Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 28
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 28: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 28. Na haɗiyi yawu ina cire takalmana a kusa da wanda na ke gani,…
4,495 words
Na haɗiyi yawu ina cire takalmana a kusa da wanda na ke gani, ƙafafuna suka ɗaga da kansu suka shigar da ni ciki, da yanayina na sanyi nayi sallama da ƴar ƙaramar muryar da zata ɗauki hankali ko ai'na ne, kamar wata sokuwa haka na maƙale a bakin ƙofa kaina a ƙasa na kasa sarrafa kaina saboda yacca na ke jin ido ya manne akaina da kallo.
A karo na biyu na ƙara cewa,"Salamu alaikum". Ban sani ba ko an amsa a wannan lokacin domin kuwa kunnena a toshe yake dumm haka na ke ji a cikinsa tun ɗazu. Wucewar bugun zuciyata sau ɗaya, biyu, uku, huɗu naji kamar babu motsin halitta a ɗakin saboda haka na ɗago ido a tsorace, karaf ƙwayar idona ta sauka akansa da yay saurin sadda nasa kan ƙasa kamar ba daga kaina ya sauke kallonsa ba.
Zaune yake a gefen katifa, ya miƙe ƙafafunsa da na gansu dogaye, hularsa da ya cire ta yare a gefensa, yana wasa da yatsun hannunsa, kallonsa na ke da son na fahimto wani abu sai ji nayi na mugun tsorata dalilin jin ance,"Ga wani abu nan wajen ƙafarki". Ƙara na ƙwalla, kuma maimakon in yi waje sai na faɗo cikin ɗakin ba tare da sanin yanda aka yi na dira a tsakiyar ɗakin ba, idona rumtse jikina sai kyarma yake, cikin bakina ina faɗin kalmar la'ila ha'illa anta a hankali, saboda tsananin tsoro da furgicin da na shiga har hawaye na sakko min.
Na jima a haka na kasa buɗe idanuna, sai naji kamar an rufa min abu akaina wanda hakan yasa ni buɗe idanuna a hankali, sai naga mutum tsaye a gabana, faffaɗan ƙirjinsa yay min rumfar na zama kamar wata ɓeranya a gaban nasa ƴar firit, a hankali kunnuwana ke jiyo min sautin bugun zuciya wanda na tabbatar da haƙikanin ba nawa ba ne nasa ne, sai naji wani dunƙulallan abu ya wuce ta maƙoshina gabana na tsananta faɗuwa sosai, so na ke tayi na ɗaga ƙafata na matsa daga baya amma ina kamar akan tarko na maƙale sam na kasa motsa ƙafata ko guda ɗaya.
Cikin wani irin yanayi da na ke jina a cikinsa kasantuwar kusancinmu, na yi saurin ɗauke idona daga kan ƙirjinsa da na ke mamakin faɗinsa ina kai wa saman kamilallar fuskar da ta ƙawatu da kewayayyen saje me haɗe da gemu. Kuma karaf ƙwayar idon mu ta sarƙe ata juna, lokaci guda naji jiri na neman ɗibana ya watsar, nayi saurin dunƙule hannu ina riƙe kaina a tsayen, irin murmushin da ake kira da killer smile ya saki wanda sautinsa yay sanadin girgizawar allon ƙirjina nayi saurin ɗauke ƙwayar idona daga cikin tasa, ban saba da irin wannan kusancin ba sam da wanda ba muharramina ba, don haka kaina na ƙasa ina rawan jiki na shiga ja da baya yayin da ya daɗa kiɗima ni da amon muryarsa da ya fito lokaci ɗaya da cewa,"Am sorry ban tsammaci za ki tsorata da yawa haka ba, nayi hakan ne domin ƙafafun da suka maƙale wuri ɗaya su samu takowa zuwa ciki".
Ina micincina idanu na ce,"To baka san ko a addinan ce babu kyau tsorata musulmi ba".
"Tuba na ke yi ba zan ƙara ba daga ranar yau, amma ki sani kina da me ba ki kariya kar wani abu ya ƙara tsorata ki".
Ni dai ja nake da baya har na zube kan ƴar ƙaramar plastic chair ɗin ɗakin ƙirjina sai faman sama da ƙasa yake yi. So na ke na ɗaga ido na kalla fuskar da na yiwa kallo ɗaya saboda na tabbatar da zargina. Sai kuma ringtone ɗin iphone ya cika ɗakin, wanda da sauri naga ya matsa daga inda yake ya isa katifar ya ɗauka, sai jinsa nayi yana magana cikin wani irin yare kamar jagwalgwalo babu daɗin ji, duk sai naji maganar tana hawar min saman kai har ta kai ga na rufe ido ina gwame fuska.
