Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 29
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 29: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 29. Da kasalalliyar muryana na masu bacci na sauke numfashi tare da…
4,426 words
Da kasalalliyar muryana na masu bacci na sauke numfashi tare da yin sallama. Daga can ɓangaren ma naji an sauke numfashi kafin a amsa sallamar. "Na katse miki bacci, bari na ƙyale ki idan kin tashi ki kira ni". Kamar a mafarki haka naji muryan nasa cikin turancinsa me daɗi, kuma tuni na buɗe ido ina saurin dakatar da shi da cewa,"Ai na tashi ma, kai ne?".
"A'a Sa'ida ne". Murmushi ya suɓuce min me sauti, haka kawai sai naji kamar daɗi na ratsa ni. Ina miƙa nace,"Ina kwana". "Ba zan amsa ba". "Saboda me?" "Ba ki san kin yi laifi ba kenan?". "Ni ban yi laifi ba, wa nayi wa?". "No shikenan ai, ban bin baya ni gaba na ke tunkara".
Kawai sai na tsinci bakina da faɗin,"Kayi haƙuri". Yay shiru na sake cewa,"Kayi haƙuri don Allah".
Sai yace,"Ya isa haka, zan zo gida anjima". Zuciyata naji ta motsa, sai nayi shiru bance komai ba. "Ba kiji ba ne".
"Zan fita aiki ne by 3". "Tom shikenan ki shirya sai na zo na kai ki". "Kaii ai Abbaa ba zai bari ba". "Zai bari, zan faɗa masa".
Na ƙarasa buɗe idanu babu shiri nace,"Kace masa me?". "Zan kai matata wurin aiki".
Murmushi kawai nayi ban ce komai ba. Ya sake cewa,"Kin yi break fast?".
"A'a yanzun ai ka tashe ni". "Har eleven kina bacci, kin kwana kina kuka ko?".
Sai nayi ƙasa da murya da shagwaɓewa nace,"To ai kai ne baka yi shawara da ni ba". "Ai nayi shawara da zuciyarki shiyasa". Ya sauke numfashi kana ya ƙara cewa,"Ki tashi ki ci abinci haka, bana son zama da yunwa".
Da haka muka yi sallama, ji nayi ina ma bai kashe wayan ba, sai dai yanda na jisa ɗin kaman da damuwa a tare da shi. Har zan koma baccin sai na tuna maganarsa, haka na miƙe ba yanda na iya na buɗe ƙofa, brush da macline na ɗauka na fita, haka na shiga banɗaki sai aikin murmushi na ke yi ni ɗaya ko me yasa oho, ina dai neman zama kamar wata zararra.
Sanda na shiga ɗakin Ummani ne na ga da gaske ashe ƙarfe sha ɗaya, nayi mamaki sosai yauhe rabona da bacci irin haka, na kama yiwa Ummani ƙorafin rashin tashina tace,"Kaman zan karya ƙofan haka na dinƙa bugu, kina can sheme kamar sumamma ba ki san me ake ba".
Nayi dariya ina cewa,"Yo ina na sani ma ni, wallahi banji ba ko kaɗan. Yanzu yau haka Abbaa ya fita ban gaida shi ba".
Tace,"Yo shi ai tsoroma kika ba shi, sai da ya leƙa ta taga yaga kin jiya kwanciya hankalinsa ya kwanta".
"Allah sarki Abbaana, bara na kira shi a waya". Na faɗa ina fita a ɗakin, wayata na ɗakko sai da na shiga kitchen na ɗauko abin kari kunu da awara tukunna na dawo na samu Ummani. Ina shan kunun ina jin idon Ummani akaina wanda na san tana kallona saboda nishaɗin da ta ganni a ciki, ni kaina na rasa dalilin murmushina da kasa ɓoye shi.
"Ɗazu na ke gayawa Abbaanki kan zancen ba ki son auren nan, yace zai kira iyayen yaran ya faɗa musu zu so su karɓi kuɗinsu...".
Ai bata ƙarasa na tsinci kaina da saurin bakin ce mata. "Ummani nayi istikara jiya".
"Au tuntuni ke da ba ki nemi zaɓin Allahn ba". Kaina ƙasa na ce,"Ni dai yau ɗin naji zuciyata ta samu natsuwa da lamarin, kuma ma har naji kamar ina sonsa, ɗazu ya kira waya yace anjima zai zo ya kai ni wurin aiki, nace masa Abbaa ba zai bari ba yace zai faɗawa Abbaan, kuma Ummani sai ya iya faɗa masa ɗin ko?".
