɗa da kaina ko kuma kuɗin zan ba ki?".
Na kuma yin shiru ina daɗa kallonsa da zaƙewarsa. Kai tsaye kuma yaci gaba,"Ba zan raba muku gida ba fa tare za ku zauna, yauwa bana son kan matana da yarana ya rabu, so na ke ko da yaushe inga iyalina a tare cikin farin ciki da kwanciyar hankali, kuma kinga abokiyar zamanki bata da matsala tana da sauƙin kai kamar dai ke ɗin nan".
A wani zabure na miƙe babu shiri ina neman hanyar fita. Ban san me yasa naji zuciyata ta motsa ba, sai ya kamo rigata ya maido ni na zauna, ina cin magani na ce,"Kar ka ƙara kama rigana".
Sai ce yay,"Kuɗin jikina ba su da yawa da na bada sadaki yanzu". Baki na murguɗa kawai, ni duk ya ishe ni raina sai ƙara ɓaci yake. "Allah ba ki haƙuri, yanzu dai yaushe zan dawo? So na ke dai nayi zuwa biyu uku duk inda zan yi na huɗu sai dai ya zamana na zo ɗaukarki ne gaba ɗaya".
Na ware ido. "Dama haka ake yi?". "To ni haka zan yi kuma na tabbata Abbaa zai yarje min, idan kuma kina da kuɗin biyan jirgi ko motar ƴan kai amarya ne shikenan sai ki yi zugar jama'a, ni dai ba me kuɗi ba ne da a kano zan zauna ne dai sai in iya cewa zan biya kuɗin mota".
Na dakatar da shi,"Kaga please joke apart and let be serious". Zama ya gyara yana tallafe haɓa ya maida hankalinsa gare ni da kyau. Nayi ƙasa da kai yatsuna a sarƙe nace,"Ni da gaske na ke maka ban da ra'ayin aure, ba zan ƙara yin wani auren ba, saboda haka ka janye maganarka kawai don Allah ka tafi wani wajen".
Kawai wai sai naga ya kifa kai yana kukan wasa, har da su shashsheƙa yana faɗin,"Yanzu ni wanne kalar zunubi na aikata da ban cancanci likita ta so ni ba".
Nace,"To ai ni ban ce bana sonka ba". Ya ɗago ido ya duben, na kulle ido kafin na ce,"Kuma ban ce ina sonka ba". Shi kuma yace,"Kuma ko darajan Safiyya da Umma ba zan ci ba?".
Nayi saurin cewa,"Za ka haɗa ni da ƙawata kenan". "Bari ma na kirata na shaida mata, ai ƙanwar tawa ƙawata ce".
Da sauri nace masa,"Aa don Allah kar ka faɗa mata, Safiyya akwai taking abu so serious".
"To ki ce kina sona kuma kin yarda za ki aure ni".
Raina still a cukule na ce,"Ba yanzu ba". "To sai yaushe?". "Sai sanda na gama nazari da tunani".
Ya ɗaga kafaɗa,"Tom shikenan na ba ki lokaci...yanzu zan wuce kar Abbaa yaga na jima".
Nayi saurin miƙewa ina cewa,"Tom". Shima ya miƙe yana faɗin,"Ai dama na san kin gaji da ni, kina ta zagina ma a zuciyarki".
Shiru nayi ban biye masa ba, haka dai ya tsaya kusa da ni yana shafa waya, ban yi masa sallama ba na fita a ɗakin na barsa, wa ma ya san nayi sallama ko ban yi ba haka na shiga gida, ina shiga ɗaki na faɗa kan katifa ina ta sauke numfarfashi, kaina a kife yake kan hannuna, ba tunani na ke ba haka ban san me yake cikin kaina da abinda ke haskawa a idona ba, amma dai cikin zuciyata ina jin zafi kamar an hura wuta. Na jima a haka can naji muryan Ummani na faɗin,"Masu karɓar ɗinki sun zo na ba su".
Nayi saurin miƙewa zaune da sanyin jiki nace,"Ummani kika ba su kuma, ban fa gama sanya stones ba".
"Su suka ce a ba su a haka wai yau za su saka, ina ce stones ɗin a ƙasa ne kawai ba ki saka ba?".