"Ina wuni". Da sauri na buɗe idona ina dawowa cikin duniyar da na bari jin murya a gaf da ni, na kalle shi muka haɗa ido sai na kasa ɗauke kallona a kansa gaba ɗaya kuma na diririce. Zuciyata ta amsa da sunansa,"Salim!". Mutumin da na sani shekaru goma sha da suka wuce, mutumin da watannin baya da suka wuce naga hotonsa a album ɗin bikin Safiyya.
Naja numfashi inda na haɗe da ƙamshinsa da ke tsumani na zuƙe, sannu a hankali ƙamshin turarensa ya ɗebe ni ya kaini tunanin germany, sauka a airport, cikin napep. Ba tare da sani ba kawai na tsinci bakina da furta,"Kai ne?".
Sai naga ya ɗaga gira dukka biyu yana kallona kawai, kafin yace,"Ai na?".
Na tsuke gira ina tuna komai daki daki na ce,"A airpot ranar da na dawo, da kuma ranar ma a adaidaita".
Sai ya lumshe ido yana girgiza min kai alamun a'a. Na ɗan duki ƙafa a ƙasa na ce,"A'a wannan ƙamshin ne".
Ba zan ce ga da irin muryar da nayi magana ba don ba zan iya tantancewa ba, amma sai naji ya kwaikwayi muryan da cewa,"Ba wannan ba ne, irin wannan ɗin ne".
Kawai sai kunya ta kama ni na kai hannu ina rufe fuska, har ga Allah nema na ke na kasa controlling kaina ba don komai ba sai saboda ƙamshinsa da shi kansa da cikar haibarsa tayi gama gama da ɗakin musamman da yake zaune a gabana. Dariya naji yayi ƴar ƙarama yana maimaita gaisuwar da yayi. Sai na ɗan saci kallonsa, ni ya kamata ace na gaida shi ai to amma ta ya zan samu sakewar hakan mutum babba na zaune a gabana kamar yarona?
"Ba za ki amsa ba?".
Sai na samu kaina da cewa,"Ai kana zaune a gabana kuma ni ya kamata na gaishe ka".
"Ni dai a amsa mini domin kuwa cancantar Sarauniya ne da isarta a duƙa a gabanta a gaida ita, musamman ga mutumin da ya zo da ƙoƙon bara".
Tsintar kalamin nasa nayi har ɓargo da jijiyoyin jikina, kuma kafin na ankare sai gani nayi ya haɗe hannayensa alaman roƙo gami da ɗan karayar da kai yana cewa,"Please a amsa min, domin a ƙage na ke da na miƙo ƙoƙon barana bani a karo na biyu".
Baki na buɗe ganin yacca yay da fuska kaman ƙaramin yaron da ke shagwaɓar ayi masa abinda yake so. Sai ya miƙo hannunsa yay kamar zai zura yatsa cikin sakakkun laɓɓana nayi saurin kauda fuska gefe cike da kunyar da ta kama ni, domin kuwa surar fuskarsa ce ta ɗauki a hankali, kallon da ban samu damar yi masa a wancan lokacin ba, dama wannan kyan ne Safiyya take ta faɗa min? Amma kuwa idan haka ne Allah ya saka masa domin me hoto ma ya rage masa kyau sosai da sosai.
Yunƙurawa nayi zan tashi yay saurin dakatar da ni,"Please koma ki zauna". Ya faɗi hakan yana gyara zaman tanƙwashe ƙafafunsa tare da mayar da yanayinsa na masu magana da gasken gaske. Sai na ce,"To don Allah ka tashi a gabana".
Wani kallo yay min yana sosa gira sannan yace,"Ni fa ki ƙyale ni a yanda kika ganni, ki zauna kawai muyi magananmu, ba dafa ki zanyi na cinye ba, in ma zan yi hakan tukunna dai. Muhimmiyar magana ce ta sani na ke zaune haka a gabanki saboda haka koma ki zauna, idan kuma salon zaman ne bai ba sai na gyara".
Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa ya dire gwiwoyi a ƙasa. Da sauri na shiga girgiza masa kai ina cewa,"A'a du Allah". Komawa nayi na zauna kamar me koyon zaman, shi kuma ya shafo fuska yana girgiza kai kafin yace,"Zan iya sake gabatar da kaina?".
Kai kawai na kaɗa masa alaman ehh. Da yanayin barkwanci yace,"Awwa Allah sa dai kar ki ce wannan ya fiya naci kamar in mammake shi".
Furucin ya ban dariya na ɗan dara kafin kuma na haɗe rai. Kuma sai ji nayi yace,"Ki gama haɗe haɗen ranki indai za ki buɗen ƙofa shikenan. Anyway kamar yanda na faɗa miki a baya ne My name is Salim Sadiq Oluwa, ni ɗan ƙabilar igbo ne.....".
[2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR07FT5* Ina kallonsa ya miƙe tare da jan kujera baya ya bar wajen, haka na bi bayansa da ido kamar me shirin tashi ta bisa, har ya ɓacewa ganina ban ɗauke ido ba, sai daga baya na kulle idanuna ina kifa kai saman dining table ɗin, wannan ne irin son da yake faɗi? a haka zan yi auren ana min famin ciwo? A hakan ake cewa za'a mantar da ni baya? A haka za'a cika alƙawarin? Ji nayi na ƙoshi da abincin da na ke ta marmarin ci, me yasa ma zan damu da shareni ɗin da yay? Bayan hakan ban san me ya tsaya min a zuciya ba har na ke jin ƙunci da ɓacin rai. Tashi nayi na bar wajen, toilet na shiga na wanko fuskata nayo alwala jin ana yin kirayen sallar la'asar, ina idarwa na ɗebi kayana na bar gidan ba tare da na yiwa Safiyya sallama ba tana can sama, ni ba zan wani tsaya sauraronta ba balle ta ƙara ɓata min rai, haushinta ma na ke ji.
A mota ina ta ganin kiranta na ƙi ɗagawa, nayi jugum kamar wata mara lafiya haka na koma, tsabar nayi nisa a tunani ma me adaidaitar na tambayana canji ne a hannuna amma ina ban san yana yi ba har sai da matar da ta sauka ta taɓo ni, nayi firgigit na buɗe jaka na miƙa masa, su biyun suka ce min ya kamata na rage tunani kar hakan ya zamar min illa, kai kawai na kaɗa musu, to ni ban san ma tunanin me na ke yi ba, na dai san kawai na bar hayyacina ne, amma na rasa dalilin da yasa Salim ya tsaya min a rai, akan me zai wulaƙanta ni? Kuma da ya ɗakko bindiga ya aje mene nufinsa? Barazana zai yi min ko kuwa shima zai min tuhumar da bani da laifi akai? Ba zan so shi ba tabbas, kuma ba zan taɓa auransa ba ko za'a tashi duniya, mene tunaninsa zan kuma bari wani ɗa namiji ya wulakanta ni ne? To shi ya san wani soja ni ban sansa ba, sai kawai na rumtse ido sosai ina jin kamar na buga kaina jikin ƙarfen motar ko na samu hotonsa ya bar haska min a cikin ido.
Ba don me napep ɗin ɗan mutunci ba ne tsaf zai iya fusata yay gaba da ni, ko yanzu sai da yasa aka taɓo ni kafin na ɗago na basa amsar,"Cikin layi zamu shiga". A ƙofar gida na samu Yashaik zaune suna hira shi da su Anas ɗan wajen Baba Tijjani, na durƙusa na gaida su na wuce ciki. Hayaniya ce ta fara min maraba a tsakar gida, idona ya kai ƙofar ɗakin Ummani, naga dandazon takalma kamar ana biki, yau su Ummani ansha baƙi kenan, daɗin da naji ba kowa a tsakar gidan sai ƴan yara da ke wasan su can wajen barandar shiga ɓangaren Baba Saminu, ba na jin zan iya shiga in ta faman gaisuwa ana faman yi min tambaya kawai na tsallake na shige ɗakina.
Jaka kawai na rataye amma ko kayan jikina ban cire ba na kwanta, ba wai don bacci ba sai don samun sassaucin abinda na ke ji yana taso min a ƙasan zuciya, a haka kuma har bacci ɓarawo ya sace ni sai can cikin bacci naji ana tashina, na farka a firgice gabana na mugun faɗuwa sai ambaton innalillahi na ke yi, dama illar baccin yamma kenan shiyasa duk abinda aka ce maka babu kyau a musulunce to kawai ka haƙura da shi.