Na ƙarashe zancen ina ɗagowa na dubeta, murmushi naga tana yi wanda yasa naji kunya. Bata ce min komai ba sai na sunkwi da kai ƙasa ina bata labarin ma yanda na yiwa Safiyya jiya, sai ta bani wayarta tace na kirata da ita ai ba zata ƙi ɗaga tata ba, ina ƙoƙarin kiran wayata tayi ƙara, ban san lambar don sai da na jinkirta kafin na ɗaga, ina ɗagawan naji muryansa na cewa,"Kin ci abincin?".
Kasancewar Ummani a wurin sai na kasa yin magana, na yunƙura zan tashi tace,"Yi zamanki".
A hankali nace masa,"Ina ci ne yanzu". Sai ya marairaice da cewan,"Ki aje min nawa idan na zo za ki bani da hannunki". Sai ya sake cewa,"Na faɗawa Abbaa yace babu matsala, amma ni da ke duk muji tsoron Allah, idan su basa ganinmu Allah na ganinmu".
Nayi shiru ya katse ni. "Baby yanzu ni da ke sai mu iya aikata wani abun mara kyau? Me ma muka sani to? Ko ke kin sani?".
Na cije harshe ina cewa,"Sai ka zo ɗin dai". Na faɗa ina saurin kashe wayar. [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR09FT5* Maman Khairi da Maman Yasmin haka suka miƙe tsaye wajen gyara ni ciki da waje, kayan mata kamar hauka Maman Yasmin tasa na tura uban kuɗi aka yo aike tun daga niger, ga Safiyya ma da nata tasa aka kawo min daga sokoto, sam ba'a son raina na ke amfani da magungunan ba, haka na ke shansu a dole wani da daɗi wani ba daɗi, wani ma sai na kusa amai ma na ke iya sha, haka zan ta yiwa Safiyya ƙorafi Maman Yasmin ma na yita mata nurƙufanci, don ni a nawa ganin wannan abubuwan duk ba su da amfani duba da irin rayuwan da nayi a baya, amfanin da na dinƙi yi da su a banza.
Safiyya ce ma me cewa ai yanzu zan san amfaninsu tunda sai yanzu ne zan yi auren, in daina lissafin wancan buhun a sahun maza, in bari in zan maganar ƴan iska mahaukata sai na ke sako shi a ciki, amma na bar tuna na taɓa aure a baya tunda dai ban haifa na baro ba.
Da Safiyya muke ta shige da ficen abubuwan da na ke siya ta ɓangarena, itama haka ta tura min 100k ta account a matsayin gudunmawa, naji daɗi sosai da kuɗin na bawa Yaya Imam nace ya siyo buhun shinkafa da fulawa sai ya bawa Abbaa. Shima yay ta min godiya har da ƙwallata don ce masa nayi sirri ne tsakanina da shi. Na siya shadda nayi mana anko iri ɗaya ni da Ummani da Abbaa, sannan na siya wani kalan daban na ɗinkawa yayyuna da matansu da ƴanƴansu har da budurwan Yaya Al'amin ma, shigar da na ke so muyi ranar ɗaurin aure kenan, Uwata kuwa kayanta sunan sai ana gobe ɗaurin aure zan ɗakko in bata, don so na ke farin cikin saman fuskarta ya ninku sau dubun dubata, danƙararen less ne na siya mata guda biyu mai shegen tsada kuma nasa aka yi mata ɗinki na zamani, atamfofi biyu kowanne da shigar takalmi da mayafinsa, Abbaa nah ba da kala ɗaya na barsa ba bayan shaddar ɗaurin aure har da set biyu na yi masa na boyel.