Na ɗaga kai alamar ehh ba tare da nayi magana ba. Sai tace,"To na haɗa su da Yasmin su tafi tare ta saka musu acan kafin su gama shiryawa, bana so Abbanku yaji ne ya fito ya kama faɗan rashin gamawar".
Nasa hannu ina goge hawayen da duk ya wanke min fuska, ina jin idonta akaina kafin tace,"Sai ki yi istikara ai ki nemi zaɓin Allah ba ra'ayin zuciyarki ba, shi kukan mene amfaninsa banda ɗorawa kai ciwo, kuma dai ai ba zuwa aka yi aka ce ana ƙin ki ba".
Na waiga ina dubanta na ce,"Amma Ummani ni kawai...".
Ba ta jira ƙarashen zancena ba tace,"A'a ba da ni aka yi maganar ba yana ɗaki kije ki sameshi, mene a ciki dan kin ce masa ba kya so, mu dai ai ba kwaɗaki zamu yi mu cinye ba, lokacin kuma da kika sakko akan ƙudurin na ki ai kinga kya auri sa'an Kakanki".
Tana faɗin haka ta fita tana cewa,"Ki fito ki tankaɗe min gari, ki kuma ƙarasa haɗa miyar gata can na ɗora a wuta".
Na koma na kwanta ina ta tunanin ta yanda zan yarda na komawa duniyar aure, Mazan ba duka suka zama ɗaya ba na sani, to amma zaƙin bakin namiji fa? Ni a ganina tunda har Nazifi ya canja to tabbas kowa ma zai iya sauyawa, kuma tunda har ya daina sona ya tsane ni akan rashin haihuwa to bana tunanin akwai wani Namiji da zai iya shimfiɗa rayuwar aurensa da ni a yanda na ke. Ringing ɗin wayata ya katsen tunani, na ɗauka na duba naga Safiyya ce, ban ɗaga ba saboda fushi na ke da ita don na san ta san komai game da zuwan Salim, sau uku tana kira ni kuwa nayi biris kamar ban gani ba, sai can ga message ɗinta ya shigo da cewa,_"Zancen gaskiya wannan karon kika ƙi ɗan uwana to zamu samu saɓani da ke, kuma Umma ma kanta tace zata san zaman da zata yi da ke in har kika guji ɗanta, ke dolenki ma ki so shi ki shirya zama amaryar ending month na gama magana"._
Ina gama karantawa na tura mata da reply ɗin,_"To Sa'adatu Abdurahman Madobi"._ wato uwata kenan. Har tsawon kwana huɗu ina ta tunanin matsaya, gaba ɗaya na kasa yanke shawara akan lamarin, har yanzu ban ji ina sha'awar sake yin aure ba, haka ban san ta inda zan fara kallon Safiyya na faɗa mata cewa ta sanar da ɗan uwanta ba zan aure shi ba, Abbaa dai bai min maganar ba tun ranar, shi kansa Salim ɗin tun ranar bai neme ni ba ko irin ɗan kiran nan bayan ya tafi, Ummani kuwa sai dai tayi ta jefa min magana cikin magana, bini bini tace yo Allah na tuba tsofaffi gasu nan da yawa a duniyar. Yau tunda na zo aiki duk na ke jina wani iri, sai dai wani ɓari na zuciyata nata karanta min ki yi istikara yau ki samu mafita ki huta. [2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR04FT5* "Masha Allah! Abbaa ya faɗa yana jinjina kai.
"Salim da gaske kake kana son ƴata tsakaninka da Allah ba domin wata manufa ba?".
"Ƙwarai Abbaa ina son Sa'ida ba tun yanzu ba, ko a wancan lokacin na haƙura ne saboda ta nuna bata sona, kuma ko a yanzu ma zan iya haƙura idan har ta ce ba zata iya aurena ba, ba zan zamar mata dole ba kamar yanda ba zan so ayi mata dole ba, ni dai burina ne auren nagartacciyar mace kamar Sa'ida, idan kuma hakan bata Faru ba na san da cewa Allah ne ya rubuta cewar ba zan rayu da ita ba a inuwa guda matsayin ma'aurata, kuma zan karɓi hakan a madadin ƙaddara".