Jikina har wani rawa yake yi Maman Khairi ta ruƙoni tana,"Ke lafiya?".
Na buɗe ido na kalleta ina haɗiye yawu me wahala na ce,"Maman Khairi na tsorata ne".
"Kema ai kin san baccin yamma babu kyau, wallahi da irin baccin yammar nan wata mata bata farka da idanu a buɗe ba sanadiyar makancewarta kenan, baccin yamma har hauka yana sawa, sai kita innalillahi da la'ila ha illa anta".
Miƙewa nayi na fita nayo alwala, duk na ruɗe ma ban san magribar bata ƙarasa ba, sai bayan na yo na dawo zan tayar da sallah take ce min,"To ai ba'ai ko kira ba".
Na sauke gwauron numfashi kana na zauna muka shiga gaisawa da ita, sai naji tana wata magana ta daban da ban san ina ta nufa ba. "Ai bamu san kin dawo ba ke muke jira tun ɗazu da tuni mun wuce, to Allah ya sanya albarka ya tabbatar mana da alkhairi ya kuma sa rabo ne duniya da lahira".
Ta faɗa da murmushinta gami da nuna murna zuwa gare ni, baki na saki ina bin ta da kallo har ta miƙe tana gyara goyon Sufwan, tayi ƙofa zata fita tana ƙara cewa,"To matar soja mu mun tafi, wai sai yaushe za ki ɗinka min kayan Maama ne, ku fa telolin gida tsiyarku kenan".
Ɗan guntun murmushi nayi na ce,"Kai Maman Khairi zan bawa Babanta ya kawo mata dai in huta da mita".
Da haka ta fice, nima na miƙe na fita da mutuwar jiki raina duk a dagule, na shiga ɗakin Ummani ganina duk suka zubo min idanu, ashema ba wasu baƙi ba ne kamar yanda na zata, ƴan uwan Ummani ne yayyanta da ƙannenta, sai su Maman Yasmin ita Maman Khairi ta tafi, sai kuma wata ƙanwar su Abbaa da suke uba ɗaya Mama A'i ita yaushe rabona ma da ita.
Hajjo da ke gefen Ummani tace,"A'a likita likita an dawo".
Na shiga daga ciki ina duƙawa na gaida su, duk suka amsa min suna tambayana ya wurin aiki. Na yiwa Ummani sannu da gida ina ƙoƙarin miƙewa sai naji suma suna bina da kalmar Allah tabbatar da alkhairi, kaina ya ɗaure musamman da naji Mama A'i na faɗin,"Kun ga yanzu sai na tsokani duk wanda na ga dama a najeriya tunda dai muna da soja a hannu".
Umman Batula tace,"Ai kuwa dai mijin ƴarki guda soja, ai ki taɓa dukka wanda kika ga dama da hujja".
Suka yi maganan cikin raha ana dariya. Umman Batula ta ƙara cewa,"Yanzu ya kama watan gobe kenan?".
Sai Ummani tace,"Ehh to su da ƙarshen watan nan suka zo, kinga ya kama sati uku, amma dai sun tsaya akan cewar zai yi musu magana daga nan zuwa gobe, yace ai ba gaggawa ake ba".
Na rufe baki na buɗe yafi ƙarfin sau goma, yanda na ke kallon mahaifiyar tawa kuwa tamkar ban taɓa ganinta ba a duniya, me kalamanta suke nufi kenan? Sai kawai naga ta miƙe tana faɗin,"Kin ci abinci?".
Na girgiza mata kai ina bin bayanta wajen ficewa a ɗakin, yanda na ke tafiya kamar wadda tayi kashin wando ko wadda ba laka a jikinta. A kitchen na sameta ita dai na kasa gane yanayinta amma da bayyanuwar farin ciki a tare da ita. "Ko ba ki da lafiya ne?".
Maganarta ta dawo da ni daga gajeran tunanin da na tafi, kamar dai na gama fahimtar komai to amma ba hakan ba ne dole ina buƙatar ƙarin bayani, na kaɗa kai ina cewa,"Lafiyata ƙalau, tun ɗazu ma fa na dawo bacci nayi".
"Kuma ki dawo ba ki leƙa kin ce min kin dawo ba, ko da wata matsalar ne?".