Salim ya tura min dubu hamsin na kuɗin gyaran jiki da lalle da kitso, ranar kuwa Safiyya ta dinƙa masifa wai yaushe Brother ya koyi tsumulmula basu sani ba, zata kira shi na hanata sai ta kira Ummansu ta faɗa mata, Umman nasu ma ta kama faɗa wai ko bai da shi ai ba ya bani 50k a matsayin kuɗin gyaran jiki ba balle kuma yana da shi, itama tace zata kira shi taci mutuncinsa nayi ta roƙonta da ƙyar ta haƙura ta ƙyale, ko kusa bana sawa Salim ido musamman akan kuɗinsa, ni yanda yake nuna min bai da wani kuɗi, ko hira muke yi zai ce in koyi haƙurin zama da shi a yanda yake, shi ba mai kuɗi ba ne amma insha Allahu zai yi ƙoƙarin ganin ban nemi wani abu daga gare shi na rasa ba, ba zan yi kukan babu ba in Allah ya yarda, saɓanin yacca na san labarin kuɗinsa a wurin Safiyya, to nima dai a haka na ke binsa dama ni abun hannun namiji ba damuna yay ba, har ce yay min motan da yake zuwa da shi ma na ogansa ne, wannan dai na jisa ne kawai ban wani yarda ba, kawai dai na san kyauta a soyayya da daɗi musamman ma a wurin wanda zaka aura, to ni zan iya cewa bai taɓa kawo min wani abu da sunan kyauta ba, kuma ko da na faɗawa Ummani ma ce tayi kar in sa hakan a raina, ƙila tsarinsa ne a haka sai na shiga cikin gidansa tukunna zai buɗe min aljihunsa, kuma gwara ma hakan akan ya buɗa min a waje sai na shiga daga ciki kuma ya matse kayansa, idan kuwa na nuna masa ban damu ba babu ƙorafi babu tambaye tambamye balle sa ido sai nafi kima a idonsa, shi kansa sai yafi jin daɗin yi min, balle ma mene na damun kai tunda ina aikina ina samu sosai kuma ga kasuwancin da na ke na kawo min kuɗi.
Yau dai ƴan uwa sun ƙara cika gidanmu, Hajiya Ummani an kasa zaune an kasa tsaye, ayi can ayi nan, gidan ya kacame da hayaniya, ni da ban son hayaniya duk sai kaina ya ɗauka yay nauyi, na ƙagu ma ayi a gama taron a watse, du da ina ta faman mita akan me ma za'a tsaya yin wani taro aure ba auren budurwa ba, Maman Yasmin ta danno min zagi tace in ci gaba da maida kaina baya hakan yana da kyau ai. Yau tun asuba da na tashi kasa komawa bacci nayi, Maman Khairi ma da ta ganni da duku dukun Safiya a gidan Maman Yasmin sai ta kama tsokanata wai ta lura na zaƙu dai a ɗaura auren nan, yau ni ce babu baccin asuba. Nayi dariya kawai na shige ciki ni bata san me nake wa ba, ai kuwa na sha tsiya a wurin su Adama da duk mutanenmu dai na ƙauye da suke kwana gidan Maman Yasmin, ni da naje na ƙarasa haɗa kayayyakina takurawarsu ta hana ni sai baro gidan nayi na dawo gidanmu.
Ɗakin Kaka na shiga inda anan aka ajiye akwatunan lefena da aka haɗa guda sha biyu, ɗauke da kaya masu tsada da kaya na alfarma, da aka kawo su ni dai sai dana tofe abuna da adu'oi saboda baki, kaya kamar ɗiyan wata ƙusar, ko shi da na ɗauka hoto na tura masa sai da yace mun fitar da shi kunya, da shi aka ce ya haɗa ba zai haɗa masu kyan haka ba, har da ce min yanzu da su Granny ba su yi karo karo an haɗa masa ya kawo wannan kuɗin ba ya zai yi? Ni kuwa na ce ummm shine yay ƙwafa wai in koka da ranar haɗuwarmu.
Akwatun da ke ɗauke da abayoyi na buɗa na ɗauko guda ɗaya, pink colour tasha ado, na ɗakko agogo da yari ma har da sabon takalmi. Umman Batula ta ƙwala min kira na fita da sauri ina ɓoye kayana cikin hijabina kar a gani a ishe ni da mita, ni kuwa yau ban ga me hanani cakarewa da kwalliya ba.
"Kije ga ruwan can na kai miki banɗaki, akwai wani daban cikin koriyar robar nan ki zauna a ciki sai ya huce sai ki fito". To kawai nace mata na wuce ina ƙunƙuni, wai ba za'a kiraka gefe a faɗa maka abu a sirrance ba sai an gama yayataka a bainar nasi kowa yaji me zaka yi. Shiyasa tunda ta zo da naji kiranta ina fitowa na ke faɗawa banɗaki, sai ta ƙara wani ince gani ciki.