Abbaa yay ɗan jim kafin ya sake cewa,"Ka san da cewa ita ba budurwa ba ce bazawara ce ƙaddara ya rabata da mijinta?".
"Na san da hakan Abbaa".
Abbaa ya ƙara mayar masa da cewa,"Fatan kowanne miji ne ya samu zuri'a tare da matar aurensa, Shekaran Sa'ida goma da aure bata taɓa haihuwa ba Salim".
Ya sauke numfashi kana cikin tattausan lafazi irin nasa yace,"Abbaa komai yin Allah ne, Haihuwa da rashinta dukka lamarin ubangiji ne, wataƙila ubangiji ya jinkirta mata lokaci ne wataƙila kuma bata ɗaya daga cikin waɗanda ubangiji ya tsara za su samu rabon hakan, Allah shi ne masani kuma shi yasan daidai na yanda ya tsara rayuwarta, kuma yanda ya tsara mata ɗin shi ne mafi alkhairinta ba don baya sonta cikin bayinsa ba...Abbaa ni Sa'ida na ke so zan kuma zauna da ita a kowanne irin yanayi babu cuta babu tsangwama babu kyara face cikin nuna kalawa da soyayya".
Abbaa ya murmusa, tun farkon fara maganarsu da Salim yaji yaron ya burgesa saboda irin lafuzansa da ke fita daga bakinsa a nutse, kalami na me kaifin tunani da sanin yakamata gami da hankali. Abunda ya sani lokacin da zai aurawa Sa'ida Nazifi bai ji zuciyarsa na ƙarfafa masa gwiwar hakan ba, haka bai ji aminci da salamar da yake ji a yanzu ba.
"Salim na amince maka ka nemi soyayyar ƴata, ka shiga layin zauwaran da suke neman auranta, idan har tayi amanna da kai ni kuma zan aura maka ita, zan baka amanarta, ina son ƴata ya kamata kan da wannan, ka rubuta hakan a tafin hannunka saboda gaba...sai dai akwai sharaɗi game da auren, idan ka amince faƙat idan baka amince ba to sai dai kayi haƙuri".
Salim da kansa ke ƙasa tun ɗazu yana murmushi me kyau saboda samun nasararsa ta amincewar da Abbaa yay masa, furucin Abbaan yasa shi ɗago kai ba tare da alamu na sarewa ko kuma karaya ba, domin kuwa yana da tabbacin zai iya bin kowanne sharaɗi ne muddin zai samu Sa'ida, sai dai sam ya kasa ko da kallon gefen da Abbaa ya ke kamar yanda yay niyya saboda girman kwarjinin da Abbaan yay masa.
Abbaa yace,"Ka shirya jin sharaɗin nawa?". "Ehh Abbaa".
"Yauwa! Sharaɗin shi ne ƴata tana aikin asibiti, da aikinta ka ganta saboda haka babu batun cewar idan ka aureta zaka dakatar da ita ma'ana zaka hanata zuwa aikinta, sannan tana burin ƙaro karatu anan gaba shima ba zaka hanata ba, bayan haka tana ƴan sana'ointa na hannu, ka yarda da wannan yarjejeniyar ko kuwa ya?".
Yay murmushin da sautinsa ya fita a ƙasan ransa, leɓensa kuma ya tale, to taya Abbaa yake tunanin cewa zai dakusarwa da Sa'ida karatunta ko kuma ya dakatar da ita aikinta? Idan da haka why zai shiga ya fita wajen ganin ta kawo wannan matsayin? Abinda yay mata don Allah yayi, kuma alƙawarinsa ne ba zata taɓa sanin hakan daga gare shi ba sai in Safiyya ce tayi katoɓarar faɗa mata duk da itama tayi masa alƙawari har abada ba zata sanar da Sa'ida ba shi ya ɗauki ɗawainiyar karatunta har matakin aikinta ba. Kuma ba ya so kowa ya sani ɗin domin za'a ga kamar yayi ne domin ya mallaketa, kuma itama with that reason zata iya zama with no other option ta tilastawa kanta saboda rama halacci da halacci.
"Abbaa na amince na karɓi sharuɗanka, ba zan zama me sauka daga kai ba, illa iyaka ma ni zan zama wanda zai ƙara tallafawa lamuran nata".