Na sake girgiza mata kai alamun a'a amma a haƙikanin gaskiya tambaya ce fal a bakina. Ta miƙo min kwanon abincin tana cewa,"To ungo idan kuma ba za ki ci shinkafar ba akwai sauran gurasa da Umman Batula ta kawo gata can ɗaki ki ɗakko ki kwaɗanta ko ki ci da miya".
Na ɗan kalleta na ce,"Gurasar zan ci, amma Ummani to naji kuna yin wata magana ne".
Tayi min wani duba kafin tace,"Maganar me?".
Sai nayi ƙasa da kai ina wasa da yatsu na ce,"Kaman maganar aure kuke yi".
Ta ce,"Ehhh mana, da safe bayan tafiyarki Alhaji Babangida suka kawo kuɗin aure da sa rana, amma dai zai neme ki ai ki jira ya dawo kiji daga bakinsa".
Sai naji maganartata tamkar saukar aradu, na ɗago ido wanda tuni ya cika da ruwan hawaye na kalleta na ce,"Ummani kawai sai ya kawo kuɗin aure bai ji ta bakina ba, Ummani tun fa ranar da ya zo bai ƙara nemana ba, kuma ni ban ce masa na amince ba, har yau ban ba shi amsa ba, bafa sona ma yake yi da gaske ba Ummani, ta ya Abbaa zai yarda ya karɓi kuɗinsa".
"Yo shi Abbaanki da yaji ba ki tunkare shi da maganar ba ai zatonsa kunya kike ji, shi yasa ya ɗauki shirunki a matsayin ehh, idan ya dawo kya masa bayani ba zai ji daga bakina ba".
Tana gama faɗin hakan ta wuce ta barni nan tsaye, hannu nasa na goge hawayena, wacca gurasa kuma zan iya ci bayan mugun soja na neman sakani a tsaka me wuya, Haka ake aure dama babu soyayya? Haka ake aure babu fahimtar juna da amincewar juna? Haka ake aure da nuna isa da gadara? Me ya taka kuma me yake shirin aikatawa? Ɗaki na wuce jiyo wayata na ringing, Hassana Tijjani ce yaushe rabona da ita, kamar ba zan ɗaga ba saboda kar taji yanayin muryata ta kama tambayata menene, sai daga baya kawai na ɗaga ɗin dai, bayan na amsa sallamarta sai ta kama ƙorafin amana bata ce haka ba, bata yi tunanin bare na ɗauketa ba, yanzu zan yi aure shi ne ban faɗa mata ba, to taga invitation a status ɗin Safiyya kuma ta gode, ba zata ɓoye min ba zancen gaskiya bata ji daɗi ba.
Ba ta jira cewata ba kawai ta kashe wayarta, ni kuwa ina zan iya bin bayanta in bata haƙuri alhalin ni kaina ba cikin jin daɗin na ke ba, bata san nima rashin kyautawa aka min ba, sai kace wata ƙaramar yarinya za'a nemi ayi min auren dole. Tunawa da Safiyya raina ya ƙara tugunzuma na ɗauka wayar na danna mata kira, tana ɗagawa ban jira cewarta ba cikin masifa na ce mata.
"Yanzu abinda ku ka yi min ke da Yayan na ki kun kyauta kenan? Ke tsabar zaƙewa ma har da su zuwa kina faɗawa duniya, yaushe nace masa na amince zan aure shi da har ya iya rawan jikin kawo kuɗin aure? to ni ba zan aure shi ba ki faɗa masa, ba zan auri wanda bai da kulawa ba, idan ma ya aure ni to ya tabbata gangar jikina zai aura ba zai samu soyayya daga gare ni ba kamar yanda nima ba zan yarda da soyayyar dole ba, kuma ina faɗa miki tsakani da Allah banji daɗin abinda kika min ba kuma ba ki kyauta min ba, wannan ai shiga rayuwata ne".
Kawai kuma sai na fashe da kuka ina ce mata,"Ni fa ban ce masa ina sonsa ba Safiyya, har yau ban yanke decision ba, ni ban san me na ke ji game da shi ba, idan ina sonsa ma ba ke za ki fara sani ba, Safiyya tunanina matarsa taya zata yarda ta zauna da kishiya? Kishiyar ma bahaushiya, bayan naji ana cewa matan Ƙabila mugwaye ne, tarwatsa aure suke yi basa yarda su zauna da kishiya, kuma babu abunda suka iya sai mugun asiri da makirci, a hakan to kike so na aure shi? Ke da kike sona ya kike neman jefa mi cikin rana, me zan yi da auren ƙabila fisabilillahi, kuma ƙabilan ma me mata, Shikenan sai na ƙare a aure ina fitowa ina faman yawon zawarci".