Kamar dai wata zautacciya haka nayi wankan nan na fito sai aikin imagination na ke ina ta murmushi, yau ɗin dai kana ganina kasan cikin farin ciki na ke sosai, kamar ma ranar ɗaurin auren, annurin fuskata sam yaƙi ɗaukewa duk murnar zuwan Salim ne, kwanana tara kenan ban gansa ba, na riga na saba duk kwana uku yake zuwa, waya ma bama samun damar yi sosai, idan ya tasheni da safe sai zan kwanta zai ƙara kira, nan ma ba zamu jima ba 2-3mints ne zai ce naje na kwanta yana cikin aiki ne.
Sun je taro ne can garin Ekiti, suna tare da shugaban ƙasa sun masa rakiya, kuma a can ɗin suna tattaunawa ne akan matsalar tsaro na ƙasar nan, to duk basu da wani isashshen lokaci, a hakan ma yau ɗin sato hanya zai yi ya taho, yace shima ya gaji da missing ɗina, ƙwayar idonsa kullum zafin rashin ganina take yi, kuma idan yay kuka duk bai da me lallashinsa. Ina zancen zuci sai ga kiransa ya shigo, naji ƙirjina yay duka, wani sanyayyan abu ya ratsa jikina, da azarɓaɓina kuwa na ɗaga.
"Myyyy". Ya kira sunan da wani irin salo da ya saukar min da kasala. Na lumshe ido kana na amsa,"Na'am Salim". Sautin murmushinsa ya fito, yayi yayi na canja masa suna nace ni haka zan ke faɗi, da haka kuma sai ya koma cewa nafi kowa iya faɗin sunan, kamar ni na raɗa yafi daɗi a bakina.
"My mun dawo fa, gani a ƙofar gida". Basarwa nayi irin ban damun nan ba na ce,"Ah dama yau zaku dawo, amma kun yi sauri, ai ce na ke sai kun yi good one month".
Na tabbata sai da ya tsotsi leɓensa kafin yace da ni,"My abu ɗaya yasa na ke ɗaga miki ƙafa, ni za ki munafurta ki nuna min ba kiji daɗin dawowana ba, to fito da sauri kafin na kasa jurewa na shigo gidan da kaina".
Idona a waje na ce,"Kuma sai ka iya?". "Kina mamaki? Ki ƙara five minutes kika ga ni sai dai ki tsince ni ina tsallake mutane, kuma a gaban kowa zan kamo hannunki na fito da ke".
Dariya nayi sosai nace,"Yi haƙuri Sojansu kar ka bani kunya".
Aje wayan nayi na leƙa na ƙwalawa Yasmin kira na ce taje ta buɗe masa ɗakin Yaya Al'amin. Na dawo daga ciki na shiga shiryawa, kamar wanda zata je gasar kyau, ba fa wani makeup na tsaya yi ba, powder kawai da kwalli sai lip bam shikenan amma kamar a sace ni a gudu, ni kaina ba ƙaramin kyau na yiwa kaina ba. Na fito ina wani takun ɗaiɗai, na leƙa ɗakin Ummani bata nan na bita ɓangaren Ummansu Hindatu, wanda bai sonka dai har a bada ba zai so ka ba, tunda aka fara hidiman bikin nan ƙala Umma bata ce da mu ba, kamar ma bata san da za'ai biki a gidan ba, ranar da aka buɗe lefe ma Sha'awanatu ƴarta ce kawai ta zo taga kayan, amma har yau Allah sanya alkhairi bata ce da Ummani ba, ni kuwa idan taga gimlawata sai da ta harare ni, nima kuwa na koyi shareta ko gaida ita bana yi, me zaka yi da mutumin da bai gamin mahaifiyarka da mutunci.
"Ummani zan tafi". Suna awon masarar da za'a kai niƙa ayi tuwon dare na yau saboda baƙi, ta ɗago tana kallona tace,"Kika ce kin ɗau hutu".
Umman su Hindatu tace,"A'a ƴata irin wannan kyau haka, ko dai sirikin nawa ne ya zo".
Nayi murmushi ina cewa da Ummani,"Bana faɗa miki zan je karɓo sauran ɗinkuna ba".