Abbaa yace,"Shikenan duk san da ka shirya kana iya zuwa ku gana da ita, amma bana so a ɗauki tsawon lokaci ana abu guda".
Wannan karan sai da Abbaa ya jiyo sautin sanyayyan murmushinsa na samun nasarar da yay. Yana kallon yacca ya gyara tankwashe ƙafarsa kafin ya shiga cewa,"Na gode sosai Abbaa, na gode da bani dama, kuma da yardar Allah ba zaka yi nadamar aura mini ƴarka ba, nayi maka alƙawarin riƙe amanar da ka bani da dukkan ƙarfin ikona, zan kula da ita bisa gaskiya da aldalci".
Abba ya murmusa kafin yace"Ina fatan hakan ta kasance, Allah ya baka ikon tsayawa a tafarkin da yake daidai, Allah yay maka albarka".
"Amin ya Allah Abbaa, Allah ya ƙara muku lafiya da tsawon cin kwana".
Shiru ya gimla tunanin Abbaa sun gama da shi ko zai tafi ne, amma sai yaga ya gyara zama yana aikin jujjuya yatsunsa, Abbaa dai kallonsa yake tayi da murmushi tare da fatan Sa'ida ta amince. "Za ka wuce ne?".
Salim na ƙara yin ƙasa da kai da ƙyar ya iya buɗe baki cikin jin nauyi yace,"Abbaa idan ba damuwa ko zan iya ganinta kafin na wuce?".
Abbaa ya yunƙura ya miƙe yana cewa,"Babu matsala ka ɗan jira".
Abbaa ya wuce cikin gida, kai tsaye ɗakin Ummani ya shiga, tana zaune ita da Walida tana tsefe mata kai ya same su. Ummani ta bisa da kallo tana faɗin,"To ya ake ciki?". Tayi tambayar da zaƙuwa.
"Yana jiranta sai ki mata magana, amma kin san bani son tsayuwan ƙofar gida".
Ummani ta saki kan Walida tana cewa,"Ahh ai dama tun da safe nasa ta kimtsa ɗakin Al'amin, ko kuwa su zauna a soron?".
Yay ɗan jima kafin yace,"Shikenan su zauna can ɗin".
"Ɗakin Al'amin ɗin?". "Ehh". "To bari na faɗa mata ta kimtsa ko".
Ta faɗa tana fita a ɗakin shi kuma Abbaa na tsokanar Walida da ƙwaƙwido, ta miƙe tana taɓara ya kama hannunta suka wuce ɗakinsa. Ummani na fitowa ta ƙwala kiran Yasmin wacca ke can wurin Kaka, sai gata da sauri ta fito tana zuwa Ummani ta bata maƙulli tace,"Je ki soro za ki ga baƙo ku gaisa ki buɗe masa ɗakin Al'amin kice an ce ya shiga, idan ba ya nan ki duba shi a ƙofar gida".
Yasmin ta karɓa maƙullin ta fita, a soron ta sameshi zaune yana karkaɗa maƙullan hannunsa, ta durƙusa tana gaida shi, bayan sun gaisa ne ta buɗe ɗakin kana ta dawo ta kuma durƙusawa gabansa tace,"Ummani tace ka shiga daga ciki". Yanayin ladabin yarinyar sai ya burge shi, yana mata murmushi yace,"Mene sunanki?".
"Sa'adatu amma Yasmin ake ce min".
Yace,"Umm nice name, kice ina gaida Ummani idan kin shiga".
Ta amsa da to daga bisani shi kuma ya miƙe ya shiga daga cikin ɗakin. Zamansa ba daɗewa Yasmin ta kuma dawowa ɗauke da farantin tangaran da jug da ƙananun kofuna akai sai purewater guda uku.
Ina zaune a ɗaki ina saka stones ɗin rigar dana gama ɗinkawa ɗazu, ban san me ya same ni ba tun a ɗazun dai na ke jina a cikin wani irin yanayi da na kasa gane masa. Abunda ban taɓa yi ba tun mutuwar aurena wai na zauna ina tunanin aure ko sha'awarsa, amma tunda na hau kan keke wani banzan tunani ke neman dagula min lissafi. Kuma rabon da inji a raina na tuna da tsohon mijina da irin rayuwar da nayi a gidansa wallahi tallahi har na manta, amma yau ni ce tunanin Nazifi ke zuwar min da jin cewa ina ma na haɗu da shi ya ganni yaga yanda na koma da kuma irin matakin da Allah ya kai ni, kuma har na ke sha'awar ina ma na samu mijin da zai goge min tabon da Nazifi ya bar min shi da ƴan uwansa.