Ina yin shiru tace,"Madallah Na gode Sa'ida, na gode sosai da ci min fuska, ba laifinki ba ne laifina ne da na nace miki, kuma na ɗauke ki ƴar uwa har na ke so ki shigo cikinmu, to Alhamdulillahi duk da muke ƙabilar mu tamu zuciyar a wanke take fesss, ba ma nufar kowa da sharri balle mugunta sai alkhairi, kuma ita kanta Anty Kudrat ɗin da kike ma mummunan zato kin ɗauka hakkinta wallahi, kuma kar ki damu Brother Salim ne bai da matsala zan sanar masa da duk abinda kika faɗa, muma ai da zuciya a ƙirjinmu inda ake son mu nan muke zuwa, saduwar alkhairi...".
Ƙit ta kashe wayanta, ni gaba ɗaya ma ban san nayi wancan katoɓaran zancen ba sai yanzu, na yi ta bin bayan kiranta taƙi ɗagawa. Haka dai na samu na tura mata saƙon ban haƙuri da shaida mata ba yanda ta zata ba na ke nufi. Maman Yasmin ta shigo ta sameni tana ce min za su tafi, yanayina yasa ta zauna tana tambayana meke faruwa, ni da ya kamata a ganni farin ciki kuma sai a ganni a akasin hakan.
Ganin idan nayi shiru zan cuci kaina nace mata,"Maman Yasmin ni fa bana da buƙatar na sake yin aure, nafi so inyi zamana a haka, zaman gidan iyayena yafi min daɗi da kwanciyar hankali, in je aikina na dawo nayi sana'ata na fi farin ciki da hakan".
Sai ta numfasa tana dafa kafaɗana da cewa,"Sa'ida ya kamata ace kin mance baya kin fuskanci gaba, ke ba ki ga sauyin da Allah yay miki ba ne? Kin taɓa tsammanin za ki taka wannan matakin ne? Ba fa iyayenki da na ki ba kawai hatta wasu mora suke daga jikinki, to ko wannan ba ya isa ki kyautatawa sabuwar rayuwar auren da za kiyi zato me kyau ba, kuma ki kalla fa wanda Allah ya aiko miki, wallahi Abbaan Yasmin ce yay da Abbaa ya tura su bincike kar kiji yabo da kyakykyawan shaidar da ake yi masa".
Sai tayi shiru kafin ta sake cewa,"Kuma fa bacin haka kefa macece me lafiya, ina za ki iya riƙe kanki? Dole kina da buƙatar abokin rayuwa, wallahi wallahi zaman aure shi yakamace ki shine mutuncinki da ƙimarki da darajarki".
Na goge hawaye na ce,"Na sani Maman Yasmin to amma ni ina gudun matsalolin rayuwar ne, kar lamura su zo su taɓarɓare min kamar wancan, kinga har faɗa masa nayi ina da matsalar rashin haihuwa amma bai ɗauki zancen nawa da muhimmanci ba".
"Kinga yanzu dai magana duka ta ƙare, ba ki ɓoye masa komai ba kin sanar da shi kin fita hakkinsa, kuma magana ma har ta kai ga an saka rana, don haka kawai ki durfafi adu'a ki faɗawa Allah".
Haka dai tayi ta ban shawara tare da kwantar min da hankali sannan daga bisani ta tashi suka tafi don Yashaik nata aikowa akan ta zo ta ba shi maƙulli idan anan zata kwana.
Bayan fitarta naji ƙwala kiran Abbaa, na miƙe da azama na sanya hijabina na fita zuwa ɗakinsa, na sameshi ya gama cin abinci suna zaune suna magana shi da Ummani, daga gefe da su na zauna nayi masa sannu da zuwa, ya amsa yana kai hannu ya rage volume ɗin rediyon da yake ji.
Ƙirjina sai bugawa yake yi kamar wadda ke jiran zartar da hukuncin laifin da ta aikata. Abbaa ya kalle ni yana cewa,"Kun yi magana da Babarki?".
Na ce,"Tace min dai sai ka dawo".