"Ohh haka ne, to ke da wa zaku tafi? Ko ta gidan Safiyya za ki biya".
Na ɗan yi ƙasa da kaina ina sosa gira cike da kunya na ce,"Salim ya zo shi zai kai ni".
Ta ɗan shiru kafin tace,"To sai kun dawo Allah ya kiyaye ya tsare hanya, kinga idan ki samu dama ki biya asibitin ki duba ƴar gidan Baaba mai ƙosai".
"Ai kuwa gwara da kika tuna mini, wallahi na manta kuma fa ko jiya sai da ta kira ni tace ko da nurse ɗin da zan taimaka na haɗa su".
"To inda hali sai ki ƙoƙarta musu, yarinyar naji ance sai an ƙara yi mata wankin ƙunar".
Ina jinjina kai da tausayawa nace,"Allah sarki, Allah ya bata lafiya. Bari na tafi".
"To sai kun dawo Allah ya tsare, a kula don Allah Sa'ida". Ni wai sai kace wata ƙaramar yarinya, indai zan je wurin Salim ko zance zai ne Ummani ta dinƙa a kula a kula, balle kuma idan na ce zamu fita tare ai sai an ja kusan rabin awa ana min wa'azi da nasiha, yau ɗin ma don tana cikin hidiman aiki ne da tana nan tana min nasihar yau da kullum, ni duk idan tana haka sai nayi ta tsarguwa ina cewa ko bata yarda da ni ba ne.
Umman su Hindatu tace,"Ƴar uwar taki dai sai gobe zata samu shigowa".
"Ai ki rabu da ni da ita Umma, duk rashin mutuncin da zan mata kar kusa baki".
Suna dariya duk ɗin su na wuce Umma na faɗin mun fi kusa, a tsakar gidanmu su Gwaggo Talatu na ta faman yabon kyan da nayi, wata Kakarmu ta ɓangaren su Ummani na zolayata da cewa ko dai gasar kyau zan tafi, wata ƙawar Ummani kuwa na faɗin gaskiya wadda tayi min gyaran jiki tayi mugun iyawa, fatata sai sheƙi take yi na zama kamar ƙwanduwar ƙwai, ko da madara da kankana ake wanke ni kullum ai sai haka, ga ƙamshi na tashin hankali tun daga nesa, su Juwairiyya gulmammu na tsokanata wai ai nan dai da jibi ne in kwantar da hankalina sunga ina ta rawan ƙafa, dama tunda suka ga mota a waje suka san shine ya zo, Mubaraka na bada labari wai ya zo da kakin soja ya fito duk ya tsorata ƴan unguwa, yara har da masu gudu.
Zuwana soro ƙamshin turarensa ya dakeni na lumshe ido, har ga Allah ƙamshin nan shi ne ke rikitani na kasa sarrafa kaina a duk sanda na ke tare da shi. Ina tsaye Maman Khairi ta zo wucewa zasu kai buhun fulawa gidan da za'ai kayan gara, ta mintsine ni da cewa kar dai in kai kaina in yi haƙuri in bari su kaini, kunya ta rufe ni nayi saurin rufe fuska ina saurin shigewa ɗakin Yaya Al'amin. Yana zaune gefen katifar Yaya Al'amin, dama ya saba duk sanda ya zo anan yake zama, na ce me yasa bai son zama kan kujeran, sai ce yay gwara ya ke zama kan abu me taushi da ɗumi kar sanyi ya shige shi in zo ina cika shi da mita a shimfiɗa, haka ya saki baki yana ta zuba maganganun da suka sa har ya tafi ban ƙara kallonsa ba saboda mugun kunya, mamaki ya bani sosai sam ban san haka yake ba, hmmm dama namiji ka gansa kawai sai in bai samu wuri ba, duk da na san komai amma haka yasa naji kalaman suna neman su fi ƙarfin kaina.
Ni dai ko da na shiga sai na kasa motsi, na maƙale a wuri ɗaya shauƙin ganinsa duk ya game min ilahirin tsoka da jinin jikina, har wani abu na ke ji yana tsikarina a yatsan ƙafa, ƙafafuwana suka yi bala'in sanyi saboda kallon da ya kafe ni da shi wanda ke neman kassara gaɓɓaina gaba ɗaya, ya lumshe ido yana sauke wani wawiyan ajiyan zuciya da yasa na ɗago babu shiri na ƙura masa ido.