Ummani ta shigo ɗakin da sassarfa tana cewa da ni,"Ke tashi yi da sauri ki gyara jikin ki".
To na san fita zamu yi dama, saboda haka na miƙe ina gyara fuskata, ina ta kallon Ummani da farin ciki a tare da ita nace,"Wai me ya faru Ummani naga sai murna kike".
"Aa to ba ki so kiga ina farin ciki ne?". "Ina ni, ai burina ku kasance cikin farin ciki a ko da yaushe".
Na faɗa ina sanya pin a jikin veil ɗin da na yafa na ke kallon Ummani da annurin fuskarta ke ƙaruwa na ce,"To Ummani ai ke ba ki shirya ba".
Tana murmushi me faɗi tace"Ai mun fasa waccan fitar, wannan shirin na ki ne ke ɗaya, kin gama?".
Nace,"Ehh to amma me yasa kika fasa? Allah yasa ba Abbaa ne ya hana ki ba kinga dai kar a kuma abin kunyar da aka yi aƙi zuwar Hajiya Tabawa gaisuwa".
Tasa hannu cikin jakata tana ɗauko turare ta buɗe tana ƙara feshe ni da shi kamar wadda akewa kamun aure tace,"Bar batun can ko gobe ma je insha Allahu, kije ɗakin Al'amin akwai baƙo ku gaisa da shi".
Da mamaki ƙarara na ke kallonta na ce,"Gaida baƙo kuma Ummani sai naje a haka, ina lefin hijabi ma".
Ta ɓata fuska tana kama hannuna,"To matar liman, yau dai ɗaya mene laifi a ciki, ba ki ga kyan da kika yi a hakan ba ne, duk wanda ya kalle ki sai ya ƙara kallonki yanda kika san balarabiya".
Murmushi nayi da har haƙorana dukka suka bayyana. "Allah kin yi kyau da gaske na ke faɗa miki, tsab sai kin daɗa sace zuciya".
Sai naji kunya ta kama ni, tare da sabon mamaki wanda na kasa samun haske a inda Ummani ta dosa. Tare muka fito a ɗakin ina aikin ɓata fuska don tunda tace baƙo naji sam ban son zuwa gaisuwar balle kuma a cikin shigar da na ke. Zungurar kai nayi ina faman jan ƙafafu takalmi na sharaf sharaf Ummani ta figo ni,"Wai ke ƙaramar yarinya ce, ya za ki tafi a haka".
Na rufe ido na buɗe ina karyar da kai na ce,"Ummani shin baƙon wajen wa ya zo ne?".
"Wurin ki ya zo, don haka ki natsu ki yi tafiya a yangance irin ta mace me tsada kamar ki".
Na ƙanƙance ido da cewa,"Baƙo ya zo wurina? Kuma Ummani kike ta murna? Ni ai na muka yi da wani zai zo wurina? Gaskiya ba inda zani idan ya gaji ya tafi". Na faɗi hakan da haƙiƙanin bɓacin rai a tare da ni ina nufin juyawa na koma ɗaki.
Harara ta wurga min tana cewa,"Idan ke baku yi da shi zai zo ba ai yayi da Abbaanku, na faɗa masa kin ce ba za ki ba ko ƙaƙa?".
Jin haka na turo baki gaba ina haɗe gira sama da ƙasa na nufi soro ba don son raina ba, sai dai me! da zuwana soron naji gabana yayi mugu mugun faɗuwar da sai da na kai hannu na dafa bango, haka kawai na tsinci ƙafafuna da yin karkarwa. Da ƙyar na dawo hayyacina daga fitar da nayi daga cikinsa na ɗan lokaci, domin kuwa ƙamshin turaren da ya gauraye dukka soron da kuma tsadaddan takalmin da idona ya sauka akai sai ya nemi ya burkita ni.