Ya jinjina kai kafin ya ce,"Ɗazu iyayen yaron can da ke neman aurenki sun zo, sun kawo kuɗin aurenki da na kayan sa rana da kuma kuɗin lefe wanda haka suke yi a al'adarsu, sun bada miliyan ɗaya da rabi na kuɗin kayan lefe, dubu ɗari biyar kuma kuɗin kayan sa rana da kuɗin aure, gaba ɗaya dai miliyan biyu suka bayar, to na so ma su rage don ba yanda ban yi da su ba suka ce a'a hakan za su bayar, to ga kuɗi nan dai na karɓa, sun kuma yi batun wata guda nace musu a'a muna buƙatar lokaci duba da yanayinmu, to kuma ɗazu Kakanku sai yace wata guda ɗin yayi, nama kira su na sanar musu".
Duk sai naji jikina yay sanyi, da gaske Aure zan ƙara yi bayan alwashin da na sha na ni da aure har mutuwa, yanda na ke jina kamar dai ba ni ba, A hankali ruwan hawaye na kawowa idona nace,"Tom Abbaa Allah ya kaimu".
"Kun yi magana da shi Salim ɗin?". Ina girgiza kai nace,"A'a". "To yanda ku ka yi sai ki faɗa min amma kar ya wuce zuwa gobe, ga kuɗinki nan zan bawa mahaifiyarki amana bana so a ci musu ko ƙwandala, yanda suka bayar da sunan abinda suka ce haka na ke so ayi amfani da shi, Allah ba zai hana yanda za'ai ayi miki sauran buƙatu ba, sai kuje wajen Saleh kafinta ki duba kayan ɗakin da kike so".
Nace,"Tom Abbaa".
Da haka na miƙe nayi musu sai da safe na wuce ɗaki. Ni dai tun bayan dawowana daga wurin Abbaa kuka na ke yi sosai tamkar wadda aka yiwa mutuwa ko wani abun alhini ya sameta, har Ummani ta shigo ta kore min sauro ta ɗauka abu a firij ta fita ban ɗago ba haka ina ji taja ƙofa ta rufe tana faɗin,"Idan kin gama aikin wahalar sai ki tashi ki saka sakata, ba kya son nasa kika ja baki kika yi shiru saboda gulma, yanzu da kika je ai da sai ki faɗa masa, kina neman ƙaryata kanki akan gaskiya, ni dai Allah ya bamu alkhairi".
Ai kamar ta tunzura ni fa sai kuka, ni fa bana son Salim, kuma bana ganin laifina don naƙi aure, haka kowa ma kar yaga laifina, auren nan na yi banji daɗi ba, na shekara goma har da ƴan kai amma jin daɗi da farin cikin da na tsinta a cikinsa ba za su wuce ƙirgen yatsu ba, nayi bautan aure gwargwadon iko, na kasance irin macen da ake kwaɗayi da fatan samu a gidan aure, amma sai zaman auren nawa ya kasance da wulaƙanci da tozarci, to tsakani da Allah ta ya zan sake sha'awar komawa duniyarsa? Wallah ko da naji cewar ina so ko saboda mahaifiyata da naga ta damu, idan na tuna batun haihuwa duk sai in ji inaaa ta ina zan soma? Ba zan iya ba, wahalar da na sha a baya ma ta isa, ina ni ina kuma auren me kuɗi su ci mutuncina shi da danginsa, balle ma me mata har da ƴaƴa.
Ban gaji da kuka ba har ƙarfe daya, in kukan in saƙe saƙe da babu warwara, a lokacin ne kuma na miƙe na fita na yo alwala na dawo na kulle ɗakin, tun a wancan ranar sai a yau Allah ya nufa zan yi sallar istikara, bayan na idar na jima hannuna sama ina hawaye ina roƙon Allah akan ya shiga lamarin auren nan, idan alkhairi ne ya tabbatar idan babu alkhairi ya kawo sassauƙar hanyar da za'a fasa shi ba tare da anyi nisa ba.
Haka na raya daren da sallah da karatun ƙur'ani tare da tarin adu'oi, bayan nayi sallar asuba ne kuma bacci me daɗi ya zo min, Allah ya so ba morning duty gare ni ba evening ne da ban san ya zanyi da tarin baccin da na ɗauka ba. Cikin bacci naji ƙarar wayata, a firgice na buɗe ido ina saurin miƙewa zaune tare da kai hannu na rarumota. Na maida kai na kwanta a sa'ilin da kiran ke yankewa, kuma ina lumshe ido da zummar komawa kiran ya daɗa shigowa nayi azamar ɗauka na kai kunne.