Yau ne ranar farko da na gansa cikin shigar uniform complete, ashe haka kayan suke masa bala'in kyau, har ga Allah sai da naji ina ma ya zama halalina in ƙarasa gare shi da sauri in rungume shi cikin shauƙin soyayyarsa da ƙaunarsa, ai ko kamar ya san me ke raina sai gani nayi ya buɗen hannaye wai in zo in hugging nasa, ina murmushi na maƙe kafaɗa ina a'a.
Abin dariya kuma sai ya kama buga ƙafa a ƙasa sai kace yaro, na ware ido ina cewa,"Kayii". Sai kuwa ce yay,"Ai yaronki ne ni, nan gaba kaɗan ma breast feeding ɗina za ki ke yi". Ya faɗin hakan yana kashe min ido guda, nace,"Ban hanaka ba irin wannan maganan ba".
Tasowa yay ya zo gaba daf da ni ya tsaya, nayi saurin sunkwi da kaina ƙasa ina wasa da yatsun hannuna, idan na gansa gabana irin haka daf daf duk sai na nemi na ruɗe in kasa fassara irin yanda na ke ji a tare da ni. Ban ankara ba naji hannunsa cikin nawa, da sauri na nemi na zare ya hana hakan, nima kuma sai na tsinci kaina da hana ƙwacewar, sai dai murya can ƙasan maƙoshi nace da shi,"Kasan fa babu kyau, idan kayi haƙuri kwanaki kaɗan suka rage".
Bagarar da maganar tawa yayi da cewa,"Baby ina kika je aka sauya min ke haka? Kinga kyan da kika yi kuwa, ga rigar tayi fitting ɗinki, Baby faɗa min sirrin me kika samu da a kwana tara kika ƙara fidda shape".
Sai yay shiru yana cewa,"In faɗi wani abu?". Sai na masa wani kallo don idan yayi irin wannan muryan na tabbata zai min katoɓara ne, ile kuwa sai ce yay,"Naga twins ɗina ma sun ƙara cika, ko wani abu kika sa suka ɗago don ni dai ba a haka na tafi na bar su ba".
Dukan wasa na kai masa yay saurin ja da baya yana dariya, ya tsare ni da tambayan lallai alalla sai na faɗa masa me na sha na daɗa cika gaba da baya, ƙwayar idona ma har haske ta ƙara yi. Ban iya cewa da shi komai ba kamar yanda na kasa wani ƙwaƙwkwaran motsi dalilin yanda na ke jin yana kewaya babban yatsansa akan tafin hannuna, sai naji ina neman fita a hayyacina na haɗiye yawu ina rumtse ido.
Na ƙware wajen buɗe baki nace masa,"Salim ka bari".
Ai ban ida rufe baki ba ya sauke min mintsine a weast ɗina. "Ya sunana?". Dariya na ƙyalƙyale da ita dalilin cakulkulin da ya sakar min, na manne jikin bango ina cewa,"Salim sunanka". Ganin yana neman yi min rumfa na rumtse ido da kyau ina marairaice murya da cewa,"Kayi haƙuri ba sunanka haka ba, sunanka Lieutenant Onochie, kuma fa kaga kar wani ya zo wucewa".
"Ina ruwana ke za ki ji kunya ai, ni dama a ƙage na ke a bani abata na tafi, dama hotel ɗin da muka sauka idan za ki kwana kina ihu babu me kawo miki agaji". [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR06FT5* Agogo ya kaɗa ƙarfe biyu, na miƙe ina tattara takardu na saka cikin file ɗin da ke aje kan ɗan ƙaramin table ɗin cikin nursing station ɗin namu. Na saka wayata cikin aljihun rigata na uniform tare da cire after dress ɗin da ke jikina na saƙale ta jikin hanger, in ka dubeni gwanin ban sha'awa, kayan na mini kyau tun balle da kullum na ke wani ƙara yin fresh da ni, wanda bai sanni ba ma sai yace ƴar Daddy ce, hankali da natsuwa sun wadatu babu wata makusa a tare da ni, a ganni a kushe sai maƙiyi, don ko daga aiki na dawo da uniform ban ɗora hijabi ko after dress akai ba, ƴan anguwa an dinƙi bina da kallo kenan me cike da burgewa, masu gulma suyi masu adu'a su yi, to surutun ma bai damuna tunda dai ina da iyaye a raye nima kuma ban yar da adu'a ba.
Na isa gaban firij na buɗe na ɗakko allurai a ciki. Ina jin Sister Maryam na faɗin,"Wai ni na rasa irin Sister Sa'ida, ki ta gume baki ba za kike magana ba, daga murmushi sai uhmm da ummm haba kamar kina jin haushin zama cikin mu, in haka ne to ayi maki office ɗinki mana don naga kina da ƙafa a asibitin".
Na waigo ina murmushi da cewa,"Allah ba don ko wulaƙanci ba ki daina faɗin haka Sister Maryam, ni kawai magana ce bata dame ni ba, kinga ko zaman nan da muke ku yi ta hira ana hayaniya wallahi hawar min kai take yi, kowa kin san da yanda nature ɗinsa yake, ni na kasa sabawa surutu har yanzu ko a gidanmu haka na ke".
Ta taɓe baki tana cewa,"Tab ai kuwa dai to ba hali ba ne wannan ɗabi'ar girman kai ce, ka yi magana kace zaka faɗi gaskiya ne aji haushinka".
Ban ƙara tankawa maganarta ba, gudun kar mu zo muyi rigima, rigima ba halina ba ce, haka Ummani ma tana cewa da ni kar na taɓa biyewa kowa muyi rigima. To ni ban san dalilin da yasa take jin haushina ba, har ga Allah ta takura min, babu siɗi ba saɗaɗa ta ke ƴar tsama da ni, amma ina ga don ina kama kaina ne ban shiga sabgar kowa, ba zaka ji ana gulmace gulmace ko munafurcin wani da ni ba, hira ma idan ana yi jefi jefi zaka ji na saka baki, ko kuma don fifita yabona da Dr yake yawan yi akansu ne oho, da su kansu mutane idan suka zo asibitin, haka ko a cikin ma'aikata asibitin kowa ya tashi kaji yace Sa'ida Sa'ida, ta dai ga Allah yay min ɗaukaka hakan sai ya tsaya mata a rai, don ita ko da yaushe cikin sukana take yi, tayi ta faman habaici akan ina da girman kai tana gaggaya min magana mara daɗi, ko kyauta aka bani a asibitin bata iya ɓoye baƙin cikinta ƙarara take fitowa ta nuna, ni kuwa bana taɓa nuna mata na san ma tana yi, idan tayi wani abun ne Khadija da Maman Nana ke shigar min su caccaketa, sai sun gama da ita su dawo kaina suyi ta zazzaga min masifa akan rashin baki, ya kamata in koyi maida martani idan anyi min, haka kuma in daina barin ko ta kwana, ni dai to kawai na ke ce musu, me zan ce wanda ya wuci hakan? Na riƙe adu'a na riƙi azkar don haka na sha gaban kowanne mutum babu faɗa balle tashin hankali.
Ina ƙara kallon agogon hannuna nace,"Maman Nana bari na je duba waccan patient ɗin".
"Wadda tayi miscarrage ɗin nan?". Nace,"Ehh ita". "Oak tom sai kin dawo".
Na fita a ɗakin cikin hanzari don ko kusa bana son yin latti wajen kula da majinyacin da ke ƙarƙashin kulawata. Na tura ƙofar ɗakin na shiga da sallamata, muka gaisa da patient relatives, suna girmama ni kamar yanda nima na ke girmama su, ga yabona da suke yi wanda har Dr sai da suka faɗawa irin ƙoƙarin da na ke yi akansu, har da cewa na iya mu'amala da mutane, mijin matar kuwa kusan ko da yaushe sai yay min ihsani saboda jin daɗin yanda na ke kula da iyalinsa cikin sauƙin kai.
Wadda ke zaune gefen gadon kusa da mara lafiyar tayi saurin tashi daga wajen, Na aje file ɗin hannuna bisa loka na isa gaban mara lafiyar wanda yay daidai da ƙarewar drip ɗin da ke shiga jikinta. Ta buɗe idanuwa a lokacin tana kallona, na mata murmushi na ce,"Sannu, ya sauƙin jikin?".
A hankali tace,"Da sauƙi, sannu da ɗawainiyarki na gode".
Na amsa da faɗin,"Aikina ne ai, Allah ya ba ki lafiya".